Showing 216001 words to 219000 words out of 381117 words

Chapter 73 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

1980

cover din pack din, saida yasha ya koshi ya maida sauran kafin ya koma Inda take tsaye daga gefenta  meysa kike gaba dani, is it because& 
Saurin ajiye knife din salima tayi ta kalleshi  baba gaba dakai, babu dalilin da zaisa nayi gaba dakai,
Katseta yayi saurin yi yana matsawa kusa da ita  then why are you ignoring me?nine ya kamata nayi ignoring dinki saboda ni kika yima breaking heart tho I ve moved on ya karashe yana daga mata kira, kallonshi tayi kafun ta kauda kanta gefe  ni bana gaba dakai kaine de&  ta fada tana jin yanda zuciyarta ke pounding,
Murmushi kawai yayi ya miqa mata hannu fuskanshi dauke da murmushi  friends
Kallon hannun nashi tayi hawaye na shirin zubo mata Tayi saurin dannewa tace  no
 Please!!!!! Ya fada yana Jan word din kamar mai riko
Kauda kanta gefe tayi tana jin zafin shi sosai Wai friends may yake nufi da ita kenan,
 Kinyi shuru friend ya sake magana
Wani irin maqoqon bakin ciki ne ya turniketa yana ganin haka, wata irin dariya ce ke ciyo bai Ganin yanda yake take reacting ba tare da saninta
A harzuke tace  okay but don t call me frind call
Me with the name you usually call me
 You mean baby sal? Or sal? Or salima
Y tambayeta yana kallon cikin idanunta, saurin kauda nata idanun tayi da suka kawo ruwa  anyone ta bashi amsa tana kokarin slicing green pepper, maganar da yayi ne ya Dakar mata zuciya  okay but banda baby sal, sabod ayanxu baby daya gareni kinga bai kamata na dunga hadata da kowa ba ko sal?
Rai abace ta dago ta kalleshi  just call me with salima, and please kaje kana distracting dina idan Ka gama abunda kakeyi tana kaiwa nan ta juya mashi baya ta wuce wajen sink ta fara wanke veggies sun hawaye na sauka akan idanunta tana gogewa, sarai yaga yanda yake goge hawayen tana basar wa, baice komai ba ya danyi dariya ta gefen baki kafin ya tabe baki  au harda korata salima? yanda ya karashe maganar da suna ta kamar an buga mata mashi a zuciya, saurin runtse idanunta tayi ba tare da da tace mashi Tak ba,  daman Zan taimaka maki da wasu ayyukan ne but tunda an koreni bari nayi tafiya na
Yana shirin juyawa call ya shugo wayanshi, saurin muting call din yayi ya kai wayar kunnenshi kamar ya amsa yace  hello baby na how are you today?Kinci abunci kuwa?
Ya fada yana fucewa daga kitchen din, wani maqoqon bakin ciki ne ya turnike salima ta juyo ta bishi da harara  Allah ya isa Wallahi, shegiya koma wacece bazaki taba samunshi ba
Ta fada ahankali tana goge hawaye kafin ta maida hankalinta wajen girkinta, Aman da ya dan labe a hanyar kitchen din sarai yaji abunda tace don Har darawa saida yayi  zanyi maganin ki ne ya fada yana dariya shi kadai kamar wani zautacce, wayar hannunshi ce ta sake yin ruri, kallon wayar yayi ganin Amar na kira don shine ya kira dazu ma, saurin dagawa yayi ya kafa wayan a kunnenshi, magana Amar yayi daga chan bangaren kafin ya soma amsawashi  Bari na duba dakin nata, yanxu nake shirin haura wa saman ma
 Okay thanka, idan kaje Ka kirani zanyi amra magana Amar ya fada yana kokarin kashe wayar
 Okay Aman ya amsashi kafin ya wuce sama.
Dakin ammah ya wuce direct, da sallama ya bude kofar,budurwar nurse din dake kula da ammah ce a tsaye hannunta rike da wayanta, kallonshi tayi fiskanta duake da murmushi, shima kallonta yayi, black beauty ce ga ido ga diri saidai gajeriya ce sosai don sai ya zamana dirin nata ya dunkufe, kallonta Aman yayi yana karasowa inda ammah ke kwance tana barci saboda maganin da aka bata wanda kesa barci sosai sannan yana hana jin yunwa sosai,  welcome sir nurse din ta fada anatse tana kallonshi tana lankwashe murya don tunda ta shugo gidan tasan gidan masu hannu da shuri ne, don haka taci alwashin cusa kanta itama, kallon gefenta yayi fuskanshi duake da murmushi yace  thanks, tasha magani ne?
 Yes sir, maganin yana aka barci but zata Tashi in 2hours ta bashi amsa tana kallonshi da manya manyan idanunta kamar na mujiya, juyawa kawai tayi ba tare da yace mata komai ba ya fuce daga dakin ya sauko kasa, dialing number Amar ya fara yi ya shiada mashi tana barci don daman ya kirata ne bai sameta ba don yanason yaji ya lafiyar jikinta sannan yana son ya shaida mata ya futa sai yamma zai dawo  na shiga yanxu tana barci saboda magani data sha, she will be up in the next 2 hours, will call you zuwa lokacin daga chan bangaren Amar yace  thanks, please let me know idan wani abun ya faru
 Don t worry I will watch over Aman ya bashi amsa kafin ya dauke wayan daga kunnenshi ya wuce dakin shi.

