Showing 324001 words to 327000 words out of 381117 words

Chapter 109 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

2037

baya futowa ma sosai.
  zo ga breakfast na kawo maki, na sanki da son dumame  ammah ta fada tana karasowa baking ado ta ajiye mata akan carpet   bismaillah, zoki zauna kici dear 
Cikin jin dadi amra ta karaso inda ammah ke tsaye kanta har lokacin a kasa fuskanta fayau said an murmushi da ya wanzu akan fuskanta   thank you ammah, daman dashi na tashi wallahi 
Murmushi kawai ammah tayi mata kafin ta juya hanyar futa tace   idan kin gama ki sauko kasa, yaudai kid an zagaya estate din, ga salim nan saiya rakaki 
  tohm ammah  amra ta bata amsa.

Ammah na fucewa ta zauna ta nadi tuwon nan sosai, saida taci ta koshi harda sude hannu kafin ta wuce bathroom ta wanke hannunta, tana wanke hannun ta fito ta dauki plate din ta fuce daga dakin.
Kasa ta fara saukowa babu kowa a kasan don haka ta wuce kitchen kai tsaye ta ajiye plates din, gaban fridge ta tako ta dauka bottle of ice water kafin ta fuce daga kitchen din.
Tunda ta gifta ta wuce kitchen ya dago ya kaleta harta futo daga kitchen din batama san yana wajenba, itako amra bata lura dashi ba kwata kwata kanta a kasa saida tazo daidai wuce hanyar dining din ta jiyo karar spoon, duk a tunaninta ma ammah ne a wajen don haka ta dan dago da idanunta, karaf idanun nata suka sauka akan nashi, hannunshi rike da toasted bread yana kokarin kaiwa baki, samun kanta tayi da galla mashi harara tayi wani farr da idanu tare da turo mashi baki kafin ta kauda kanta gefe tana kokarin amsa kiran da ammah dake zaune a sitting room takeyi mata   daughter daughter, kin sauko ne? 
  eh na sauko ammah, plate na ajiye ne a kitchen  tana kaiwa nan ta sake mashi kallo daya ta dauke kanta ta cigaba da catwalk tafiyanta kamar wata tarwada,mazaunanta yabi da kallo har saida ta gifta ma kallonshi kafin ya sauke wata nauyayyiyar ajiyar zuciya   ya allah,  ya furta ahankali, tunani ya soma yi aranshi har lokacin bread din na hannunshi bai kai baki ba,   yarinyar nan na neman haukatani  ya fada aranshi kafin ya danyi wani murmushin da shi kadai yasan ma anar shi   zanyi maganinki ne 
Tura bread din yayi abakinshi, da farko kwata kwata bayajin cin komai saidai yanxu daya ganta da yanda tayi wannan abun da tayi mashi da fuskanta saiya tsinci kanshi da jin dadin cin abunci,.

