Showing 3001 words to 6000 words out of 381117 words

Chapter 2 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

1951

ya daga hannunshi waiter yazo, card dinshi ya basu sannan yayi payment ya miqe, amra kuwa tana nan daga gefen wajen inda ya zauna hankalinta nakan abincinta wanda ta saya, saida taci tayi nak sannan ta bada payment dinta da cash anatse ta mike da paper bags dinta da tayi shopping niki niki sannan ta juya zata wuce, idonta ne karaf ya sauka kan na amar wanda yake shirin fita, tana ganinshi kuwa ta bude baki zatayi Magana shiko yayi kamar bai taba ganinta baya wucewar shi, mamaki ne ya cikata na irin wulaqancin general dinan, don saura kiris ta gaishesa don da tayi hakan da saidai ya jizgata awajen, haka yasa sumi sumi ta wuce abinta aranta tana ayyana irin isa ta mutumin.

Shiko amar sarai ya ganta saidai baiyi tunanin zatayi Magana ba don ba wani kusanci ne yake dashi ba da staff din headquarters shiyasa baimabi ta kanta ba kuma shima yayi mamakin ganeta da yayi domin its hard for him ya gane mutane don shi bai fiye shiga sha anin mace ba.
?
Washe gari Monday shirinta tayi sosai cikin wata Lebanese gown red wanda tayi mata kyau sosai, rigar tana da adon flowers ajiki, ta zauna dam ajikinta, fuskar nan tata fayau babu komai saidan kwalli data sanya wanda ya kara mata wani irin kyau sosai, anatse ta dakko dan vine flat shoes dinta shima red ta saka sai yar channels hand bag dinta maqale ah kafadarta, anatse take tafiya harta shiga motorn datayi requesting, tafiyar minti ashirin sukayi suka iso headquarters tana sauka cikin asibiti ta wuce, tana zuwa ta tarar da haifa zaune ah office dinta, gaisawa sukayi kafin suka shirya cikin lap coat dinsu suka fara ward rounds, saida suka duba patients din da sukaje last operation tukunna suka dawo office nan suka tarar da hafiza tana ta sassarfa hankali atashe, kallonta amra tayi sannan tace   sis hafiza is there anything wrong  & ko kallon inda take batayi ba ta fuce..nan take ran haifa yabaci tace   babe wallahi idan da nice nake zaune da wannan wallahi wataran sai an raba dambe, she s so rude bata da mutunci ko kadan  ..dariya kawai amra tayi sannan tace   haifa wallahi she s nice, idan kin ganta acikin wannan mood din to fah lallai an tabo mata inda yake mata zafi ne  & dariyar mugunta haifa tayi sannan tace  wai har yanxu ita nan son general din take? Haha gaskia tana cikin matsala indai wannan zata so  & jin haka yasa amra kallonta fuskarta dauke da tambaya tace   why did you say that  & ..gyara zama haifa tayi tana fuskantar ta tace   kinga wannan general din idan bazaki manta ba kin tuna lokacin da mukaje flower garden park dake har muka hadu da hammam  ? girgida mata kai amra tayi alamun gamsuwa.. sanan haifa ta cigaba   idan kin tuna ay tare yake da wani guy wanda kikeji nace besfriend din mu, toh ay shine general din  & tabe baki amra tayi tace   oh no wonder inata tunanin inda na san shi ashe shine, kai haifa mutuminnan badai wulaqanci ba, jiya fa naje shopping ah mall saina tsaya yin launch ah t&t restaurant na ganshi, I was so surprise banyi tunanin ganinshi ba  , murmusawa haifa tayi sannan ta cigaba   toh nima dai haka nace amma hammam yace min he s easy going fah, kawai dai baya shiga sha anin mata kwata kwata kuma yana da zafin zuciya sosai shiyasa it s hard to live with him   & & & ..saida suka gama tsegumin amar tukunna sukayi sallama kowa ta wuce office dinta.
'?('***Auren Katin Kasa ***('
'?
(Unexpectedly fallingd'?
Story and written by:
QueenMarh=?x?

