Showing 63001 words to 66000 words out of 381117 words

Chapter 22 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

1993

yace   to abokina sai gobe idan na dawo, Allah ya basu lpy akwai aikin da zanje nayi, kasan talaka bawan allah saida nema  ..yana kaiwa nan sukayi sallama ya wucewarshi.
Iliya na wuce hanyar gidan ya cire mustache din daya manna a gaban bakinshi ya cizge gashi daya manna cikin facing cap, wipes ya zaro ya goge yan pente pente da yayi ma fuskarshi saida y agama ya dago kanshi, wani mutumin ne daban ba iliyan da audu suka sha hira dashi ba, wannan kana ganinshi kaga tantiran yan legas, kanshi ma sol yake babu digon gashi, wayarshi ya daga yayi yan typings sannan ya tura komai da yayi recording lokacin da suke Magana da audu da duk wani information daya samu daga wajen shi,yana sending ya tari mai mashin ya wuce abinshi.
?
Kano private hospital& .
Muhammad na isa asibitin da kanshi yaje ya duba su, bakamar jiya ba har sun dan marmare don kuwa salima harta dan watsake saidai itama bata farfado ba amma an gyara ta, an wanke kanta dake da muguwar dauda har waka saida nurses suka mata a kwance, shima salim an gyara shi saidai shi yayi wani irin haske kamar gawa jikinshi yayi wani irin sandarewa don har lokacin bai yana coma, ammma ana fatan ya tashi anytime soon, anan asibitin ya wuce shida ya kamat ya fara aiki Monday sai gashi yayi reporting tun ranar friday, wunin ranar shine ke dubasu da assistant dinshi, every 2 hours saiya dubasu har aka cire drip din salima sai jiran farfadowarta ita,
Karfe tara daidai na dare ya koma gida agajiya, saida yayi wanka ya saka jellabiya ya rama sallar da bai samu yayi ba kafin a wuce dakin mama kareema, yana shiga tana zaune gaban gadonta ta rabka uban tagumi, gefen khady ce wadda take ta rafka uban bacci kamar wadda tayi maye, abugen take saidai karyar data zagba ma maman nata na cewa ciwon kai takeyi wanda ya jawo mata jin juwa akanta, tana nan zaune har barci ya kwashe don tayi high sosai, haj kareema wanda tunanin duniya ya mata yawa na rashin Ibrahim yasa batama gane cewa khady a buge take ba, saida tashi muryarshi kafin yta dawo nutsuwarta,   mama is everything okay?akwai wani abu dake damunki ne  & gyara zamanta tayi tace   daga ina kake tun safe muhammad  & atakaice yace   naje asibiti  na dauka sai Monday zaka koma duty maisa ka koma yau?,&   inada patients ne shiyasa na fara yau  .. nunfasa tayi kafin ya sake kallonshi   yayan badaru kakai asibiti ina yayan badarun suke, waima tukunna ina ruwanka Muhammad da rayuwar wasu,  , mamaki ne karara dauke a fuskar shi ?don baiyi tunanin ta haka zatayi tambayar ba ya dauka zata tambayi ya lafiyar dasuke ciki, jinjina kanshi yayi aranshi yace   lallai akwai matsala, what going on in this house meke faruwa ne  , bai amsata ba yace   mama abinci fa,  im hungry,  , ganin bai amsata ba yasa ta bar zancen kawai don batason karama kanta matsala kan wadda take ciki ta rashin jin labarin Ibrahim kamar an shafe babin rayuwar sag aba daya, abinda yafi damunta yanda dady ya nuna bai damuba kwata kwata. Anan yaci abinci sukayi sallama ya koma dakinshi ya kwanta abinshi. 89-90
