Showing 69001 words to 72000 words out of 381117 words

Chapter 24 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

2001

cikin kunnenshi in a harsh sexy tone wanda baisan yayi ba yace    Haka kike yawo yanxu idan Nace bakida kamun kai nayi laifi? Ahankali ya gangarar da kanshi zuwa wuyanta kamshin body wash dinta na fita azafafe, wani irin Zazzafan nunfashi ya sauke mata akan wuyanta zuwa kunnenta da sauri ta runtse idanunta tare da damko towel din nata da kyau don kiris ya rage subuce daga hannunta ya fadi tsabar kidimewa datayi shikuwa yana kaiwa nan ya hankada ta gefe ya tabe baki kamar yaga kashi yace  kina yar kwailarki,ki bari saikin zama cikakkiyar mace kafin ki dinga tallata jikinki yar tsuka ya ja ya wuce ya barta anan tsaye sakeke ta sandare a tsaye, itama wannan mutumin mamaki yake bata kamar hawainiya mai chanza launi, saida ya gama kafeta da idanu kafin ya Gaya mata baqaqen maganganu Wai kwaila, gakiya ya cuceta Wai ita zai cewa kwaila meyake nufi kenan, bata da komai kenan wani irin kukane mai ciwo ya zo mata yanxu laifinta ne donta tsaya ta kashe gas baima tsaya ya saurare ta ba yayi mata muguwar fasaara wani irin maququn baqin cike ne ya turniketa tana kumbure kumbure tayi hanyar dakin kamar zata shiga Sai kuma ta juya wata zuciyar tata na ingizata  ashe ke matsoraciya ce ta fada aranta, tabe baki tayi ta share hawayenta ta koma wajen sitting room ta bude box din kayanta ta saka riga da wando masu santsi sulub blue color, wanda ya danyi buje ta kugunta saiya fidda shape dinta sosai saidai bai dameta ba while rigar takai daidai kasan cikinta, sai tayi kyau sosai cikin kayan, wayan ta ta dauka ta kira haifa ta bata labari, dariya kawai ta dunga yi mata karshe dai ta fara tsokanarta   babe tunda ya kiraki da kwaila ya kamata ki koya mashi hankali, kinsan wasu mazan idan sukaga kana da kananun shekaru saisu dinga maka kallon raini, ko su dunga maka kallon kamar ke yarinya ce babe ni wallahi gani nake kinfi karfinshi ma,  gwalo idanu amra tayi kamar haifa na gabanta tayi saurin cewa   kaii haifa karkiyi sabo fah, wannan mutumin yafi karfina ko a mafarki kekam bare ma ni banson maza irinshi, masu masifa da miskilaccin ga girman kai badani ba  shuru amra tayi tana sauraronta da zugar data fara mata akan wallahi ta nuna mashi itafa ba yarinya bace kuma itama tana da class, saida haifa ta zuga ta sosai kafin sukayi sallama, da farko dai ta watsar da zancen, saidai tunawa da kwaila daya kirata dashi abun ya tsaya mata arai kuma yana baqanta mata rai sosai, watsar da zancen kawai tayi kafin ta miqe ta deba abincin datayi wanda ya soma kone wa saida taci tayi nak anan kitchen din kafin ta wanke hannunta ta plates din ta koma sitting room, ganin karfe 1:30pm yasa ta zumbula hijabinta ta fuskanci kibla, tana idarwa tayi addu oin data saba na nemawa kanneta kariyar allah da kanta kafin ta nannade ta aje ta koma kan couch tana kallon tv har barci ya kwashe ta anan.
?
