Showing 240001 words to 243000 words out of 381117 words

Chapter 81 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

2043

wayar ammah ta sake shigowa, saurin dagawa yayi yace  ammah gani nan na iso,
Kashe wayar tayi tana kallon amra dake faman kelayar da amai, ta kasa cin komai, avocado dinma ta cinye shi tass tana neman kari gashi babu.
Cikin minti biyu sai gashi ya shugo cikin sitting room security s na biye dashi da da ledoji, anan parlor ya basu umarnin ajiyewa, nan suka jera komai anan parlor, ammah ne ta fara saukowa kasan bayan ta ajiye wayarshi don tabbatarda ko ya dawo, kallon ledojin da ake ta shugowa dasu tayi kafin ta maida kallonta kan Amar, karasa takowa tayi parlorn ta tsaya daga nesa ta kalleshi  Muhammad wannan fah?
Kanshi a kasa ya amsata  abubuwan ne
Sakin baki ammah tayi tana kallonshi tana kallon ledojin,  yanxu son Ina zata shanye wannan abun duka?
Sunkuyar da kanshi ya sake yi yama rasa mai zaice  daman na sayo da yawa ne saboda bansan ya ake amfani dasu ba, and I thought maybe zata buqata nan gaba
 Fruits ne fah? Zasu iya lalacewa yanxu ina zamu kai wannan
Yar tsuka kawai ammah tayi ta soma bude ledojin, saida ta bude duka tace  ya banga dataa ba?
 Ammah Wallahi babu na duba ban samu ba
Ya fada ranshi a hade kamar an sashi dole, dukda kanshi na kasa,  Ay kuwa saika nemo shi Wallahi, kaje wannan dinma yayi
Tana kaiwa nan ta deba ko wanne guda biyar ta wuce dashi kitchen, nan ta zuba su cikin sink ta wanke mata su tass kafin ta yanka mata yanda zataji dadin sha, yana nan tsaye ammah ta fito hannunta rike da tray harta wuce sama batabi ta kanshi ba, shiko binta yayi da idanu yana mamakin abubuwan da suke wanzuwa.
Kasa daga kafafunshi yayi har saida ta bace mashi daga gani kafun ya dan cije lebe nshi ya wuce bedroom dinshi don watsa ruwa.

Ammah na hawa sama dakinta ta wuce direct inda ta tadda amra harta koma wani barcin wahalar, cikin tausayinta ammah ta kalleta, ciki, haihuwa,goyo , ba abu bane mai sauqi ko kadan shiyasa take tausayinta sosai, Nunfasawa tayi kafin ta karaso bakin gadon ta ajiye mata tray sun kan gado, anatse ta soma tashinta  daughter daughter
Bude jajayen idanu ta tayi da suka koma ciki sosai, ramar datayi ta futo sosai a fuskanta,  sorry dear gashi an kawo maki ammah ta fada cikin lallami
Ahankali ta soma gyara kwanciyar ta mike tana cije lebe,  sannu dear it s not easy, allah ya raba lafiya kasa dagowa amra tayi kanta a kasa, turo mata tray din ammah tayi gabanta  gashi nan an kawo daughter
Cikin sauri ta dago idanunta ta sauke su akan tray din, da sauri takai hannu ta dauki agwaluma hannunta Har yana karkarwa takai Bakinta ta soma sha, har wani lumshe idanu take yi na samun abun da take so, she has been craving for it sosai, saida ta shanye kusna uku kafin ta ajiye ta dauka kwakwa, guda daya kawia taci ta ajiye ta janyo yalo, haka ta dunga ci hannu baka hannu kwarya, saida tasha da yawa ta ture,  ya isheki daughter? Ammah ta tambayeta,  eh, Nagode ammah
 Alhamdulillah bari na ajiye maki, Akwai wani abun da kikeso again? Girgiza mata kai kawia amra tayi tana lumshe idanu saboda barcin da bai gama sakinta ba , ammah na Ganin haka tace  shikenan dear kwanta abinki
Kwanciya amra tayi ammah ta janyo mata duvet kafin ta fuce da sauran zuwa kasa, tana sauka salima na dawowa daga school agajiye, tundaga bakin stair ammah tace  yarinyar kirki Har an dawo
Hammar gajiya salima tayi ta kalleta tace  barka da rana ammah na, Wallahi yau nasha wahala,maths mukayi and it s so hard but Alhamdulillah
Karasowa inda take tsaye ammah tayi tace  sannu dear, Allah ya taimaka, kije kiyi wanka saiki sauko ki diba abunci
 Tohm ammah na, yau adda ta barki da aiki ke kadai ko? Ni na kasa gane wani irin barci ne wannan takeyi kullum
Murmushi kawai ammah tayi kafin ta juya zuwa kitchen da tray din hannunta  yarinyar kirki basai surutu ba, Ina ruwan Ki da barcin ta
Tabe baki salima tayi cikin shagwaba tabi bayan ammah tace  Toh Ay ammah barcin ne ya wuce normal barci wannan, Allah ya kamata take asibiti a duba ta
Ajiye tray din ammah tayi a gefen kitchen island kafin ta maida duba ta ga salima  Toh naji, kije ki wanka saiki sauko kici abunci
 Tohm ammah,
Juyawa salima tayi ta fuce daga kitchen din.


