Showing 15001 words to 18000 words out of 381117 words

Chapter 6 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

1961

ya kashe wayan nashi.

Kwanciya yayi rub da cikin sa, saida ya kwashi wajen minti ashirin yana jin dripping din da yake kafin bacci ya daukeshi.

AMRA s apartment& .
Tunda haifa ta sauketa a gida, tayi wankanta sannan ta shirya cikin riga da wando na baccinta, ruwa ta debo a glass cup ta zauna a bakin gadonta wayanta a hannu tana jujuyawa, tunani takeyi akan abunda zatayi, saida ta shanye ruwan sannan ta aje cup din a bedside.

Hayewa tayi gaba daya kan gadon sannan ta gyara zamanta ta soma danna wayan, ..rubuta number tayi sannan tayi saving da agent, tana gamawa ta bude message sannan ta fara typing kamar haka   good day to you, i and my best friend called you earlier today around 4;30pm,mun kira ne sbd muna neman taimakon ku, mun karba contact dinne wajen jemima wadda kuka taimaka wa ta samu katin qasa, dan Allah idan har kunyi receiving message dinnan kuyi responding, ina buqatar taimakon ku cikin gaggawa, nagode  tana gama typing tayi sending message din sannan ta aje wayen agefenta ta kwanta, sai wajen karfe uku na dare taji karar vibration, bacci ne mai nauyi ya dauke ta hakan yasa batako san ma an turo message dinba.

Lokacin sallar subh nayi wayanta yayi vibrating, hakan yasa ta mike don yin sallah, tana idarwa ta fara karatun qur ani, sai wajen 6 ta tashi sannan ta wuce toilet don yin wanka, tana fitowa ta zauna kan dresser tana shafa mayukanta cikin nutsuwa, kallon kana tayi cikin mirror, girma yazo mata fah, don sai yanxxu ma budurcinta ke futowa sosai, ko ina na jikinta ya bude tayi kyau sosai sai sheqi takeyi skin dinta na glowing.
Anatse ta gama komai sannan ta shirya cikin wani English gown mai kyau red color, rigar mai kamar flow sai ta zauna dam tayi mata kyau, dukda bata dameta ba, shirin ta tayi a tsanake sannan ta sha tea da pancakes.
Saida ta gama tsaft ta tattara duk wani abu da zata buqata sannan ta wuce parlor ta zauna don tayi requesting ride din da zai kaita, wayan ta bude daman bata wani damu da saka password ba, tana dannawa taga message yayi popping akan screen din da sauri ta bude ganin number da tayi saving da agent, hannunta har karkarwa yake wajen danna message din, da sauri ta miqe ganin reply din da suka mata, wani irin farin ciki ne ya lullube ta, da sauri ta shiga typing   thank you, thank you so much, let s meet later by 5 as you requested  & .
Tana sending ta fara kokarin kiran haifa, haifa wadda harta kama hanyan zuwa office jin karar rining tone dinta yasa tayi saurin picking tace   babes how far? cikin murna tace Haifa tayi responding  wowww hamdullah let s meet at the office ni ina kan hanya na kusa  & ..

Ride din amra na karasowa ta wuce don allah allah take kawai ta ganta a cikin hospital don ta hadu da haifa.
Tana isowa direct office din haifa ta shige wadda itama wayanta a hannu, murmushi dauke fuskanta tace   babe agent dinnan sunyi reply, gashi sunce mu hadu a rosalle private loung eatery by 5, jin haka yasa amra cewa   babe nima sunmin message, kinsan jiya na kasa hakura shine nayi masu message, ashe sunmin reply tun wajen 3 na dare, sai dazu nake ganin reply din, yanxu bari muga zuwa anjiman sai muje ko  & cikin farin ciki da murna suka dunga aikinsu har wajen karfe 2 tayi, tsabar zumundi amra tace   haifa kodai mu tafi tun yanxu mu jira su ne, nifa I can t wait wallahi  dariya haifa tayi mata sannan ta kalleta   babe calm down, ki bari 4 yanayi saimu wuce gaba daya,.
'?('***Auren Katin Kasa ***('
'?
(Unexpectedly fallingd'?
Paid book =???