Amra kuwa wani irin haushinsa takeji yanda yake kokarin maidata kamar wata toy dinshi, don sai ayanxu ta lura da take takenshi na neman coffee da daddare, saboda yasan ammah zata ce takai mashi, tun kafin ta karaso parlor ta soma Magana a zuciyarta   ay kuwa bazan kara kai maka ba wallahi, daman na lura da take taken ka 
Kaarsowa tayi parlor har lokacin tana tunani aranta,muryar ammah ne ta katseta   daughter kayannan baya damunki? 
Dan dagowa tayi kafin ta maida idanunta kan kayan   ah ah ammah, baya damuna 
  toh shikenan, ki dauko mayafi salim ya rakaki ku zagaya  ammah ta fada tana maida kallonta ga tv
  tohm   tana kaiwa nan itama ta wuce sama anatse, tana shiga daki ta dauka dankwalin doguwar rigar ta tsaya gaban mirror ta daura dankwali, ba karamin kyau daurin yayi mata ba dukda bata iya ba, tana gama daurawa ta dauka kohl ta sanya a idanunta da suka dan fada kadan, tana gamawa ta dan jaa baya ta karema kanta kallo, dan bumb dinta ya futo sosai don sai a lokacin ta lura dashi saboda yanayi rigar jikin nata daya fiddashi dan kiff, shafa cikin tayi tana murmushi,   yanxu da baby anan wajen  ta fada tana shafa cikin nata tana murmushi, ta dauka kusan minti biyu a tsaye tana shafen cikin nata kafin ta tuna da wani abu, take yanayinta ya sauya tana tausayin kanta, duk sanda ta tuna yanda ya Muhammad ke treating dinta tana jin rashin dadi aranta, ta rasa dalilin dayasa hes always cold to her, kowani aure tasan koda babu soyayya akwai mutuntawa da kulawa da juna saidai ita batayi sa a ba, don ko fara arshi baifi sau biyu ta taba gani ba, baya sake mata ko kadan, doguwar Magana ma bata shiga tsakaninsu saidai fada, har lokacin ta kasa gane wani irin mutunne shi, da farko bayan rashin lafiyar ammah har tana cewa ya chanza ashe ashe bai chanza, koda yake what did she expect? Baka taba chanza mutun daga yanda yake dlilin wannan yasa ta kasa tantance a wani matsayi ta sakashi a zuciyarta, bata jin zai taba sonta a duniya don haka bata daurama kanta bama saida ta kawo zancen soyayya aranta ta tuna da Haifa,ada chant un tana tunaninta sometimes harda kuka idan tayi missing dinta saidai yanxu komai ya chanza, but har lokacin tana ranta.
Nunfaswa tayi ta janyo mayafin ta ta nada shi kan kafadarta ta fito daga dakin har lokacin bottle of ice din data dauko yana hannunta, natse take tafiya harta sauko kasa, dan dagowa tayi daga nesa ta hangoshi zaune kusa da ammah ya daura kafa daya kan daya, wayarshi maqale a kunneshi yana responding calls,   har kin sauko?  ammah ta tambayeta tana kallonta
  eh,  ta amsa ta kai tsaye kanta a kasa
  toh tashi kuje salim, ku zagaya ko ina ki danyi exercise kafin ku dawo  ammah ta fada tana kallon salim dake zaune yana buga ball
Mikewa salim yayi ya zagayo inda take   ammah sai mun dawo  amra ta fada tana bin hanyar futa daga cikin parlor hannunta rike dana salim suna tafiya ahankali.
  toh daughter saikun dawo  ammah ta fada tana maida idanunta kan tv.
Saida y agama wayar ya dan kalli ammah ta gefen idanu, kamar bazaice komai ba chan kuma ya hade rai yace   ina zasuje da safen nan 
Yanda yayi maganar yana basarwa kamar bashi ba,ammah bata kalleshi ba ta bashi amsa kai tsaye   zasuje strolling 
Dan tabe baki yayi kmar bai damu ba, yna son mikewa saidai kuma yana ganin kamar amma zatayi tunanin wani abun don haka ya soma latse latsen wayarshi.
Tunda ta fuce yake kallon time din wayarshi don ya dauka suna fita zasu dawo saidai yaga akasin haka don kusan 30mins basu dawo ba, kasa sukuni yayi daga zaunen da yake dukda bazaka taba tantance hakan akan fuskanshi ba sai tsaki daya dunga jerowa har lokacin idanunshi nakan wayar, ganin tsukar tashi taki karewa yasa ammah juyowa ta kalleshi   is everything okay son?  dan dagowa yayi ya kalli ammahn kafin ya sauke kanshi   wani aiki nasaka ayi shine akayi min shirme 
Ammah dai bat ace mashi qala ba don ta lura da yanda ya yanayin nashi bayan futarsu amra, babu abunda tke sai murmushi aranta ta so Magana   zama ka saukar da wannan ego din naka ne 

Zumbur ya mike tsaye ya wuce bedroom dinshi, cikin yan mintuna qalilan sai gashi da key a hannunshi, don gaba daya hes anxious akan futan nata, gani yake kamar wani abu zai sameta ko kuma za a kalleta wanda hakan ke tayar mashi da hankali sosai, ganin ya nufi hanyar futa yasa ammah cewa   futa zakayi? I thought kace yau wuni zakayi a gida 
  akwai wani abu da zanje na karba ne  ya amsata
  okay adawo lafiya  ammah ta fada tana dauke idanunta daga gareshi tana dan murmusawa irin nasu na manya.

