Showing 210001 words to 213000 words out of 381117 words

Chapter 71 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

2506

don haka ya juya kawai ya wuce paediatric ward daman nan yake aiki.
Tunda ta karbi basket din ta juyo batayi gigin dagowa ba ta wuce cikin dakin.

Tana shugowa ta tsaya chak tana shirin sakin basket din Ganin ammah a zaune, salima a gefenta da aman sai wata nurse a tsaye tana examining dinta, da sauri amra tace  ammah!!!!
Hakan ya fargar dashi daga sake sakin da yakeyi na magani ta da zaiyi na abunda tayi, da sauri ya shugo cikin dakin jin ta ambaci ammah, da sauri ya karaso ya tsaya kyam shima ya kasa motsawa yana kallon ammah dake kallonshi fuskanta dauke da murmushi tana miqa mashi hannu shida amra, cikin sauri ya karaso inda take salima na Ganin haka ta matsa fuskanta a washe dan dadi, aman ma wani irin dadi yake ji tun daga dare jiya zuwa yau don tun wajen karfe biyu ta farfado, dukda batayi magana ba alokacin Har zuwa yanxu,
Hannunta yayi saurin kawowa ya rungumeta sosai fuskanshi dauke da murmushi da farin ciki, gaba dayansu. Kallonshi suka fara yi don kusan zasu ce this is the first time suka ganshi cikin farin ciki babu abunda yake cewa sai  Alhamdulillah ya Allah alhamdullah
Saurin dakin ammah yayi yayi sujudul shukr ya godema allah, dukkansu suka kallonshi sukeyi kowannanen su fuskanshi dauke da murmushin jin dadi, amra dai baya ta danyi ta kafa masu idanu shida ammah, babu abunda yake hangowa sai tsantsar kaina da yake yima ammah sosai, saurin mikewa yayi ya sake rungumeta yace  ammah na ammah!!!
Shafa kanshi tayi hannuna na yin karkarwa tace  so& son runtse idanunshi yayi don bai taba tsammanin zai sake jin sunan a Bakinta ba, fadin irin farin cikin da yake ma bata lokaci ne,  son tun yaushe nake kwance anan?
Dagowa yayi ya kalleta tare da riko hannunta biyu murya shi chan kasa yace  don t worry ammah, Zan fada maki komai
Maida kallonshi tayi kan nurse yace  yaushe ta farfado, why didn t you inform me? Ya karashe yana kallon Aman, shuru Aman yayi kafin ammah ta kalli Amar  son ina daughter? Waigowa sukayi nan amra ta tako Har inda ammah ke zaune akan gadon marasa lafiya an tokare bayanta da pillow, hawaye ne kwance fuskanta tayi saurin karasowa inda yake zaune, zame hannunshi ammah tayi ta rike na amra tace  daughter ya kike? Meysa kika rame sosai
Fashe wa amra tayi da kuka har tana dan tureshi ta rungume ammah sosai a jikinta  Alhamdulillah ammah na Allah Kun Gode maka, mun shiga fargaba sosai ammah
Shafa bayanta ammah tayi kamar ba surukarta ba tace  why are you crying dear, ya isa haka kukan, sai mu gode ma Allah ko kallonsu Amar yayi ya kalli amra ya tabe baki, mamakin yanda ammah ta nuna damuwa akanta karara yakeyi daga farfadowarta
[7/11, 11:17 PM] +218 92-2035171: Update continuation
Matsowa su salima suma sukayi don ayi dasu,kowannen su kana ganinshi kasan yana cikin farin ciki, kallonsu ammah tayi gaba ayansu tana jin wani dadi a cikin ranta sosai dukda bata san dalilin kawota asibitin da ayi ba saidai doctor da yazo daxu yayi mata bayanin kusan satinta guda akwace anyi mata operation saboda zuciyanta daya buga, suna nan zaune doctor ya shugo fuskanshi dauke da murmushi yace   masha allah, hajiya allah ya albarkaci zuria arki, babu wanda ya runtsa gab dayansu saida kika farfado, allah ya kara lafiya 
Godiya sosai duk sukayi ma doctor kafin ya buqaci ganin amar a cikin a office dinshi, mikewa yayi ya bi bayan doctor, yana tashi amra na zauna a inda ya tashi tana jin dadin, kallon ta ammah ta sakeyi tace   daughter meysa kika rame? Bakya cin abunci ne? 
