Showing 204001 words to 207000 words out of 381117 words

Chapter 69 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

2591

shiga uku 
Gaba daya ta gama susucewa kamar wadda tayi karamin hauka babu abunda take cewa sai   yaya dan allah ka tashi, ammah bata mutu ba bazata mutu yanxu ba insha allah 

doctor ne ya kira nurses sukada janyo gado aka saka amar akai don yayi passing out gaba daya, amra dake tsaye itama kunnuwanta zun gama jiyo mata abunda doctor fada ga amar a kwance shima kamar babu rai hankalinta ya gama tashi sosai har wani dishi dishi take gani, haka aka gangara da gadon da aka kwantar da amar har zuwa wani daki amra na biye dasu duk ta gama susucewa, har aka kwantar dashi aka mashi allura don ya samu shock ne, amra dai babu abunda take sai maimaita innalillahi a zuciyanta, shikenan ammah ta mutu, innalillahi wa inna ialihi rajiun, kallon amar tayi kawai saita fashe da wani matsanan cin kuka, haka ta duga sintirya agaban gadonshi tana hawaye ga jiri na dibanta, hankalinta y agama tashi don bata san mezai faru dashi ba shima,gabanshi ta karaso ta tsaya tana kuka ta rike hannunshi da kyau   yaya&   tana fadin sunan shi ta sake fashewa da wani matsanancin kukan sosai, ta dauka tsawan minti talatin a kusa dashi har ya soma motsa hannunshi, da sauri ta dago ta kalleshi lokacin harya bude idanunshi da sukayi jaa sosai, zumbur ya miqe ya dafe kirjinshi dake bugu fat fat fat, amra na ganin haka ta soma toshe bakinta ta kalleshi, shi baima kalleta bay a soma juya kanshi yana cewa   no nooo nooo innalillahi wa inna ilaihi rajiun, wannan wani irin mafarki ne haka  ya fada yana confusing kanshi, shuru amra tayi tana kallonshi ta kasa cewa komai har nurse ta shigo don ta duba koya tashi don alluran da akayi mashi relaxing mind takeyi idan mutun ya samu shock, after 30mins kuma zai farka, don haka tana shigowa ta kaarso gabanshi zata duba yanayin bugun zuciyarshi tana karasowa ya daka mata uwar tsawa   don t fucking touch me, get outtttttt!!!  yanda ya fada saida ya razanar da nurse din harda amra, aguje nurse din ta fuce don idanunshi sunyi jaa sosai jijiyoyin wuyanshi duk sun mike, amra dai bata motsa ba dukda ta tsorata sosai baya ji baya gani haka ya sauko da kafafunshi kasan gadon yana kokarin fucewa daga dakin   karya kuke wallahi, ammah na tana raye 
yana miqewa ya fara tangal tangal zai fadi, da sauri amra ta taroshi, nauyinshi ne ya rinjayeta nan take suka fadi gaba dayansu a kasa, da sauri yafusge jikin shi ya juyo da jajayen idanunshi ya kalleta, kafin ya yunkura zai sake tashi, bai kaiga daga kafarba ya sake faduwa kasa,yana ganin haka ya dafe kanshi kawai, amra na kuka matso kusa dashi da kyar ta karaso hannunta na rawa ta fara kokarin dafashi ya daka mata tsawa   leave me alone, ki fitaaaaa 
muryanta na rawa ta dafa   ya& ya 
  ki futa nace, bana son ganinki  ya fada yana sunkuyar da kanshi, idanunshi sunyi jaaa sun tara ruwa, kwata kwata hawaye suqi futa daga idanunshi, abunda yakeji kadai ya fi kuka ciwo, yau ta kasance rana mafi baqanta a cikin rayuwarshi, har lokacin ya kasa believing abunda kunenshi suka jiyo mashi, yana nan zaune ya dunqule hannunshi ya fara bugun tiles din dakin,amra na ganin haka tayi baya tana hawaye ta fara girgiza kanta ta toshe bakinta da hannunta tana, gaba daya ya sauya kamar bashi ba, babu abunda ke shimfide afuskanshi sai pain,he s in so much pain, bugun hannunshi yake akan tiles din yana   noo noo nooo ammah noooo 
Yanda yake bugun nan saida tiles din ya fashe, hannunshi ya soma fidda jini, arazane amra ta karaso gabanshi jikinta na bari fara kokari rike hannunshi nashi, kasa hanashi tayi don kamar ta rike rock har jini ya fara Malala akasan dakin, tana kuka haka ta miqe ta rungumoshi gaba daya zuwa jikinshi ta kankameshi,   yaya dan allah ka bari, zaka jima kanka ciwo 
Baya jinta ma kwata kwata don y adage sai bugun hannunshi yake yana   nooooo ammah na nooooo 
Rukoshi tayi da kyau ta soma karanto mashi addua a kunenshi, tana jin yanda kirjinshi ke bugu kamar zuciyarshi zata futo, har razana saida tayi saidai hakan baisa ta sake shi ba saima dagewa datayi tana mashi addua a kunneshi,ta dauka kusan minti goma tana yi har ya daina bugun hannunshi nashi ya fara sauke ajiyar zuciya,   shikenan, ammah kin tafi abu ya tafi,kun barni ni kadai, innalillahi wa inna ilaihi rajiun,  ya fada yana kankame amra sosai, kwata kwata ya kasa fidda hawayen dake cikin idanunshi, zuciyarshi is so tough, when it comes to ammah hes so weak, itace weakness dinshi, lokaci guda yaji kamar an toshe mashi farin cikin rayuwarsa gaba daya.
Yanda yake maganganu ba karamin karya zuciyar amra yayi ba,fadin irin tausayinsa da take ji a lokacin ma bata lokaci ne, she can feel his pain don ta shiga irin yanayi daya shiga lokacin da nasu iyayen suka mutu, tana kuka shabe shabe ta soma mashi Magana anatse cikin kunnenshi   yaya, youre not alone, you have us you have me, allah yana tare dakai yaya, dan allah ka sauke hawayen dake cikin idanunka ko zaka samu sauki, 
Gaba daya ya gama sandarewa ya zama kamar dutse, zuciyarshi ta dashe gaba daya ta sauya daga haske zuwa baki.
Suna nan zaune saiga doctor ya shgo dakin& &
[7/11, 11:17 PM] +218 92-2035171: Update
Unedited

