Showing 294001 words to 297000 words out of 381117 words

Chapter 99 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

1985

ta, knocking din da akayi ne yasa ta dan dago kanta don Duk a tunaninta ammah ne  yea come in ta fada ahankali muryanta chan kasa tana kokarin rike dafe bayanta da hannu daya tana  washh
Ahanakli ya bude kofar ya shugo anatse kafin ya rufe kofar ya tsaya yana binta da idanu.
Jin shuru yasa ta dan dago da kanta, nan idanunta ya sauka a nashi, sai kamshinsa daya bade dakin gaba daya lokaci guda,
Saurin kauda kanta tayi gefe ta mike tsaye ta nufi hanyar bathroom yana Ganin haka yayi saurin takowa zuwa inda take, cikin sauri ya kama hannunta  Aisha!!!
Chak ta tsaya ta kasa motsawa don gab take da shigewa bathroom din gashi ya rike hannunta, ahanakli ya Kara matsawa inda take ya tsaya a bayanta  Aisha please!!!
Gabanta ne ya dan fadi yanda yake mata magana da yanda ya kira suna ta calming kamar bashi ba sai taji kamar wani Amar dinne a tsaye a bayanta bashi general din data sani ba, kokarin kwace hannunta ta fara yi, yana Ganin haka ya rike hannun nata sosai kafin ya dan juyo da juyo da ita tana fuskantarshi, kasa dagowa tayi ta kalleshi kanta a kasa, fuskanta a hade babu annuri ko kadan,  Aisha please look up ya fada in a calming tone, Har voice dinshi na cracking
Samun kanta tayi da dagowa ta kafe shi da idanu Har lokacin bata sakin fuskanta ba,
Bakinsa ya soma budewa yana son ya fada mata abu ya kasa, haka ya dunga mimicking ya gaza Tara courage dinshi, ganin haka yasa Tayi saurin kauda idanunta akanshi  Zan shiga bathroom tana kaiwa nan ta zame hannunta daga nashi ta juya mashi baya ta nufi hanyar bathroom
Taku daya yayi ya cinmmata tare da rungumeta, ya hade bayanta da kirjinshi, Lumshe idanu yayi yana jin wani irin natsuwa na zuwan mashi, itako tunda ya rungumeta taji ranta ya baci sosai, kokarin kwacewa ta soma yi ya qi bata damar haka don kwakwaran rungume yayi mata, ahankali ya sauke kanshi daidai kafadarta, ahanakli yake sauke mata nunfashi anan wajen kafin ya matso da fuskanshi daidai wuyanta, yana sauke fuskanshi a wajen ta lankwasar da wuyanta,
Daidai bakinshi yayi wajen kunnenta kafin ya soma magana ahankali kamar mai rada  I m sorry ayeeeshhh& .I m sorry for what I did the other time
Yana kaiwa nan ya saketa tare da juyo da ita sautin fuskanshi ya saqalo hannunshi a kugunta kafin ya matso da fuskanshi saurin fuskanta nunafshinsu na gugan na juna,  I& I& .
Saurin katseshi tayi ta hanyar yin baya ta nunfashinta na fita sama sama, hawaye na gangarowa daga fuskanta, amaimakon kalamanshi su mata dadi sai suka bakanta mata zuciya, ya kaita maqura sosai inda take jin bata kaunar ganinshi ko kadan saboda abunda yaso yi kata shekaran jiyan, she begged him, but bai damu ba he s selfish kanshi kawai ya sani, bayan abunda ya mata sai Yanxu kuma yazo yace sorry? Me yake nufi kenan? Ta hakura daga just saying sorry,
Saurin girgiza kanta tayi tana tunanin tana hawaye  no no,
Ta dunga furtawa a zuciyarta, ya kaita bango sosai bazata iyaba, sorry dinshi is nothing to her compare to abunda ya mata all this while, Yan a Ganin haka ya soma matsawa inda take  stop please karka matso inda nake
Chak ya tsaya jiki shi ya mutu sosai, harga Allah so yake yayi reconciling da ita Kodan saboda ammah don yasan tabbas bata huce dashi ba, dazun ma ta kulashi ne saboda zai tafi badan haka ba bazai ga murmushi ta bama.
 Why? Ya tambayeta kai tsaye
Dan dago da jajayen idanunta tayi ta mashi kallo daya kafin ta sauke idanun nata ta kauda kanta gefe, yana Ganin haka yasa ya juya ba tare da yace mata komai ba,saida yazo daidai kofar futa daga dakin ya dan jinkirta  take care of your self and your siblings
Yan kaiwa nan ya fuce daga cikin dakin, yana futa ta shige bathroom sai hawaye,haka nan ta dunga kuka ita kanta bata san dalilin kukan nata ba, ta dade sosai a cikin bathroom din tana hawaye kafin ta wanke fuskanta ta dawo cikin bedroom din.

