Showing 207001 words to 210000 words out of 381117 words

Chapter 70 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

2046

maimaita abunda yace da farko ba ya bude kofa ya fuce daga dakin, salima ce ta kalleta tace  yace kuje wai
Jiki a mace amra ta mike tsaye ta kalli Salim tace  muje Salim
Kallonta salima tayi tace  zai tayani kwana kije kawai
Badan taso ba haka ta nufi kofar ta fuce daga dakin jiki a mace donma tana buqatar komawa gidan ne don kwanciya anan wahala
Yake bata badan haka ba bazata bishi ba don gaba daya ya fita aranta dukda tana nan kan bakarta bazata taba rabuwa dashi ba, saidai haka kawai cikin kwanakin nan take saurin fushi da jin haushin sa da abubuwa ma gaba daya.

Ahanakli take tafiya harta zo bakin harabar asibitin wajen parking lot, Har tana shirin wucewa inda Aman yayi parking Tayi saurin tsayawa saboda horn dayayi mata, juyowa tayi gafe ta kura ma motar idanu, batayi tunanin da wata motar yazo ba don haka ta dan tsaya don tabbatar da shi dinne, saida ya sakeyi naga horn kafin ta fara takowa jiki a mace ta karaso ta bude gidan gaba ta zauna.
Tana shiga bata idasa rufe kofar ba ya figi motar, ta Lura da take takenshi don haka tayi banza dashi kamar batasan yanayi ba.

Tunda suka fara tafiya babu wanda yace Tak tsakanin su, shi gaba daya ya maida hankalinshi ga tukin da yake while ita kuma ta juyar da kanta gefe tana kallon hanyar,
Waigowa yayi ya mata kallo daya kafin ya kauda kanshi gefe ya cigaba da tukin.
A Daidai wani haddaden waje yayi parking don bazata ce ga ainahin sunan wajen ba, saidai tundaga wajen parking da ya aje motar tabi wajen da idanu, wajen ya hadu sosai don Duk manyan motoci ne a wajen.
Bai kashe motar ba ya bude ya fuce daga cikin motar, yana fita tabishi da idanu kafin ta kauda kanta gefe, zaman minti goma tayi sai gashi ya fito hannunshi rike da manya manyan ledoji guda biyu, harya shugo ya bude motar ya saka ledojin a bayan mota bata kalli inda yake ba, shima ya Lura da yanda take wani babbasarwa don haka ya kauda kanshi gefe kawai shima bai ce mata qala ba don haushinta yake ji sosai, ya kasa gane dalilin da yasa ma ya kasa mata magana akan dazu.
Reversing motar yayi ya fuce daga compound din wajen, anatse yake tukin cikin kwarewa, cikin Yan mintuna qalilan suka iso taura estate, horn yayi aka bude main gate kafin ya wuce apartment dinsu,nan ma sai dayayi horn securities suka bude kafin ya saka hancin motar wajen parking space dinshi.
Yana parking ya kashe motar ya dan saiga gefenta Ganin bata motsa ba, barcin ta take yi hankali kwance, baya Ganin fuskanta don haka bai tantance a wani yanayi take barcin ba,saida ya dauka about 10mins yana tunanin tashinta, don haka kawai ya tsinci kanshi da son barinta tayi barcin saboda yanda yake hidima da ammah gashi alamu sun nuna bata jin dadin jikin ta amma tana boyewa, shuru shuru saida suka dauke kusan awa guda, yayi relaxing kanshi a jikin kujeran inda yake zaune yana tunani wasu abubuwan.

