Showing 336001 words to 339000 words out of 381117 words

Chapter 113 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

2056

ba laifi don yanxu kana ganinta kasan tana da ciki, yanxu cikinta watan shi bakwai da sati guda.

Shugowa tayi dakin atsanake ta karaso Ind ammah ke zaune Har zata zauna a kasa ammah ta kalleta jiki a mace kana ganinta kasan tana cikin damuwa sosai  haba daughter, baba hanaki zaman kasa ba yanda kika fara nauyin nan
Murmushi amra ta danyi kafin ta zauna gefen gado ta gaisheta, cikin fara a ammah ta amsa mata. Shuru ne ya buyo baya kafin amra ta soma magana  ammah, Akwai abund ake damunki ne?
Shuru ammah tayi kafin ta nunfasa  babu komi daughter,kinci abunci?
 Eh naci tuwo amra ta bata amsa
 Ammah please Ki fada min abunda ke damun ki, bakya cikin walwala kwanakin nan
Kallonta ammah ta danyi baya son ta saka mata damuwa don haka tace  daughter yau wata guda kenan rabon da na samu son a waya, wayarshi baya shiga kwata kwata, Ina jin kamar wani abu ya faru
Hannunta amra ta kama kafin ta soma magana in a calming tone  ammah ki kwantar da hankalin ki, nasan he s perfectly fine Insha Allah, maybe Har yanxu basu gama operation sun bane shiyasa bakya samunshi a waya

Haka amra ta dunga tausasa ta da kalamai masu kwantar da hankali harta danji nauyin da zuciyarta keyi ya ragu, hira suka danyi don yanxu inka gansu kamar uwa da ya babu wani kunya, amra ta sake sosai da ita.

Washe gari suka shirya da ammah da salima da amra suka wuce asibiti don salima tace Yanxu dole da ita za a dunga hidiman baby, suna zuwa doctor ya duba lafiyar baby Har alokacin ammah taki yarda Suga gender na baby don haka doctor ya bata magungunan Karin jini da wanda zai dunga sakata cin abunci don zatafi buqatan hakan ayanxu don ta kusa shiga wata takwas wanda ya zamana anzo gangara.


Bari mu Yan katsina& .
Duniya ta juyama wannan family baya, yanxu taluacin da suke ciki haryaci uwar na da saboda da khady kawai suka dogara da take saida gwanjo itama ribar yanxu tayi kasa saboda hidiman gidan daya dawo hannunta dukda ba wani kudin arziki take fiddawa ba idan zasuyi cefane kullum, dari biyar ce safe da dare don ba a cin abuncin rana a gidan, dady kuwa tun bayan wannan targade da yayi har kayi mashi gyara a hannu da kafa, inda a hannunshi samu karaya while kafar kuwa ya samu targade, Toh da dai gyaran karayan nan baiyi ba kafarcema ya dan samu sauqi saidai hannun ne ya shanye gaba daya baya wani amfanuwa, sai kuma jan ruwa da yakeyi saboda inda ya ciwo wajen hannun ba a yi dressing ba haka gudaje da bad environment din wajen yayi affecting hannun, nan ya dunga Jan ruwa sai wani karshe dai hannun shanyewa tayi babu wani amfani.
Haka kullum zai zauna a gida baya uban komai, tun kareema na jin tsoro shi lokacin daya gano tana da cikin shege har tazo ta daina tsoronsa take gasa mashi aya a hannu, zagi cin mutunci babu wanda basa yima juna agaban yayansu, yaranma Har sun saba da yanda iyayensu keyi ma junansu, ah anguwa kuwa babu wanda baisan kareema matar mustapha mai damfara nada cikin shege ba, tayi cikin shege da aurenta, wannan zance yasa ko fita bata iyayi yaranma idan sun futa da irin zagin da ake jifansu dashi kenan, khady dai ta gama zama yar tasha idan ma an fada bata wani damuwa don Har cewa take  Toh saime idan tayi cikin shegen idan uwar wani ce Tayi ku fada min badai tawa uwar bace to munji tayi ciki
Yanda ta zama yar daba daba yasa wasu idan sunso goga mata magana suke kyale ta saboda kangararren saurayin ta.

