Showing 285001 words to 288000 words out of 381117 words

Chapter 96 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

2028

dan dagowa yayi ya kalli ammahn kafin ya sauke kanshi   wani aiki nasaka ayi shine akayi min shirme 
Ammah dai bat ace mashi qala ba don ta lura da yanda ya yanayin nashi bayan futarsu amra, babu abunda tke sai murmushi aranta ta so Magana   zama ka saukar da wannan ego din naka ne 

Zumbur ya mike tsaye ya wuce bedroom dinshi, cikin yan mintuna qalilan sai gashi da key a hannunshi, don gaba daya hes anxious akan futan nata, gani yake kamar wani abu zai sameta ko kuma za a kalleta wanda hakan ke tayar mashi da hankali sosai, ganin ya nufi hanyar futa yasa ammah cewa   futa zakayi? I thought kace yau wuni zakayi a gida 
  akwai wani abu da zanje na karba ne  ya amsata
  okay adawo lafiya  ammah ta fada tana dauke idanunta daga gareshi tana dan murmusawa irin nasu na manya.

Yana futa ya wuce wajen zabgegeiyar benz dinshi ya budeta ya shige ciki, cikin hanzari ya kunna motar yayi reversing, wani irin mahaukacin horn yayi don gab daya securities din suna cikin cctv room sai karar horn dinshi sukeji.
Da sauri daya daga cikin securitis din ya futo ya bude mashi gate din, a harzuke ya karaso da motar inda securities din yake ya zuge glass din motar ya soma Magana cikin fada   what the hell is going on with your head? Kana son loosing job dinka ne?
Da sauri secuty yace   no sir sorry sir 
  so you better do your job properly, this is your last warning  ya karashe yana fuzgar motar aguje kamar zai tashi sama, bin kan titin estate din ya farayi don street kusan uku ne a cikin estate din, haka yabi first street baiga alamunsu ba, gaba daya ranshi a dagule yake shi kanshi ayanxu kasa controlling kanshi yakeyi akanta, haka ya dunga bin street din estate dinnan yana zagayesu yana dawowa tass bai samesu ba, saida yazo dab da last street ya hangosu daga chan nesa, rage gudun motar tashi yayi ya soma tafiya ahankali, nan ya soma hangosu da kyau, tana daga zaune kan wani dakali wajen kofar gate din wani apartment salim na daga gefenta shima a tsaye yana wasa da wani farin cute kare, itama idanunta nakan Karen tana kokarin shafa kanshi, saurin taka burki yayi kiii lokacin da wani mutumi ya fito daga cikin apartment din yana masu Magana, dan jim yayi yana kallonsu zuciyarshi na boiling sosai, abunda ya kara harzuka shi shine ganin tana murmushi tana shafa kan Karen wanda mutumin ya janyo ring din da ake kama Karen dashi da alamu nashi ne, amar dai idanunshi sunyi jaa sosai, ranshi yayi mugun baci sosai har baisan lokacin daya karaso inda suke da mot aba ya zuge glass din motar fuskanshi babu annuri yace   get in 
Tunda ya tsayar da motarshi amra ta dago ta kalli motar,baka hango na ciki don saida ya zuge glass din ta ganshi, gabanta ne yadan fadi haka kawai ba tare da sanin dalilin ba, ganin yanda fuskanshi ta hade sosai yasa ta danji wani iri,   do I have to repeat my self 
Mikewa ta soma yi ahankali tana kokarin mikewa, kafanta da ya dan sake mata ya jaaa jinni ne yasa ta danyi baya ta danyi kara   washh  da sauri mutumin ya mika hannu zai taimaka mata karta fadi kasa, aamar da yaga haka yayi saurin buga mashi tsawa   don t you dare, don t you dare touch my wife!!!!! Are you insane!!! 
Yanda yake fada a cikin motar da yanda gaba daya a susuce yasa gaba dayansu suka sha jinin jikinsu harma da mutumin, kallonshi mutumin yayi in a calming tone yace   sorry yallabai, naga zata fadi ne shine!!! 
  shut the fuck up ka wuce cikin apartment dinka ko na koreka daga.. 
Kallonshi mutumin ya dunga yi tun lokacin daya soma Magana, sai a lokacin ya lura da koma waye,   the owner of the estate,  ya fada aranshi, cikin sauri ya akste amar daga abunda yake shirin fada yace   dan allah kayi hakuri sir, tsautsayi ne  yana kaiwa nan ya wuce cikin apartment dinshi da dan Karen sa a hannu.
Amra dai komawa tayi baya ta zauna saboda zugin kafarta, idanunta sunyi jaa sosai,   keee  amar ya sake fada yana kallonta, bata dagoba don at this point dayace kee dinnan ya hasalata sosai   idan kika bari na sake repeating kaina saina&  
  saikayi me?  tayi saurin katseshi ranta a bace, itama idanunta yayi jaa sosai, mai ciki da jaraba, lokaci guda idanunta ya rufe ta soma Magana   nace me zakayi min? dukana zakayi?, ehhh? da fada da dan karfi daya salim matsowa kusa da ita yana jan gyalenta alamun tayi shuru, saurin ture hannunshi tayi ta hankadashi gefe idanunta yayi jaa sosai bata ji bata gani   matsamin a waje kai kuma, 
Tana fadin haka ta maido da idanunta kana amar   ina ruwanka dani yaya? Naga dai baka damu da alamarina ba? Baisa yanxu kake shiga cikin rayuwata?,  
Ranshi ne yayi mugun sosuwa don haka ya mata wani irin kallo mai wuyar fassara, cije lower lips dinshi yayi ya fusgi motarshi yabar wajen yana jin haushin kansa da yanda ya sauke kanshi har tana iya fada mashi Magana, gaba daya maganganunta basu bashi haushi ba sai Kalmar dukana zakayi datace, abun ya bata mashi rai sosai, me take nufi Kenan? Hes not that ruthless, bazai taba koda bugun hannunta ba saboda tana da wani matsayi babba a zciyarshi.