Paid book =???
50-51


Hankali atashe hafiza ta karasa office din amar,ahankali ta kutsa ta shiga ciki, yana nan zaune da army uniform dinshi kamar kullum amma yau ya cire rigar sama sai yar ciki wadda white top ce mai kyau wadda ta amshe shi sosai faffadan qirjinshi wanda ya cika rigar ya futo tsam, arms dinshi kamar zasu farka hannun rigar tsabar murdewa fuskarnan kuwa kamar kullum ahade babu ko alamun murmushi saidai kyawun fuskar ya rinjayi hade rai da yayi, ahankali ta tako gaban table dinshi tace   good day sir, I m mss hafiza from hospital  ..baiko kalli inda take ba yana latsa waya yace   why have nt I received my last medical report,? Management team dinku basu fada maku qa ida na ba?duk wani medical report dina office zaku kawo min?..yana kaiwa nan ya buqi table din gabanshi da karfi. Girgiza kai ya fara, duk shekarun daya yayi a headquarters wannan ne karo na farko da yake samun matsala da health care team, da zarar yagama abinda ke gabanshi zaisa asake recruiting sabbin medical staffs cause wadannan suna saka mashi ciwon kai sosai  & hafiza wadda cikinta ya duri ruwa da sauri ta soma koro mashi bayana   sir I m so sorry, last time kace karna sake zuwa yi maka blood test so I send my assistant to.. baima bari ta karasa ba ya kalli m5 yace   get her now  da sauri m5 ya fuce don shima ta shafesa.
kallon hafiza amar yayi ataqaice yace   you re excused  ..da sauri ta fuce, shiko tabe baki yayi kamar yaga kashi sannan ya miqe yana shafa few suman kanshi da tafin hannusa ya tsaya gaban view din office din don curtains din abude suke, hannunshi ya sanya cikin aljihun kakin jikinshi kamar maiyin nazari, mamaki gaba daya ya cikashi da takaici don wannan ne first time da akayi delay wajen kawo mashi medical report dinshi wanda tunda ya samu daukaka sosai baya ajewa a files room sbd yana da enemies da yawa har acikin office wanda zasu iya using health issue dinshi as his weakness don su ci galaba akanshi dukda yawanci a report din baya bari sunayin test din abinda ya shafi mazantakar shi kwata kwata.

Cikin hanzari m5 ya shiga cikin asibitin, nan yasa aka kira office din su amra. Amra wadda tunda suka dawo daga salla itada haifa ciwon kai ya dameta ya sa ta dan kwantar da kanta kan table dinta, jin knocking yasa ta dago da kanta, idonta harsun fara jaa sbd ciwon kai da damuwa data sakama kanta gashi ta fara jin zazzabi kadan kadan, anatse ta dago ta kalli staff din tayi mata murmushi tace   yes  , kallonta matar tayi sannan tace   ana nemanki a reception  .. fita matar tayi nan amra ta bi bayanta, ganin soja a tsaye yasa gaban ta faduwa da kyar ta dan nutsar da kanta sannan ta karasa gaban m-5, tana isowa yace   are you mss hafiza s assistant?..jin haka yasa ta girgida mashi kanta tace   yes I am  .. juyawa yayi ya fara tafiya sannan yace   follow me now  ,.. hankali atashe ta fara binshi, gaba daya sai taji wani irin zazzabi ya taso mata gadan gadan, tana nan biye dashi har suka karaso gaban office din general ganin haka yasa ta fara qoqarin saita natsuwarta, bude qatuwar kofar m5 yayi sannan suka shiga, gaban wajen guest chair ta tsaya while m-5 ya tsaya abayanta don jiran order daga oganshi, jin tsayuwar mutun abayanshi yasa ya juyo ataqaice sannan ya kalleta wanda zan iya cewa kallo na biyu Kenan da yayi mata na qurulla, anatse ya fara takowa dan gab da ita sannan yace   where s my last medical report,? 
Ganin yanda ya tsaya dab da ita yasa ta daburce lokaci guda turancin nata ya kubce tama rasa me zata ce mashi, chan dai ganin kamar zata bata mashi lokaci ya sashi calming voice dinshi don yaga kamar tana da masifaffan tsoro, haka yasa ya kuma maimaita mata tambayar cikin harshen bahaushe..anatse ta dago ta mashi kallo daya ta sauke kanta qasa tace   Na kaishi file room  & ..runtse idonshi yayi da sauri, wani irin balbalin masifa yana taso mashi, furzar da huci yayi sannan yace   what the hell& jin haka yasa m-5 saurin ficewa direct 4th floor wajen file room, ahankali ya fara dubawa har yazo kan wani green box wanda ake aje health report files na manya manyan sojoji, anatse ya zaqulo na amar sannan ya fuce,& bangaren amra da amar kuwa kamar yaqi don fitar m-5 da wuya ta zube qasan gwiwoyinta, ta fara kuka, tama rasa me zatace don kwata kwata ta kasa gane menene ainahin laifinta, shiko oga kallonta yake cike da mamaki, yama rasa mai zai mata, ganin kukan nata ya fara cika mashi kunne yasa yace   get the hell out of my office now, kuma na baki 5 minutes kije ki kawo min file dinnan yanxu, and karkiyi tunanin haka zan barki, purnishment dinki yana nan yana jiranki  yana kaiwa nan ya wuce wajen table dinshi ya zauna, amra kuwa baiwar Allah da sauri ta miqe ta fara neman hanyan fita hartana harde qafafunta, batama tsaya bin lift ba ta wuce stairs ta fara hawa matattakalar har takai 4th floor, tana shiga ta wuce wajen inda ta aje report din nashi, ahankali hawaye ke zubowa daga idanunta, zuciyanta sai faman harbawa takeyi da zafi, kamar mahauciya haka ta dunga fidda files din daya bayan dama hankali atashe.