Bangaren wahab yana chan a kurkuku don asad saida ya tabbatar an yanke mashi hukunci daidai da abunda yayi, nan aka kaishi prison na shekara goma,don Akwai diyyar daya kamata ya biya wanda yayi ma yarinyar maqocinshi na chan lagos fyade inda aka tuntubi iyayenshi ko zasu iya biya don in ba a biya ba shekarun da zaiyi a prison zai karu, nan aka tuntubi Alhaji mustapha, lokacin da suka kirashi ma yana gida a zaune babu uban abunda yake sai zaman banza don haka da sukayi mashi bayani nan take yace  ku rufeshi kawai babu abunda zaku samu a waje na
Yana kaiwa nan ya kashe wayar baima tsaya sauraron su ba, da kareema ta tambayi ko da wa yake waya kai tsaye ya mata bayani, nan take ta dunga kuka tana tsine daddy kan Duk shine ya janyo masu wannan masifa Har yayanta suka wulaqanta gaba daya saboda zalumcin shi da cin amanar dan uwansa da yayi na wulaqanta yayansa.
Nan suka dunga Sarfa ma junan su zagi ta uwa ta uba  kije kiji da shegen ciki wahallaiya asararriyar mata Wallahi nayi dana sanin aurenki kareema kina da kaso mai girma a cikin lalata rayuwata kece ma baqar kafar data lalata kin komai, badan kin sa an zubar da waennan yarannan ba da tuni na samu wani abun a wajen yayarsu
Kallonshi karima tayi tana takaici ace Wai mutun baiyi nadama ba ko kadan,  shiyasa zaka kare a haka a wulaqance, Har yanxu zuciyarka a mace take
Nan suka cigaba da cece kucensu dagashi Har ita aka rasa wanda zai jaa baki yayi shuru maqota na jin su.

Bangaren Muhammad kuwa yana chan Australia, yau watanshi biyar kenan, acahn yaqi dawowa don daddy s ya kirashi ya shaida mashi uwarshi tayi cikin shege don haka ya tura masu da kudi, ranar da yaji wannan baqin labari ya shiga tashin hankali sosai inda ya ko sun kirashi ma kasa daukan wayan yakeyi don yana Allah wadai da iyaye nashi, wannan yasa yaqi dawowa yayi zamansa acahn ya maida hankali wajen aikin shi inda yake taimakawa kaninshi ishaq daya dage yana masters dinshi anan Australia don bayan ya gama karatu ya dawo wajen Muhammad nan ya muyi sponsoring dinshi ya samu schorlaship nan ya fara masters.

Bangaren kakarsu salima kuwa, rana daya Allah ya dauki ranta anan kauye inda take zaune wajen dan uwanta, tayi jinya sosai inda suka dunga bata maganin gargajiya da farko kamar komai ya lafa sai daga baya kuma gadan gadan ciwon nata ya dawo Har Allah ya dauki ranta bata samu damar Ganin marayun jikokinta ba.

Bangaren labaran shima bayan noma haka ya samu yayi renting wani kanti nan kusa da inda yake yake haya, nan yayi amfani da kudin da ammah ta bashi ya zuba provision a cikin shagon don bashi da wani girma sosai, cikin wata biyu wajen ya bun kasa don haka ya hade da shagon dake kusa dan wanda yake haka, cikin ikon Allah Allah ya by kasa mashi, don Allah ya bashi wannan baiwar da zarar ya saka hannu akan abu sai Allah ya bukata mashi, kullum kuwa saiyayi mafarkin yarannan guda uku ada chan baya yana mafarkinsu baya Ganin fuskokoinsu saidai shadow dinsu kuma yana jin saurin kukansu Yanxu kuwa yakan iya ganin su a fili saidai Har yau baiga fuskokinsu ba saidai yaji su suna dariya.
Bayan wannan Har yanxu zane kam yana. Yin shi, don idan ya dauka alakali yana Zane kamar wani pro nan ya gane cewa yayi ilimi don saida ilimi zaka iya zane irin wannan da ake kira da architecture.
Abunda yafi daga mashi hankali kuwa shine Akwai ranar da yazo tsallaka titi bayan ya dawo daga shago, nan take wata mota taso bugeshi Allah ya rufa asiri mutumin ya Taka burki nan take flashback din wani mummunan accident yazo mashi, inda anan ya gane lokacin da yayi accident ne kenan, everything was dark don haka bai gane komai ba.