Salima ce tayi karaf tace   wallahi ammah bata ci, kullum sainayi mata Magana batason cin abunci saidai barci kamar shine abuncinta  juyowa amra tayi ta galla mata harara,
Murmusawa ammah tayi tana jin wani irin dadi aranta ta riko hannunta tace   allah yayi maki albarka daughter, allah ya tsareki ya sanya farin ciki a cikin rayuwarki, doctor yayi min bayanin komai 
Sunkuyar dakai amra tayi tana jin wani iri, muryanta chan kasa tace   ameen ammah, allah ya baki lafiya 
Gaba daya suka amsa da ameen, salim ne ya sake mastowa inda ammah take ya rike hannunta, kallonshi ammah tayi ta shafa fuskanshi   hope kaima kana cin abunci? 
  chap wannan ay baya barin kwano  salima ta fada tana hararshi, dariya sukayi gaba dayansu banda aman daya sunkuyar da kanshi, saida ammah ta dago ta kalleshi   son, zo  ta fada tana kallonshi, amra ce ta matsa mashi gefe ya zauna ya riko hannun ammah ya sumbaceta yace   allah ya baki lafiya ammah, we miss you a lot 
Shafa kanshi ammah tayi tace   I miss you all too,ka fito min da mata aurar dakai kaima zanyi karka tsufan min a gida  dariya sukayi gaba dayansu
Banda salima data hada kirar sama da kasa gabanta na faduwa, dan dagowa yayi ya kalleta ganin tayi gum kamar ba itace ke zolayar amra da salim ba, kauda kanshi yayi daga kanta ya kalli ammah yace   insha allah very soon ammah  ya fada yaan murmusawa, gaba daya hira suka dunga yi mata suna saka ta dariya banda salima data koma gefen kujera ta hade rai jikinta a mace da maganar da aman yayi, tuaani ta soma yi aranta wato harya samu wata Kenan, saurin danne abunda ke ranta tayi don tana gab da fashewa da kuka, ya lura da ta don haka bai damu bay a kauda kanshi ya cigaba da hirar da sukeyi dasu ammah.
?
Amar na shiga office din doctor ya zauna ya kalleshi, nunfasawa doctor yayi yace   alhamdullillah sir saidai mu godema Allah, jikinta yana da kyau sosai don masu larura irin tata da wuya ake samun waenda suka rayu, bazamu sallameta yanxu ba saboda zamuyi watching jikinta for couple of days don mu tabbatr da komai koma normal, bayan wannan inason nayi informing dinka akan abu daya da bamu fada maka ba saida mukayi bunciken mu tukunna, a cikin magungunan da akeyi ma hajiya prescribing wanda doctor hafiz ke bata mun gano akwai maganin da bai kamata ya bata ba, wanda yayi violeting medical rules dinmu,board member sunyi suspendin dinshi akan wannan dukda yanxu kusan sati guda Kenan rabonda yazo nan asibitin, bazamu hanaka kai kara ba idan har zakayi dukda zaiyi tarninshig imagine din asibitin, saidai muna neman alfar.. 