Yana barin wajen ta sauke wata ijiyar zuciya don batayi tunanin zasu wanye da sauqi haka ba don duk a tunaninta da sanin da tayi mashi da zafin rai bazaiyi shuru yayi walking out haka ba, salima e daya rakube gefe ya tako inda take ya rike hannunta ya taiamaka mata ta mike suka bi hanyar dazai maidasu gida.
Cikikin yan mintuna ka??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????lilan suka karaso gida, babu abunda take sai haki har suka karso cikin gida, ammah suka tadda a zaune yanda suka barta   sannu daughter kinyi kokari 
Murmushi kawai amra tayi ta samu waje ta zauna ta mikar da kafarta   washh ammah na gaji anya zan iya kuwa 
  zaki iya mana daughter, sannu haka zaki dage harki saba ammah ta fada tana kallonta
  dauko min ruwa mai sanyi salim  amra ta fada tana kallonshi
Mikewa yayi tsaye ya wuce kitchen kallonta ammah tayi tace   ku hadu da son akan hanya kuwa yanxu shima ya futa 
Hade rai amra tayi tadan tabe baki kafin tace   eh munga fucewarshi lokacin muna dawowa  & ..
[7/11, 11:17 PM] +218 92-2035171: Update
Unedited page
Hade rai amra tayi tadan tabe baki kafin tace   eh munga fucewarshi lokacin muna dawowa 
Shuru ne ya biyo baya bayan dawowar salim da ruwan data buqata, tunda tayi resting bayanta ta soma jin barci barci sama sama, ammah na dake duban ta jefi jefi tana ganin yanayinta tace   dear kije ki kwanta kafin anjima da yamma saiku sake futa ko? 
Kamar daman jira take ta mike tsaye tana dan yin nishi sama sama   toh ammah, 
Tana kaiwa nan ta wuce hanyar stairs zuwa dakinta, datayi dan taku daya biyu saita huta kafin ta cigaba, ammah na kallontta daga zaune, fadin irin farin cikin da take ji idan ta kalli amra dake dauke da cikin Muhammad mara misaltuwa ne, shes so happy, kusan kullum sai tayi sadaka, duk dare kuwa bata barcin daya wuce awa biyu, haka zata tashi ta kafa goshinta akan sallaya tana godiya ga Allah daya basu wannan kyauta ta musamman, she s just waiting for the perfect time ta fada ma Muhammad, dalilin dayasa ta boye mashi kuwa shine, yanda ta lura yana qaunar amra sosai amma yaqi futowa fili ya nuna yana son ta, bayan wannan tafison sai ya nuna yana buqatar matarshi da kanshi kuma yayi accepting dinta da kanshi kafin ta fada mashi. Ayanxu ta zuba masu idanu tana karantarsu sosai, daya daga cikin abunda ta lura dashi shine, yanda yake pushing amra don duk hidimar datakeyi mashi akan idanunta ne shi kuma yana basarwa saboda ego dinshi daya kasa barinshi ya saukar da kanshi kasa, da farko taso ta barsu a yanda suke ko zasu dawo dan kansu saidai kuma amaimakon komai ya falling into places sai akasin haka, don yanda yake pushing din amra yasa take baya baya dashi, don da gayya ammah take aikata dakinshi don ta lura ta daina kwana anan dinma, bata takura mat aba haka ta kyaleta tana kwana inda takeso saboda yanayin ta.