Rayuwa juyi juyi wasu najin dadi wasu na cikin wuya, rayuwa dai ta gama juyawa su salima, don cikin wata uku abubuwa da dama sun samesu ciki kuwa shine azabtuwar da suka sha wajen rita, wadda ta gano wayan ta da salima ta dauka watannin baya da suka shude, yanda ta ganota kuwa akwai ranarda cutar salim tayi tsananin kamar zai mutu hakan yasa ta burkicewa ta zaro wayar hankalinta baya kanta ta nufi dakin rita arikice, tana zuwa ta fara dube duben charger ko zata samu, rita wadda futowanta kenan daga toilet din cikin dakinsu na masu aiki, idanunta ne suka sauka akan salima dake barbaza maka kayanta ganin yanda salima ta burkita mata katifarta kayyaakin data sato da yawa daga dakunan yan gidan duk sun zuba a kasa yasa ta dago kallonta ga salima, ganin tsohuwar wayrta a hannun salima yasa ta tako gadan gadan ta kwashe ta da maruka wajen hudu ajere, salima kuwa wadda yunwa ta gama busar da ita ta dago ta kalli rita, ganin yanda take kallonta yasa rita cewa   ke dan uwarki barauniyace ke dama, kece kika sace min waya, to yau kuwa saina nuna maki ni cikakkiyar yar bariki ce mai lasisi, fadowa tayi kan salima saida ta mata dukan tsiya kafin ta kwace wayar ta hankadata gefe, dakyar salima ta rarrafa zuwa kofar dakinsu dukda bakinta bai mutu ba babu abin take cewa sai Allah ya isa, tun daga ranar rita ta dunga gana masu azaba, yanxu takaiga har line din wutar dakinsu gaba daya tasa mai gyaran wutar gidan wanda suke soyayya dashi ya kashe ta bangaren su salima, haka zasu kwana cikin zafi ga duhu, abinci kuwa yanxu kamar dabbobi haka take basu, wani sa in zata zuba masu shinkafa banda miya ko mai haka zasu ci suna kuka, wani sa in kuwa abincin da take diga masu ko salim baya koshi balle ita ta samu taci,duk wannan wahalar da suke sha basu taba attempting guduwa ba, to ko sun gudu ma ina zasuje? Duk wannan rayuwar da suke babu wanda ke lekensu daga yan gida gaba daya dukda yanxu suma abubuwa sun fara juya masu, don akwai wani tashin hankali da gaba daya gidan suka shiga wandalabarin kamawar ya Ibrahim ya riskesu na safarar mugayen kwaya da yake yi daga manyan kasashe daban daban, wanda haka ya mugun tayarma da dai hankali, ya kashe maqudan kudi sosai akan belin Ibrahim har ta kaiga ya sayarda gidan su salima don sunanshi ne akan takardun gidan as their guardian dukda sune masu gadon gidan, saida ya dauke wata uku a kulle duk ya jeme ya lalace yaci uwar wahala kafin alhaji Mustapha yayi yan cuku cuku aka samu aka fito dashi don da kyar aka samu aka danne zancen don case din yaje har gomnati kasar nageria don abin ya shafi sauran kasashe da taimakon wani abokin alhaji Mustapha babban general of police aka samu zancen ya kwanta don o su manyan government din bazasu so zancen ya fitaba don zai zame masu babbar matsala tsakanin kasashe da akeyin safarar don ayanda report din yazo daga Nigeria ake futar da kwayoyin meaning daga nan ake hadata da wasu sinadarai da anan Nigeria kawai ake samu haka zalika idan gomnatin kasashen suka gane zai iya jawo matsala sosai wanda gomnatin Nigeria bazata so haka ba kwata kwata.
Tunda aka fito da ya Ibrahim aka fito da Ibrahim babu wanda yasan inda yake, hajiya kareema tayi kuka tayi magiya akan dadi ya fada mata inda danta yake amma fir yaki fada mata, karshe ma yace ta cire dan da ya jawo mashi bal in da bazai iya saukewa ba daga duk kudin shi daga jerin yayansa, don ya sallama shi.
?