Yana shiga dakin ya sauke nannauyan ajiyan zuciya, anatse ya tako gaban gadonshi yana kallon ko?na yanda yake fess fess ?ga kamshin bakhoor daya gauraye ko ina, kayan jikinshi ya soma tubewa ya wuce toilet don a gajiye yake daga airport yake ya taho apartment dinshi don ko penthouse dinshi bai leka ba saidai luggage dinshi dayasa m5 yakai mashi chan penthouse dinshi, daman tafiya yayi zuwa india na sati guda, wanda duk akan rashin lafiyanshi ne wanda doctor shi ya mashi recommending wani likita achan india doctor dirsham don ya duba shi idan da akwai yanda sauqi zaizo mashi, saidai kash kamar koda yaushe answer da yace bashida wani option, wanka kawai yayi ya dauro alwala ya futo, wani irin azabbaben ciwon kaine ke damunshi, saida ya idar da sallan dhuhur kafin ya miqe, duk yanda kanshi ke ciwo hakan bai hanashi jawo laptop dinshi bay a soma aiki har akayi sallan asr, daman bai cire jallabiyanshi ba hakan yasa ya miqe kawai yah au kana bin sallah ya tayarda sallah, yana idarwa ya zauna yayi azkar bai tashi ba har akayi sallah magrib da isha I yana nan zaune, sai wajen karfe 8;30 ya mike ganin call din m5 na shugowa, miqewa kawai yayi baibi takan wayan ba ya fuce daga dakin, haryazo ya gitta ta a kitchen bai ce uppan ba, amra kuwa wadda kamshinsa ya mata sallama tun kafin ya doso hanyan hakan yasa bata juyo ba ta cigaba da dafa rice and stew din da take yi tana juya miyar dataji naman kaji zuqu zuqu aciki, bude kofar futa yayi ya karba basket din hannun m5 kafin ya rufe kofar ya tunkaro hanyar kitchen din, aje basket din yayi kan island kafin ya zauna akan chairs din yana latsa wayan shi, saida ya zauna na kusan minti goma still idanunshi nakan wayan shi kafin cikin nutsuwa ya soma Magana   serve me  , tsayawa tayi da juye abincin da takeyi a containers sbd tana storing din su idan ta dafa dayawa don idan taji yunwa in bata son girki saita dumama taci kayanta, anatse ta aje container din da serving spoon din hannunta kafin ta juya bata ko kalli inda yake ba ta bude wajen plates da spoons da serving spoon ta kwaso ta dauraye ta goge kafin ya karasa gabanshi, bude warmer din tayi ta zuba mashi white soup din sai cheesy creamy pasta data gani agefe, tana gamawa ta tura mashi gabanshi ta bude fridge ta zaro mashi ruwa maid an sanyi kamar yanda yake sha, miqa hannunta tayi ta dauko pineapple and coconut juice din datayi, kamar ta aje don tsoron karya duzgata takeyi, da sauri ta maidashi ta wuce gabanshi ta aje mashi a gabanshi kafin tace   bismillah  , dagowa ayi ya mata kallo daya kafin ya kauda kanshi ya dauka spoon din ya soma cokalawa cikin bowl din, wani irin zazzabi yake ji sosai wanda ya sashi loosing apetite dinshi, dagowa yayi ya kallet lokacin tana gama saka containers din cikin fridge bayan ta deba wanda zataci acikin plate ta jawo pincolada juice din datayi tayi kafin ta gitta ta gefenshi ta wuce duk agaban idanunshi, bata kaiga wucewa ba ta tsinkayo muryarshi   wannan jagwalgwalon zakici?  tsayawa tayi chak batace mashi komi ba haka zalika bata cigaba da tafiyanba ranta ne yadan sosu, tabe baki yayi ya jawo tissue ya goge bakinshi ya wuce ta gefenta yana yar tsuka da gefen bakinsa harya isa daki, toilet ya wuce dakyar yayi wanka don zazzabi harya soma rufe shi, idanunshi sunyi jaa sosai, wanda tunawa da maganar doctor ya kara tabbatar mashi da side effect din freezing din sperm dinshi da akayi ne wato zazzabin dare, don yaqi yaje ayi de-freezing don bai samu soluton ba har yanzu, yana fitowa ya jawo wandon pjs dinshi masu santsi da tsada, dakyar ya saka yanajin wani irin weekness na zuwan mashi sosai, ga wani irin abu da yakeji yana taso mashi tun daga yatsun kafafunshi zuwa kanshi wanda ke haifa mashi da tashin tsikar jiki da kasala, anatse ya lallaba ya karasa gaban gadon ya shige cikin duvet din nunfashinsa na sauya wa zuwa mai zafi sosai, runtse idanunshi yayi yana kokarin sanya kanshi bacci kozai samu salama, da kyar bacci ya fisgeshi, daga yanda yake fidda nunfashi da sauri ga zafi zaka gane yana jin jikinshi.