Aman na kashe waya shima ya aje wayarshi ya maida hankalinshi kan tukin da yakeyi anatse, tafiyar minti goma ta maqoshi Nigerian military headquarters, anatse ya shige da motarshi kamar koda yaushe, yana parking ya dauki wayarshi dake kan dashboard ya futo daga motar kafin ya rufe ta ya nufi hanyar shiga cikin headquarters din, bai tsaya ko ina ba sai office din asad, da sallama ya bude office din yasa kai ya shige ciki.
Asad ne zaune kan kujeran office dinshi, sanye yake da kakin sojoji, saurin miqewa yayi, nan Amar ya tako inda yake ya miqa mashi hannu, musabaha sukayi kafin amar ya zauna, shin zama yayi fuskanshi dauke da murmushi yace  ya jikin hajiya? Allah yasa kaffara ne
 Alhamdulillah,taji sauqi mun dawo gida ma
Amar ya bashi amsa yana kokarin duban wayarshi
Kallonshi asad yayi ya tura mashi file din gabanshi yace  Masha Allah Zan shugo yau da daddare, Allah ya bata lafiya
 Ameen Amar ya amsa shi a taqaice
Kallon file din yayi kafin ya soma budewa,  oga ga approval ta iso, you have the right to take him zuwa uae,
Kallon file din Amar yayi saida ya gama karantawa gaba daya ya rufe file din ya tura gaban asad, kallonshi asad tayi tana neman Karin bayani,
 No need for that anymore, Zan barshi anan kuyi mashi hukunci daidai da abunda yayi,
Da mamaki asad ya dago ya kalleshi don yasan saboda wannan abun ne ya kasa komawa bakin aikin sa acahn uae saboda yana son ya tafi dashi don a hukuntashi achan,  but oga..
 No but, lieutenant asad, saidai Ina rokonka don Allah karka bani kunya,
Amar ya fada yana kallonshi fuskanshi a hade tauuu kamar baiso hakan ta kasance ba,
 Yes sir, justice will served
Asad ya fada yana Sara mashi, fuskanshi a hade ya cigaba  suma ku hukuntasu gaba dayansu, nabar komai a hannunta nasan bazaka bani kunya ba?
 Insha Allah sir,but oga& why did you suddenly change your mind asad ya tambaya yana kallonshi don gaba daya he s confused, yayi mamaki sosai don yasan idan Amar yace zaiyi abu sai yayi babu wanda zai hanashi haka zalika daya nemi abashi kabiru koda military ta hanashi zaiyi using power shi ya karbeshi ta karfi da yaji, saidai yanxu dayaga akasin haka yayi mamaki.
Bai amsashi ba ya mike tare da miqa mashi hannun  thank you so much for your help
Jinjina kai asad yayi  nine da godiya oga fir trusting me on this case