Akwai wata ranar asabar tana zaune kusa da salim wanda ya jeme ya rame kamar wanda yayi shekaru yana jinya,saboda ciwon zuciya dayake fama dashi tun bayan rasuwar iyayenshi don yanxu har ta kaiga baya iya Magana sannan abu kadan ke furgitashi koda kuwa karar kofa ne sai ya zabura ya kankameta ya fara kuka, ayanxu kam ta fawwalama allah kawai don rayuwar su ta gama tagayyara, babu makaranta, babu gata, babu walwala, babu cima mai kyau sai rama da rayuwar kunci,itama kanta ciwon cikin da take ya gama maidata kamar mahaukaciya don duk dare saitayi shi, kallon salim tayi wanda ya maqalqaleta sosai a jikinta yana futar da wani irin nunfashi dakyar, tun safe yake wannan nunfashin wanda daga jiya zuwa yau ya chanza daga nunfashin da yakeyi, shafa kanshi tayi ahankali tace   Allah ya baka lpy salim, allah yana tare damu, nasan yana kallonmu kuma yana jinmu kuma zai kawo mana dauki insha allah  , haka ta dunga surutanta ita kadai don baya iya Magana shi, ganin lokacin sallah yayi yasa ta kwantar dashi gefenta kan carpet ta miqe ta wuce toilet dinsu, gaba daya toilet din ya fita hankalinshi yayi wani irin dauda saboda baya samu gyara daya kamat da omo don rita ta daina basu koda sabulun wanka ne, fanfon toilet din ta bude wanda shima tsatsa tasa kan famfon ya balle saidai ruwa yana bulalowa idan aka kunna ta gefen wajenda bai balle ba, alwala ta dauro sannan ta fito ta jawo hijabinta wanda dauda tasa ya kode don kayansu ma ba samun wankin arziki yake ba saidai ta dauraye masu da ruwa zalla idan dattin yayi yawa sosai, tana idar da sallah ta miqe ganin yanda salim ya takure yana rawar sanyi da sauri ta arsa gabanshi ta tallabo shi sosai izuwa jikinta ta daura shi kan gado wani irin tari ya soma yi kamar ranshi zai futa, zama tayi gefenshi tana mashi sannun, ganin tarin yadan lafa yasa ta gyara mashi fuskarshi daya toge da gadon, tana zare hannunta idanunta ya sauka akan jinin dake Malala daga tafin hannunta, kallonshi tayi da sauri, jikinta na bari ta soma furta   innalillahi wa inna ilaihi rajiun  , kai salim tashi mene, wannan jinin na mene  ..afurgice ta janyoshi sosai don ganin daga inda jinin ke futa, kurama fuskarshi ido tayi bakinta na karkarwa    na shiga uku salim, me nake gani innalillahi wa inna ilaihi rajiun  , jijigashi ta soma yi ammam ina kamar nunfashinsa ya tsaya, da sauri ta miqe ko ganin gabanta batayi wani irin juyawa da kanta keyi yasa ta kwala ihu ta fice aguje, har tsakiyar parlor rabonda ta fito harabar wajen harta manta, kallon ta daya bayan daya waenda ke zaune a parlor sukeyi, ya Muhammad wanda daga ya Ibrahim saishi wanda saukarshi Kenan kowa yazo tarbarshi don tafiya yayi ma tsayi sosai don ya shafe shekara kusan bakwai rbonshi da gida, su hajiya kareema da yayanta, khady dasu amina da jabir da jalal kananun duk suna zazzaune suka juya jin wani irin wari na doso parlorn, kallonta ibrahim yayi wanda shima warin jikin nata ne ya mashi iso zuwa hancinci anatse ya soma Magana cikin kamewa da nutsuwa sannan   mummy ina kuka samu masu tabin hankali a ckin gidan nan, kudai da kwashe kwashen yan aiki  , tabe baki haj kareema tayi tace   yar badaru ce fah  , gwalo idanu yayi yace   wani badarun?  , bata bashi amsa ba ta miqe ta haye sama abinta bayan ta tattara kananun yayanta suka wuce sama,don kar warin salima ya cutar mata da yaya.