Amar kuwa yana futa daga dakin amra ya sauko kasa, kai tsaye ya nufi Inda yabar jakanshi.
Saida ya karaso ma ya Lura da ammah dake zaune a sitting room din, sanye take da hijab tundaga sama Har kasa, kallonshi tayi fuskanta dauke da murmushi kafin ta mike ta tako Har Ind a yake ta karba laptop bag dinshi, yana Ganin haka ya rike hannunta suka fuce zuwa inda driver yayi parking, suna karasowa shida ammah ya saki hannunta ya dan rungumeta yace  bye ammah take care of your self for me pls
 I will son, kaima Ka kula da kanka, don t forget to call us idan kaje chan
 I will Insha Allah ammah na yana kaiwa nan ya shige bayan motar driver yaja motar suka fuce daga gidan,
Jiki a mace ammah ta juya ta koma cikin gidan tana mai yi mashi addauar kariya da tsari.

Wunin ranar dai ammah da amra sunyi shi ne cikin rashin jin dadi,kowannen su na zaune a daki, karshe dai amra barci tayi wanda ya fusge ta batare da ta sani ba, while ammah kuwa tunda ta zauna kan sallaya bata mike ba tun bayan sallan dhuru datayi.

Amar kuwa suna fita da motar airport suka wuce direct, suna isa airport management suka shaida zuwanshi don haka takanas Aka saka mutun daya daga cikin officials yayi masu jagora zuwa wajen jets departures, bai fito daga cikin motarshi ba Har suka iso babban cikin da jet ke sauka, daga dan nesa jirgin driver yayi parking, ahankali amar ya futo anatse hannunshi cikin wandon kakin sa,kwarjinin sa ya gama cika wajen gaba daya, ahankali ya soma takowa cikin kamewa while wasu officials biyu na rike da baggage dinshi da laptop bag dinshi, direct gaban jirgin uae armed force ya tsaya, saida ya dan tsaya ya suke nauyayyiyar ajiyar zuciya kafin yayi addua yana gama wa fara hawa matattakalar jirgin, tundaga kan steps din jirgin yaranshi dake tsaye sunsha uniform dinsu kowannen hannunsa rike da manya manyan bindigu kamar zasuje yaqi, fuskokinsu a rufe da wani black helmet, sai inner bullet prove Riga da Kowannen su ya daura akan kakin, haka suka dunga Sara mashi Har ya shige cikin jirgin kafin su bi bayanshi, su kansu zasu kai akalla su talatin, wani special waje aka bashi nan ya zauna ya daura kafa daya kan daya, cikin sauri m5 y a karaso inda yake shi baima saka helmet dinba don Ana Ganin fuskanshi,  welcoming sir m5 ya fada yana kamewa, kallonshi Amar yyi kafin yace  drop the formalities, seat
Zama m5 yayi ind a yake mashi nuni nan opposite kujeran da yake zaune, nan ya buqaci da yayi mashi bayani akan operation din da komai daya kamata ya sani.

Cikin Yan mintuna qalilan jirgin su ya daga sararin samaniya& ..
Adawo lpy sir general=?-?