Fucewa sukayi atare daga office sun suka wuce criminal room inda aka aje Alhaji kabiru, gaba daya nan bangaren babu wuta kwata kwata don cikin duhu ake ajiye criminals Ana Kiran wajen ma da dark room don azabar da ake gamawa a ciki, asad ne ya bata umarnin aka kunna wutar wajen nan take haske ya hade ko ina, dakunan ne aqalla zasu kai kusan goma sha biyar Kowanne da manya manyan criminals a ciki gefen su kuma na kananun criminal ne da ake kamawa suma Ana ajiye su, cikin dakin da aka ajiye Alhaji kabiru suka shiga
Kallon inda Alhaji kabiru ke maqure amar yayi, an kulle hannayenshi da karafuna gaba daya ya sauya fasali ya yanqwane ya zama kamar tsumma, ahaka ma in aka barshi ya gama lalacewa gaba daya, takowa Har gabanshi amar yayi ya tsugunna ya kalleshi  yanxu menene ribarka na abubuwan da kayi? Ka cuci kanka kuma muka Ka cucemu
Dagawa kabiru yayi ya kalleshi dakyar don idanunshi a kumbure suke, yana gane amar ne ya babbake da dariya, kamar mahaukaci  finally!!!! Burina ya cika yanxu, you re miserable, yanxu saika kashe ni ko?
Alhaji kabiru ya fada yana dariya, murmushi amar yayi sai yanxu ya gane abunda ammah ta fada mashi jiya, ganin yana murmushi yasa Alhaji kabiru tsagaita dariyar shi ya kafa mashi idanu kamar mahaukaci, kallonshi amar yayi kallon ina tausaya maka  in kashe Ka saboda na zama kamar kai ko? Haka kake so? Nunfasawa amar yayi ya cigaba  bazan taba zama kamar kai ba, kuma bazan kashe ka ba, Zan barka kasha azabar duniya da hakkin waenda ka salwantar da rayuwarsu, shi kadai ma ya isheka, 
Mikewa Amar yayi bai sake kallonshi ba ya juya ya fuce daga cikin dakin, Alhaji kabiru dai ba haka yaso ba, don haka ya dunga ihu yana surfa ashariya,  Wallahi saika kashe ku kasheni dan Allah na gaji da wannan masifar na shiga uku
Kallonshi asad yayi don shima sai alokacin ya gano dalili da yasa amar ya fasa tafiya dashi chan  ay mutuwa ba yanzu zakayita ba sai lokacin Ka yayi bayan munci ubanka
Asad ya karashe yana Kiran yaranshi don zuci ubansa.

Futowa yayi ya tadda amar a tsaye kafin su wuce dakin mata da aka ajiye lantana, bude dakin asad yayi kafin amar yabi bayanshi, a zaune take a kasa kan cement don ko leda babu a cikin dakin, dago da idanunta da sukayi jaa tayi, da sauri tayi baya Ganin Amar a tsaye, gaba daya furgicewa tayi kamar mahaukaciya don bazata taba mantawa da dukan da yayi mata ba din taji kamshin lahira, kallonta Amar yayi daga nesa, ta rame sosai ta koma kamar wata mai kanjamau saboda rashin abuncin kirki, hawaye ta soma yi jikinta na bari  dan darajar Allah ku yafe min, dan Allah yallabai Wallahi sharrin shaidan ne
Takowa Inda take Amar yayi idanunshi sunyi jaa, aduniya babu wadda ya tsana kamar lantana dukda yana kokarin dannewa saboda itace ta kusa sanadin rabashi da farin cikin sa wato mahaifiyarsa,  dan Allah yallabai ku yafemin l, hajiya ta yafemin Wallahi sharrin shaidan ne
 Ba sharrin shaidan bane, da saninki cewa abunda aka baki kiyi ba daidai bane kika karba kikayi, kinci albarkacinta don saboda ita ne kike nunfashi Har yanxu,
Yana kaiwa nan ya fuce fah dakin asad na biye dashi, ganin yana shirin sauka kasa yasa asad saurin cewa  oga Dayan doctor fah?
 No need, Zan wuce gida yanxu saikazo ya fada yana mikama asad hannu, sallama sukayi kafin ya fuce daga cikin headquarters din ya nufi inda tayi parking motarshi.
Yana shiga motarshi ya sauke nauyayyanijiyar zuciya yana jin zafi aranshi sosai, saidai yanda ya saki komai a hannun asad sai yaji kamar ya sauke wani nauyi ne daya rataya akanshi, ya dauka kusan minti goma a zaune kafin ya kunna motar shi ya fuce daga headquarters din.


