Showing 57001 words to 60000 words out of 381117 words

Chapter 20 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

2030

harta wuce cikin toilet dinshi, saida ta rage mararta kafin ta sakarma kanta hot shower saida ta dade sosai ta gasa jikinta kafin ta fito da kayan jikinta, hijab dinta ta maida sannan ta fara takowa ahankali har ta futo parlor, idanunta ne suka sauka kan nashi daya tsaya gaban fridge hannun shi rike da ruwa alamun ya gama sha, ledan daya aje a kitchen lokacin daya shigo wanda daya maganinta ne daya kuma abincine ya kwaso ya tako Har inda take ya aje agabanta , karba tayi tare da mashi godiya, baiko amsa ta ba ya wuce cikin bedroom dinshi don shima yana buqatar warm shower sosai.( ( Ganin ya koma daki yasa tayi saurin tube kayan jikinta ta saka mara sa nauyi sannan ta sauya hijab dinta ta tayar da salla domin Rama wanda suka wuceta.( ( Bayan ta idar ta zauna tayi adduoi sosai sannan ta jawo ledojin daya aje mata ta fara budewa daya bayan daya, kamshin brown veggies pasta ne ya fiki hancinta, anatse ta soma ci Har ta samu taji ta koshi don Lkita yace ta takaita cin abinci sbd aikin da aka mata, mikewa tayi da sauran abuncin ta wuce kitchen ta aje sauran a fridge sannan ta bude drawers ta dauka glass cup ta Debo warm wata a cikin dispenser tasha kadan sannan ta koma parlor da cup din ruwan, zama tayi a kan couch din parlor ta jawo ledan magungunan ta balla wanda ya kamata tasha sannan ta aje agefe, anatse ta gyara kwanciyanta taja hijab din jikinta ta kukaje idanunta don tunda ta soma cin abinci baccinta soma fuzgarta, Ringinawa tayi don karya fama aikin da akayi mata acikinta. 87-88
Washe gari bata tashi da wuri ba don wani irin bacci ne mai dadi ya dauketa tun bayan sallar asuba datayi sai wajen karfe 11am na safe ta tashi daga bacci, wanda karar bude kofar fita da yayi ne ya sata farkawa, ganin ya fice yasa kamar kullum ta miqe ta wuce bedroom tayi wankanta a bathroom hankali kwance tayi brush da alwala ta futo kai tsaye, shiri tayi cikin baqar abaya wadda tasha stones masu kyau sosai, parking gashinta tayi wanda yake buqatar kulawa ta musamman sannan tayi rolling veil din abayar, wani irin sihirtaccen kyau tayi na musammam, rigar ta zauna dam a jikinta, tayi mata masifar kyau, red lipstick kawai tadan Mirza a lebbanta sai dan kohl data shafa a idanunta ta sannan tadan fesa turaren ta na hermz wanda yawan ci bata rabo dashi,agurguje ta karasa shiri ta kafin ta kashe tv dake Kara ta tattara parlor saida ta kammala kafin ta zari wayan ta ta saka flat shoes baki na Zara dake cikin akwatin ta sannan ta fuce, anatse ta rufo kofar sanin babu buqatar saka wani pin yasa ta wuce gaban lift cikin natsuwa ta shige ciki, dannan grown floor tayi within seconds ta iso ground floor, saida ta tsaya gaban compound na Yan mintuna kafin motar haifa ta kunno kai,saida ta tsaya daidai gaban ta kafin ta daga kafafunta ta karasa cikin motar murmushi kwance a fuskarta na kewar aminiyar Tata, tana zama tayi facing haifa tace  babeeee I missed you so badly kallonta haifa tayi fuskarta dauke da murmushi tace  bridey Ay na barki ne kisha honeymoon bfr mu samu baby sainazo na kula Dake da babyn dariya haifa ta kyalkyace dashi ganin yanda maganar da tayi yasa amra tabe baki murmushin