Showing 225001 words to 228000 words out of 381117 words

Chapter 76 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

1986

aman, fridge ta bude ta janyo pack daya na hollandia bata ma san shi ta dauka ba don tunaninta ya gushe, damuwar da soyayyar aman na burkita mata lissafi harta fito daga kitchen din ba tareda tana kallon gabanta ba, hanyar stair ta nufa tana tafiya kanta a kasa, buge kafarta tayi da karfen handrail, da sauri tayi baya   wash allah na  ta furta ahankali, dan dukawa tayi tana kokarin duban kafar tata,
  dan allah ayi min Magana da hajiya  labaran dake zaune tun bayan saukowanta ya hangota daga nesa harta shige kitchen ta fito, daman ya dade a zaune yana jiran wanda zai sauko dan yayi fada ma hajiya yazo, har cikin kwanyarta taji muryarshi, anatse ta soma dagowa, tana shirin waigawa inda taji muryar aman ya sha gabanta, yanda ta ganshi a gabanta ba zato ba tsammani yasa gabanta faduwa cikin tsiwa tace   meye haka kuma, 
Yanda suka saba cikin kwanakin idan suka hada hanya yawanci harara ce ke biyo baya saidai yanxu taga akasin haka don murmushi yake mata, sauke kanta kasa tayi tana tausayin kanta don ya maidata as a joke, don haka ta nemi giftawa ta gefenshi, hannunta ya rike in a calming tone ya soma Magana   sorry for what I said earlia idan ya bata maki rai 
Dan dagowa tayi ganin yanda ya marairaice, kauda kanta ta sakeyi tare da zame hannayenta tace   bakayi min komai ba 
Hannun nata ya sake kamawa ya bude tafin hannunta ya dora mata leda akai kafin ya juya ya wuce dakinshi, kallon ledar tayi kafin ta wuce sama itama, labaran dake zaune yana kallon ikon allah harsuka bar wajen.
Salima na haurowa sama har zata wuce daki ta tuna da maganar mutumin dake zaune a kasa, dakin amah ta wuce ta sanar mata da wani yazo yana kasa kafin ta futo ta wuce dakinta ta bude ledar daya bata, bunch of chocolate ne a cikin ladar hade da apology card a ciki, dukda taji dadin kyautar hakan baisa ta tabe baki ba tana tausaya ma kanta.

Saukowa kasan amah tayi cikin mutunci, anatse ta karaso har cikin sitting room din   lale maraba, malam labaran sannu da zuwa 
Zama tayi kan kujera tana fuskantarshi, yana zaune akasa ya dukar da kanshi   ina wuni hajiya, ya karfin jiki, ashe bakiji dadi ba, nazo shekaran jiya ay baba mai gadi yake fada min, allah yasa kaffara ne 
  ameen ya allah malam labaran, ay naji sauqi sosai, ya noma? Kwana biyu baka zoba  amah ta fada tana kallonshi
  wallahi nayi rashin lafiya ne tsawon wata guda hajiya shiyasa na kwana biyu ban zo ba  malam labaran ya fada cikin girmamawa
  subhanallahi shine baka kira ka fad aba labaran  amah ta fada in a concerning way.
  ay naji sauqi sosai hajiya, allah ya kara arziki da lafiya 
  ameen ya allah  amah ta amsashi
  kun gaisa da mutan gidan kuwa?  amah ta tambayeshi tana kallon gefensa
  eh mun gaisa da yallabai na dubai,don tare mukayi sallah a masallaci ma, dan uwansa ne dai bai lura dani ba lokacin daya shugo 
Malam labaran ya karashe yana sunnar dakai
  madallah, ay kwanaki inataso na fada maka yayi aure ma  amah ta fada tana murmsuhi
Cikin fara a malam labaran yace   masha allah , allah ya sanya albarka, ya kade fitina 
  ameen ya allah ya aikin gona  amah ta tambayehsu anatse
  ay sai godiyar allah hajiya, tun shekaran jiya naso na kawo kwasar wannan shekarar, an samu buhu talatin na shinkafa, buhu ashirin na masara 

  ahhh madallah, allah yasa albarka, akai kasuwa kawai 
  toh shiknan hajiya 
Sun danyi hira kafin yayi mata sallama ya wuce bayan ya kara yi mata godiya akan abubuwan datayi mashi.