Gidan gona&
Futowa malam labaran yayi daga cikin gidan gonar ammah bayan ya gama ban ruwa saboda cikin kwanakin Ana rana sosai,gidan gonar nada girma sosai don babu abunda baya shukawa a ciki Harda kiwon kaji Duk yana yi, fitowa yayi hannunshi rike da buta, sanye yake da triga da wando da yadi fari, ya rame sosai ba kamar yanda yake abaya ba saboda rashin lafiya da yayi ta tsawon sati uku, don hakan ne ma bai samu yaje ya kaima ammah abunda ya fidda na cikin nima wanda ya gyara, don Duk shekara saiya fara kai mata gida idan ta diba sauran sai akai kasuwa idan an sayar sai ya maido mata da kudin dukda kusan Rabin kudin take bashi a matsayin ladan shi wani sa in ma haka zata ce ya rike gaba daya kudin, ammah wadda yake kira da hajiya ta gama yi mashi komai sosai, don yanda take kyautata mashi, bata sanshi ba bata san asalin shi ba hasalima tsintarshi tayi ta bashi ci ta bashi sha da sutura da yanda ta damka mashi amanar gonarta ba tare da ta waiwayeshi ba hakan na sashi jin Duk duniya babu abunda zata nema a wajen shi da bazai yi mata ba, fatanshi kullum Allah ya kawo ranar da zai saka mata da alkairin datayi mashi.
Zama yayi bakin bishiyar dake gefen gonar yayi ya daura alwala, yana gamawa ya shimfida abun sallah ya tafa kabbara yana idarwa ya zauna yana lazimi yana bin tsirarrun mutane dake yawo,
Mikewa yayi ya tattare abun da yake sallah dashi tare da butarsa ya shige cikin gidan gonar, bin ko ina ya soma yi da kallo yau sati shi guda kenan rabon da yazo gona sai yau saboda rashin lafiyar da yayi na zazzabi da matsanancin ciwon kai dake hanashi yin komai don Har dishi dishi yake gani idan ya Tashi da safe don haka ya zauna a gida ba tare da ya futa ba Har saida ya danji dama dama.
Gaban buhunhunan shinkafa kusan guda talatin ya tsaya ya bude yana duba su sosai, shinkafar tayi kyau sosai daman ya bari sai ya tara bugu talatin kafin ya kaima hajiya don ta gani, saida ya duba duka kafin ya zaro wayarshi dake cikin aljihun wandonshi, yar Nokia ce karama da ya saya cikin Albashin da ammah ke bashi dukda yana da kudin da zai saya babba hakan baida ya saya ba saboda babu wani amfani, he s leaving a lowkey life.
Kira ya fara yi ana daga ya kafa wayar a kunnenshi  iruu ya aiki, Ina buqatar akori kura karama wadda zata diba buhu talatin gobe
Shuru ya danyi yana sauraron shi daga chan kafin yace  yauwa Nagode sosai.
Yana kaiwa nan ya kashe wayar ya futo daga gonar ya rufe inda yake Adana shi kafar kafin ya wuce bakin titi, tunda ya taaya bakin titin ya dafe kanshi dake Sara mashi sosai, wani irin dishi dishi yake gani, kwata kwata baiyi tunanin tsaywan shi kan titi ke kawo mashi ciwon kai ba sai yanxu, da kyar ya samu ya tsallaka ya tari mai machine don ya kaishi GRA.
Tafiyar minti a shirin ta kawosu high way dake hade da titin taura estate don mashin baya wucewa ta wajen,saukowa yayi ya zaro dari biyar ya bama mai napep, godiya yayi mashi ya fara takowa zuwa eatate din, tafiyar minti goma ta kawoshi taura estate, bai wani sha wahalar shiga ba don an sanshi, yana shugowa ya wuce babban apartment din estate din kai tsaye, da sallama ya karaso inda securities suke dukda ba musulmai bane hakan baisa basa amsawa ba, gaisawa sukayi kafin su bude mashi ya shige ciki, da baba mai gadi yaci karo a compound din gidan yana zuba ma flower ruwa, yana ganinshi labaran yayi saurin karasowa inda yake suka gaisa tare da yaushe gamo.