Alhaji kabiru dai Ana chan prison shima an kaishi gidan yari inda zai gama rayuwar shi acahn gaba daya, irin dukan dasu asad sukayi mashi yasa yayi loosing site dinshi daya, ya rame ya jeme ya zama kamar wani mai kanjamau, talking of kanjamau lokacin da yayi wata irin rashin lafiya anan prison aka kaishi asibiti nan akayi mashi test take kuwa aka gano yana da hiv.
Haka aka sallamoshi bayan ya danji sauqi aka maidashi prison aka rufe shi, Har lokacin he can t imagine rayuwarshi zata juya ta zama haka ba, ya zama kaskantacce, ya lalace kuma naka sasshe bashida kowa bashida komai, dukiyar daya tara ta hanyar haramci bata amfaneshi da komai ba saima jefa shi cikin mawuyacin hali datayi.
Aman Duk wata yana zuwa nan prison yana dubashi, wani sa in yakan futo ya ganshi wani sa in kuwa haka zai Karaci zamanshi daddy yaqi futowa don yanxu blaming dinshi yake yi akan cewa ya cuceshi yana matsayin ubanshi ya fallasa asirin sa.

Su lantaana da doctor ma ana chan ana serving a gidan yari, kowannensu an bashi shekara biyar for attempting murder.



Abuja Nigeria& &
After 2 months&
Yau wata biyu kenan da tafiyar Amar, Har ranar dai shuru babu labarinshi, at this point hankalin ammah ya gama Tashi don haka ta fara neman manyan mutane da ta sani acahn dubai en, shuru dai Har lokacin don haka ta fara tunanin zuwa dubai din saidai kuma tunawa da amra tayi nauyi yanxu yasa tayi cancelling tafiyar.

***
Ammah ce zaune a sitting room hannunta rike da charbi tana lazimi gefenta Salim ne dake ta faman yin game a wayar Salima don batama san ya dauko ba tana barci.

Ahankali ta soma saukowa tana dingisawa harta sauko daga stair tana nishi, amra ce sanye da doguwar rigar chan iska wadda ammah ta sayo mata su da yawa saboda ta dunga sakewa a cikin rigar, saurin nishin da takeyi ne yasa ammah ta kalli inda take tsaye bayan ta sauko kasan, murmushi kawai ammah takeyi harta karaso parlor, kallonta ammah tayi da yanda yake tafiya, cikinta ya futo sosai kamar mai wadda zata haihu yau ko gobe, daman doctor ya fada masu cewa da zarar takai wata takwas cikin nata zai bude, yanxu kuwa cikin nata yakai 8months da sati daya, cikin ya futo sosai kuma yayi mata kyau sosai, ta Kara fresh da kyau kamar bamai ciki ba babu wannan kumburu fuska da na hanci, dass dass abunta.
 Wash barka da yamma ammah ta karashe tana zama gefen kujera mai zaman mutun biyu
 Sannu daughter kina kokari, wannan babyn namu tubarkallah
Dariya amra ta danyi kafin ta kalli inda Salim yake tace  kai kuma baka daddara ba ko, saita sauko ta mammake zaka daina daukan mata wannan wayar yar gold din
Dan murmusawa ammah tayi tana kallonsu.
Salima ce ta sauko rai a bace Har tana grade kafafunta daga stairs, tana karasowa parlorn tayo kan salim,  kai Ka gama rainani ko? Toh Wallahi yau Saina koya maka hankali
Tana kaiwa nan tayo kanshi, ammah ne Tayi saurin hanata  haba yarinyar kirki, yi hkui bazai sake ba kinji
 Ki barta ta bugeshi ammah tunda baya ji, haka ya lalata min yawa Yanxu kwata kwata idan an kirani baba jin kara amra ta fada tana kallonsu
 Ah ah baza ayi haka ba daughter karban wayar ammah tayi daga hannunshi kafin ta mikama salima  ungo yarinyar kirki yaci albarkaci na
Dungure kanshi salima tayi kafin ta karbi wayar, alokacin call din Aman ya shigo don haka ta wuce sama abunta tana murmushi.
Kallonta amra tayi da yanda jikinta ya dau zumudin Kira harta wuce sama, shuru ta danyi don sai a lokacin amar ya fado mata, dukda tana kokarin hana zuciyarta tunanin shi saidai hakan ya gagara don yanxu idan babyn cikin ta ya danyi motsi shine yake fadi mata arai.