Suna karasowa Madina tayi parking gefen da Aman yayi parking motarshi, atare Duk suka fito, amra ba gefen Madina while salima na gefen su itama sai Aman da Salim da sukayi gaba.
Anatse take ta kawa kanta a kasa, Madina ta Lura da yanda tayi sanyi sosai saidai bata tambayeta dalilin hakan ba, anatse suke tafiyar Har suka karaso dakin ammah, Aman ne ya bude kofar Duk suka shigo atare, babu kowa a cikin dakin sai ammah da nurse dake tsaye a gefenta tana goge mata jiki da towel cikin wani warm towel, juyowa nurse din tayi suka gaisa daman ta gama goge ma ammah jiki don haka ta wuce bathroom ta zuba Mr da ruwan ta fuce daga dakin.
Takowa Madina tayi tare da amra gefen ammah suka tsaya, kallonta suka fara yi, babu abunda ya sauya a tattare da ita sai nunfashi da take fitarwa ahanakli, kallon amra Madina tayi tace  Allah ya bata lafiya ya Tashi kafadunta,
Madina ta fada fuskanta na nuni da jimamin da take yi, salima ce ta karaso inda suke tace  Ameen anty Madina mun gode
Amra dai bata ce komai ba tana tsaye ita ma gefen gadon ta kame jikinta, sanye yake da abaya baqa tayi rolling kanta, gaba daya itama she looks pale,suna nan tsaye Aman ya shugo tare da doctor, gaba daya matsawa sukayi daga gaban gadon don su basu waje, Madina ce ta fara gaishesa, bai ma kalli inda take tsaye ba kamar kullum fuskanshi a hade babu fara a ya amsa kafin su salima suma gaishesa, amra dai na daga gefe, don koda ya shigo bata dago kai ta kalleshi ba balle ta gaishesa, gaba daya wani irin haushinsa take ji sosai, don ko muryarshi bata son jin, shima koda ya shigo bai dago ya kalli kowa ba so bai wani damu da wanda ya gaishe shi ba da wanda bai gaishesa ba,

