Showing 159001 words to 162000 words out of 381117 words

Chapter 54 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

1996

a cikin motar sai ita kadai gashi ta maqure sosai gefe guda jikin kofa saboda gefenta namiji ne, ga tafiyar a takure ake yin ta saboda yanayin motar, tunda ta janyo gaban wuyan hijab din ta ta rufe fiskanta bata bude ba Har suka fita daga garin abuja, ahankali ta fara jin faduwar gaban na sauka, runtse idanunta tayi Har barshi ya soma fusgarta don batayi wani barcin kirki ba kwata kwata,tafiya ce sukayi ta kusan awa daya dukda hanyar bata da kyau, ahaka driver nan ya dunga bin titin inda babu wasu mutane dake yawo Sai daji Sai kuma motoci dake wucewa.
Dammm taji gabanta ya fadi lokacin da mutanen cikin motar suka fara doka salati, babu abunda kake ji Sai innalillahi wa inna ilaihi rajiun, afurgice ta bude idanunta da sukayi jaa gabanta na faduwa don ganin abunda ke faruwa, tun daga nesa driver ya hango dandazon mutane a kwance amma dake dan tasha ne hakan bai da shi ya tsaya ba, tun kafin su kaiga karasawa daya daga cikin mutanen gaban motar yace  innalillahi jama a Mun shiga uku Yan kidnapping
Tassss sukayi karar bindiga nan take motar su ta fara juyi Har saida ta tsaya sakamakon tayar motar tasu data bayansu da aka harba, mutane ne gandama gandama hannayensu dauke da bindigu manya manya ak 47, ga mutane a gabansu kwance wasu cikin jini wasu kuma sun kwanta, yanda motarsu ta lula yasa ta buge kanta sosai harya dan soma jini, saida motar ta tsaya chak dan nesa da mutanen kafin mutane biyar daga cikin kidnapers su su karaso biyu suka tsaya wajen motar su amra uku suka wuce motar baya, mutane biyun nan na karasowa suka fara bude motar ta bangaren driver da amra dake gefenshi, tunda uwarta ta kawo ta duniya bata taba ganin tashin hankali irin na yau ba,  Ku fito wata irin murya mata dadin jii ta karade wajen, haka suka dunga futowa suna layi daya bayan daya amra dai suma ne kawai batayi ba don Har wani jiri jiri ke dibanta, haka aka taso su gaba, driver ne a gaban line din kafin ita abayanshi Sai mutumin dake gefenta, suna zuwa inda mutane ke kwance tsoro da furgici yasa ta kwala uwar kara, da sauri ogan cikin kidnappers din yazo gaban wajen su idanunshi jaa kamar garwashi fuskarshi ba kyan gani, yana zuwa baiyi wata wata ba ya fasa kan driver dake gabanta, wanwas driver din yayi baya kan jikinta, jini na malala sosai har kan fuskanta, da sauri ogan ya kalli kowa dake wajen yace  Duk wanda yayi yunkurin dogon nunfashi mai sauti wannan ne sakamakon shi
Haba wa da sauri amra ta damke Bakinta yanda driver dinnan ya zube haka ta zube wanwas kamar matacciya, ko motsin kirki bata yi, tsabar furgicin data shiga zuciyar ta ta kusa bugawa don kwata kwata nunfashin Ma dauke wa yayi gaba daya, tun bayan wannan abun daya faru bata kara sanin inda take ba don na bayanta Ma ya dauka itama mutuwar tayi.