nata ya dauke lokaci guda tace  in your dreams that s impossible my dear ay badan hakan akayi auren ba ko har kin manta & ganin dariyar Haifar taqi karewa yasa ta saurin cewa  wallah Zan koma idan bazaki bari ba mu wuce & , anatse haifa ta ja motar suka fuce daga harabar compound din saida suka hau kan babban titin dar jamal kafin haifa ta kalleta  babe yanxu da Ina zamu fara, ni inason zuwa shopping na karba black card din Abu Ma ( Latsa wayanta take bata dago ta kalli haifa ba tace  no babes mu fara zuwa saloon Ina buqatan hair treatment Kinsan yanda natural hair dina ke bani wahalaa Wallahi kamar na aske & (  Okay tohm, but kema nace maki just relaxed the hair kinqi kin tsaya gayuu, anyway yanxu na gane dalilin gayun da kikeyi it s because of& . ( Bata Bari ta karasa ba tace  haifa please!!!! Don t spoil my mood & dariya haifa ta dunga mata Har suka iso saloon, as usual Yauma saida aka fara Gyaran gashin nata kafin aka fara masu pedicure da menicure, Sai full body polish wanda haifa tayi requesting suyi, kusan awa biyu suka dauka kafin aka gama masu gaba daya, dakyar amra ta yarda haifa tayi payment din wanda bata so hakan ba, saida suka fito suka shiga mota amra ta fara jin yinwa, Sai alokacin ta tuna batayi breakfast ba gashi almost 2pm, da sauri haifa ta jasu zuwa wani cafe suka dan rage yunwa kafin suka wuce mall, basuyi wani sayayyya sosai don amra pir taqi yarda haifa ta kashe mata kudi wanda ganin hakan take yanxu bai daceba wanda akayi mata a baya Ma ya wadatar don babu mai maka irin wannan abun Sai mai sonka sosai, lallai haifa ta zama mata yar uwa wanda ta shigo rayuwarta babu sani babu tsammani, Duk yanda amra tayi kicin kicin haifa saida ta saya mata wasu kayan bacci Sai Yan abubuwan da zata buqata nan kusa kamar turare dasu sabulai wanda itama haifa din ta dauka Ma kanta, saida suka shafe wajen awa uku a mall kafin suka fito, lokacin wajen karfe 5 na yamma, tsayawa sukayi wajen grocesy shop wanda amra tadan saya kayan abinci don kwanakin da take duk a wahale takeyin shi ga kudin saving dinta yana neman yin kasa sbd yanda take kashewa tana ordern abinci ba kamar lokacin da take apartment dinta ba, bata yawan order lokacin sbd babu amfani indai har zata girka, few abubuwa ta saya hardasu fruit da vegetables sai shinkafa dasu pasta da seasonings da meats duk wani abun buqata saida ta sayo sannan tayi payment suka nufa mota, tafiyar 20mins sukayi suka iso lokacin wajen karfe bakwai na dare daidai compound din haifa tayi parking, da kyar ta lallaba amra ta karba sayyayan datayi mata a mall kafin tayi mata godiya sukayi sallama ta fito haifa kuma ta wuce, karasawa tayi cikin building din apartments din, agajiye ta karasa gaban kofarsu, saidata zo daidai kofar ta tuna bata san pin din ba hankalinta atashe tunawa da tayi last time da irin haka ta kasan ce mata kuma tana ta Allah Allah ta tambaye shi sai kuma ta manta,tunawa da ya rigata fita yasata tunanin maybe ya dawo, cikin hanzari ta soma danna door bell din, saida ta dauka Kusan 30mins tun bayan ta danna Sai uku shuru, hakan yasa tayi tunanin bai dawo ba sanin baya dawowa Idan ya fita wani lokacin ma harsai tayi bacci yake dawowa da daddare, aje shopping bags din da Haifa ta bata tayi da sauran kayan abinci