Dagowa yayi ya kalli doctor din ya katse shi   no need for that, saidai inason ku duba staffs dinku da kyau, I will turn a blind eye on this saidai babu next time 
  yallabai muna fatan hakan bazai s aka cire membership din asibitin  doctor ya tambayeshi.
  duk wani tallafi da company sukeyima asibitin nan baza a daina ba saidai bana buqatar service dinku  yana kaiwa nan ya mike ya bama doctor hannun shi kafin ya fuce daga office din a wuce dakin ammah, da sallama ya shugo, gaba dayansu waigowa sukayi suka zuba mashi idanu suna kallonshi, wani irin mugun kallo ya zabga ma amra dayasa ta dauke kanta daga kanshi ,ammah ta lura dasu saidai bata ce masu komai ba saima kallon amar da tayi tace   son harka dawo?, yaushe zasuyi discharging dina? Kasan yanda bana son zaman asibiti kwata kwata, kaarsowa yayi cikin dakin ya zauna bakin gado yace   no ammah ba yanxu ba tukuna sai doctor sun tabbatar komai ya dawo normal tukunna 
  no son, kaje ka masu Magana su bani sallama naji sauqi 
  ammah please to ki bari zuwa gobe, kinga ko dinkin da akayi maki baiyi healing ba  ya fada a marairaice, amra ce tayi saurin kaste ammah dake shirin mashi Magana tace   ammah please, ki bari kiji sauqi sosai saimu koma gida 
Kallonta amah tayi tana murmushi tace   toh shiknan daughter allah ya kaimu 
Gaba daya suka amsa da ameen banda amar dayake kallon ammah da amrar yana mamakin yanda ammah keyi mata ba.
?
  sister inalw yau babu breakfast ne  aman ya fada yana kallon inda amra ke zaune don ya tashi ya bata kujerar gaban ammah, sai alokacin tama tunada basket data shugo dashi, kallon inda salima ke zaune lost in her thought tayi tace   laa bata zuba maku ba, nazo da breakfast gashi nan a basket  amra ta fada tana mikewa ta bude kwandon ta zaro kulas din abuncin gaba daya da plates, kallon inda ammah ke kwance tayi tace   ammah fa? Doctor yace zata iya cin abunci   amra ta tambaya tana kallon inda salima ke zaune, aman ne ya amsata don salima kwata kwata batsan sunayi bama   no not yet saboda operation di da akayi mata 
Sauke kanta kasa tayi ta zuba ma aman abunci kafin ta zuba ma salim ta miqa masu, godiya aman yayi mata kafin ya koma wajen carpet ya zauna ya soma cin abunci.
Ammah ce ta kalli salima dake zaune akan kujera tace   daughter bazakici abuncin ba kema 
Takowa inda take zaune amra tayi ta dan buge kafadarta tace   bakiji ana Magana bane 
Furgigig ta dago tace   naam? Kinyi Magana ne? 
  abunci? Bazakici bane ke, tunanin me kikeyi  amra ta tambayeta
  sai anjima bana jin yunwa,  salima ta fada tana doka tagumi, yar tsuka amra tayi ta wuce inda basket din yake ta fiddo da plate zata zuba mata tana dan haki,kallonta ammah tayi tace   daughter ki kyaleta idan batasonci yanxu, kizo ki zauna ki huta haka nan ki daina wahalar da kanki 
Kallon ammah amar yayi, ita dake kwance bata da lafiya shes showing so much concern for amra,bai kawo komai aranshi ba saima danganta hakan yayi da maybe taji cewa amra ce ta bata jininta.
?
Sun dade sosai wajen ammah hara man ya fita ya karbo masu lunch a kitchen, nan suka baje sukaci, banda amra dataci kadan ta ture tace zuwa anjima zata kara, salima kuwa haka ta zauna sukuku tana tunain maganr aman da yayi dazu, shiko ya lura da ita kuma yana karantarta saidai bai fassara hakan da komai ba don bayason ya sama kanshi false hope.
?