Gyara zamanta ta yi saboda yanda kwanciyar datayi yasa jikinta ya fara mata ciwo, ahankali ta bude idanunta ta kalli gefen window kafin ta maido da kanta gareshi, ya lumshe idanu kamar mai jin barci hankali kwance, lumshe idanun ta tayi ta kauda kanta gefe ta bude kofar motar ta fuce daga cikin motar,

Tunda ta farka yanajin motsin ta harta fuce daga cikin motar bai bude idanunshi ba sai da ya dauka kusan minti biyar kafin ya bude jajayen idanunshi ya futo daga motar ya bude gudan baya ya janyo ledojin ya rufe motar ya wuce mai entrance, lokacin daya bude kofar parlor ya shige harta hau sama abunta don haka ya karo kofar ya rufe ya wuce part dinshi da ledojin, anan parlor shi ya aje ledojin kafin ya wuce bedroom dinshi kai tsaye, yana shiga dakin ya sauke wata nauyayyiyar ajiyar zuciya ta gajiya kafin ya soma rage kayan jikinshi, saida ya aje wayanshi a gefen bedside kafin ya wuce bathroom din ya watsoo ruwa ya fito daure da towel, bai tsaya shafa mai ba ya feshe jikinshi da turarukanshi masu sanyin kamshi kafin ya janyo pjs dinshi na cotton Riga da wando baqaqe, zama yayi bakin gadon shi ya janyo wayarshi ya soma latse latse, da message din asad ya fara cin karo, bai bude ba don yasan idan ya bude ma ranshi ne zai baci don haka ya kashe wayar ma baki daya ya aje ta a gefe ya mike cikin kamewa ya zura bedroom slippers dinshi ya fuce daga cikin bedroom din,anatse ya bude kofar da zai sadashi da parlorn shi, daga nesa ya dan tsaya ya karema ledojin daya ajiye na grilled fish daya sayo,fiddo da ledojin yayi gaba daya ya wuce dining ya ajiye kafin ya wuce sama, anatse yake tafiya kamar wani basarake harta zo daidai kofar ta, fuskan nan yasha mur babu fara a harya danyi knocking kofar kafin ya sa kai ya shige ciki,yana shiga dakin tana fitowa daga bathroom daure da pink towel jikinta na digar ruwa tundaga kanta zuwa wuyanta, saurin kauda idanunshi yayi daga kanta ya danyi gyaran murya yace  Idan kin gama ki sakko kasa yanxun nan
Yana kaiwa nan ya juya ba tare da ya sake kallonta ba ya fuce daga dakin, ita kuwa tunda ta fito ta ganshi tsaye batayi wani mamaki ba don ya saba shugowa babu excuse don haka bata wani damu ba a wani yanayi ya ganta don haka bayan ya fuce ta tabe baki tabi bayanshi ba tare da ta saka komi ba, haka ta sauko kasan anatse tana tafiya kamar dawisu Har wani kwarkwarsa takeyi ba tare da saninta ba Har ta karaso parlorn, tana shirin karasowa part dinshi ya katseta,  over here ya fada anatse, juyowa tayi ta nufi inda tajiyo muryan nashi daga wajen dining, takowa tayi harta shugo dining din kanta a kasa ta tsaya qiqam a gaban dining din, tunda ta shigo ya kafa mata idanu ya kasa daukewa, harya dauka kusan minti biyu baice mata komai ba, itama bata ce mashi komai ba don bata son magana dashi yanxu kuma saidai hakan baisa taji zata ki amsa kiranshi ba Duk sanda ya nemeta, gajiya tayi da tsayuwar ta dago ta kalleshi shima ita yake kallon soma haka yayi saurin tattara natsuwarshi yace  come and serve me
Kallon ledar gefenshi tayi kafin ta juya zuwa kitchen bata ce mashi qala ba, yayi mamaki sosai yanda take bashi wani silent treatment, haushi yaji sosai, who s she da zata dunga bashi silent treatment tana qin bashi amsa idan yayi mata magana, kokarin danne zuciya shi yayi harta karaso dining din, Har lokacin towel dinnan ne a jikinta haka zalika ruwan jikinta bai bushe ba yana bin lausassan fatar jikinta dake sheki babu gashi ko digo daya very soft, hannunta rike da plate da serving spoon sai spoon and fork da knife, ta karaso dining din ta tsaya daga gefenshi ta ajiye komai akan dining din kafin ta koma kitchen din, bin bayanta yayi da kallo harta wuce kitchen din ta fito hannunta dauke da bottle water da orange juice sai glass cup
a dayan hannunta, cikin natsuwa take komai harta iso Inda yake zaune ta aje mashi a gabanshi, ledojin data gani a gefe ta janyo ta soma budewa,ledar farko data bude grilles fish ne da yaji dankali dasu cabbage a ciki sai kamshi daya bade hancinta Har tana lumshe idanunta don dadi, yawunta ne ya dan tsinke kafin ta fara zuba mashi,saida ta zuba mashi yanda zai ishesa kafin ta tura mashi gabanshi ta juya zata wuce sama dukda ranta ya biya sosai,