Yau kwana biyu kenan bayan tafiyar Amar, gidan yayi shuru kamar an dauke masu annurin gidan, ammah kullum tana daki, abu daya ke fiddata daga daki shine dubo amra don sanin yanda ta Tashi, aranar da Amar ya tafi wahee gari ya chanza masu securities na gidan gaba daya, Banda baba mai gadi, sannan ya sanya asad yayi mashi inspecting wani babban company da suke kawo helps daga wata kasar, nan yasa asad yayi mashi kwakwaran buncike akansu kafin a kawosu gidan, ya mata ne guda biyu akalla zasukai shekaru talatin talatin, dukkansu Yan phillipines ne, bai yarda ya kawo Yan Nigeria ba,
Salima ne tayi kokarin training dinsu akan ayyukan gidan don kusan a tare suke yin komai, daya danganci abunci don basu iya abuncin mu na nan Nigeria ba,yanxu ayyukan gidan Duk ya koma hannunsu.
Yau sati guda kenan da graduation din salima, don haka amra tayi deciding fada mata komai, don daman dalilin dayasa ta ki fada mata was saboda Karta fada ma Aman don idan ta fada mashi zai ita fada ma Amar shiyasa ta qi fada mata a wanchan lokacin, yanxu kuwa inka ga yanda suke ma junansu kamar zasu cinye juna.

Zaune take akan gado hankali kwance tana chan mango da salima ta yanka mata,ayanxu bata da wata damuwa kwata kwata, don daman Amar ne ke bata ciwon kai, tun bayan tafiyarshi kuwa hankalinta ya dan kwanta, bata wani damu ba da alamarinshi don harta ma manta dashi saboda basu da wani memories mai dadi da zaisa ta tuna dashi saidai sometimes yakan dan fado mata arai.
Sallama salima tayi hannunta rike da wani plate din ta sake yanko mata saboda ta buqaci hakan, tana zuwa gaban gadon ta ajiye mata akan gado tana turo baki don hira take da habibinta a sabuwar wayar daya bata don yaje office shine ammah ta tado akan tazo ta yanka ma amra mango.
 Gashi nan, dan Allah abarni na huta haka nan, Wallahi adda lamarinki gaba yakeyi kamar wata mai ciki tana kaiwa nan ta juya, amra kuwa mai zatayi Banda dariya din haka Tayi saurin katseta  ba laifina bane laifin danki ne ay
Da sauri salima ta juyo don bata gane inda ta Dosa ba, shafa belly bump dinta tayi kafin ta maida kallonta kan salima  kingani ba? Shike damunki bani ba
Da sauri salima ta tako inda take idanunta a waje Bakinta ya kasa rufuwa ta shafa cikin amra  adda baby ne anan?
Salima ta fada tana shafa cikin amra, girgiza mata kai amra tayi tace  yes& 
Fadin irin farin cikin da salima ta shiga a wannan rana bata lokaci ne don kowa saida ya shaida hakan a gidan, she s so happy Harda dan kukanta.


After one months& .
A kwana a Tashi babu wuya yau wata guda kenan da tafiyar Amar, ayanxu hankalin ammah ya gama Tashi, wata guda kenan tun bayan tafiyarshi da sukayi waya sau daya lokacin daya shaida mata sun isa wajen operation inda bai fada mata ba saboda basa fadin work related to anyone hatta family wannan dokar sojoji ce.
Fadin irin tashin hankalin da ammah ke ciki bata lokaci ne ta rame sosai saboda tunanin Amar, this is the first time hankalinta ya Tashi da tafiyar da yayi don this is not the first time yake tafiya operations, don Duk sanda zaije koda yana chan dubai saiya fada mata kuma haka zasuyi kusan wata biyu basuyi magana ba idan yana chan Duk bata damuwa saidai akasin na wannan Karan abun ya dameta sosai, Wai irin unnecessary tunani take yi aranta wanda ada bata yinsu kwata kwata,  what if wani abu ya sameshi? What if something is wrong? Kullum tambayar da take ma kanta kenan, abunda yafi damunta shine sai yanxu take dana samun fada mashi maganar cikin amra.
Tana nan zaune amra ta shugo dakin, kallonta nayi sama Har kasa sanye take da doguwar rigar atamfa bubu anyi nata free gown da ita, tayi wani irin bulbul skin dinta yayi haske sosai kamar jini zai fita, fuskanta tayi fayau, ga dan baby bump dinta daya futo ba laifi don yanxu kana ganinta kasan tana da ciki, yanxu cikinta watan shi bakwai da sati guda.