Chapter 60

KANO NIGERIA
Salima tun sanda wayan rita ya mutu hankalinta ya tashi , ga samu ga rashi, kullum idonta akan motsin rita yake sbd tanason duk yanda za ayi ta lalubo charger kafin ta kamata, ganin yau kwata kwata bataji motsinta ba yasa tayi saurin fitowa, tun kafin takai bakin kofar dakin saiga rita ta yo corner din dakin su, hannunta riqe da kayan da ta sato daga dakin khady, ganin salima wanda dukta jeme a tsaye gaban dakinta yasa ta saurin cewa   keeee what are you doing here, wayace ki fito daga dakin ku?  juyowa salima tayi afurgice tace   dan Allah kiyi hkuri daman yunwa mukeji shine nazo na fada maki  ..tunawa da abubuwan da ta kwaso a hannunta kuma batason salima ta gane yasa tace   jeki zan kawo maku  ..da sauri kuwa salima ta koma daki don kada ta rafko ta.

Haka suka dunga kame kame ita da rita dukda har yanxu bata kamata rudu rudu ba, tun salima na saka rai akan charger harta hakura kawai ta aje wayan cikin kayansu na sawa ta boye.
?
Daddy kuwa duniya sabuwa ya bude, don wannan gidan nasu salima da amra na gadon su, shi ya bada haya wanda tashin farko ya samu kusan 100 million for rent duk shekara, wannan abu yayi mashi dadi sosai, daga gefe kuwa yana sane da su salima da halin da suke ciki, ya kyalesu ne don dasu zaiyi threatening amra domin ta biyashi kudin da yake tura mata, ya bari ne sai sun gama wahala yanda idan ta gansu hankalinta zai tashi kuma daya tambayi abu wajenta bazata qi bashi bashi ba, sannan yana jiran time ne kafin ya fara aiwatar da qudurun shi akansu.
Wannan Kenan& & & & ..
?
?
Abuja Nigeria
?
The taura estate
Babban gidan dake ciki taura estate motar da ta dauko ALIF-SUDAIS daga airport ta kutsa kai ciki, gidane mai dauke da part biyu daya babba daya karemi, tundaga bakin gate zaka gane gidane bana qananun mutane ba, ahankali driver ya soma bude bayan haddaddiyar lexus, farar kafar wanda ke cikin motor ne ya bayyana, ahankali ya karasa fitowa, kyakyawan babban mutumi ne sanye da kundura irin ta masarautr kasashe waje na larabawa kana ganinshi zaka san badan Nigeria ba ne, malam labaran wanda ke zaune gefen bencin mai gadi ne ya dago yayi ma mutumin kallo daya, ahankali ya soma dafe kanshi don idon har ya fara tuna wani abu saiya dafe kanshi dake sarawa, da sauri mai gadin ya karasa ya fara kwasar gaisuwa wajen babban aminin mai gidan, Alhaji kabiru wanda ke saukowa daga benen gaban gidan ne ya karaso gaban abokin nashi, fuskarsa dauke da murmushi sukayi musabaha ta manya,anatse suka fara gaisawa, ahankali alh kabiru yayi mashi iso har cikin tamkeken parlor wanda ke dauke da hoton AMAR DA AMAN DA KUMA AMMA, zama alif yayi akan kujera 3 seater sai kabiru ya zauna gefen tashi wadda itama 3 seater dince suna fuskantar juna, kara gaggaisawa sukayi sannan ya umarci da afara kawo ma baqonshi abin sha.