Amra bata Tashi ba sai wajen karfe biyar na yamma, tana mikewa zaune ammah ta shugo dakin, gefen inda yake zaune ta zauna tana kallon ta fuskanta dauke fa murmushi  daughter kin Tashi? Ya jikin? Daman yanxu nake shirin zuwa na tasheki kiyi sallah
Muryanta a kasa tace  Alhamdulillah da sauqi ammah, bari naje daki
Miqew amra tayi ta fuce daga dakin, tana fitowa taci karo da amar, bata ma dago ta kalleshi ba kanta a kasa ta wuce daki don wani jiri jiri take ji, shiko saida ya tsaya ya kare mata kallo, fuskanshi tam babu fara a,harta shige daki bai daina kallonta ba yana waya tunani.
Yar tsuka yayi kafin ya wuce dakin ammah.
Yana shiga ya same ta a zaune, hira suka danyi inda ta tambayeshi maganar Gyaran gidan nan ya nuna mata abubuwan daya sauya na gidan, ba karamin dadi ya gani a tattare da ita ba lokacin da yake nuna mata abubuwan,  Allah yayi albarka son, gida yayi kyau sosai, Allah ya saka da alkairi
Da mamaki ya dago yana kallonta jin yanda take zabga mashi godiya sosai,baice komai ba sai sauke kanshi da yayi kasa.
 Asad zaizo anjima, bai samu zuwa dubiya ba kwanaki saboda ayyukan da mukeyi tare
Kallonshi ammah tayi fuskanta dauke da murmushi don batayi tunanin suna zumunci sosai ba kamar yanda iyayensu sukayi,  Masha Allah asad dan gidan Alhaji abdallah abokin marigayi?
Girgiza mata kai amar yayi yace  uhm shi
 Ahh to Masha Allah, Allah ya kaimu
 Ameen ya amsa kai tsaye