mikewa Aman yayi ya bashi hannu shida doctor sukayi misabaha, kafin doctor ya sake duba jikin ammah, Yan gwaje gwaje yayi kafij ya waigo ya kallesu yace  Masha Allah, tana healing cikin ikon Allah, don yanxu bata buqatan oxygen sabod nunfashinta yayi stabilising,sannan rashin farfadowartaba matsala bane saboda dole daman zata dauka dan lokaci kafin ta farfado sannan alluran da mukayi mata suna dade wa kafin su saki mutun
Yana kaiwa nan ya miqa ma Amar hannu, godiya ya mashi sosai kafin ya fuce daga dakin.

Doctor na fita salima ta kalli Amar daya tsaya bakin gadon ammah ya kafa mata idanu tace  ya Muhammad ga abunci an kawo ko azuba maka
Bai waigo ba cikin kamewa yace  no
Shuru sukayi gaba dayansu babu wanda yace qala Duk suna daga tsaye, kallon amra Aman yayi yace  sister inlaw ku zauna mana bismillah yayi masu nuni da kujeran visitors doguwa inda Salim ne zaune.
Juyowa Madina tayi ta kalleshi kafin ta maida kanta kan amra tace  Ay ni wucewa ma zanyi, amma Zan dawo da daddare Insha Allah
Kallonta amra tayi jiki amace tace  Toh anty Madina muje na rakaki
Tunda amra ta fara magana ya danyi jim ya lumshe idanunshi, bai yi tunanin da ita aka zo ba don bai dago ya kalleta ba, sai alokacin yayi mamaki sosai.
Sallama Madina tayi masu kafun ta nufi hanyar fita amra na biye da ita.
Tun a kan hanyar futa daga reception Madina ta dan tsaya ta kalleta  amra meke damunki? Nayi sensing abu na damunki, now tell me,meysa kika rame haka? Duk jikinki yayi sanyi
Dan dagowa amra tayi tana dan qaqalo murmushi tace  babu komai anty Madina stress ne kawai na yawon asibiti, bayan wannan ma tashin hankalin da muka shiga na rashin lafiyar ammah kadai ma zaisa hakan
Shuru Madina ta sakeyi tana nazari kafin ta dubi wayarta Ganin tana lattin zuwa aiki,  Zan dawo anjima da daddare Insha Allah zamuyi magana,
 Toh anty madina allah ya kaimu amra ta fada tana lumshe idanunta alamun gajiya da tsayuwan da sukayi,  ki koma kawai na hutar dake amaryar general
Dan murmusawa Madina tayi kafin ta wuce parking lot amra kuma ta samu waje anan gefen reception ta zauna ta doka uban tagumi kamar wadda aka aikoma mutuwa, abubuwa da dama suna yawo a kwakwalwarta.

Cikin dakin ammah kuwa, Amar ne ya miqe ya kalli su salima da Aman yace  zan wuce gida yanxu, idan wani abu ya taso call me
Aman ne ya kalleshi yace  okay, zaka wuce da sister inlaw ne?
Hanyar kofa amar yabi kafin yace  no, bazan dade ba Zan dawo
Yana kaiwa nan ya fuce daga dakin ya nufi hanyar reception l, anatse yake tafiya kamar basarake Har ya kusa karasowa Inda take zaune ya doka uban tagumi ta fada duniyar tunani, Har ya kusa giftata ta dago tana shirin miqewa, kallo daya tayi mashi ta kauda kanta gefe, shikam
Bai dauke idanunshi akanta ba haka zalika bai tsaya ba ya wuce abun shi, itama tana Ganin haka ta juya ta nufi hanyarshi dakin ammah jiki a mace, da sallama ta shiga cikin dakin, kallonta Duk sukayi gaba dayansu kafin ta karaso Har cikin dakin ta zauna kan kujera ta dan jingina don gaba daya babu abunda ke mata dadi, Har akayi sallah zuhur Duk sukayi sallah bai dawo ba, Aman da Salim Har suka je masallaci suma suka dawo, suna dawowa salima ta zubama kowa abunci Banda amra wadda tace bata jin yunwa sai zuwa anjima, kallonta salima tayi tace  adda ko breakfast sun kirki fa bakiyi ba dazu? Ko baki jin dadi ne?
Dago da jajayen idanunta tayi don ta sauke kanta kan gwiwanta tana jin wani irin ciwon kai sosai, anatse ya soma magana  kaina ke ciwo zanci anjima
Salima naji haka ta kyale ta ta zauna gefen Aman dake zaune kan carpet ta fara cin abuncin da suka taho dashi din hankali kwance.
Har suka gama salima ta tattara amra bata dago ba kanta akasa.