Kallonta muhammad yayi da kyau sai a lokacin shima ya wani tuna da yayan kawun su daya rasu, hankali atashe ta dora hannu aka a fara sambatu, kallonta yayi lokaci guda ya fuskaci bata da lafiya don karatun likitanci da yayi,   keee ki nutsu  ya dan fada da karfi, juyawa tayi idanunta na dishi dishi ta kalleshi don bata shaida fuskarshi da sauri ta karasa gabanshi har yana dan matsawa gefe ta durkusa tace   dan allah ka taimaki dan uwana zai mutu na shiga uku  , saida tayi Magana ya tabbatar ba mahaukaciya bace da yayi tsammani ?  ina kanin naki  , da sauri ta miqe tace   yana daki hancinci da bakinshi suna fito da jini, da sauri ya miqe tayi gaba ya bita abya suka shige dakin, wani rin kura da datti asa shi toshe hancinsa, da sauri ta yaye labulensu wanda yaji jiki sannan ta nuna mashi salim dake kwance kamar gawa har jinin ya fara bushewa akan gado, da sauri ya karasa gaban gadon ya taba wuyanshi don neman pulse dinshi, jin yanda pulse dinshi yayi weak sosai ya sashi tsayawa akanshi sosai cikin yan mintuna pulse din ya tsaya, shuru ya mhammad yayi yace   I thik hes gone  , salima na jin haka wani irin hajijiya tahau kanta, atakae a wajen ta anke jiki ta fadi itama wanwas, akidime Muhammad ya mike yana kallonta da kanin nata, da sauri ya karasa gabanta jin pulse dinta yayi weak hankalinshi ya tashi da sauri ya mike ya fuce daga dakin, yana zuwa daidai hanyar futa ya kwala ma masu gadin gidan kira da driver daya daukoshi daga airport da gudu suka karasa cikin yayi masu jagorar cikin dakin tare da masu nuni da yaran yace, ku futo dasu akaisu asibiti, mai gadin baba dan ladi wanda shima rabon da ganin yaran kusa shekar biyu Kenan, don tun yana tunanin suna gidan har yazo ya yarda da zancen hajiya kareema na cewa duk wanda ya nemesu ace basa nan, da sauri suka sungume su, Muhammad na biye dasu aka saka su cikin motar daga salim din har salima, da sauri driver ya shiga gaba shima Muhammad ?ya shige baya gaban owner coner suka ja motar suka fuce daga gida, duk wannan akan idon hajiya kareem wadda tun daga window dakinta take hangensu, karshe ta tabe baki tace   zaka dawo ka sameni ne, sometimes I wonder ko nina haifeka, don jinina bazai tsaya bata lokaci akan walqantattun yayan nan ba,  & .
Cikin wani babban private hospital suka tsaya inda nan ne muhammd sai fara aiki, yana karasawa ciki ya miqa id card dinshi a chan kasar daya baro as professional health personel receptionalist din na ganin sunanshi ta kira nurse da babban likitan dake duty aka dauko gado suka wuce waje, yanda aka kwasosu daga gida haka nan suke kwance babu chanji, da sauri nurses din da taimakon driver aka fito dasu aka kwantar akan gadon aka shiga dasu cikin emergency, Muhammad kuwa office dinshi ya wuce wanda aka tanadar mashi tun kafin a iso kasar don part time job zaiyi a cikin asibitin kafin wasu yan watanni ya koma jordan don achan yake aiki, agajiye yake ga gajiyar tafiya ga wanda ya tarar a gida, mamaki ne ya cikaci sosai, nazari ya fara ya akayi yarannan suka wulqanta haka, bayan lokacin daya tafi ma suna kananu sosai cikin gata, kuma lokacin iyayen sun a raye, do mutuwar kawun nashi ma bai sani ba sai bayan yan shekaru cikin Magana daddy ke fada mashi, runse idanunshi yayi tausayinsu na ratsa shi.