?
Tana gama cin abincinta da yake kirirari da jagwalgwalo ta tattara komai har wanda ya rage ta saka a frigde ta wanke kwanuka ta sha ruwa sosai don juice din data sha akwai madara wanda ya haifar mata da kishiruwa sosai, saida ta tabbatar ta gama komai ta kashe hasken kitchen ta koma sitting, wayanta tayi plugging a chargy kafin ta cire rigar jikinta ta saman ya zamana daga ita sai wandon rigar da yar vest din rigar kayan wanda ya zamana set ne, anatse ta soma karanto addu oin kwanciya kafin ta kwanta.
?
Karfe biyu da rabi na dare ta miqe zumbur kamar wadda a tsungula, wani irin futsari ne ya matso ta, da sauri ta yaye dan blanket din da take lulluba dashi ta zuro kafarta kasa ta sanya fuffy bedroom slippers dinta, a gurgurje ta nufi dakin nasa, ahankali ta dora hannunta kan handle din ta bude, ganin dakin so dim don ko tsakiyan dakin ba a gani yasa ta fara tafiya ahankali don gudun tuntube har takai bakin kofar toilet, tana shiga ta rufe kofar ahankali ta kunna light din toilet din ta zauna kan wc, saida ta gama buqatunta ta wanke hannunta da handwash kafin ta nufi kofar ta bude ?ahankali ta futo, anatse take takowa harta zo gittawa gefen gadonshi, kunnuwanta suka fara jiyo mata sautin nunfashinsa wanda ke fita da sauri sosai kamar mai asma, jinkirta tafiyarta tayi don tabbatar da kodai ba lafiya ba, juyawa tayi saitin gadonshi, kanshi na cikin duvet din don ko alamun fuskanshi bata gani don da dan hasken bedside lamb, addua oin neman sauqin wurin allah ne da yake yi ya tabbatar mata ba lafiya ba, cikin sauri ta karasa gabaon gado, daburcewa tayi sosai jin yanda nunfashin nashi ya tsananta sosai, cikin tashin hankali da rashin abinyi ya sata Magana ahankali   uhm& are..you okay?  , jin shuru gashi ya fara jijjiga har gadon nashi na kara ya sata ta kara burkicewa, hankali atashe ta sake maimata tambayar datayi mashi ganin kamar ma ba jinta yake ba yasa ta daga hannunta cikin tsoro da fargaba ta janye duvet din daga kanshi gaba, arazane tayi baya don gaba daya hankalinta ya tashi da ganin yanayinshi, fuskarshi tayi jaa sosai kamar an shafa mashi barkono, ga zufa data gama wanke mashi fuska hade da tururin zafi dake futa daga jikinshi wanda daga tsayen datake tana jin yanda nishinsa ke fita da zafi zafi sosai, kallon fuskarshi da take a lumshe tayi kafin ta matso sosai gab da shi ta dan tsugunna daidai fuskarshi ahankali ta sanya hannunta akan goshinsa da sauri ta cire don wani irin zafi ne da shock ya hade mata waje daya, a razane ta kalleshi tare da dabbin fuskanshi ahankali   yaya& yaya whats wrong are you? Youre burning up, innalillahi na shiga uku ya zanyi  , daburcewa tayi zata mike tsaye ya chafke hannnunta wanda yaji wani irin confort data saka akan fuskanshi don wani irin boiling jininshi keyi, kamar mahaukaci haka ya dunga jan hannunta akan fuskarshi yana gogawa, har