Bayan fitar amra kuwa kifa kanshi yayi akan table din, kanshi yana mashi wani irin zafi, kukanta har lokacin yana jinshi cikin kwakwalwar shi, babu abinda yake fado mashi aranshi face Amma shi, idan yaga mace na kuka itace kawai take fado masa, sbd irin kukan da takeyi akan aman wanda shi kuma baya so kwata kwata ko kadan.

Yana nan zaune karar emergency ta fara cika mashi kunne nan take aka fara announcing,   everybody evacuate now!! Fire fire.  & ahankali ya dago kanshi wanda ke sara mashi sosai saida ya dauka wajen minti goma kafin ya miqe babu wani fargaba ko tsoro a tattare dashi, bude kofar office dinshi akayi wanda m-5 ne yazo domin yayi escorting dinshi, futowa sukayi atare shida m-5 har suka sauko qasa, wanda kowa ya fuce babu kowa tundaga office dinshi, anatse ya futo daga headquater ya tsaya ah harabar inda sauran sojoji kowa ya tsaya don jiran fire fighters wanda qa ida ne su fito don ba aikinsu bane kashe wutan saidai fire fighters, saida kowa ya tattaru gaban tapkeken compound din lokacin wutan ta fara ci sosai ah floor din da ta fara ci, yan medical team wanda suma karasowarsu Kenan suma suka tsaya gefen sojojin, amar wanda ke gefe kamar baisan da mutane a wajen ba sai faman latsa wayar shi yake, chan ya dago ya kalli ko ina da kowa na wajen, ahankali idonshi ya sauka kan yan medical, kawar da kanshi yayi kamar wanda ya tuna wani abu, ahankali ya fara nazari kamar mai tunanin wani abu sannan ya kalli m5 yace   call the medical team here  da sauri m5 ya isar da saqon shi sannan ya dawo tare dasu, daya bayan daya suka gaidashi cikin girmamawa sanin koshi waye, babu wanda ya amsa cikinsu saima kallon hafiza da yayi yace   where s your assistant? ..kallonshi tayi cikin mamaki sannan tace   sir tunda ka aiko a kirata bata dawo cikin hospital ba  .. jin hakan yasa amar kallon m-5 wanda shima ya kalleshi lokaci guda kuma yaji hankalinshi yadan soma tashi, da sauri ya fara tafiya zai shiga bulding din, nan fa sojoji suka taho gaba dayan su suka mara mashi ba, shiko baimabi takansu baya wuce gaban lift, ganin sun biyoshi gadan gadan yasa ya daga masu hannu hakan yasa duk suka sha jinin jikinsu suka tsaya curko curko don babu halin hanashi don su saidai ya basu order badai su bashi ba ciki kuwa harda m5, hammam ne kawai daman zai iya tsaidashi shima badon rank dinshi ba sai
don shi abokinshi ne wanda kowa ya sani. Da sauri ya fara taka matattakalar benen azafafe har ya iso 4th floor wanda wuta ta fara cin abubuwa sosai, ahankali ya fara kutsa kai wajen roll din floor din, daya bayan daya ya dunga bin kofofin da kallo, har yazo daidai wata jar kofa da aka maqalama tag din health record room, da sauri yasa hannu don ya bude handle din, tunawa da handle din karfe ne yasa yayi sauri cire hannun nashi, yayi baya, da sauri ya taho gadan gadan ya buga kofar da kafa daya tashin farko ta balle, wai maza fa akwai karfi, da sauri ya kutsa kanshi ciki wanda duk hayaki ya dabaibaye ko ina, ko haske ba a iya ganin, ahankali ya zaro mask din aljihunshi ya saka sannan ya fara dube dube, ganin babu alamun mutun ya sashi fara Magana   hey hey anyone here  chan ma dai shuru yaji, hankali atashe yama rasa me zaice don baima san sunanta ba,   keee keee  !! ahankali amra wadda sumanta na biyu kenan ta soma jin Magana sama sama, ahankali idonta ya soma budewa, bakinta wanda ta shaqi hayakin harya cika mata baki yasa ta kasa Magana ko neman agaji, ahankali ta fara motsa hannunta har tadan bugi wani abu kamar dusbin, da sauri ta dunga jan hannunta harta tabo dusbin din sannan ta hankadashi da duk karfinta, jin motsi ta wajen wani sako yasashi sauri zuwa wajen, aikuwa yana karasawa yaji yadan bugi hannun mutun da kafarshi, da sauri ya tsugunna ya tabo ta don tabbatar da mutun ne, ahankali ya soma cewa   ke tashi let s go  .. ganin kamar bata motsi ya sashi saurin jawo hanunta, da sauri ya taro ta don ta koma zata fadi, ganin idan ya kara mintuna a wajen rayuwar ta zai salwanta ya sashi runtse idonshi ya rankwafo ya sabota gaba daya in a bridal way, amra kuwa wadda ta fita hayyacinta jin wani kamshi da dumi yasa ta fara tura kanta a haukace cikin faffadan kirjinshi, gaba daya saida ta cukwikwiye mashi rigar jikin nashi har buttons din sun fara fita, jin nunfashinta na dawowa yasa ta kara bada himma ta zagayo da hannunta wajen qugunshi ta nade su tsam sannan ta cusa kanta cikin kirjinshi wanda farar shirt din ciki ta hanata samun access to bare skin dinshi, da sauri ya futo daga sakon ya fara shirin ficewa, yana karasowa daidai kofar kuwa inda ya dauketa gefen bangon wajen ya fara ruguzowa, da sauri ya kauda kai ya fuce, haka ya dinga kaucewa wutar nan ya fara taka stairs,har suka sakko last floor, hankalinshi bai kwanta ba saida ya fito nan m-5 ya taho da gudunshi gabansa sannan yace   sir are you alrigt  & baiko bashi amsa ba yace   take her to ER she has lost her conscious,  .. da sauri m-5 ya mika hannu zai cicibeta..kallonsa amar yayi kawai sannan ya kauda kai yace   just lead the way  .. fita sukayi tare wanda m-5 har ya isa gaban health team da suka tsaya cirko cirko yace su kawo gadon patients, da sauri aka kawo nan amar ya sauketa, dakyar ya banbare jikinshi daga hannunta don duk ta fita hayyacinta, duk wannan abin akan idon hafiza wadda idon ta tap da kwalla ita bama ta rashin lafiyar amra take ba, a a kawai dana sani take, yanxu da tuni ita zai dauko a precious hannun nan nashi&
Toh fah hafiza abin nata ya fara yawa fah& & &
?
Saida aka karama amra ruwa kafin ta dawo daidai, karshe dai harda allura akayi mata don ta samu bacci ta huta, allah ma ya taimaka an yi rescueing din ta da gaggawa da saidai a dauka gawarta don babu wanda yayi tunanin da mutun acikin floor din.