data saya a Kasa sannan ta fara laluben wayanta dake cikin aljihun abayar dake jikinta, tana zaro wayan ta fara tunanin yanda zatayi laluben contact din haifa tayi, bata kaiga danna call din ba aka bude kofar, da sauri ta dago ta kalli fuskarshi don ta tsorata sosai batayi tsammanin yana nan ba tsawon lokutan data shafe a tsaye, idanunshi ya soma lumshe wa da alamu bacci yake mai nauyi sosai,white shorts ne kawai a jikinshi wanda ya kamashi sosai guntu don daidai wajen ma ajiyar dic** dinshi ne kawai ya samu rufuwa cikin shorts din, bai saka rigaba wanda haka ya same mashi kamar alada idan yazo kwanciya yakan tube ta sometimes, bin kirjinshi tayi da kallo wanda yake afafade ga fadi ga kwantaccen gashinsa da suka kwanta lub a kirjin zuwa ga damtsen hannunshi wanda yanda ya damke kofar karfaffen hannunshi hade da jijiyoyin wajen suka bayyana sosai, da sauri ta fara kokarin sauke idanunta saidai akan six packs dinshi suka sauka da sauri ta runtse idanunta lokacin da suka sauka kan tiny tight short dun jikinshi wanda suka ka mashin sosai kuma suka bayyanar da manhood dinshi sosai kamar a fili da yanda gabanshi ya ciko sosai Har wajen na yin tozo kamar zai fiddo kasa, gabanta ne ya fara bugawa pat pat, da sauri a dfe kirjinta tayi saurin kawar da idanunta bakinta na karkarwa tana furta adduar fargaba kawar da idanunta tayi daga shi gaba daya, ganin ta tsaya sototo yasa shi Jan dogon tsuka ya juya afusace ya koma daki don ta katse mashi daddaen bacci da ya daukeshi bayan ya dawo daga wani private meeting da yayi da wasu private investigators baimayi tsammanin ita ke knocking ba dukda lokacin daya dawo bai ganta ba kuma bai damu ba don ba shiga harkar ta yake ba sbd baya son raini ko kadan and shi bamai son mutane bane.
( Yana shiga daki ya wuce toilet yayi wanka ya dauro alwala don gabatar da sallolin da bai samu yayi su ba, yana idarwa ya cire jallabiyan ya sauya zuwa nighties masu laushi don garin ya soma sanyi sosai cikin Yan kwanaki, wanda idan sanyi ne to fah sanyi za ayi sosai idan kuwa zafi ne shima haka za ayi zafi sosai don wether din uae babu sauqi, anatse ya lalubo wayanshi ya kunna lokaci guda yaci karo da messages da yawa wasu daga doctor shi wanda reminder ne yake mashi akan de-freezing sperm dinshi da ya kamata ayi tun last week don daman due date din 3 months ne yana gama duba message din doctor ya bude na Hammam shima dai akan aiyukan office ne wanda za ah koma monday gaba daya, Sai last message daga private investigator daya saka yayi mashi bincike akan amra, qurama message din idanu yayi yana maimaita abinda mutumin ya rubuta  good day sir, I have a new update,both the children are been admitted yesterday night, which one of them is brutally injured I want to confirm if I should keep digging about their sickness ( Saida ya gama karantawa tsaf kafin ya tura mashi message  go ahead, keep a close eye on them,if there s need of any help go to them anonymously ..yana tura mashi ya aje wayan, tunani da yawa na yawo a kanshi, tabbas yarinyar nan rayuwar ta da kanneta abin dubawa ne, dukda ya gane cewa kamar bata da sanayya akan matsalar da qannenta ke ciki, yana nan zaune tayi knocking a natse saida ya dauka kusan minti biyar kafin yace  come in ,budewa tayi ta shugo Har