Dakyar likitoci suka samu nunfsashi salima ya dawo, kafin suka fara bata treatment sosai, karshe dai harda operation aka kare ayi mata don hantarta guda daya ta lalace saida aka cire, salim kuwa sun dauka kusa awa shida ana fama, dank iris ya rage zuciyarshi ta buga wanda hakan yasa komai ya tsaya chak ajikinshi, wannan dalilin yasa Muhammad yayi tunanin yam utu don baisan yana da ciwon zuciya ba, shima dai saida aka kare da operation an samu komai ya daidaita saidai kuma ya fada coma.
Hankalin ya Muhammad ba karamin tashi yayi ba lokacin da manya manyan likitocin da sukayi operating dinsu suka mashi bayanin matsalolin yaran, wato bayan ciwon zuciya da ya salim ya kamu dashi wanda yanda tayi mashi mugun kamu don gab take da bugawa a kananun shekarunshi da ciwon kidney da salima take dashi wanda itama badan an cire wanda ta lalace dinba zai jawo dayan da ya rage mata yayi affecting, hankalinshi ba karamin tashi yayi ba, wani irin tausayi suka bashi kamar ya masu kuka don duk gidan bayan ishaq saishi waenda suke da tausayi da jin qan marayu duk yaya alhaji Mustapha.
Daga asibiti ya barsu cikin kulawar likitoci da nurses din dake da duty din daren ranar, sai wajen karfe takwas yabar asibitin ya wuce gida direct, yana isowa bai tsaya ko ina ba sai bangaren sun a samarin gidan, dakinsa ya wuce wanda yake kusa dana wahab, shiga yayi ciki ko ina fess fess, kayan jikinshi ya rage ya wuce toilet don yin wanka, saida ya tsaftace jikinshi kafin ya futo ya wuce bakin gadon sa, saida ya kira asibitin yaji yanayin lafiyar su kafin ya aje wayan, sallolinshi da ake biyanshi ya rama, yana idarwa ko abinci bai nema ba don baya jin zai iyaci don wani irin bacci yakeji sosai.
Haka hajiya kareema tayi zaman jiranshi har kusan karfe goma bai leko bangarenta ba ganin haka ta yanke shawarar neman shi washe gari, damuwa tayi mata yawa, business dinta yana neman yin kasa sbd itama saida ta fitar daga cikin savings dinta wajen fitar da Ibrahim.
?


Washe gari karfe goma ya ibrahim ya shirya fess cikin manyan kaya jumper skyblue, yana gama shirinsa yafuce daga gidan don da alamu yawanci babu wanda ya tashi sai rita dake kai kawo na abinci tana leken shi kamar munafuka aranta tace   chineke, this guy fine dieee, ahhhh  , baima san da mutun a wajen ba ya futo wajen garage din motocin gidan ya kira haladu driver daya kaishi asibiti jiya, suna gab da juya kan motar zasu fice motar haj labiba ta danno kai, yana ganin haka yasa ya tsaida driver ya sauka, domin su gaisa, tana ganinshi cikin fara a ta futo daga bayan mota, takowa yayi har gabanta yace   good morning mummy, na sameku lpy  , cikin fara ar ta ta amsa mashi tare da yabon shi don duk gidan babu wanda ya kaishi daraja na gaba dashi ba kamar sauran ba, wucewa tayi daman tafiya ce ta taso mata zuwa niger don abbanta dake jinya tsawan wata Kenan sai ayanxu kannenta suke fada mata ganin kamar yana gab da rasa ranshi kuma yana nemanta, bayan tace airport dinne jirginsu yayi delay har ta kaiga akayi cancelling flight din saina karfe biyar shiyasa ta dawo gida kawai, tana hawa sama ta wuce dakin hilma don ganin kota tashi don da safe ta shiga dakinta taga tana barcinta hankali kwance, ganin baccin take hankali kwance yasa ta wuce dakinta tana mamakin yawan baccin da hilma takeyi yanxu, gashi yanxu sun shiga 100 level amma kota


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login