Kallon agogon dake maqale a bango ammah tayi kafin ta miqe  Bari na dubo daughter ko zata buqaci wani abun
Tana kaiwa nan ta fuce daga dakin ta barci a zaune sakeke.
Ammah na futa daga bedroom dinta dakin amra ta wuce, a zaune ta taddata ta hada kai da gwiwa, saurin karasowa inda take zaune kan sallayan ammah tayi kafin Tayi saurin miqa da ita  daughter Yadai? Ko zamuje asibiti? Akwai abund ake damunki?
Ammah ta jero mata tambayoyin, fuskanta dauke da damuwa don saida ta dagata taga yanda idanun ta yayi jaa sosai alamun kukan da tayi, hankali atashe ammah ta riko hannunta ta zaunar da ita bakin gadon tace  muje asibiti ne dear?
Kanta a kasa ta kasa dagowa ta kalli ammah, ah ah basai munje ba kaina ne ke dan ciwo
 Subhanallah Allah ya sawaqe, now tell me me kikeso kici ko akawo su agwaluman ne?
 Wainar fulawa amra ta fada anatse jiki a mace, kanta a kasa
 Tohm Bari ayi maki,Kinsha magani kuwa?
 Ah ah ban sha ba ammah, amai yake saka ni amra ta amsata
 Daughter haka zakiyi hakuri kina sha saboda ki samu kuzari keda babyn okay?
 Tohm amra ta amsata kanta a kasa.
Mikewa ammah tayi ta fuce daga dakin ta sauka kasa, nan ta tarar da salima tana diban abunci a kitchen, kallonta ammah tayi tace  Har an sauko ni kam Ina Salim ne?
 yana chan yana game,Ay Wallahi Saina fada ma ya Muhammad ya kwace game din ammah, dariya ammah tayi tana kokarin diban flour tace  ki kyaleshi ya huta, anyi hutu ay
Kallonta salima tayi Ganin tana kwaba kulli  Ammah ne zakiyi? Kawo nayi maki
 No dear kici abunci, kafun ki gama ma na soya mata daughter ke son cin wainan flour ammah ta fada
Ajiye abuncin salima tayi tace  Toh fa yanxu kuma har wahalar dake takeyi ammah, hmm nidai Wallahi ammah Kin fison adda Wallahi,
Dariya ammah tayi ta kalleta  inason ku duka kowa da irin son da nake mashi, kinga bata jin dadi shiyasa dole na tausaya mata

Turo baki salima tayi ta karbi kulli tace  shikenan Ay, kawo nayi Wallahi bazan iya tsayawa ina Ganin kina aiki ba, daman bana jin wani yunwa sosai, kawo nayi
Karba salima tayi ta karasa hada komai kafin ta fara so yawa ammah na tsaye harta gama soyawa tass daman bashi da wani yawa don baifi guda uku ba, tana gamawa ta zuba akan plate tace  bari na kai mata
Tana kaiwa nan ta fuce ta wuce sama zuwa dakin amra.

Da sallama salima ta shiga dakin, ahanakli amra dake jingine bakin gado, har lokacin towle ne a jikinta ta amsa mata sallaman da tayi.
Karasowa cikin dakin salima tayi hannunta duake da plate din wainar, zama tayi gefen amra kafin ta ajiye plate din a gefenta  barka da yamma addah ya jiki? Ammah tace bakya jin dadi
Dan dagowa mara tayi kafun ta kauda kanta gefe jin turaren dake Tashi daga jikinta na danunta tace  Alhamdulillah!!, kije bana son wannan scent din
Da mamaki salima ta mike tsaye tana kallonta tana wani nazari, dukda tana da kananun shekaru hakan baisa ta Lura da changes a tattare da yar uwar Tata ba  kije banson scent dinki pleas
Da sauri salima ta mike ta fuce daga dakin, tana futa ta mike ta wuce bathroom a guje tana kelayar da amai m, saida ta fidda komai kafin ta dawo agalabaice, kallon wainar tayi, ranta naso saidai tana tsoron amai, haka nan ta janyo plate din ta tsakuri kadan ta kai bakinta, haka ta dunga tsakura tana ci tana tsoron amai harta ci guda daya kafin ta ture plate din ta kwanta kafin a kira Sallar magrib.
Tunda ta kwanta take juye juye don ta hana kanta yin barcin.

Salima na fitowa ta sauko kasa zuwa kitchen lokcakin ammah ta wuce bedroom dinta, abuncin data ajiye ta dauka kafin ta koma sitting room ta kunna tv ta fara kallo.

Tana nan zaune Har aka kira sallan magrib tana kallo saboda she s off bata sallah.
Kitchen ta mike ta wuce ta Dora simple dinner, stir fry noodles, saida ta gama ta jera akan dining kafin ta dawo parlor ta cigaba da kallonta

Ahankali yake takowa bayan ya hangota daga nesa don daga masjid yake, a bayanta ya ya tsaya ya sauke kanshi saurin kunnenta daga bayan kujeran murya shi chan kasa ya soma magana  my beautiful wifey to be
Da mamaki salima ta juyo don ta tsorata kafun ta dan turo baki  haba yaya Ka bani tsoro
Zagayowa yayi ya zauna gefenta  sorry baby kinyi sallah?
Sunkuyar da kanta kasa tayi ta kasa cewa komai  uhm I guess mun tafi off kenan,
Saurin rufe fuskanta tayi tana jin kunya, hira suka shiga yi ta masoya anan zaune.