zuwa kirjinshi, da sauri ta fara kokarin janye hannunta amma inaa,yayi mata wani irin damka kamar ranshi na hannunta, miqewa tayi don neman mafita wajen kwace hannunta don ta neman mashi magani acikin dakin, jin hanunta na neman kufce mashi yasa ya janyo gaba dayanta zuwa jikinshi, wani irin nannauyan ajiyar zuciya ya sauke don yaji kamar an zuba mashi ruwan sanyi a cikin jikinshi, da sauri ya kankameta sosai, amra kuwa wadda tayi suman tsaye dukta daburce da yanda yake maqalmqale jikinta, ga yanayin yanda dumin jikinshi ke shiga cikin nata, hankali atashe ta some kokarin Magana, dim tunaninta ya dauke jin gabadaya kanshi cikin rigarta wadda babu ko bra ajikinta sai yar shimin, yanayin yanda ya figota ta fado akanshi ya zamana tana kanshi yana kasa, da sauri da sauri yake fidda nunfashin neman salama wanda ke sauka akan fatar kirjinta zuwa wuyanta, hankali atashe idanunta ya fara kawo ruwa da sauri ta soma furta innalillahi wa inna ilaihi rajin, bat agama shiga tashin hankali ba saida tayi yanda ya farke rigar tata gaba daya ji kake qiiiiit yayi wurgi da ita, gaba daya ya futa hayyacinsa, wani irin sanyi ne ke shiga jikinsa wanda ya kasa gane menen akanshi shidai yasan kawai yana jin saukin zafin zazzabin da yake ji, kuka amra ta fara ciki ciki don ya damke kugunta sosai babu hanyar tsira ga yanda ya cusa kanshi tsakanin nonuwanta yasa tsikar jikinta tashi sosai, hankali atahse don wannan ne first time da jikin namiji ya sauka kan nata, body contact din yayi yawa sosai,saqalota yayi sosai a jikinsa kirjinta akan nashi sosai, ahankali nunfashinsa ya soma daidaituwa tare da sakin jikinshi sosai, sun dauke wajen awa biyu a haka, jikinta duk ya soma tsami da irin rukon dayayi mata da yanda ya saqalo da kanshi ta wuyanta yana sauke mata zazzafan nunfashinsa ya rungumeta sosai akan jikinshi, kirjinta tsam manne da nashi har baccin wahala ya kwasheta bata sani ba, shima baccin wahalan ne ya dauke shi mai zurfi sosai wanda ya danji saukin zazzabin dukda har lokacin baya cikin hayyacinsa, har kusan karfe shida suna kwance a hakan, ahankali ta soma bude idanuwanta akan fuskanshi wanda take dab da tata, runtse danunta tayi tare da budesu tar akanshi don tunawa da abinda da ya faru a cikin daren ranar, hamdala tayi da allah ya taimake ta ita ta fara farkawa, anatse ta soma janye jikinta daga nashi, jin yanda ya saqalo kugunta da hanneynshi yasa ta soma janye hannun nashi ahankali har ta samu ta cire hannayen nashi gaba daya, ganin yana juyi zai chafkota yasa tayi saurin yin wuf ta fado kasan gadon har tana buge bumbum dinta, ahankali ta furta   ouchhhh  da dan karfi, anatse ta dago ganin yana gab da da farkawa yasa tayi saurin rarrafawa ta fuce daga dakin don bata fatan ya ganta har tana mance rigarta don batabi takan rigar bama don hankalinta a mugun tashe yake idan ya ganta adakin nashi.