Da daddare nan yace wajen ammah zai kwana, amra dai ta kafe saita kwana while salima na ikirarin yau a wajen ammah zata kwana, ammah dai na zaune tana kallonsu tana jin dadi aranta, kallonsu duka yayi yace   babu wanda zai zauna duk ku tafi gida 
Turo baki amra tayi bata kalleshi bat ace   ammah dan allah ki mashi Magana inason kwana anan 
Dariya amma tayi tayi   daughter kiyi hakuri ki koma ki huta abunki kinji, nida na kusa dawowa gidan ma, gobe da safe sai aman ya dawo daku 
Kallon amr ammah tayi tace   kaima son dam aka biyu you don t have to stay tunda ga doctors da nurses, kuje ku huta 
  no ammah I will stay with you, banason mu tafi gaba daya babu wanda zai tsaya a wajenki 
?
Haka nan badan taso ba ta bisu suka wuce gida tana jin haushinsa na qin barinta da yayi ta zauna da ammah.
Suna fita shima ya fita ya kira doctor don ya sake duba ammah don ya tabbatar da babu abunda yake damunta, a cikin daren ya kira doctors yafi sau biyar duk after 20 mins, ammah dai kallonshi take tana jin kaunarshi sosai aranta.
Wajen karfe?goma suna zaune yana matsala ammah kafafunta da suka kumbura don komai daga kwance take yinshi, kallonshi tayi tace  son,& !
Yana jin haka yasan maganar da zatayi don haka yace  Ammah please mu bari saikin samu sauki inmun koma gida please
 No, yanxu nake son muyi magana ta fada seriously
Sauke kanshi yayi kasa bai sake cewa komai ba saida ta tace  will explain abunda ya faru kafin ku kawo ni nan ko Saina tambaya? Ta fada tana kallonshi fuskanta a hade,
 Ammah Duk abunda nayi she deserves more than that, bazan taba tsayawa ina kallon wadda ke shirin illataki ba ya fada ran shi Adan bace
 Muhammad sai yaushe ne zaka rage wannan halin naka na kaifin zuciya? Muhammad mace Ka kusa illatawa fah? Duk laifin ya bazaka kaita ga hukuma ba?
Dago da jajayen idanunshi tayi da sukayi jaa sosai yace  ammah kashe kinga taso yi?
 Yea na sani, and tun ba yanxu nasan da hakan ba ammah ta amsa shi, sa mamaki yake kallon fuskanta don jin Karin bayani.
 Yea son, nasan lanatan tana saka min kwaya a cikin green tea kuma Ina sha ammah ta fada kai tsaye
 But ammah why? Kinsan illataki zatayi kika sha
 Kwarai kuwa kuma nayi hakan ne saboda idan har ban karba ba zasu biyo ta wata hanyar, shiyasa dana ga hakan na karba,
Mikewa tsaye yayi yana zarya tsakanin dakin hannunshi Har karkarwa yake,  ammah whyyy, kinsan how tough it was for me seeing you akwance ammah? I thought zaki mutu, rayuwa a cikin kwananin turns upside down ammah
Hannu ammah ta miqa mashi alamun yazo, takowa yayi inda take ya rike hannunta kafin ya zauna, anatse ya soma mashi magana,  son, Duk abunda kaga ya faru da mutun rubutacce ne, Allah ya kaddara hakan daman zai faru, yau kina mutu nasan nan barka kai kadai ba
Nunfasawa tayi hawaye na zubowa a fuskanta, furgice yayi sosai idanunshi sunyi jaa ga hawaye nan kwance cikin idanunshi yaqi bari su sauko don yana son ya zama very strong,  son, nasan at this point kasan komai basai nayi maka bayanin komai ba, wannan azzalumin mutumin bazai taba gamawa da duniya lafiya ba, ya cuce mu ya cuci alummar musulmai gaba daya,
Hannunta ya rike gam ya kalli ammah yace  hawayenki bazan taba bari su zuba a banza ba, tun bayan lokacin dana gane shine ya kashe dada, I can t even imagine how you ll feel shiyasa nayi alkawarin boye maki Har labari na saidai ayanxu bana jin Zan iya barin mugun mutumin nan ya sake nunfashi a dorar kasa, I will make his life miserable,