Nunfasawa ammah tayi tana tunanin, harga allah tana son tagansu kamar kowanne mata da miji, saidai hakan kamar bazai samu ba saboda kafiya irin ta amar, tunanin yanda zatayi dasu ta fara kafin takai kan decision dinta.
Tana nan zaune salim na gefenta yana barcin daya saba a doguwar kujera akayi sallama, kallon inda yake shugowa ammah tayi fuskanta dauke da fara a da bata barin fuskanta,   malam labara maraba lale 
Har inda take zaune ya karaso ya zauna a kasa ya fara gaisheta   nace ka daina zama a asa malam labaran, ga kujera nan manene amfaninta kenan 
Cikin girmama way ace   hajiya nan ma yayi, ina wuni ya iyali? 
  lafiya kalua alhamdullahi ya aykin gona?,ya kuma jiki 
  da sauqi hajiya alhamdullahi,   ya bata amsa
  toh madallah allah ya taimaka  amma ta amsa shi tana kokarin kallon tv.
Hannunshi ya zaro cikin aljihun shi yace   hajiya ga wannan, kudin wannan shekarar ne, shine nace bari na akawo 
Kudin ya ajiye mata da paper a gefe   wannan list din komai ne na rubuta a ciki, murmusawa ammah tayi ta kalli kudin daya nade a leda kafin ta maida idanunta kanshi,   masha allah, ka rike a hannunka, duk wani abunda za a buqata a gonar saika saya dashi sai kuma amfaninka kaima 
Kanshi a kasa yace   hajiya akwai duk wani abunda za a buqata, wannan&  
  Toh ka rike kaja jari  ammah ta kkasteshi, wasu ahwaye ne suka fara zarya akan fuskanshi, kafin ya dan dago ya soma jero mata adduo sosai.
  babu komai malam labaran ka daina min godiya? Yauwa daman inata so na tambayeka, ya maganra memories dinka kuwa, akwai improvement?  nunfasawa ya danyi yana murmushi yace   alhamdullahi, gaskia akwai, saboda yanxu idan na kalli wasu abubuwan wani shafi daga cikin rayuwata yana zuwanmin 
  toh alhamdullah allah ya kawo sauqi cikin lamarin  ammah ta fada tana murmusawa
  ameen hajiya, bari na wuce,  ya fada yana mikewa,   toh madallah malm labaran nagode sosai.  Dan waigawa yayi ya kallli inda salim ke kwance ya juyamasu baya don baya fuskanta inda suke zaune, murmushi kawai malam labaran yayi ya fuce daga gidan yana jin yanda hajiyar take kara qima da daraja a idanunshi,   oh ashe waennan ne yaran da ta rikesu, allah sarki samun mutane irin hajiya sai an tona, baka sansu ba basu sanka ba ka rike su amana kamar naka allahu akbar  malam labaran ya fada yana tafiya shi kadai har yazo bakin wajen mai gadi, don shima maganar yara da hajiya take rikewa daga wajen baba mai gadi yaji zancen.
Sallama yayi ma baba mai gadi kafun ya fuce daga gidan.