Bangaren Amar yana komawa gida ya watsa ruwa ya kwanta don idan sunyi switching baya barci haka zai kwana a zaune yana yima ammah addua tare da fatan farfadowarta, sai wajen karfe uku da rabi ya Tashi daga barci, ba karamin dadin barcin yaji ba don wani irin mafarki yayi mai wuyar fasaara,dukda yajin dadin mafarki don Harda amra a ciki hakan bai hanashi tabe baki ba yayi tsaki ya wuce bathroom ya sake wani Sabon wanka kafin ya futo ya shirya cikin branded kananun kaya marasa nauyi, kamshinsa ne ke Tashi ta ko ina harya fuce daga gidan ya kullo kofar.
Yana fitowa wayar asad na shugowa, kallon wayar yayi kamar bazai daga ba, Har ya shiga cikin motar ya fara warming dinta, nan take wani call din ya sake shugowa, saurin daga wayar yayi tare da sallama,daga chan bangaren asad ya amsashi kafun ya soma mashi bayani,  oga mun kama doctor hafiz tun Daren jiya, naso
Na kira na maka bayani tun alokacin sai nayi tunanin hakan bai daceba saboda kana tare da Mara lafiya, jiya wajen karfe sha daya na dare kuka kamashi a nnamdi ezikiwe international airport yana kokarin gudu wa tare da iyalinshi, ayanxu haka yana cikin interrogation room ban fara interrogating dinshi ba na bari saika zo tukunna
Shuru amar yayi yana wani nazari, tabbas ya kamata ace yana tsaye akan Duk wannan interrogation din don he needs to, saidai kuka bayajin zai iya barin ammah a yanxu inhar ba Ganin ta yayi ta farfado ba, ayanxu Duk mintuna da seconds da yake fiddau nunfashi a duniya yanada mugun amfani a wajen shi saboda ya girgiza sosai da abunda suka faru a cikin kwanakin, Nunfasawa yayi kafin ya danyi gyaran murya yace  asad, banida lokacin wannan ayanxu saboda inhar ba Ganin ammah nayi ta farfado ba bazan iya yin komai ba, kayi interrogating dinshi Duk wani abu da kasan zamu buqata, yanxu lokacina nayi dedicating dinshi to mahaifiyata ne, bazan taba samun natsuwar yin wani buncike ko interrogation, but inason Duk wani abu da kasan Zan buqaci sani Ka buncika, bazansake yin sake ba akan family na ba, this should be the last Insha Allahu
 Okay yallabai ba matsala, zanyi kokarin rukesu for now sannan zanyi maka Duk wani buncike,
Godiya amar yayi mashi kafin ya kashe wayar ya yo reversing motarshi ya fuce daga gidan gaba daya.

Tunda ya fara driving ya maida hankalinshi kan hanya, babu abunda ke Tashi a kofar sai karatun Qur an na sudais, anatse yake driving harya iso asibitin, saida ya tsaye a masjid yayi sallahr asr kafin ya wuce cikin asibitin.