Amma wadda ke tsaye gaban gas cooker tana juye chicken peper soup ta kalli mai aikinta tace   da alamu baqin Alh sun iso, ki aje sharan da kike ki wanke hannunki ki fara kai masu drinks da ruwa kafin na fito  , amsa mata tayi da to sannan ta wuce tayi abinda aka umurceta, anatse aka shirya komai shaqe gaban su, kafin ammin ta fara fitowa daga kitchen din, sanye ta ke da doguwar riga ta tsadadden lace, wadda ta amshi jikinta sosai kuma tayi mata kyau ba kadan ba, tayi daurin ture kaga arziki wanda ya fito da fuskarta sak irin ta amar , karasowa tayi suka gaisa da alif baqon alh kabiru wanda itadai tunda take da kabiru bata taba sanin ina suka hadu ba, shidai alif din duk farkon shekara sai ya zo kasar kuma zuwan nashi lokaci guda babu sanayya, tun tana mamaki hartazo kuma ta cire kanta daga cikin mamakin hakan don ba huruminta bane.
Suna gama gaisawa ta wuce sama wanda kusan bene uku ne,sallah kawai tayi sannan ta fara laluben aman, don yanxu kwana biyu ya dan natsu yana dan zaman gida,baya fita kwata kwata,kiranshi tayi kusan sau biyar bai dauka ba ganin haka yasa ta kyaleshi kawai tayi kwanciyar ta don tunda alh kabiru ya sanar da ita zaiyi Baki bata zauna ba.

Bata wani dade da kwanciya ba saiga alh kabiru ya shugo, tana ganinshi tayi mamaki don bai fiye shigowa dakin nata ba don ita kanta bata son haka, hannunshi riqe ta milk mai sanyi, karasowa yayi da fara arshi sannan yace,   wifey kinsha gajiya nasan baki saka komi ah cikinki ba, ga wannan na kawo maki  ..abinda yake burgeta ta wani bangare da kabiru, akwai shi da soyayya da nuna kulawa, dukda wani sa in tana jin nauyin karbar ko wace irin soyayya daga gareshi don hakan yana tuna mata da baban amar.

Godiya tayi mashi sannan ta karba, saida ta shanye sannan ya umurceta data kwanta sannan ya lulluba mata bargo don ta samu ta huta, cikin yan mintuna kadan bacci ya dauketa kuwa mai nauyi sosai.

Kabiru na fita ya sauka qasa sannan ya umurci yar aikinsu lantana data je dayan part din domin gyarama baqonshi, tana gamawa kuwa yayima abokin shi iso zuwa dayan bangaren wanda nanne bangaren sa lokacin da matarshi ta farko wato amina maman aman ta zauna kafin ta rasu.
Ba laifi part din akwai dan girma don yana dauke da dakuna biyar da katon parlor, kofofi biyar ne duk kusan iri daya saidai kofa dayace akayi mata wani smart opener handle, suna shiga ciki basu wani tsaya ko ina ba suka wuce dakin, saida alif ya saka thump print dinshi sannan shima kabiru ya saka nashi suka kutsa kai ciki.