Bangaren amra kuwa tana shiga daki ta soma zame kayan jikinta ta wuce bathroom don jikinta har wani yami yami yake mata saboda dan zufar datayi, a gaggauce ta watsa ruwa ta fito daure da towel tayi kwanciyarta nan take barci ya debeta.

Bangaren amar shima tun bayan ya fusgi motarshi yabar estate din ranshi a bace bai tsaya ba, haka ya dunga zagaye da motar yama rasa ina zaije, ranshi yayi mugun sosuwa da abunda amra tayi mashi, bait aba tunanin zi sauke kanshi to this level ba har ta samu damar fada mashi Magana son ranta and abunda yafi bata mashi rai shine yanda ya kasa ce mata komai,   why why  ya fada da karfi yana bugun steering motar shi, gefen titi ya gangara yayi parking don idan rasnhi ya baci baya careless driving, yana parking motar yayi shuru yana dafe kanshi dake sara mashi sosai, shi maganganun ma data fada mashi bai dameshi ba kamar ganinta da yayi zaune wani asararre yana mata Magana ita kuma tana murmushi, abun ya staya mashi arai sosai yanda mutumin ya tsaya yana kallonta har yana kokari taba jikinta,   fuckkk  ya fada da karfi yan sake bugun sterring din kamarzai ballah ranshi amugun bace yake   why would she smile 
Ya fada aranshi, meysa zatayi ma wani murmushi, murmushinta mai tsada ne wanda baya son kowa ya gani bayanshi ya fada aranshi, wata zuciyarshi ce ta tambayeshi   why? Why would you care idan tayi ma wani murmushi?meysa zaka damu 
Dan jim yayi ranshi a abce kafin ya furta   cause shes my wife, as long as shes my wife no one will ever see that smile 
Wata zuciyar ce ta sake tambayarshi,   but kace baka buqatarta why now? Why are you acting like that ko dai kana sonta ne? are you ready to accept her? 
Dafe kanshi yayi ya furzar da wani nunfashi mai zafi kafin yace   no no nooo, bazai taba yuwu hakan ne ba kawai obsession ne da tausayi that s all, nothing else 
Wata zuciyarce ta sake tambayarshi   then why would you care, why are you jealous? 
Haka nan zuciyarshi ta dunga mashi wasi wasi, yama rasa taka maimain, ainihin abunda yake damunshi, he cant lie baya wuni day aba tareda ta fado ranshi ba every seconds, gashi lokaci guda allah ya saka mashi damuwa akanta, don ayanxu sai yayi tunanin sau nawa baima san yana yi ba, hes craving for her, he wants her badly, he cares for her saidai wani bangare na zuciyarshi na ego dinshi bazai barshi ya sauke kanshi ba, infact why would he do that? Haka yake yawan tambayar kanshi daga nan kuma komai saiya sauya, haka zai fara denying feelings din da yake mata,thinking about this kadai yana damunshi sosai, ya dade a cikin motar yana saqa da warwara, sai wajen yamma yabar wajen ya juya akalar motarshi zuwa gida.

Karfe biyar daidai ya shugo gidan bayan ya tsaya a masjid yayi sallan asr, lokacin daya shugo gidan babu kowa don motar ammah bata garage don haka ya gane cewa bata gidan, yana nan tsaye a parlor ya zaro waya shi ya soma dialing number ta, ammah na picking tun kafin ya soma Magana ta katse shi don tasan nagging zai fara   sorry son ka dawo bana nan ko? Naje groceries shopping naga abubuwan fridge sunyi kasa 
Sauke ajiyar zuciya yayi har tana jin sautin sa   ammah na, maysa baki fada min dana futa ay dana biya na sayo 
  sorry son,nag aka futa ne cikin gaggawa, shiyasa banyi maka maganar ba 
Saida takai aya ya cigaba   ammah please..bana son kina yawan futa ke kadai, ga aman ne, idan ma bana nan he can go and get it 
  son, calm down, babu abunda zai faru dani cikin ikon allah, besides aman baya nan, zaije daukan salima daga school yau zasu gama exam very late, bazan dade b azan dawo nan kusa ne fah 
Ahankali ya sauke ajiyar zuciya for the second time yace   okay tohm, allah ya kiyaye 
  ameen yauwa ka shiga ka duba min daughter ko zata buqaci wani abu, na barta tana barci 
Shuru ya danyi kamar bazaice komaiba har saida tace   hello kana ji? 
  yess ammah  yana kaiwa nan ya kasha wayar

Part dinsa ya wuce direct, yana shiga parlor ya zauna a kan couch dinshi ya danyi resting kanshi tare da lumshe idanunshi, yanayin fuskanshi bazaka taba tantance yanayin da yake ciki ba kwata kwata, ya dade a zaune kafin ya mike ya wuce bedroom dinshi.

After like 30mins sai gashi ya futo sanye da farar riga mai gajeran hannu ta kamashi sai sai gajeran wando daya kai har wajen gwiwarshi, hannunshi rike da wayarshi while dayan hannun ya saka shi cikin aljihun wandon nashi, kafanshi sanye yake da wani sandals baki wanda ya fidda kyawawan yatsun kafafunshi dogaye, fuskanshi sai sheki yakeyi, he look so damn handsome, kamar ka sace shi ka gudu sai kamshi jikinsa ke fiddawa duk inda ya gifta, cikin kamewa yake tafiya harya bi hanyar stairs, walking majestically kamar basarake, fuskanshi a hade kamar koda yaushe, yana hawa sama hanyar dakinta ya wuce direct kai tsaye, yana zuwa daidai kofar nata ya sanya hannunshi kan handle din kofar ya bude,
Yana budewa ta juyo arazane don harta zame towel dinta kasa tana shirin daukan doguwar rigar da zata saka, cikin saurin ta dago idanunta ta sauke akanshi, shima ita yake kallo tundaga kanta dake digar ruwa zuwa kafadarta dake sheki da sauran ruwa a jiki zuwa santatala cinyoyinta data saka wani blue lace pants, juya mashi baya tayi tana kare kirjinta ranta lokaci guda y abaci da wannan behavoiur nashi na shigowa dakin mutane babu sallama babu wani excuse kawai ya bude kofa, abunda yafi kular da ita shine yanda ya kafeta da idanu, dukda ta juya mashi ba she can feel yanda


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login