Duk wannan drama da akayi haifa bata sani ba don sun fita wani restaurant ita da babyn ta hammam ba tare da an sani ba, sai wajen karfe uku suka dawo wanda ganin lokacin tashi yayi yasa suka dawo. Abakin gate ya sauketa don kar aga sun dawo tare, itakuma ta tako har ciki, ganin mutane cirko cirko da kuma motar fire fighters manya manya yasa ta saurin karasawa ta fara tamnbayan meya faru, nan kuwa wani yayi mata bayanin wuta ce ta kama a 4th floor har an kusa rasa wata black African girl, jin haka yasa hankali haifa tashi don tasan amra ce kawai black African acikin headquarters da asibiti gaba daya hakan yasa da sauri ta wuce ER nan taga amra kwance tana baccin wahala, tausayinta ne ya dabaibayeta, nan take kwalla ta zubo mata ta fara Magana   I m so sorry babe, bai kamata na barki ba har kika shiga cikin halin nan,  tana kaiwa nan ta kamo hannun amra ta fashe da kuka sosai, jin taushin hannu yasa amra dan bude idanunta da bacci bai ishesu ba ta sauke akan haifa wadda ke zubda kwalla, da kyar ta dago ta zauna ganin hakan yasa haifa taimaka mata ahankalin bakinta ya soma furta   water please  & ruwa haifa ta debo mata ah dispenser ta kawo mata gabanta saidata shan??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ye wajen cup uku sannan ta tsagaita ta kalli haifa tace   babe waye ya fito dani daga cikin hayaqin nan and maysa kike kuka   ..jin hakan yasa haifa saurin rungumeta tace   I m so sorry babe ki yafe min na barki cikin wannan halin ban sani ba I m so sorry  ..lallabata amra tayi sannan suka tattara domin shirin tafiya gida, saida haifa ta cire mata Karin ruwan sannan ta deba mata magunguna a pharmacy sannan suka wuce wajen moton haifa, anatse take takawa sbd jirin da take ji kamar zata fadi, saida sukazo daidai wajen parking din staff


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login