The next day&
Da sassafe amah ta wuce dakin amra don ta shigo da asuba ta sanar mata da wuri zasuje asubiti don bata son amar ya sani saboda zai iya suspecting wani abun ko yace zai bisu don haka ta shaida mata da wuri zasu fita.
Da sallama amah ta bude dakin, a kwance take cikin shiri don saida tayi wanka ta shirya barcin nata yazo mata, takowa har inda tae amah tayi tana murmushi,   wannan jika nawa akwai barci  amah ta fada tana murmsuhi,
Dafata amah tayi   daughter, tashi muje ko 
Bude jajayen idanunta tayi ta sauke su akan amah kafin ta miqe da kyar   good morning amah, harkin futo 
  yes dear muje kar muyi latti 

Atare suka sauko amah naga ba amra na biye da ita, sanye suke da abaya gaba dayansu, tasha stone tundaga sama har kasa, sai colors din daya banbanta, amah na rike da wata haddaiyar handbag mai shegen tsada ta manyan mata, fuskanta da farin glass mai kara kwarin idanu tayi masifar kyau, hausawa sunce lafiya uwar jiki kana ganinta kasan ta samu sauyi sosai a rayuwarta compare to lokacin da take yawan rashin lafiya, ramar datayi ma kara mata kyau tayi sosai, inka ganta bazakace ta haifi amar ba kwata kwata, skin dinta sai glowing yake daman ga haske ga kyau duk ta hada don a jikinta amar yayi gadon komai, amra dake gefenta ma tayi kyau sosai dukda gama daya kana ganinta kasan tana jin jiki.

Inka gansu yanda suka fito atare cikin abaya zaka dauka sisters ne saboda amra nada jikin girma sosai fuskanta ne kawai ke nuna kankantar shekarunta, sai kuma amah in ka kalli fuskanta ta zaka ga ta manyanta dukda manyancen nata bai futo sosai ba, she s looking so beautiful and young kamar ba ammah ba, bata da damuwar komai ayanxu sai ta iyalinta don yanxu ita kadai ta rage masu gaba dayansu.

Duban agogon dake maqale a hannun ta tayi ganin kusan bakwai da rabi yasa tace   daughter ay bazamu jira driver bama ni zanyi driving dinmu 
Murmushi amra tayi tace   toh ammah  kafin tabi bayanta har suka karaso inda motoci suke, da sauri baba mai gadi yazo ya gaishesu gaba daya kafin amah ta bada umarnin ya cire car cover din motarta don it has been long tayi driving tun bayan rashin lafiya data farayi,

Baba mai gadi na bude cover motar amah saida na kalla na sake kalla, wata bugaggiyar range rover ce rr2023 white color, fadin irin haduwar motar bata lokaci ne da alamu ma sabuwa don kamar ba a shiganta,
Motar ma gaba daya smart car ce, don bata danna key din motar ba kofar ta bude ta, amra dake biye da ita ma tana tsayuwa motar ta bude da kanta, anatse ta shige gaban motar ta zauna.
Saida amah tayi warming motar kafin tayi revarse ta juya, nan securities suka bude gate suma suna kwasar gaisuwa kafun su fuce daga gidan.

International specialist hospital&
Daidai wani haddadden asibiti amah tayi parking, amra na kwance tana barci batama san sun iso basaida amah ta tasheta, bin asibitin ta sma yi da kallo, ya hadu sosai har yafi wanda aka kwantar da amah.
Atare suka fito amah ta taimaka mata wajen rike mata hannu don she looks pale and weak,har suka shiga cikin asibitin .
Suna shiga amah ta barta anan reception ta wuce wajen receptionist ta bude mata file, cikin yan mintuna kalilan ta gama yi mata komai har tayi booking appointment.
Tana gamawa ta dawo ta taimaka mata ta mike suka wuce wajen vips don anan zataga doctor, idan lokacin appointment dinsu yayi daman by 8am dctor zaizo.
Zama suka danyi har doctor yazo, nan ma saida amah ta taimaka mata suka shiga har office din doctor, fadin irin haduwar wajen ma bata lokaci ne don ya fita daban a cikin asibiti, don ana kiran wajen da presidential root lol, zama sukayi inda doctor yayi welcoming dinsu kafin amah ta soma mashi bayani, a bayanin da amah tayi mashi saida ya tsaya y agama sauraron ta kafin ya soma Magana   well hajiya ance komai na allah ne inda rai akwai rabo, we have a lot of patients muma anan nigerai waenda sukeda ospermia kamar aynda kikayi explain mujinta nadashi, kuma cikin ikon allah zakiga basu da kwayayan haihuwar cikin ikon allah zakiga allah ya akwo wata hikima allah ya basu haihuwar, yanxu ayanda kikayi bayanin yanayinta it obvious shes preg, but zamu mata blood test baya daukan 10mins result ke fitowa don munyi upgrading facilities dinmu na nan, sannan zanyi mata scanning yanxu so that we can know how far she has gone then after that sai muyi tunanin wani irin medication zamu daurata.