Kamar daga sama suka fara jin karar helicopter na yawo a zarar yin samaniya don kamar an wullosu, da sauri ogan ya kalli gabas kafin ya cije lebenshi yace  an tarfo mu, kowa ya gudu
Haka suka dunga gudu, dayake mugaye ne haka suka dunga harbin mutane da suka mimmike don neman hanyar guduwa, tun daga sama sojajin suka so su fara Harbi ganin suna neman guduwa saidai babu hali don zasu iya hallaka mutane, haka sukayi landing wasu suka bi hanyar dajin da sukabi sauran kuma suka tsaya,tunda sukayi landing ya Kasa motsawa don tun daga sama ya hango yanda mutane ke kwance, asad ne daya rigada ya fita ya ga situation din wajen kafin yayi saurin tura health team da suke cikin daya daga cikin helicopters din don su duba masu taimakon gaggawa, mutane biyar ne kawai suka rasa rayukansu ciki Harda driver Sai kuma mace daya ta suke tunanin kamar zuciyarta ce ta kusa bugawa, asad baisan wacece amra ba don hotonta ya gani kawai, sannan cikin mutanen wajen bai kura da itaba don Har gaban inda take kwance bayan an daura ta kan emergency bed, dalilin hijab dinta dake kan fuskanta data jawo Har hancinta yasa bai Lura ba, takowa yayi har gaban Amar dake zaune fuskanshi tamm bazaka taba tantance a wani yanayi yake ciki ba, dago da rinannun idanunshi yayi yana kallon asad tare da sauraron bayanan shi  oga mutane biyar ne suka mutu, sauran mutane babu wanda ya samu rauni, Sai mace daya da Muna kyautata zaton kamar zuciyarta taso bugawa don Har yanxu she s not responding Muna bata taimakon gaggaw& .
Bai tsaya sauraron asad ba ya fito a gaggauce ya fara wucewa, mutane kamar sun san waye shi suka fara bashi hanya Duk tashin hankalin da suke ciki bai hana sun zuba mashi idanu ba ganin yanda yake tafiya cikin izza da qasaita.
Saida ya duba ko ina bai ganta ba, da sauri ya fara bin motocin wajen da kallo daya bayan daya kusan guda goma ajere, nan take idanunshi suka sauka kan motar driver da suka karbi number shi da plate number na motar tashi, dan waigowa yayi wajen mutanen dake zaune yace  waye driver motar nan
Daya daga cikin mazan da suke cikin motar ne yayi saurin cewa  yallabai gashi nan Akwance shima an kashe sa
Saurin runtse idanu yayi sosai yace  Duk wanda yake cikin motar ya miqe tsaye
Nan duka suka mike su kusan shida saidai babu amra a cikin su kuma baiyi tunanin itace matar da asad ke magana akai ba, wani irin zazafan numfashi ya sauke idanunshi sun sake yin wani jaaa sosai, ganin haka yasa asad saurin zuwa gabanshi ahankali cikin rada yace  I think bata cikin motar nan,
Kwata kwata baya Ma jinMaganar da asad ke mashi, saida ya dauka kusan minti ashirin kafin daya daga cikin health team tace  sir Mun samu pulse din wannan, I think she s alive
Dago da idanunshi yayi ya dubai matar kafin ya sauke idanun nashi kan matar da take magana akai, idanunshi ya bude sosai, ya kasa koda motsawa, tabbas hijab din da ya gani ne a jikinta lokacin data fito daga gidan ta cikin cctv camera, kamar zaki haka ya dunfaro wajen ya yaya chak ya kura mata idanu, jini Duk ya bata gaban hijab din nata, cikin sauri ya sa hannu ya zame hijab din daga Bakinta, yana yin arba da fuskar ya runtse idanunshi ya budesu sosai, ya kasa cewa komai ganin haka yasa asad shima matsowa Har inda take ya kafa mata idanu Sai a lokacin ya gane itace suke nema.
 Oga she s the one
Shuru asad yayi baice qala ba don kamar tunani yake kafin ya kalli health team din yace  what s her condition?
Da sauri wata soja budurwa ta kalleshi tace  she s stable sir, shock ne ya kamata wanda yasa zuciya ta ya kusa bugawa, she needs somewhere peacefuly da rest zata dawo daidai
Bai kalli budurwa ba ya sake tambaya  and this blood stain?