Hannunshi ya daga biyu ya kame bakinshi yana kallon ikon Allah Har tazo fucewa daga dining din,  Aisha!!! Ya Kira sunanta, chak ta tsaya ta kasa motsawa kwata kwata harta juyo ta fuskanceshi,  zo nan!!
Ya sake fada yana kallonta hannunshi akan habar bakinshi, takowa ta soma yi jiki a mace ta tsaya nesa dashi batace mashi komai ba,
 Seat!! Ya fada sounding commanding wanda abun ke bata mata rai sosai, bata musa mashi ba ta zauna gefen seat din da yake zaune, tana zama ya maida idanunshi ga abuncin dake gabanshi ya saka spoon ya soma ci hankali kwance, ta dauka kusan minti goma kanta a kasa tana jiran jin abunda zai ce mata daya dakatar da ita daga tafiya jin shuru baice mata qala ba ta dago ta kalleshi, ya maida hankali sosai ga abuncin da yake ci ahanakli kamar baya son ci, saida ya dago suka hada Ido ya kauda nashi gefe yace  lower your gaze
Ba zat ba tsammani yaji amsarta  why? Haramunne don na kalli mijina? Why would I lower my gaze?
Da mamaki ya dago ya mata kallo daya kafin ya dan murmusa ta gefen baki ya kauda kanshi daga gareta baice mata qala ba don da alamu ta zama mafadaciyar karfi da yaji,
Haka kamshin grilled fish dinnan ya cikata gashi baiyi mata tayi ba ga takaicin abunda yace mata don haka ta hade rai tamm kamar hadari,  are you waiting for me to ask you to eat? Ya tambayeta kai tsaye ba tare da ya kalleta ba,  bana jin yunwa bata gama fada baa cikinta ya fara qugin yunwa qiii, atare suka dago ya daga mata gira daya alamun karya kike yi, saurin sauke kanta qasa tayi ta hade rai tam, harya kusa cinye nashi wanda ta zuba mashi a plate din tana zaune ta nade hannunta akan tudun kirjinta daya dan futo sosai, kwata kwata baiyi gigin kallonta ba saboda komai nata haukatashi yake, abuncin ma zai iya kasa ci idan ya dago,saida yaci kusan rabi kafin ya tura mata gabanta ya dago ya kalleta fuskanshi babu wasa yace  eat!!!
Dan dagowa tayi ta kalleshi kafin ta maida idanunta kan plate din nashi, shuru ta danyi tana nazari, me yake nufi kenan da ita? Saida yaci ya rage zaice taci, Ay kuwa ko sama da kasa zata hade bazata ci ba,, maidoda kallonta tayi zuwa gareshi  bana ci
 You know I& .
 You hate repeating your self na sani, bana jin ci ne kawai tayi saurin katseshi kafin ta miqe tsaye ta juya zata wuce, bata idasa taku biyu ba taji ya janyo waist dinta baya ya hade da gabanshi ya rike tam  why are you so stubborn huh? Shuru tayi mashi batace komai ba tana sauraron yanda nunfashinsa ke sauke a shoulder dinta don ya dan rankwafo wajen wuyanta, daidai ta natsuwarta tayi ta soma kokarin same jikinta daga nashi, yanda ta soma jaa baya haka ya sake janyota sosai zuwa jikinshi ya yi mata rikon daya fi wanchan ma, saurin runtse idanunta tayi ta budesu tace  dan Allah inason zanje na kwanta kaina na ciwo