Shugowa tayi dakin atsanake ta karaso Ind ammah ke zaune Har zata zauna a kasa ammah ta kalleta jiki a mace kana ganinta kasan tana cikin damuwa sosai  haba daughter, baba hanaki zaman kasa ba yanda kika fara nauyin nan
Murmushi amra ta danyi kafin ta zauna gefen gado ta gaisheta, cikin fara a ammah ta amsa mata. Shuru ne ya buyo baya kafin amra ta soma magana  ammah, Akwai abund ake damunki ne?
Shuru ammah tayi kafin ta nunfasa  babu komi daughter,kinci abunci?
 Eh naci tuwo amra ta bata amsa
 Ammah please Ki fada min abunda ke damun ki, bakya cikin walwala kwanakin nan
Kallonta ammah ta danyi baya son ta saka mata damuwa don haka tace  daughter yau wata guda kenan rabon da na samu son a waya, wayarshi baya shiga kwata kwata, Ina jin kamar wani abu ya faru
Hannunta amra ta kama kafin ta soma magana in a calming tone  ammah ki kwantar da hankalin ki, nasan he s perfectly fine Insha Allah, maybe Har yanxu basu gama operation sun bane shiyasa bakya samunshi a waya

Haka amra ta dunga tausasa ta da kalamai masu kwantar da hankali harta danji nauyin da zuciyarta keyi ya ragu, hira suka danyi don yanxu inka gansu kamar uwa da ya babu wani kunya, amra ta sake sosai da ita.

Washe gari suka shirya da ammah da salima da amra suka wuce asibiti don salima tace Yanxu dole da ita za a dunga hidiman baby, suna zuwa doctor ya duba lafiyar baby Har alokacin ammah taki yarda Suga gender na baby don haka doctor ya bata magungunan Karin jini da wanda zai dunga sakata cin abunci don zatafi buqatan hakan ayanxu don ta kusa shiga wata takwas wanda ya zamana anzo gangara.


Bari mu Yan katsina& .
Duniya ta juyama wannan family baya, yanxu taluacin da suke ciki haryaci uwar na da saboda da khady kawai suka dogara da take saida gwanjo itama ribar yanxu tayi kasa saboda hidiman gidan daya dawo hannunta dukda ba wani kudin arziki take fiddawa ba idan zasuyi cefane kullum, dari biyar ce safe da dare don ba a cin abuncin rana a gidan, dady kuwa tun bayan wannan targade da yayi har kayi mashi gyara a hannu da kafa, inda a hannunshi samu karaya while kafar kuwa ya samu targade, Toh da dai gyaran karayan nan baiyi ba kafarcema ya dan samu sauqi saidai hannun ne ya shanye gaba daya baya wani amfanuwa, sai kuma jan ruwa da yakeyi saboda inda ya ciwo wajen hannun ba a yi dressing ba haka gudaje da bad environment din wajen yayi affecting hannun, nan ya dunga Jan ruwa sai wani karshe dai hannun shanyewa tayi babu wani amfani.
Haka kullum zai zauna a gida baya uban komai, tun kareema na jin tsoro shi lokacin daya gano tana da cikin shege har tazo ta daina tsoronsa take gasa mashi aya a hannu, zagi cin mutunci babu wanda basa yima juna agaban yayansu, yaranma Har sun saba da yanda iyayensu keyi ma junansu, ah anguwa kuwa babu wanda baisan kareema matar mustapha mai damfara nada cikin shege ba, tayi cikin shege da aurenta, wannan zance yasa ko fita bata iyayi yaranma idan sun futa da irin zagin da ake jifansu dashi kenan, khady dai ta gama zama yar tasha idan ma an fada bata wani damuwa don Har cewa take  Toh saime idan tayi cikin shegen idan uwar wani ce Tayi ku fada min badai tawa uwar bace to munji tayi ciki
Yanda ta zama yar daba daba yasa wasu idan sunso goga mata magana suke kyale ta saboda kangararren saurayin ta.