Suna nan zaune wayar ammah tayi vibrating, dan waigowa ammah tayi, kamar a mafarki idanunta ya sauka akan sunan Amar, cikin sauri ta dauka wayar Har hannunta na karkarwa yau wata biyu kenan rabonta dashi,  hello hello son is that you
Cikin jin dadi da murna Amar yace  yes ammah nine
 Subhanallah!! Son in Ka shiga Ka barmu cikin damuwa, wata biyu& 
 So sorry ammah na shiyasa na kira ma yanxu, ko sauka bamuyi daga jirgi ba ayanxu haka maganar da nake dake
 Ya kake are you okay babu abunda ya sameka? Kana cikin koshin lafiy& 
Saurin katseta yayi  I m fine ammah, please don be worried I m perfectly fine okay? Hope kuma kuna nan lafiya?
 Yes son we re fine alhamdullah yaushe zaka dawo? I have something very important to tell you
 I don t know ammah, saimunyi rounding up komai anan, but inason ki kwantar da hankalinki I m perfectly fine, Muna gama operation Zan dawo Insha Al& .
Dip wayar ta dauke, amra data gyara zama tana. Kallon ammah data sauke wayar, gaba daya ta maida hankalinta kan ammah haka zalika Salim shima yana daga gefe yana kallon ammah Duk sun zama curious suji ko lafiya,
 Ammah lafiya dai ko?
Dan Nunfasawa ammah tayi tace  Alhamdulillah, son ne yace yana lafiya Har yanxu basu gama operation bane
Wata ijiyar zuciya amra ta saki Har yasa ammah ta juyota.
 Har hankalina ya kwanta daughter, yau wata biyu da kenan, alhamdullah ya Allah
Sauke kanta kawai tayi kasa batace komai ba, saima wasa da Yan yatsunta data fara.

Washe gari wajen karfe biyu suka fito gaba dayansu, da yake weekends ne, sunyi kyau gaba dayansu daga kan amra zuwa salima sai ammah, Duk sunsha native kaya, atare suka fito gaba sayansu suka wuce motar ammah, ammah ne ke jan motar sai salima a bayan motar,
Anatse ammah ke drinving while tana dan duban amra ta jikin mirror, hira suka dan farayi a tsakanin au inda amra dai saidai tace uhm ko ah ah saidai kuma in anyi abun dariya Harda ita ake kyakyatawa.