Yana futa ya wuce wajen zabgegeiyar benz dinshi ya budeta ya shige ciki, cikin hanzari ya kunna motar yayi reversing, wani irin mahaukacin horn yayi don gab daya securities din suna cikin cctv room sai karar horn dinshi sukeji.
Da sauri daya daga cikin securitis din ya futo ya bude mashi gate din, a harzuke ya karaso da motar inda securities din yake ya zuge glass din motar ya soma Magana cikin fada   what the hell is going on with your head? Kana son loosing job dinka ne?
Da sauri secuty yace   no sir sorry sir 
  so you better do your job properly, this is your last warning  ya karashe yana fuzgar motar aguje kamar zai tashi sama, bin kan titin estate din ya farayi don street kusan uku ne a cikin estate din, haka yabi first street baiga alamunsu ba, gaba daya ranshi a dagule yake shi kanshi ayanxu kasa controlling kanshi yakeyi akanta, haka ya dunga bin street din estate dinnan yana zagayesu yana dawowa tass bai samesu ba, saida yazo dab da last street ya hangosu daga chan nesa, rage gudun motar tashi yayi ya soma tafiya ahankali, nan ya soma hangosu da kyau, tana daga zaune kan wani dakali wajen kofar gate din wani apartment salim na daga gefenta shima a tsaye yana wasa da wani farin cute kare, itama idanunta nakan Karen tana kokarin shafa kanshi, saurin taka burki yayi kiii lokacin da wani mutumi ya fito daga cikin apartment din yana masu Magana, dan jim yayi yana kallonsu zuciyarshi na boiling sosai, abunda ya kara harzuka shi shine ganin tana murmushi tana shafa kan Karen wanda mutumin ya janyo ring din da ake kama Karen dashi da alamu nashi ne, amar dai idanunshi sunyi jaa sosai, ranshi yayi mugun baci sosai har baisan lokacin daya karaso inda suke da mot aba ya zuge glass din motar fuskanshi babu annuri yace   get in 
Tunda ya tsayar da motarshi amra ta dago ta kalli motar,baka hango na ciki don saida ya zuge glass din ta ganshi, gabanta ne yadan fadi haka kawai ba tare da sanin dalilin ba, ganin yanda fuskanshi ta hade sosai yasa ta danji wani iri,   do I have to repeat my self 
Mikewa ta soma yi ahankali tana kokarin mikewa, kafanta da ya dan sake mata ya jaaa jinni ne yasa ta danyi baya ta danyi kara   washh  da sauri mutumin ya mika hannu zai taimaka mata karta fadi kasa, aamar da yaga haka yayi saurin buga mashi tsawa   don t you dare, don t you dare touch my wife!!!!! Are you insane!!! 
Yanda yake fada a cikin motar da yanda gaba daya a susuce yasa gaba dayansu suka sha jinin jikinsu harma da mutumin, kallonshi mutumin yayi in a calming tone yace   sorry yallabai, naga zata fadi ne shine!!! 
  shut the fuck up ka wuce cikin apartment dinka ko na koreka daga.. 
Kallonshi mutumin ya dunga yi tun lokacin daya soma Magana, sai a lokacin ya lura da koma waye,   the owner of the estate,  ya fada aranshi, cikin sauri ya akste amar daga abunda yake shirin fada yace   dan allah kayi hakuri sir, tsautsayi ne  yana kaiwa nan ya wuce cikin apartment dinshi da dan Karen sa a hannu.
Amra dai komawa tayi baya ta zauna saboda zugin kafarta, idanunta sunyi jaa sosai,   keee  amar ya sake fada yana kallonta, bata dagoba don at this point dayace kee dinnan ya hasalata sosai   idan kika bari na sake repeating kaina saina&  
  saikayi me?  tayi saurin katseshi ranta a bace, itama idanunta yayi jaa sosai, mai ciki da jaraba, lokaci guda idanunta ya rufe ta soma Magana   nace me zakayi min? dukana zakayi?, ehhh? da fada da dan karfi daya salim matsowa kusa da ita yana jan gyalenta alamun tayi shuru, saurin ture hannunshi tayi ta hankadashi gefe idanunta yayi jaa sosai bata ji bata gani   matsamin a waje kai kuma, 
Tana fadin haka ta maido da idanunta kana amar   ina ruwanka dani yaya? Naga dai baka damu da alamarina ba? Baisa yanxu kake shiga cikin rayuwata?,  
Ranshi ne yayi mugun sosuwa don haka ya mata wani irin kallo mai wuyar fassara, cije lower lips dinshi yayi ya fusgi motarshi yabar wajen yana jin haushin kansa da yanda ya sauke kanshi har tana iya fada mashi Magana, gaba daya maganganunta basu bashi haushi ba sai Kalmar dukana zakayi datace, abun ya bata mashi rai sosai, me take nufi Kenan? Hes not that ruthless, bazai taba koda bugun hannunta ba saboda tana da wani matsayi babba a zciyarshi.