Da sauri daya daga cikin mutanen yace  Jinin driver ne don shi aka harba maimakon ita lokacin da tayi ihu
Nan take jini shi ya sake boiling inda Ana measuring zafin zuciya za a gane yanda yayi high sosai babu abunda yake fada aranshi sai  hmmm
Ya rasa mema zaiyi mata yaji dadi aranshi, zuciyar shi ta hasala sosai, yayi warning dinta bataji magananshi ba.
Kallon asad yayi yace  ka sa akawo available motoci daga kusa su tafi da mutanen nan inda zasuje,let s move with those that got injured
Asad najin haka yasan me yake nufi don haka yasa manyan sojoji guda goma su tsaya don kula da lafiyar mutanen wajen sauran waenda suka mutu aka debesu zuwa helicopter din health team, saida akazo tafiya da amra yace su dakata, nuni ya masu da su sakata a helicopter sun da yake, haka suka gurgura emergency bed din zuwa cikin helicopter din suka saka ta tare da likitoci biyu daga cikin health team, shi dai asad bai bisu ba ya tsaya tukunna saboda motocin da zasu zo su dauki mutanen wajen.
Tunda ya suka Tashi sama bai sake kallon ko inda take ba, saboda yanda yake jin wani zafi ganin yanayin da take ciki,tunanin yanda zaiyi dealing da ita yake yanda bazata sake tunanin taka umarnin daya bata ba, kamar wanda aka tsungula ya zaro wayanshi ya soma kira, yana gamawa ya kashe ya kira landline din gidan shi na larrics, Nadine dake zaune hankali tashe tayi picking call din kafin ta saka a kunnenta,  go and bring her few clothes and pack your belongings, damm gabanta ya fadi da jin abunda yace bata gama tunani ba ya cigaba,  driver will be waiting for you outside, come along with your passport
Yana kaiwa nan ya kashe wayar, da sauri ta miqe ta tattara kayanta Harda kukanta don tunaninta korar ta yayi saidai tayi mamakin jin yace driver na jiranta a waje, agurguje ta fito da yar jakar kayanta ta shige motar driver ya jasu,
Agaban headquarters driver ya dire ta, cikin Yan mintuna qalilan helicopter su ya dira a field din headquarters, ahankali ya soma saukowa kafin a sauko da amra wadda Har lokacin bata dawo hayyacinta ba, dan asibitin dake cikin headquarters aka wuce da ita aka cire mata kayan zuwa wasu wanda Nadine ta taho dashi kafin a mata allura don zuciyarta ta samu relive din shock din data shiga.
Takowa Nadine tayi Har gaban gadon da aka kwantar da ita ta kare mata kallo, fuskarta tayi fayau Har wani yar rama tayi, dukda bata san wani hali take ciki ba tausayinta ya gama dabaibaiye zuciyarta take tayi alqawarin koma menene damuwarta zata taimaka mata.
Manyan ambulance ne suka shigo cikin headquarter aciki aka saka ta tare da Nadine, kowa dake cikin headquarters saida ya shaida qila yar governor ce aka ceto ko kuma yar wani minister din, baibi motar ambulance ba ya shige cikin Tashi ya figi motar, wayarshi dake Kara yayi saurin picking yana dauka ya saka a hands free, daga chan baba garen aka soma magana  sir the visa is ready, and the private jet also
 Okay kawai yace ya kashe wayan kafin ya Kara ma motarshi speed sosai.
Agurguje dai saiga amra a airport ita da Nadine, dayake ya rigada yayi proceeding komai in less than an hour suna zuwa airports aka wuce dasu wajen private jet Har aka shige da amra wanda ke kwance kamar gawa, kallon Nadine yayi don shi bazai bisu ba tukunna saiya gama abunda ya kawo shi
 When you arrive my personal guard will be there to pick you up,
Kallon agogon shi yayi ya juya harzai tafi ya dawo yace  take care of her
Yana kaiwa nan ya fuce suna suka hau jirgin, abun mamaki Nadine na ganin jirgin tana an rubuta Taura baro baro, tasan sir yana bearing sunan saidai bata kawo ko nashi bane ko ba nashi bane saidai taga abunda ake kira da luxury lokacin da ta shiga cikin jet din gashi sak nan nan ake da su.