 Kayi wuyar gani labaran, yau kusan wata guda rabonka da gidan nan mai gadi ya fada yana zuba ma flower ruwa
 Wallahi baba nayi rashin lafiya ne sosai, baba iya futa ma, sai cikin kwanakin nan na samu zuwa gidan gona labaran ya fada yana dariya
Kallonshi baba mai gadi yayi ya aje tiyo din ruwa yace  Allah sarki shiyasa, Ay hajiya ma an kwantar da ita a asibiti yau sati biyu kenan, jiya aka sallamesu
 Subhanallahi Allah kasa kaffara ne ay ban sani ba dana zo
Dan matsawa baba mai gadi yayi labaran na Ganin haka yasan gulma zaiyi don haka ya dan dara kawai baice mashi komai ba yana sauraron sa,  labaran baka da labarin abunda ya samu hajiya?
Da mamaki labaran ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?yace  ah ah fatan dai ba wani munmunan abu bane
 Hmm rayuwar nan dai babu tabbas, Ka janyo mutun Ka sashi a inuwa ya jefa Ka a rana, wannan la ananniyar matsiyaciyar yarinyar nan ya take da suna yar aikin nan
Da mamaki labaran yace  lantana?
 Ee ita fa, la ananniya aje guba ta dunga zubawa hajiya a abun sha, rana daya Allah ya tonu asirinta matar yallabai ta kamata
Da mamaki labaran ya zaro ido yana innalillahi,  yaushe akayi hakan labaran ya tambaye da yana kallonsa
 Ay nake fada maka dalilin da yasa hajiya ta fadi kenan an dauka ma bazata rayu ba baba mai gadi ya fada yana sauke muryarshi kasa
Zaro idanu labaran yayi yana jin tsanar lantana yace  gaskia wannan matar anyi azzaluma,allah ya saka ma hajiya ya tsareta,
 Ameen fah, Ay badan matar yallabai ba da tuni saidai gawar hajiya baba mai gadi ya fada yana jimami
Wani irin kallo labaran yayi mashi najin rashin dadin kalamanshi na karshe, saurin katseshi labaran yayi don yasan baba maigadi Akwai surutu haka zai dunga zance babu kan gado don haka yace  godiya ta tabbata ga Allah, Allah ya tsare wannan ahalin gaba daya
Tabe baki baba mai gadi yayi yana yau at goro baya son zancen yayi ending don haka yace  Ashe shi yallaban aure yayi achan wata kasar, itace matar tasa data taimaki hajiya ay
Jinjina kai kawai labaran yayi ba tare da yace komi ba kafin yadan nunfasa yace  yanxu ana iya Ganin hajiya?
 Haba kai kuwa, jiya fa ta dawo Ka bari sai zuwa jibi saikazo baba mai gadi ya fada yana daukan tiyo yana Jan ruwa,
 Toh shikenan bari na koma baba, sai zuwa goben sallama sukayi labaran ya juya,

salima ce ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login