Ammah ne ta sauko fuskanta dauke da murmushi ta kallesu  son abarmin yarinya haka Kar a cikata da surutun karya na sama din zamani
Dariya ya danyi yace  barka da dare ammah
 Barka my dear, karasowa parlor tayi ta zauna, nan suka shiga hira gaba dayansu anan zaune.

Karfe takwas daidai saiga Amar ya shugo shida asad don, da sallama suka shugo atare, har zuwa parlor, su ammah dake zaune ne suka amsa sallamansu, kallonsu ammah tayi fuskanta dauke da murmushi tace  lale maraba yau PA alhaji ne a gidan namu
Saurin sunkuyar da kai asad yayi don baiyi tunanin zata tuna da sunan ba saboda sunan ne dada ke kiranshi dashi Duk sanda suka zo gidan..
Karasowa sukayi, Har kasa asad ya tsugunna ya gaisheta, da fara a ta amsashi tana tambayar mutanen gida da hajiyarsa.
Amar na daga zaune ya hakimce ya Dora kafa daya kan daya, salima ce Tayi saurin dukawa ta gaisheda da asad, kallonta tayi fuskanshi duake da murmushi ya amsa, maida kallonta tayi ga amar shima ta gaishesa, fuskannan Tashi a hade ya amsa ta.
 Kunzo a daidai, bari a kawo dinner
Da sauri asad yace  Wallahi hajiya akan hanya nake, daman ayyuka ne sukayi min yawa shiyasa ban samu nazo ba
 Ahh Toh ko dan lemo Ay Ka tsaya kasha ammah ta fada tana murmushi kafin ta maida kallonta ga salima,  yarinyar kirki a kawo ma baqo juice ko
Mikewa salima tayi ta fuce daga parlor asad ya bita da kallo wanda Aman ya ga hakan, take ranshi yadan sosu saidai bai nuna ba harta dawo da tray a hannunta, serving dinshi ta fara yi kafin ta miqa mashi.
Godiya ya mata in a calming tone kafin ya karba yana mata wani irin kallo mai wuyar fasaara da alamu dai asad ya kamu.

Saida ya gama sha yace  Alhamdulillah Zan wuce hajiya Allah ya Kara lafiya
 Tun yanzu PA? Baka tsaya Kun gaisa da matan abokin naka bama bari a kirata
Da mamaki asad ya kalli Amar daya hade rai yana latsa waya Har lokacin baice qala ba,

Kallon salima ammah tayi tace  Kira min daughter
Mikewa tayi asad ya sake binta da kallo harta wuce sama, tana zuwa ga taddata zaune kan sallaya ta idar da sallar isha I, daga nesa salima ta tsaya ta soma magana  adda kizo inji ammah
 Okay amra ta fada jiki a mace, saida ta dauka kusan minti biyu kafin ta mike tabi bayanta don harta fuce.