Karfe hudu da rabi daidai na yamma yayi ma amra da haifa a rosalle private lounge, dan karamin waje ne kamar sauna, da kuma spa sai wajen shaqatawa, zama sukayi ta wuraren kujerun wajen, kowannensu zullumi ne tap a zuciyoyinsu hade ta kuma dan fargaba, sun dauka wajen minti talatin wajen karfe biyar da rabi saura,   are you amra?  jin an kira sunan amra yasa suka dago da kansu atare, wata matace wadda akalla zata kai shekaru 35 harda yan kai, miqewa sukayi atare gaba dayansu suna kallonta, sanye take da kayan ma aikatan wajen, kamarma itace ke handling wajen spa din, murmushi tayi masu sannan tace   lets go  ..atsorace suka fara binta har cikin sauna, inda ta basu kayan spa suka saka bathrob mai laushi, kofar dakin sauna shige suka bita har ciki, wuri suka zauna itakuma ta fara hada incense saida ta gama tukunna ta zaune gefensu tace   na barku a zaune tun daxu ko, daman inason na tabbatar da gaske kuke kafin na bayyana agabanku,  ..murmushi sukayi atare sai a lokacin suka danji dama dama, kallonta haifa tayi sannan tace,  mune muka kiraki jiya ni sunana haifa wannan kuma amra  ..ta nuna amra, saida suka gabatar da kansu kafin ta tambaye su dalilin nemanta da suke, nan suka fada mata komai game da buqatarsu basu boye mata. Shuru tayi nayan mintuna kafin ta dago tace   na tausayama halin da amra take ciki, amma ni ayanxu na daina harkar taimakon samun katin qasa, don kamar yanda kuka gani ni worker ce anan, wannan ne abinda nake yi don na taimaki kaina  ..shuru amra tayi hawaye na zubo mata ta tsugunna har qasa gaban matar tace   aunty ki taimake ni, wallahi qanne na suna cikin mawuyacin hali, inason taimakon su  .. tana kaiwa ta fashe da matsanancin kuka sosai, kallonta matar tayi, zuciyarta ta gama karaya tace   get up please kinji, zan taimaka maki, amman duk abinda ya buyo baya babu sunana aciki,kuma baku sanni ba baku taba ganina ba sbd I can t risk my own life and my children,  ..miqewa amra tayi tana share hawayenta sannan suka fuskanceta dakyau suna sauraron abinda zatace   first of all, shi katin kasa na nan dubai yana da wahalan samu sosai, na farko akwai hanyar aiki wanda akeyima government for 30 years kafin asamu, na biyu kuma auren dan kasar wanda shi kuma shekara biyar akeyi kafin asamu shikuma dole ki biya wanda zai aureki kuma kudi ne mai yawa sosai, na uku shine idan kinada wanda kike soyayya dashi kuma sai marriage consent group management sunyi bincike akan soyayyar taku don ke ba yar qasar bane, hadarin wannan shine yawanci kasarnan basa yarda da auren wanda ba cikin al adarsu yake ba,so if acikin danginshi an samu wanda basu amince da auren ba koda kuwa yaro ne dan shekara hudu to fa auren bazai yuwu ba,ahaka ma acikin uae marriage consent group idan aka samu wanda bai gamsu da soyayyarku ba to shima hakan zaisa aqi approving din katin kasar.