Bangaren Amar kuwa wata zuciyar nashi na mashi fadan yin hakan don yasan zai sha wahala idan bata kusa don ya fara sabama kanshi da abubuwan da Allah ya albarkaceta dashi, saidai kuma yana ganin wannan opportunity ne da zai tabbatar idan Har cikinshi ya shiga jikinta ko bai shiga ba bayan wannan plans dinshi da yake akanta na nan yanda ya tsara tun farko kafin ta dawo Nigeria.

Gida ya tafi direct don wani irin ciwon kai ne ya addabeshi sosai, yana zuwa ya wuce dakinshi ya watsa ruwa ya kwanta don ya samu ya danyi barci kozai ji saukin abunda yake ji, saidai kuma barcin gaba daya ya kaurace masa, tunanin da baya son yin ya tsaya mashi arai, zuciyar shi nayi mashi wani irin nauyi ganinta da yayi a wannan yanayi, runtse idanunshi yayi sosai aranshi yace  why won t you get out my mind
Tsaki ya danyi ya sake juyawa tare da kure ac din dakin ya janyo duvet Har ya samu barci ya nasarar daukanshi.

Dubai United Arab Emirates Uae Jet dinsu na sauka a uae international airport akayi masu Duk wani arrangement na shiga kasar ba tare da sun motsa ba, Nadine dai tana ganin rayuwar manya, don gaba daya ta gama tsurewa, Duk rayuwar a Cameroon bata taba shiga jet ba, amra dai tana daga chan wani bangare na cikin jet din da masu bata kulawa don Har lokacin bata farfado ba, minti bayar da landing din wata ambulance din ta karaso, m5 ne ya shigo Har cikin jet din ya jagoranci Nadine din suka sauka kasa zuwa motar dake harabar filin jirgin, iska ce mai dadi ke kadawa sosai. Ahankali aka saka amra cikin ambulance din itakuma Nadine ta shiga wata haddaiyar motar daban wanda m5 yazo da ita suka wuce gida tare da special doctor din Amar don shi zai kula da lafiyar amra.
Tafiyar minti talatin suka iso tafkeken penthouse din general Amar,inda tundaga shigarsu Nadine ta soma bama idanunta hakkinsa, tunda take harkar aiki wayo house keeping bata taba ganin gida makamancin wannan ba, Har m5 yayi parking bataji ba don ta Lula tunani, saida ya bude mata kofa kafin ta dawo hayyacinta ta fito daga cikin motar, already motar data shugo da amra tayi parking itama Har an sauko da ita daga cikin motar, m5 ne yayi gaba suka bishi abaya dukkansu, doorbell ya dannan pablo dake expecting dinsu yayi saurin budewa kafin su saka kai cikin main parlor din, Nadine dai ta zama kamar jaka don da kyar ta shiga cikin gidan, direct wurin suka wuce kafin m5 ya Danna floor 2 don nan ne masaukin su, fadar haduwa floor dinnan Ma bata lokaci ne don dakuna ne ajere Sai babban cozy sitting room tamkeke da yasha kayan duniya na gani na fada, babban dakin aka wuce da amra nan Ma ba a cewa komai Sai Masha Allah don an zuba duniya ba kadan ba, akan wani hadadden English bed aka kwantar da ita da taimakon nurse din dake tare da doctor din kafin su fara dubata don Har lokacin barci take sakamakon allurar da akayi mata.
A Last floor m5 ya nunama Nadine dakinta wanda yaci uwar na wanda aka bata a larrics don itama harda dan coffee table and chairs aka aje mata da tv Sai tamkeken bed dinta..