Tana fita ya soma bude idanunshi wanda sukayi jaa sosai tare da kankancewa, addua yayi kafin ya mike ya sauka daga kan gadon yana dan tangal tangal kamar zai fadi don wani irin jiri ne ke debanshi, toilet ya fada saida ya sakarma kanshi ruwan zafi sosai kafin ya danji dama dama ya dauro alwala ya fito, gaban closet dinshi ya tsaya ya fiddo da farar jallabiyan shi ya sanya ya shimfida sallaya, saida ya dauka kusan awa yana zaune yana azkar, lokacin gari ya dan soma haske kadan, miqewa ayi ya nade sallayan ya koma kan gado yadan jingina da gadon, tare da lumshe idanunshi, ahankali kamshin da banashi bay a soma gaurayewa da nashi a dakin, ahankali ya dan bude idanunshi wanda suka danyi jaa sosai suka sauka kan duvet dinshi daya dan yamutse sai dan jan abu dake lekowa daga cikin duvet din, kauda kanshi yayi daga kan duvet din ba tare da wani dogon tunani ba ya jawo wayanshi ya danna kiran doctor shi, ringing biyu ya dauka   good morning mr amar  .. anaste amar ya soma Magana cikin kamewarshi kamar koda yaushe   morning doctor, Im coming to the hospital now, please book an appointment  , yana kaiwa nan ya kashe wayan tare da miqewa ya chanza zuwa kananun kaya masu laushi ya jawo wayanshi da keys dinshi ya fuce daga dakin, koda ya futo bai tsaya kallon parlor ba yasa kai ya fuce daga gidan gaba daya.
Amra kuwa wadda saida ta futo daga daki tana fidda nunfashi tsira da sauri sauri ta samu waje ta zauna akan kujera, sai alokacin ta lura da shirmen datayi na barin rigarta a dakin, tashin hankalin data shiga bai barta ta tuna ba saida tabard akin, da sauri ta janyo hijab dinta ta fara kiciniyar sanya hijab din, idannta ta sauke akan boobs dinta da suka danyi jaa daga yanda ya yamutse ta har shati shati wajen yayi sosai, tunawa da yanayinsu na dazu ya sanyata saurin saka hijab din don bata son tunawa kwata kwata, zama tayi anan har akayi sallan subh, tana son yin shiga toilet don yin alwala amma ta kasa don wani irin tsoron shiga dakin ne ya darsu a cikin zuciyarta sosai tana nan zaune har ya fito, kanshi turarenshi ne ya mata sallama, har ya fuce bata dago ba haka zalika shima bai kalli inda take ba harya fuce, sauke nannauyan nunfashi tayi don ba karamin tsorata da futowanshi tayi da sassafe don duk a tunaninta ya gano wani abun ne ya mashi muguwan fassara, miqewa tayi ta wuce dakin domin dauro alwala don har kusan takwas da rabi saura. 92-93
Yana fucewa ya shige motar shi yaja bai tsaya ko ina ba sai gaban private hospital din da yake zuwa, saida ya sanya facemask a fuskanshi kafin ya futo daga motar ya wuce ciki hannunshi rike da wayanshi, saida ya zo daidai da kofar shiga main entrance na cikin asibitin message ya shugo cikin wayanshi, dubawa yayi ya fara karantawa har ya buge da mutun wanda bai lura bama ya gifta ta gefen matar ya wuce, hankalinshi yayi gaba sosai wajen wayar da yake kalla bayan an sake tura mashi wani message din da same number, da sauri ya dago ya kalli ko ina na harabar wajen daga karshe ya sake duba wayan nashi yana maimaita last message din da aka sake tura mashi ta cikin wata anonymous number da akayi hidden,   I m coming for you, I promise to destroy you  maimaitawa yayi kafin ya sake karanta na next masseage na karshe da aka tura mashi wanda yafi bashi mamaki   watch where you re heading too  mamaki ne karara a fuskarshi wanda ba kowa ke gane hakan ba don yanayin fuskanshi abu ne mai wuyar tantancewa, tabbas wadda suka danyi clashing yanxu wanda ya kasa tantance macece ko namiji dan bai kalli fuskar wanda suka bige dashi dinba, tabbas shine ya tura mashi wannan message din, so bibiyar shi akeyi Kenan, tsaki yadan jaa chan kasan maqoshinsa don shi duk wannan threat baya daga mashi hankali, don ya wuce level din nan, babu abinda yake zaman mashi threat yanxu don shi jarumine da baya tsoron komai da kowa, tura wayan nashi yayi cikin aljihun wandonshi kafin ya karasa cikin asibitin, baima tsaya gaban reception bay a wuce office din likitanshi, azaune ya tadda likitan nasa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login