Murmushi amah tayi tace   okay tohm 

Kiran wata nurse doctor yayi don ita zata taimaka mashi tana shugowa office din ta ajiye abubuwa test data dauko daga mini lap dinshi dake cikin office din, nuni yayi mata da amra yace   overall blood test za ayi mata yanxu but ina buqatan pregnancy test immidiately 
  okay sir, it will be ready in 5 mins; 
  okay thank  ya amsa nurse din, gaban amra ta karasa ta soma diban jininta tana gamawa ta ta wuce general vip lap don tayi running test din daya buqata, cikin mintuna biyar saigata da result har biyu, karba doctor yayi, tunda doctor yak araba gaban amra ya soma bugawa pat pat, ammh kuwa babu abunda take sai murmushii tana godema allah don tasan ma mai zai buyo baya, bayan doctor ya gama karantawa ya kalli amah fuskanshi dauke da murmushi yace   hajiya congratulations, shes 5 months and 3weeks pregnant, by next week zata shiga 6months zata fara zuwa antenatal, sannan akwai magungunan da ya kamata ta dunga sha don jininta is very low shiyasa take zama weak, 
Tunda ya fara Magana amra kebin bakinshi da kallo gabanta na faduwa, yanxu itane ake cewa tana da ciki? Cikin ya muhammd?

Bangaren ammah kuwa Fadin irin murna da farin cikin da take ciki a wannan lokacin bata lokaci ne karshe ma bude Jakarta tayi ta zaro bundle din kudi yan dudu dubu guda uku ta ajiye akan table din doc tace   wannan tukwicinka ne for this good news, I m sure idanda agaban mijinta kayi breaking wannan news din abunda zai baka saiyafi wannan ma, but ayi managing wannan 
  no hajiya ia cant take it 
Kaste amah tayi   I insist, 
ta karshe tana hamdala, hannun amra ta rike tana kallonta ta fara zabgo mata albarka,  allah ya shi maki albarka daughter, allah ya saukeki lafiya, allah ya biyaki da gidan duniya kin gama yimana komai, youre a blessing to us dear thank you so much  hawaye ne suka soma zubowa akan fuskan amah itama kukan takeyi sosai tana rungume amah, saida sukayi mai isarsu shiko doctor don farin ciki shima yak washi kudin da aka bashi ya ajiye a locker shi.

Saida komai yadan lafa doctor yace   yanxu scan zamuyi ko? At this time zaku iya sanin gender of the baby ma 
  no doctor, bazamuyi ma allah shishigi ba kuyi scanning din kawai it s a gift from allah so we want to keep it basai munsan komai ba ta hanyar yima allah shishigi 
Dariya doctor yayi yace   toh shikenan hajiya, zan duba lafiyan babyn kawai 
Mikewa yayi ya nuna ma amra kan gadon da zata zauna anan office din nashi kafin ya janyo scanning machine, anatse ya soma observing cikin nata saida ya dauka kusan minti goma kafin ya mike ya dawo saet dinshi, amra ma mikewa tayi dakyar don tana jin kamar karta tashi ta kwanta tayi barcinta.
yan rubuce rubuce yayi a laptop ammah dai na zaune tana kallonshi, saida ya gama ya dago a kallesu su duka,  she is having a healthy baby, the breathings are nomal, babyn yana inda ya kamata, 
  toh likita banga bumps ba? Kuma naji kace ta kusa wata shida  amah ta tambaya
  yes that is not a problem yanayin jikinta Kenan, baya nuna bumps din, mostly matan yanxu haka suka fi so saboda basa son suyi teba da stretvh marks but intakai 8 months definitely she will be very very heavy saboda cikin 
  alhamdullah alhamdullah  abunda amah ke fada Kenan har doctor ya rubuta masu magungunan da zata buqata ayanxu da allurai.
Godiya amah tayi ma doctor suka futo tana rike da hannun amra dake ta faman sunnar dakai, ta kasa believing cewa wai ciki ne da ita cikin ya muhammd, shes so emotional right now, bata san me zatayi ba farin ciki ko akasin haka, shi uban dan ma ba sonta yake ba,saidai ganin yanda amah ke farin ciki yasa hankalinta ya dan kwanta, yanxu koba komai ta sakama amah da yanda ta rike yan uwanta ta zama gatansu kuma ta riksu amana.