[7/11, 11:17 PM] +218 92-2035171: Update
Unedited page
Bai dawo gidan ba saida ya tsaya akayi sallar isha I dashi kafin ya shugo gidan, lokacin daya shigo main sitting room babu kowa a kasan don haka ya wuce bedroom dinshi direct don hes not in a good mood.
Bangaren amra tun bayan fitar ammah wani irin zazzabi ya rufeta, babu wanda yasan da situation din da take ciki, don ko sallar magrib kasa tashi tayi don ta samu tayi, tana nan kudundine cikin blanket akayi knocking kafin a shugo, lantana ce ta shigo hannunta dauke da tray da ammah ta zubama amra abinci, da sallama ta karaso dakin ta aje a kasan carpet, ganin amra a duqunqune tana rawar sanyi yasa ta karaso gaban gadon tace   anty baki da lafiya ne?  kasa Magana amra tayi don gaba daya ta zama very weak, sai karkarwa da jikinta keyi, ganin haka yasa lantana fucewa daga dakin zuwa part din ammah, da sallama ta shiga sitting room din ammah don bata shiga cikin bedroom dinta kai tsaye, tundaga bedroom ammah taji sallamanta don haka tace   shugo 
Ahankali lantana ta bude bedroom din ta shugo daga bakin kofa ta tsaya tace   hajiya nakaima bakuwar abunci saidai na ga kamar bata jin dadi, 
Ammah dake zaune gaban dresser ta juyo ta kalli lantana tace   subhanallah, bari nazo dakin 
Futa lantana tayi ammah ma ta miqe tabi bayanta, amar dake shirin hawowa part din yana ganin ammah da yanda ta rude yayi saurin kallon inda take shirin shiga,ammah ma bata lura dashi ba don yana tsaye wajen stairs, dakin amra ta shige direct cikin sassarfa, lanatana na biye da ita,kai tsaye gaban gadon ammah ta tsaya ganin yanda amra take rawar sanyi, idanunta na neman rufewa, hankali atashe tace   daughter meke damunki subhanallah  tallafota ammah tayi ta janye duvet din data qanqame a jikinta kallon lantana ammah tayi tace   jeki dubamin ko Muhammad ya dawo akaita asibiti 
Lanatana na juyawa don kiranshi sai gashi ya shugo dakin shima kai tsaye, sanye yake da doguwan jellabiya fara har kasa, hannunshi cikin aljihun rigar ya zuba masu idanu, juyowa ammah tayi ganin shi tsaye tace   yaka tsaya anan, shugo mana ka dauketa Mukai ta asibiti 
Kasa daga kafafunshi yayi, ranshi ya a dagule, ganin ya tsaya kyam ya qi motsawa yasa ammah juyowa ta kalleshi tace   muhammad? Kana jina kuwa 
Anatse ya bude baki yace   I will call doctor yazo ya dubata  yana kaiwa nan ya janyo wayarshi yayi dialing contact din family doctor dinsu, doctor na daga ya fuce daga dakin.
Kauda kai kawai ammah tayi tana mamakin hali irin nashi, me Kenan yake nufi? Badai yana kan bakarshi na sakin yarinyar ba, tasan shi da kafewa akan abu saidai wannan karan zata nuna mashi ta isa dashi don ita ta haife shi bashi ya haifeta ba, kallon lanatana ammah ta sakeyi hannunta rike dana amra dake karkarwa   shiga bathroom ki kawo min luke warm water da towel 
  toh hajiya  lanatana ta fada tare da shigewa bathroom din dakin, agurguje ta debo ruwa a cikin bowl da towel ta karaso gaban ammah tare da dukawa, karwan towel din ammah tayi ta jiqashi kafin ta fara gogama amra a fuskanta da wuyanta,ta dae sosai akan amra tana shafa mata ruwan don taji dadin jikinta saidai kamar ma kara mata zazzabin akeyi don jikin yayi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login