Bangaren wahab yana chan a kurkuku don asad saida ya tabbatar an yanke mashi hukunci daidai da abunda yayi, nan aka kaishi prison na shekara goma,don Akwai diyyar daya kamata ya biya wanda yayi ma yarinyar maqocinshi na chan lagos fyade inda aka tuntubi iyayenshi ko zasu iya biya don in ba a biya ba shekarun da zaiyi a prison zai karu, nan aka tuntubi Alhaji mustapha, lokacin da suka kirashi ma yana gida a zaune babu uban abunda yake sai zaman banza don haka da sukayi mashi bayani nan take yace  ku rufeshi kawai babu abunda zaku samu a waje na
Yana kaiwa nan ya kashe wayar baima tsaya sauraron su ba, da kareema ta tambayi ko da wa yake waya kai tsaye ya mata bayani, nan take ta dunga kuka tana tsine daddy kan Duk shine ya janyo masu wannan masifa Har yayanta suka wulaqanta gaba daya saboda zalumcin shi da cin amanar dan uwansa da yayi na wulaqanta yayansa.
Nan suka dunga Sarfa ma junan su zagi ta uwa ta uba  kije kiji da shegen ciki wahallaiya asararriyar mata Wallahi nayi dana sanin aurenki kareema kina da kaso mai girma a cikin lalata rayuwata kece ma baqar kafar data lalata kin komai, badan kin sa an zubar da waennan yarannan ba da tuni na samu wani abun a wajen yayarsu
Kallonshi karima tayi tana takaici ace Wai mutun baiyi nadama ba ko kadan,  shiyasa zaka kare a haka a wulaqance, Har yanxu zuciyarka a mace take
Nan suka cigaba da cece kucensu dagashi Har ita aka rasa wanda zai jaa baki yayi shuru maqota na jin su.

Bangaren Muhammad kuwa yana chan Australia, yau watanshi biyar kenan, acahn yaqi dawowa don daddy s ya kirashi ya shaida mashi uwarshi tayi cikin shege don haka ya tura masu da kudi, ranar da yaji wannan baqin labari ya shiga tashin hankali sosai inda ya ko sun kirashi ma kasa daukan wayan yakeyi don yana Allah wadai da iyaye nashi, wannan yasa yaqi dawowa yayi zamansa acahn ya maida hankali wajen aikin shi inda yake taimakawa kaninshi ishaq daya dage yana masters dinshi anan Australia don bayan ya gama karatu ya dawo wajen Muhammad nan ya muyi sponsoring dinshi ya samu schorlaship nan ya fara masters.

Bangaren kakarsu salima kuwa, rana daya Allah ya dauki ranta anan kauye inda take zaune wajen dan uwanta, tayi jinya sosai inda suka dunga bata maganin gargajiya da farko kamar komai ya lafa sai daga baya kuma gadan gadan ciwon nata ya dawo Har Allah ya dauki ranta bata samu damar Ganin marayun jikokinta ba.

Bangaren labaran shima bayan noma haka ya samu yayi renting wani kanti nan kusa da inda yake yake haya, nan yayi amfani da kudin da ammah ta bashi ya zuba provision a cikin shagon don bashi da wani girma sosai, cikin wata biyu wajen ya bun kasa don haka ya hade da shagon dake kusa dan wanda yake haka, cikin ikon Allah Allah ya by kasa mashi, don Allah ya bashi wannan baiwar da zarar ya saka hannu akan abu sai Allah ya bukata mashi, kullum kuwa saiyayi mafarkin yarannan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login