Yana barin wajen ta sauke wata ijiyar zuciya don batayi tunanin zasu wanye da sauqi haka ba don duk a tunaninta da sanin da tayi mashi da zafin rai bazaiyi shuru yayi walking out haka ba, salima e daya rakube gefe ya tako inda take ya rike hannunta ya taiamaka mata ta mike suka bi hanyar dazai maidasu gida.
Cikikin yan mintuna kalilan suka karaso gida, babu abunda take sai haki har suka karso cikin gida, ammah suka tadda a zaune yanda suka barta   sannu daughter kinyi kokari 
Murmushi kawai amra tayi ta samu waje ta zauna ta mikar da kafarta   washh ammah na gaji anya zan iya kuwa 
  zaki iya mana daughter, sannu haka zaki dage harki saba ammah ta fada tana kallonta
  dauko min ruwa mai sanyi salim  amra ta fada tana kallonshi
Mikewa yayi tsaye ya wuce kitchen kallonta ammah tayi tace   ku hadu da son akan hanya kuwa yanxu shima ya futa 
Hade rai amra tayi tadan tabe baki kafin tace   eh munga fucewarshi lokacin muna dawowa  & ..
[7/11, 11:17 PM] +218 92-2035171: Update
Unedited page
Hade rai amra tayi tadan tabe baki kafin tace   eh munga fucewarshi lokacin muna dawowa 
Shuru ne ya biyo baya bayan dawowar salim da ruwan data buqata, tunda tayi resting bayanta ta soma jin barci barci sama sama, ammah na dake duban ta jefi jefi tana ganin yanayinta tace   dear kije ki kwanta kafin anjima da yamma saiku sake futa ko? 
Kamar daman jira take ta mike tsaye tana dan yin nishi sama sama   toh ammah, 
Tana kaiwa nan ta wuce hanyar stairs zuwa dakinta, datayi dan taku daya biyu saita huta kafin ta cigaba, ammah na kallontta daga zaune, fadin irin farin cikin da take ji idan ta kalli amra dake dauke da cikin Muhammad mara misaltuwa ne, shes so happy, kusan kullum sai tayi sadaka, duk dare kuwa bata barcin daya wuce awa biyu, haka zata tashi ta kafa goshinta akan sallaya tana godiya ga Allah daya basu wannan kyauta ta musamman, she s just waiting for the perfect time ta fada ma Muhammad, dalilin dayasa ta boye mashi kuwa shine, yanda ta lura yana qaunar amra sosai amma yaqi futowa fili ya nuna yana son ta, bayan wannan tafison sai ya nuna yana buqatar matarshi da kanshi kuma yayi accepting dinta da kanshi kafin ta fada mashi. Ayanxu ta zuba masu idanu tana karantarsu sosai, daya daga cikin abunda ta lura dashi shine, yanda yake pushing amra don duk hidimar datakeyi mashi akan idanunta ne shi kuma yana basarwa saboda ego dinshi daya kasa barinshi ya saukar da kanshi kasa, da farko taso ta barsu a yanda suke ko zasu dawo dan kansu saidai kuma amaimakon komai ya falling into places sai akasin haka, don yanda yake pushing din amra yasa take baya baya dashi, don da gayya ammah take aikata dakinshi don ta lura ta daina kwana anan dinma, bata takura mat aba haka ta kyaleta tana kwana inda takeso saboda yanayin ta.
Nunfasawa ammah tayi tana tunanin, harga allah tana son tagansu kamar kowanne mata da miji, saidai hakan kamar bazai samu ba saboda kafiya irin ta amar, tunanin yanda zatayi dasu ta fara kafin takai kan decision dinta.
Tana nan zaune salim na gefenta yana barcin daya saba a doguwar kujera akayi sallama, kallon inda yake shugowa ammah tayi fuskanta dauke da fara a da bata barin fuskanta,   malam labara maraba lale 
Har inda take zaune ya karaso ya zauna a kasa ya fara gaisheta   nace ka daina zama a asa malam labaran, ga kujera nan manene amfaninta kenan 
Cikin girmama way ace   hajiya nan ma yayi, ina wuni ya iyali? 
  lafiya kalua alhamdullahi ya aykin gona?,ya kuma jiki 
  da sauqi hajiya alhamdullahi,   ya bata amsa
  toh madallah allah ya taimaka  amma ta amsa shi tana kokarin kallon tv.
Hannunshi ya zaro cikin aljihun shi yace   hajiya ga wannan, kudin wannan shekarar ne, shine nace bari na akawo 
Kudin ya ajiye mata da paper a gefe   wannan list din komai ne na rubuta a ciki, murmusawa ammah tayi ta kalli kudin daya nade a leda kafin ta maida idanunta kanshi,   masha allah, ka rike a hannunka, duk wani abunda za a buqata a gonar saika saya dashi sai kuma amfaninka kaima 
Kanshi a kasa yace   hajiya akwai duk wani abunda za a buqata, wannan&  
  Toh ka rike kaja jari  ammah ta kkasteshi, wasu ahwaye ne suka fara zarya akan fuskanshi, kafin ya dan dago ya soma jero mata adduo sosai.
  babu komai malam labaran ka daina min godiya? Yauwa daman inata so na tambayeka, ya maganra memories dinka kuwa, akwai improvement?  nunfasawa ya danyi yana murmushi yace   alhamdullahi, gaskia akwai, saboda yanxu idan na kalli wasu abubuwan wani shafi daga cikin rayuwata yana zuwanmin 
  toh alhamdullah allah ya kawo sauqi cikin lamarin  ammah ta fada tana murmusawa
  ameen hajiya, bari na wuce,  ya fada yana


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login