Jin wannan tashin hankali yasa suka kasa cewa komai, haifa ce tayi kokarin tsaida natsuwanta tace   yanxu sister babu wata hanyar? kallonta matar tayi sannan tace  gaskia babu ayanxu saidai ku zabi daya aciki, zanyi kokari ni kuma daga nan na taimaka maku yanda zaku tafiyar da komai cikin sauqi dan komai yana da wahala dole sai tayi preparing kanta  , & kallon amra matar tayi sannan tace   why are you silent, I thought da bakinki kince kinason taimakon yan uwanki, har kin karaya ne tun daga yanxu, in kinsan zaki karaya dakin fada min tun wuri da bazan tsaya ba ina bata lokaci na ba  mikewa tayi zata tafi da sauri amra ta riqo hannunta tace   dan allah aunty ki tsaya, na amince ki zabamin duk wanda yafi sauqi don na taimaki yan uwa na  & ..jin haka yasa matar ta dawo ta zauna kusa dasu tace   okay, yanxu dai aikin government bazai yuwu ba, so kinada wanda kikeso anan kuma dan qasar??  ..girgiza mata kai amra tayi alamun ah ah,..nunfasa matar tayi sannan tace   okay yanxu kinga guda biyu cikin abinda nayi listing bazai yuwu ba, yanxu last option, kinada 50,000 dollars da zaki iya badawa, shima zanyi kokari ne na roka maki&   jin wannan uban kudin yasa amra da haifa zaro ido atare sukace   50,000 dollars  !!!!!...kallon kallo sukayi fuskar amra kamar tayi kuka tace   ni arayuwata ban taba riqe less than 10,000 dollars ba  ..haifa ma hankali atashe tace   ni yanxu konaje na nema wajen abu bazan taba samu ba  & kallonsu matar tayi sannan tace then I can t help you guys saidai idan tsoho zaki aura, ana samunsu beggers dinnan, idan muka samu wani mai sauqi zai karba 30,000 dollars,  & jin haka yasa haifa saurin cewa no bazai yuwu ba, banda homeless mutane, girgiza kai matar tayi sannan tace   well babu abinda zan iya maku yanxu  ta tashi ta nufi hanya zata wuce, shesheqar kukan amra ne ya tsaidata ahankali ta tako har gabansu sannan tace,  there s only one solution and it s the very risky of all, amma shi a cikin shekara daya zaki samu katin qasa and naji ance bashida wani tsauri da long process  ..jin haka yasa suka miqe suna kallonta itama kallonsu tayi sannan ta cigaba  the only last option is getting an army officer, be it senior or junior, that s the only solution  tana kaiwa nan ta fice abinta tana cewa   duk yanda kukayi deciding you can contact me  & ..hankali atashe suka fito daga sauna suka chanza kayansu wanda suka aje ah spa lockers din wajen,& gida suka wuce kowannen su zullumi cike aciki zuciyansu.
?
Aranar amra bata samu issanshen bacci ba, tabbas solution daya gareta wanda shine neman army officer, amma yanxu wata sani da zata nema taimakon wajen shi, har wajen karfe uku na dare bata runtsa ba, salla ta mike tayi sannan ta roka allah ya kawo mata mafita cikin gaggawa.
'?('***Auren Katin Kasa ***('
'?
(Unexpectedly fallingd'?
Story and written by:
QueenMarh=?x?

Paid book =???
Chapter 61
Washe gari ta shirya lokacin casual dressing dinta abaya baqa, tayi mata kyau sosai batako tsaya shafe shafen data saba ba ta wuce asibiti, koda ta isa haifa bata zoba, anatse ta soma rounds check up dinta sannan ta dawo office ta zauna tana tunani, sai wajen karfe tara haifa tazo, itama kwata kwata babu nutsuwa a tattare da ita, sai wajen karfe 11 ta miqe don zuwa karban blood samples, don yanxu komai ya dawo hannunta tunda hafiza ta tafi hutu,anatse take tafiya da box din hannunta kamar babu jini ajikinta don har wani jiri jiri take ji tsabar damuwa tayi mata yawa, ahankali take tafiya harta shiga cikin headquater, saida ta fara da 2nd floor wanda duk senior officers ne, tunanin abinda matar nan ta fada mata ne ya fado kanta, da sauri ta daidaita natsuwarta don ta samu ko wani zai kulata, fuskarta a sake take shiga office dinsu tana gaishesu, ko kallo bata ishesu ba kuwa, haka ta ta gama da senior officers kafin ta wuce sama domin diban sample din general, rabonta da office dinshi tun abinda ya faru tsakanin su kwanakin baya, anatse ta fara knocking har sau biyar kafin yace  come in  , shiga tayi atsanake sannan ta gaishesa, baiko kalleta ba don yama manta da mai kama da ita a duniyar, anatse ta soma mashi Magana   sir I m here for your blood sample  jin haka yasa ya dago ya mata kallo daya, sai kuma ya kawar da kanshi sannan yabar abinda yake ya tako har gabanta ya tsaya sannan ya warware hannun rigarshi, tunawa da abinda ya faru kwanaki yasa ya tsaya a tsaye yaqi zama don gudun samun matsala, distance din tsakanin su kuwa da tazara sosai, ahankali ta fidda duk abinda zata buqata sannan ta matso dab


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login