Gaban wani katon mall suka 360 mall, mall din ya gadu sosai don yana dauke da wani babban bulding mai tsayi sosai, atare suka fito gaba dayansu inda salima ta taimakawa amra ta bata helping hand saboda yanayin ta, ahankali suka shiga cikin mall, fadin irin kyau na wurin ma bata lokaci ne, babu wani hayaniyan mutane dan few mutane ke yawo, ko Ina fess fess sai kamshi, maintainance din wajen sai ba a magana saboda ko Ina clean, cikin lift suka shiga nan ma saida salima ta taimaka mata, suna hawa second floor suka wuce wani katon shop may suna baby shark, tundaga nesa zaka san shop din kayan babies ne, ammah ce agaba suna biye da ita Har suka shige cikin shop din, mutanen wajen ne sukayi welcoming din ammah kafin su fara zagaya wajen,
Katon trolling ammah tasa salima ta janyo nan suka shiga shopping, abun da suka kwasa akalla zaikai wajen miliyan uku, ammah dai sage wa tayi babu abunda bata saya ba a wajen na Abubuwan da mummy and baby zasu magana dashi don suna da kaya designer don kamar ma kayan Duk na kasar waje ne, sun kwashi wajen awa biyu Ana abu daya, amra dai data gaji zama tayi nan mutanen wajen suka kawo mata ruwa da snacks, zamanta kuwa tayi taci snacks din tana cinye wa ta buqaci a kara mata nan ammah tasa su kawo mata da yawa.

Saida su salima da ammah suka gama kwashe kwashe su Duk wani cute kayan baby saida suka dauka Harda unisex babu wanda suka bari, Harda abubuwan da amra zata buqata wajen preparing delivery bag dinta, suna gamawa ammah tayi payment, lokacin da amra taji kudin saida ta kama baki, bazata iya musama ammah ba don haka taja Bakinta tayi shuru saidai bata kam taga abunda ake kira da gata.

Daga nan saida suka tsaya ammah ta saya masu kayan ciye ciye don itama tana son kayan dadi saidai diabetes dinta dake hanata cin wasu abubuwan,
Sai wajen karfe biyar na yamma suka dawo gida da kaya niki niki, daki guda ammah ta fidda anan sama aka zuba kayan a dakin.

Washe gari Kayan da ammah tayi order daga dubai da uk suka iso, suka fadin irin yawan kayan da kudin da aka kashe akansu bata lokaci ne.
Su Aman ne suka dunga shugowa dasu suna hawa dasu sama shida salim, suna hawowa dashi ammah tasa suka wuce dashi dakin data ware, daki ne babba sosai don Har yafi inda amra take, empty room ne saidai yasha frames, nan suka dunga zuba komai a ciki daga kan crop zuwa strollers da baby swings. Suna gama ajiyewa ammah ta shugo dakin tare da salima sai maida din gidan, nan suka fara shirya komai suna jerawa inda nan Aman shima yazo ya tayasu harhada crip da sauran abubuwan da dole sai anyi assembling, amra dai bata shugo dakin ba don kwana biyu tana dan fama da ciwon baya ga kumburin kafa da yake fama dashi.

After 1 week&
A cikin sati daya ammah ta gama komai na sayayyan baby, babu abunda bata saya ba Har wanda bazasu buqata ayanxu bama Duk ta siya.
Yau last appointment din amra before delivery don haka suka wuce asibiti, a cikin satitikan nan cikin amra girma yake kullum abun Har mamaki yake bama ammah, don cikin yayi girma sosai lokaci guda babu zato, Duk wasu kayanta yanxu basa shiga ta kwata kwata, sai doguwar riga mai bubu, wadda ammah ta karo mata su da yawa tana sakawa yanxu ma rigar ce a jikinta sai mayafin rigar, ahankali take sauko tana rike bayanta, tana saukowa ta dan tsaya tasa maid ta kawo mata ice water, tana nan tsaye ammah ta sauko kasan  sorry daughter na barki tsaye ko, muje
Suna sauka saiga salima ta taho da sauri itama daga sama,  Laa ammah shine zaku tafi babu ni, dan Allah Zan biku 
 Toh muje ammah ta fada tana wucewa gaba harta karasa gaban mota, tana karasawa ta bude gidan gaba kafin ta bude ma amra baya don ta daina zaman gaba, suna shigewa gaba dayansu suka bar cikin gidan.

Suna karasowa asibiti ammah tayi parking, fitowa sukayi gaba dayansu inda salima ke rike da hannun amra tana bata helping hand, anatse suke tafiya Har suka shiga cikin asibitin, suna zuwa kuwa time din appointment dinsu na cika cif. Basu tsaya komai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login