lokacin tana sanye da abayar data futa , anatse ta dan karasa nesa dashi tace  ina wuni bata jira amsa shi ba don tasan da wuya ya amsa, hakan kuwa ta kasance don ko kallon inda take bai sake yiba saima gyara zama da yayi akan gadon yana latsa tsadaddiyar wayarshi that is worth of dollars, wucewa toilet tayi saida ta tabbatar ta kulle daga ciki kafin ta soma tube kayan jikinta don Duk sun takureta sabd wuni datayi dasu, wanka tayi da sabulunshi mai kamshi na royy soap shidai komai nashi is expensive don ta sha ganin soap din idan taje sayayyan kayan skincare dinta wurin packaging dinshi ma da slot din sabulun is different from general soap da ake saida wa, alwala kawai ta dauro, saida ta mayar da rigarta kafin ta bude kofar ta fito, yanda ta barshi haka ta same shi ahankali ta soma takawa zata fuce daga dakin saida ya tabbatar tazo tsakiyan dakin kafin ya dago ya kalleta daga sama Har qasa tunanin iri iri na yawo a ranshi, kwata kwata bai ga alamun damuwa a tattare da ita ba amma sanin irin kukan da take Duk dare da yanda tayi pushing kanta to marrying stranger don ta samu katin kasar uae don wani kudiri nata daman don har yanxu bai yarda da dalilin da suka bashi ba akan katin kasar nata amma yanxu yake ganin komai is making sense nunfasawa ya danyi kafin ya soma magana Adan fadace cikin kakkausar muryarshi  where have you been ?( Da sauri ta dago ta tsaya chak bata juyo ba, juyawa ta soma yi kanta a Kasa kafin ta dago tayi mashi kallo daya don batayi tsammanin jin tambayar daga bakin shi ba,anatse ta soma motsa bakin ta tace  uhm..daman naje Gyaran gashi ne nida haifa & . Shuru yayi kafin cikin dabara ya soma magana  Kinsan halinda Yan uwanki suke ciki mamaki ne ya cikata don bata gane wani Yan uwan yake nufi ba, ganin yanda tayi da idanu ya sashi cewa  you can go juyawa tayi ta fita daga dakin tana maimaita tambayar, ganin ta Kasa gane inda ya Dosa yasa ta kawar da zancen ta shirya cikin kayan baccinta ta daura dogon hijabinta ta tada sallah tana idarwa tayi kwanciyarta don baccin dake fusgarta, shima Sai wajen karfe uku ya koma ya kwanta bayan ya tube rigar jikinshi sannan ya shige cikin lumtsentsen duvet dinshi,( Amra wanda wani mummunan mafarkin datayi ya sata kwala uban kara tana innalillahi arazane ta zauna tayi zaman dirshen babu abinda take furtawa Sai innalillahi, wani irin mafarki tayi akan su salima wanda yayi mata zuwa kamar zahiri, don ta tsorata sosai da yanda yanayin mafarkin yazo idan Har badan tanada imani ba zata ce abin da ke faruwa kenan da kannenta, Salim ne ta gani yashe a kasa duk jikinshi jini kamar matacce Sai salima wadda itama tana kwance jina jina dukta galabaita, babu abinda take Sai kuka tana cewa shikenan Salim ka mutu innalillhi adda shikenan nima mutuwa zanyi, adda yunwa nake ji adda kizo ki taimake ni yunwaa bata kaiga karasawa ba ta yashe itama ta kasa matatta take zuciyar ta ta buga, wannan munmunan mafarki ya tayar Ma da amra hankali sosai ba kadan ba, wanda a mafarki tana kallonsu salima amma ta Kasa taimaka masu don tayi nisa sosai don ko muryarta salima bataji saidai ita tanajinta sosai saida taga salima Ma ta mutu yasa ta kwala karar data sanya ta Tashi itama afurgice, zufa ne ke tsatsofi mata Sai hawaye kamar famfo, Duk ta burkice Sai addua kawai datazo baki ta take kamar zautacciya, ?