Kallonshi amma tayi tace  no son, bazakayi haka ba, your hands are clean kuma bazan so hannunta ya baci ba Ka barshi da allah da hukumar ta mashi hukunci daidai da abunda yayi, mutuwar dada dai bazamu taba dawowa dashi ba, so promise me bazakayi komai ba, zaka barshi yaji da masifar duniya acahn kuma Allah zai saka mana
Runtse idanunshi yayi baya jin zai iya hakan don babu makawa saiya kashe kabiru, don achan uae yana da rights din hakan don basa barin mai laifi nan kuwa saidai ace za ayi sentencing dinshi life in prisonment, girgiza kanshi ya soma yi ammah na Ganin haka tasan gardama zaiyi mata don haka ta hade rai tace  idan har kana jin magana ta a matsayin mahaifiyarka kuma kana bin umarnina dole kayi abunda Nace maka Muhammad, baka gani ne son, kayi tunanin akan dalilin dayasa na karbi kwayar nan nake sha over the years ban fada maka ba dukda nasan illatani takeyi slowly? It s because I don t want you to be like him wanda na tabbatar hakan yake so, yana son yaga Ka zama miserable baka da zuciyar imani which I m seeing now, shiyasa yayi amfani da zafin zuciyarka da weakness dinka, kasan yanda kayi breaking heart dina?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? lokacin da kake dukan lantana harna fadi? I never imagine my big zaiyi haka nan taba tsammanin zafin zuciyanka zaisa Ka daki mace ba Duk laifin datayi koda kuwa kokarin kasheka taso yi, na dauka kai mai tunani ne, yanxu haka zaka zauna da matanka da wannan zafin zuciyar?itama zaka duke ta kenan? Idan zaka iya dukan mace zaka iya dukana nima a matsayina na mahaifiyarka kenan idan ranka ya baci ko?
Saurin girgiza kanshi yayi dake kasa ya dago da sauri idanunshi yayi jaa  ammah I will
Never bazan taba yin hakan ba, not only you ko wace mace a duniya nan harma da aisha bazan taba yin haka ba, ,
Nunfasawa yayi ya cigaba  itama wannan bansan may ya shiga kaina bane, because ban taba tsammanin zatayi kokarin kashe ki ba, please forgive me ammah na
Kauda kanta gefe tayi kafin ta ce  this should be the last time Muhammad da zaka saka hannu Ka akan mace,
 Insha Allah ammah na ya fada jiki a mace
Juyowa tayi ta sake kallonshi tace  and lastly naga kamar babu abunda ya sauya tsakaninka da matanka, dukda kaga yanda ta sanadiyarta Allah ya nufa zan rayu saboda jininta dake yawo ajikina saurin cije lebe ammah tayi tunawa da wani abu kafin ta cigaba  Muhammad Wallahi ko bayan raina Ka rabu da aisha ban yafe ba, aisha macece ta kwarai mace ta gari, Wallahi bazaka taba samun mace kamarta ba a duniyan nan, kasa a yanayin da take ciki kuwa ammah dukda haka ta jajirce bata damu da hakin da zata shiga ba ta bani jininta, Muhammad muhammad hmm gwara ka bude idanun Ka tunda wuri yanxu ya kamata kasan cewa bazamu rayu ba atare Har abada dole dayanmu zai tafi.
Tana karashe ta sauke zazzafan nunfashi yanda zaka san ranta ya Sosu sosai da zancen,
Saurin rike hannunta ya sakeyi idanunshi sunyi jaa jijiyoyin kanshi sun fito sosai, aduniyar nan babu wadda maganar ta ke sashi shiga rudani kamar ammah,  ammah I ve accept her, Wallahi na karbeta bazan taba rabuwa da ita ba I promise you that
 Look bawai sabodani ko dan na fada


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login