Daidai kunnenta ya sauke bakinshi ya fitsari mata da nunfashinsa mai fidda kamshin dadi yace  bazakije ba Saina bada umarnin haka
Tunda yayi maganan bata sake gigin kwace wa ba ta saki ragamar jikinta do Yanxu ta gane musu ma dashi bata lokaci ne don ba a iya mashi, haka zalika ita kuma yanxu bashine a gabanta ba, bata buqatan surutanshi kwata kwata, barcin da take ji ma ya isheta, jin tayi mashi shuru yasa ya juyo da ita gabanshi ya kura mata idanu yace  meysa kika bama ammah jininki?
Dagowa tayi ta kalleshi kafin ta kauda kanta gefe tace  saboda tana buqata shi fuye dani
 You re sick meysa baki je doctor ya dubaki ba?
Dagowa tayi Ganin yanda yake magana calmly kamar bazai yi halin nashi ba na wulaqanta mutun, turo baki kawai tayi tace  lafiya ta kalau bana buqata
 Why are you talking to me like that?ni Sa am kine ? Ya fada yana hade rai
Itama hade ran tayi tau ta kalleshi cikin ido tace  yanxu kuma me nayi? Tambayata kayi ni kuma na baka amsa,? Ta bashi amsa itama tana kallonshi, matso da ita yayi gab da jikinshi yace  bakida kunya
Bai gama sauke nunfashinsa ba ta matso daidai da fuskanshi har nunfashinsu na gaurayewa ta dan dingila kafarta gab dashi tace  mey nayi na rashin kunyar uhm,
Kasa ce mata komai yayi saima kallon juna da suka tsaya yi kamar Ana magnetising idanun suu, saida ta dan gaji da dingile kafafunta datayi ta fara kokarin saukesu kasa Dan ta bar wajen yayi saurin taro waist dinta da hannu biyu ya dauketa gaba dayanta, sai jinta tayi a sama, baiyi wata wata ba ya wuce bedroom dinshi da ita, bata ce mashi komai ba saida ya sauketa bakin gado ya wuce bathroom kamar bashi ba, Binshi da kallonta tayi harya shige bathroom din aranta tana ayyana halayenshi, mey yake nufi kenan daya kawo ta dakin shi ta tambayi kanta, badai yana nufi anan zata kwata ba ta sake tambayar kanta,  chap lallai ma, jiya Ka gaya min bakar magana Ka min korar kare yau kuma Ka wani lallabo Ka shugo dani dakinka kamar babu abunda ya faru, Ay Wallahi tunda Nace na daina kawo kaina inda kake bazan Kara ba tana kaiwa nan ta miqe tsaye ta fuce daga dakin tana gunguni, tana hawa sama kuwa ta shige daki ta rufo kofarta tayi kwanciyarta akan gado.