( Amar wanda bai dade da lumshe idanu ba bacci ya dan fisgeshi jin wannan razananniyar karar yasashi saurin miqewa ya sauko ya fito daga dakin, da sauri sauri ya karaso gaban parlor ganin ta zaune ta daura hannu aka tana rapka kuka ya sashi bin parlor da kallo, saida ya duba ko ina don duk a tunanin wani abun ne ta gani dazai cutar da ita, takowa yayi har gabanta ya tsaya ya mata kallo daya hannayenshi nade a kirjinshi kallo daya ya mata ya kawar da kanshi kafin ya soma Magana cikin kakkausar muryar shi mai amo   keeee ihun me kike yi a cikin daren nan, are you sure bakida matsalar kwakwalwa kuwa  & saida yakai karshe maganar tashi ya zuba mata kyawawan idanunshi masu kwarjini da haiba, jin saukar muryarshi ya sata dawowa cikin hayyacin ta, maimakon ta daidata saita kuma daburcewa ta guntse bakinta wani irin matsanancin kuka na ambaliya a fuskarta ta sukuyar da kanta,   hey look up  ya fada chan kasan makoshi, dagowa tayi
Ta zuba mashi eyeballs dinta da sukayi jaa sosai gwanin ban tausayi, takawa yayi gaban kujerar parlorn ya zauna ya dora kafa daya kan daya yace   zo  , anatse ta miqe, silk riga da wando ne na banci wanda suka lafe a jikinta masu santsi, wandon yayi mata kyau dukda bai dameta ba ammam yanda yake da santsi ya lafe a jikin fatar jikinta, kawar da idanunshi yayi daga kanta ganin yanda rigar ta shafe da kirjinta da babu bra sai tsayyayun bobby dinta wanda suke looking so puffy daga cikin rigar ga shatin nippy dinta dayayi tsini ta gaban rigar wanda kallo daya zakayi ma gaban rigarta zasuyi welcoming dinka, bai sake kallonta ba ?yace   whats wrong with you, kinada matsala ne?  , shuru ta danyi tana share hawayen dake zubo mata masu zafi, wani irin radadi take ji acikin zuciyarta, bata ko kalleshi ba ta ahankali karamin bakinta wanda ya zubama ido ta soma Magana   nayi mafarkin kanne na ne, sun mutu  , nazari ya soma yi kafin y ace   mafarki gaskia ne?, girgiza kai tayi alamun ah ah, kafin ya cigaba   da kikayi mummunan mafarkin meya kamata kiyi?,  shuru ta danyi kafin ta soma Magana cikin shshekar kuka   Addua  , jinjina kanshi yayi yace   kinsan da hakan shine kika zauna kina yin ihu kamar bakida ilimi,ko ihun da kikeyi ne zai kawo maki kannenki?, I will warn you this is the last time hakan zai sake faruwa idan abu ya sameki, ba shirme zaki tsaya yiba, kukanki zaki kai wajen allah  , zuba mashi ido tayi wanda shma ita din yake kallo, wani irin sanyi ne a cikin maganganunshi wanda saika natsu zaka fahimci Magana yake cikin natsuwa da kamewa, share hawayenta tayi tass sannan tace   in sha Allah bazan sake ba  ,   good for you  yana kaiwa nan ya mike ya wuce cikin dakinsa ya barta anan tsaye, ganin kusan karfe hudu da rabi yasa ya shiga toilet kawai ya dauro alwala ya futa ya sanya farar jallabiyanshi mai kamshi ya tada kabbarar sallah, yana cikin salla ta shugo dakin itama ganin dakin da dan haske yasa ta wuce toilet din ta dauro alwala ta futo, bata kalli inda yake ba ta fuce zuwa parlor ta zurma hijab dinta ta fuskanci kibla ta fara gabatr da salla dakai kukanta wajen allah ta dade sosai har aka kira sallar asuba tana nan zaune bayan ta idar ta soma azkar,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login