Anatse ta futo sanye take da dogon hijab har kasa don towel ne kawai a jikinta, gaba daya dagowa sukayi suna kallonta harta sauko Banda amar da asad, tana karasowa ta gamsu zazzaune,  ammah gani
Ta fada muryanta a kasa don bata tsaya ta tantance su waye a parlorn ba,
Dagowa asad yayi ya kalleta, kasa dauke idanunshi yayi akanta, yana tunanin inda ya santa, aranshi babu abunda yake furtawa sai  waiii perfect match
Ammah ce ta danyi Gyaran murya  daughter ga abokin mijinki,
Dagowa ta danyi suka hada ido kafin ta sauke  Ina wuni
 La..fi..ya.. ya amsa ararrbe
Saurin dagowa amar yayi don haka kawai yaji yana son ya dago, kallon Ind a take tsaye yayi kafin ya maida kallonshi ga asad, Ganin yanda ya kureta da idanu yasa yaji wani irin abu ya taaya mashi a maqoshi sa [7/11, 11:17 PM] +218 92-2035171: Update!!
Unedited page&
Wajen karfe uku na dare ya farka saboda wani irin zafi dayaji a jikinsa lokaci guda, bude rinannun idanunshi yayi ya sauke su akanta, ta maqalqaleshi gaba dayanta ta sauke mashi nauyin jikinta tana rawar sanyi, ga wani irin turirin zafi dake fita daga jikinta, saurin lumshe idanunshi ya sakeyi yi ya budesu tarr akanta sosai bakinta na gab da nashi lebanta na karkarwa sosai, saurin mikewa yayi zaune ya gyara zamanshi ya kalleta da kyau saboda akwai hasken bedside lamb dake a kunne, kyawawan ya zubama idanu inda wasu siraran hawaye ke zarya akan fuskan nata, saurin taba wuyanta yayi ganin yanda ta fara kafewa bakinta har lokacin yana karkarwa sosai, wani irin zafi yaji daya sashi saurin cire hannunshi   shes burning up  ya fada ahankali yana kallon fuskanta, saurin janyeta yayi daga jikinshi ya mike tsaye yama rasa abunda zaiyi don ya mata taimakon gaggawa, tunawa da yanda ammah ke mashi lokacin da yake karami yayi don haka ya wuce bathroom ya jiko hand towel kafin ya dawo gefen gadon ya zauna ya soma goga mata a fuskanta.
jikinta ne ya tsananta don har lokacin he can feel yanda take sauke nunfashi mai zafi sosai akan hannunshi, last option daya yake dashi wajen taimaka, kamar bazaiyi ba don yasan zaiyi affecting dinshi sosai, saidai ganin yanda take rawar sanyi ya sashi jin wani iri don haka ya mike tsaye ya kashe ac dakin ya wuce ciki closet ya dauko babban duvet mai nauyi sosai ya sauya da dayan, yanda yake yin komai a gaggauce zaka gane hankalinshi a tashe yake.
Yana nan tsaye yana nazari kamar ana fusganshi haka ya soma zame kayan jikinshi ya rage daga shi sai dogon wando pjs dinshi.
Ahankali ya hau kan gadon ya zauna kafin ya janyota jikinshi ya soma zame kayan jikinta, saida ya cire kayan barcin nata gaba daya kafin ya hade jikinshi waje daya ya rungumota, wani irin shock ya soma ji saboda yanda fatar jikinta ke gogar nashi don babu bra kwatkwata jikinta, runtse idanu kawai yakeyi jikinshi na vibrating saboda kusanci yayi yawa sosai, janyo duvet din yayi ya rufa masu gaba dayansu tundaga sama har kasa har lokacin tana cikin jikinshi tayi lamo.
Ahankali zafin jikin nata ke transferring zuwa jikinshi don shi temperation dinshi is normal, shida idanunshi suke a bude kuma yana cikin hayyacinshi shi kadai yasan irin connection din da zuciyoyinsu suka shiga, don heart beat dinsu kusan a tare suke bugawa, at the point ya tabbatar zuciyarshi is beating for her don kwata kwata ba haka zuciyarshi ke bugawa ba,
Bakinshi ya maotso saitin kunnenta ya soma karanto mata addu oin samun sauki harta daina rawar darin da takeyi nunfashinta na sauka ahankali akan kirjinshi da gashi ke kwance akai.

Har aka kira sallar asuba bai runtsa ba ko kadan yana maqale da ita, sallar ma bai samu yayi ba don sai a lokacin barci ya fusgeshi saboda wani matsanancin ciwon kai daya fara kawo mashi ziyara.

Amra dai bata san wainar da yake toyawa ba saidai daren ranar taji wani irin sanyi a zuciyarta, daman duk dare saitayi wannan zazzabin wanda ayanxu ya zaman mata jiki don duk dare saitayi.

Basu suka tash ba sai wajen karfe goma na safiya, amra ce ta fara bude idanunta saboda wata irin yunwa data nuqurqusota, saurin bude idanunta tayi ganin duhu duhu yasa tadan razana don


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login