Cikin awa guda aka gama yima amra komai aka bata magunguna akayi mata allura, ba laifi tunda akayi mata alluran nan taji wani dadi a jikinta da kuzari, nan nurse ta bata shawaran ta dunga shan ruwa sosai da lots of milk, godiya sosai amah tayi mata kafun su fuce daga asibitin, yanda amah ke lallabata kamar kwai abun har kunya ke saka ta don koda ska karaso wajen mota da kanta ta bude mata ta shiga cikin motar ta zauna kafin ta zagayo ta kunna motar,   daughter me kike son ci?, please ki fada min kinji? Ko zakici cake naga kinason kayan zaqi 
Ganin yanda ta damu sosai yasa amra ta dan murmusa tace   zanci cake din ammah 
Cikin murna amah tace   yauwa my dear, bari na kaiki wani cake shop, akwai different varieties saiki zaba
wanda kike so 
Tada motar amah tayi ta juya akalar motar suka bara harabar asibitin, wayanta dake ruri ta daga tana ganin sunan amar ta ajiye a gefe yanxu batashi take ba ta amra take.
Koda suka iso cakemeaway shop, amra bata shiga ba saboda tana jin jiri amah ce ta sayo mata different types, flavors and toppings of cake kusan guda goma, haka aka biyota da ledoji har cikin mota kafin subar wajen.
Suna kan hanya ammah taga mai agwaluma, da data, nan ma saida ta tsaya ta saya mata kafin su bar wajen, har lokacin amar waya yake mata yayi mata missed call yafi talatin hankalinshi duk y agama tashi, karshe ma message tayi mashi   son were fine, please stop calling 

Horn din motar amah ne ya karade gidan, securities ne suka bude gate, amar dake safa da marwa a parlor yana jin horn yayi saurin futowa tsakar gidan, sanye yake da shorts sai vest gaba daya bashida natsuwa tun bayan daya tashi saida yaji horn din motar amah.

Amah na parking yazo gaban mazaunin driver, bude kofar amah tayi tana murmushi, babu zato ba tsammani ta rungumeshi, da mamaki ya tsaya shima ya rungumeta,   alhamdullah alhamdullah son, im so happy today  ta kaarshe tana dariya, amra ce ta fito daga motar tdan deba kayan da suka shigo dashi zata wuce amah tace   noo noo kawo nan, muhammd zai dauka, ay shine da wannan bake ba diyata 
Kallonshi amma ta sakeyi tace   karba kayan chan ka wuce mata dashi dakinta, 
Kallon inda amra ke tsaye tayi tace   zaki iya kuwa daughter ko ya daukeki kema ya kaiki saman 
sauke kanta kasa tayi tana jin kunya sosai, amar dai baki sake ya tsaya yaan kallon yanda amah ke cikin farinciki da annushuwanda bait aba gani a tattare da it aba,   ammah whats the news? Why are you so happy 
lakatar kumatunshi amah tayi tace   it s a secret 
tana kaiwa nan ta shige ta barsu tsaye shida amra, karasowa yayi ahankali yazo gabanta, kamar baa mar bay a miqa mata hannunshi don ta bashi ledojin, dan dagowa tayi ta kalleshi nan ta shagala harta fada tunani,   ya Muhammad is the father of my baby? Hes going to be a father, allah sarki ashe yana da rabon ganin danshi shima,  saida ya dan gyara murya ya daga mata gira daya ta ankare da kallonshi da takeyi, saurin sauke kanta kasa tayi tana tausayin kanta, ayanxu data tsaya agabanshi sai taji wani irin dadi sosai koba komai zata saka mashi da alkairin da yayi ma yan uwanta ta hanyar protecting dinsu ya kula dasu ya basu ci da sha, badan shiba qila da sun salwanta saidai tausayin kanta take ayanxu kuma, don ta rigada tasan bazai tabasonta ba bazaitaba kallonta a matsayin mace ba. Fatanta allah yasa taci albarkacin abunda ke cikin ta ta samu kwanciyar hankali a cikin aurensu da soyayyarsa.

Ganin batada niyar bashi yasa ya karba daga hannunta kawai yace   muje ciki  sata yayi agaba yabi bayanta.

Suna shiga ciki suka tadda ammah ta tara su salima dasu aman da salim tana masu kyautar kudi, yaudai kowa ya shaida ammah na cikin farin ciki dukda sunyi sunyi ta fada amsu taki.
Amra dai sama ta wuce amar ya bita da kayanda ammah tace nata ne, yana shiga yaso ya tambayeta inda sukaje saidai kuma wata zuciyar ta haneshi da hakan don haka ya fito daga dakin ba tareda yace mata qala ba yana futa tabi lafiyar gado itama.

Monday morning&
Yau su salima zasu koma school don by next week zasu fara waec da neco don already bandasu yan ss3 za ayi exam din school sais u salim dake ss1 going to 2.
Haka suka jera kwanaki suna zuwa school kullum ita da salim, ta maida hankali


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login