Yana fitowa daga bathroom yaga daki wayam, babu ita babu inuwarta, saida yadan cije lebenshi kafin ya kwanta.

Washe gari da sassafe ta Tashi ta hada masu break ta jera kan dining, tana gamawa ta debi naga ta wuce sama abunta, tana shiga daki ya zauna bakin gado ta soma cin breakfast din, bata wani ci da yawa ba ta ture abuncin ta karasa shirya wa, wata atamfa ta janyo holland da akayi mata dinkin Riga da skirt ya janyo, atamfar sai kamshin bakhoor wardrobe balls din amrukht_incense take saboda ta saka balls din a cikin wardrobe dinta wanda ya bi kayan nata da kamshin dadi sosai, agggauce ta shirya ta zura skirt din, saida tazo zuge zip din skirt din ta tabbatar da ta karu sosai, tayi qiba, da kyar ta samu ta zuge skirt din ta zura rigar, bata wani iya daurin dan kwali ba don haka ta daura dan medium mayafinta akanta ta fito hannunta rike da dankwalin atamfar, cikin natsuwa ta sauko kasan, kanta a kasa ta wuce kitchen ta dauko basket din abunci data dafa ma su salima aggauce, tana fitowa ta tsaya gaban dining ba tare da ta dago kanta ba, kamshinsa ne yayi mata sallama Tayi saurin daga kanta, anatse yake takowa daga dakinsa yana kokarin gyara agogon hannunshi, kasa dauke idanunta tayi daga kanshi, yayi masifar kyau sosai, komai nashi with class da gayu naira ta gama zama a jikinshi sosai, saurin kauda kanta tayi don ya dago ya kamata tana kallonshi, tabe baki kawai yayi ya zauna kan dining,  Ina kwana amra ta fada ba tare da ta kalleshi ba,  lafiya ya amsa ta kai tsaye, baima buqaci ta zuba mashi komai na ya deba coffee kawai ya fara sipping anatse, ya dauka kusan minti goma yana sha anatse ba tare da ya dago ya kalleta ba itama bata sake gigin kallonshi ba harta kwashe basket din ta dawo parlor ta aje ta zauna zaman jiranshi.
Yana gamawa ya bar dining din ya koma dakinshi ya dauko wayanshi da ya manta a dakin kafin ya wuce hanyar futa ba tare da yace mata qala ba, batayi wani mamaki ba don ta gama karantar halayenshi yanxu, shidai kamar wahainiya yake, yau ya chanza launi gobe ma haka zai chanza wani Launin, tana Ganin fucewar shi Tayi saurin miqewa ta wuce inda ya fidda motar, anatse ya karaso inda yayi parking ta bude motar ta shige gaban motar, tana rufe kofar yaja motar suka bar compound din gidan.

Tunda suka fara tafiya babu wanda yace ci kanki ko ci kanka ba Har suka karaso asibitin, shi ya fara futowa yana kashe motar kafin ta fito itama tabi bayanshi, anatse take tafiya da basket din hannunta tana haki kamar wadda tayi gudu, mamakin yanda take zama weak takeyi sosai, saida ta dan tsaya ta huta kafin ta dauki basket din, wani saurayi ne yayi saurin saka hannunshi kan basket din shima zai taimaka mata Ganin yanda take haki sosai, hannunshi rike da lapcoat da alamu likita ne shima, saurin dagowa tayi ta kalleshi tana sauke nauyyayiyar ajiyar zuciya, murmushi yayi mata  let me help you, you look stressed ya fada anatse, turanci shi ma dadin sauraro, qaqalo murmushi tayi tace  no thank Zan iya
 No ma am let me help bai kamata kina daukan abu mai nauyi ba ya karashe sounding so caring and calming, ba tare da ta kalleshi ba tayi gaba yabi bayanta, Amar daya hangosu tun daga nesa don tana biye dashi harya wuce ta yazo gab da kofar dakin ammah, yana shirin budewa ya waiga ko zai hangota nan take idanunshi ya sauka akansu, dabanshi ne ya bada dam idanunshi Har sun fara yin jaa ganinta da yayi da saurayin suna tahowa, Har suka zo gab da kofar amra tayi saurin jaa da baya ganinshi a tsaye ya kafa mata jajayen idanunshi, ko ba a fada mata ba tasan wannan yanayin nashi da take gani kwance akan fuskanshi, he s pissed kuma ranshi a bace yake, gabanta ne yadan fadi dukda bata san dalilin fushin nashi ba don haka gudun karya dizgata Tayi saurin juyawa ta kalli saurayin fuskanta dauke da murmushi tace  thank you I will
Take it from here
Ba tare da musu ba ya miqa mata yana mata murmushi yace  it s my pleasure
Yana kaiwa nan ya juya yana murmushi don tayi capturing dinshi wanda yaso ya karbi number ta saidai mutunmin daya gani tsaye ya kafa masu idanu kamar zai cinye su ya hade rai yasa yayi tunanin maybe mijinta ne ko yayan ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login