Da sallama ya bude kofar dakin, a zazzaune suke gaba dayansu, Aman na zaune kan carpet salima a gefenshi while Salim na zaune gefen gadon ammah, amra kuwa tana kwance akan doguwar kukerar tana barcin wahala anan zaune, kallo daya yayi masu duka ya sauke kanshi ya karaso cikin dakin, gaishesa salima tayi kafin ya tambayi jikin ammah, Aman ne ya amsashi,  doctor yazo dazu ya sake dubata, babu wani changes
Shuru kawai amar yayi ya kafama ammah idanu, yana kallonta, aranshi yana cewa   allah ya Baki lafiya ammah na, y kamata ki Tashi haka ammah na I miss you so so much,can t imagine how I can survive without you,
Saurin runtse idanunshi yayi ya kamo hannunta ya fike gam.
Suna nan zaune kowa jugum Jugum amra ta bude idanunta da sukayi jaa sosai, mikewa tayi zaune daga kwance ta tare da ta kalli bangarenshi ba ta mike tsaye k???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?amar Ana ingizata, tafiya ta somayi harta shige bathroom, dan dagowa yayi ya kalleta yana tunani ko meke damunta, harta fito daga bandake daurw da alwala, ruwan na diga daga fuskanta zuwa wuyanta don ta zame mayafin abayar datayi rolling don ji tayi kamar yana shaketa ta rike shi a hannu, gashinta ya sauko Har kafadunta yayi curly wanda ya karama fuskanta kyau sosai, sai asalin kyawu ta ya fito sosai kamar ba itaba,ta dan rame kadan tayi fayau,
Amar dake zaune ya zuba mata idanu harta fito daga bathroom din ya kasa dauke kanshi akanta,harta zo inda su salima ke zaune, Aman na gefenta Kowannen su da sake sake da yakeyi aranshi, kallonsu amra tayi tace  ya Aman kudan matsa min zanyi sallah
Dan dagowa yayi ya mata kallo daya kafin ya dauke kanshi ya mike  okay sister inlaw
Salima ma Mikewa tayi nan suka dan gwara da goshinsu don kusan a atare suka miqe, saurin kauda kai salima tayi tace  sorry
Shima kallo daya yayi mata ya dauke ki gefe ya koma kujeran ya zauna, salima dai Kyam ta tsaya a gefe bata motsa ba tana tausayin kanta na dakon soyayyar shi, shida takeyima yanxu ya daina bata fuska ma kwata kwata.

Tunda amra ta tsaya gaban Aman yaji kirjinshi nayi wani irin bugu damm, runtse idanunshi yayi lokaci guda ranshi ya gama baci gaba daya sosai dalilin tsayuwar ta gaban Aman babu mayafi, kishi ne karara ke balbalal shi wanda baima san yanayi ba,babu abunda yake fada aranshi sai  bata da hankali ne zata futo daga bathroom kanta a bude, kuma ta tsaya gaban wani kato da ba muharraminta bane
Yanda idanunshi ya karade yayi jaa sosai zaka gane ranshi ya mugun baci sosai, shi kanshi mamakin bacin ran nashi yakeyi saboda yasan dole bayan kishi Akwai so, tabbas yasan he s jealous of her but so kam babu shi, bai taba jin ya sota ba saidai tausayinta ya fada aranshi, but daman Akwai kishi ne babu so? Ya tambayi kanshi,tsaki kawai yayi ya sha mur, juyowa su salima sukayi suka kalleshi Ganin yanda ya hade rai, da yanda yayi tsaki.
Amra dai bata ma san yana yi ba don tana idar da sallah ta jingina da bangon dakin, Har aka kira sallar magrib, gaba daya mazan futa sukayi suka wuce masjid while ita da salima sukayi sallah anan dakin ammah.

Karfe goma daidai ya mike tsaye yana kallon agogo, ganin haka yasa Aman cewa  zaka wuce ne?
 Yes Zan dawo da safe amar ya fada yana kallonshi kafun ya maida kallonshi ga amra babu wani wasa a fuskanshi yace  Tashi muje
Bata dago ba don kwata kwata tunaninta baya wajen saida salima ta dan ta bota  adda ya Muhammad na magana
Firgigi ta dawo hayyacinta ta dago zuba mashi mayun idanu nata da sukayi ciki ciki Ta kalleshi, bai sake


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login