Showing 6001 words to 9000 words out of 381117 words

Chapter 3 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

1954

suka ganshi shida m-5 suna takowa zasu wuce wajen motorn su, kallonshi amra tayi shima kallo daya yayi mata ya dauke kanshi sannan ya shige cikin moton shi, suka ja, sunkuyar dakai amra tayi tunani iri iri sunyi mata yawa, gida suka wuce inda haifa takira abuh ta Sanar dashi cewa zata kwana wajen amra, baiko hanata ba ya barta don ta fada mashi abinda ya faru ah asibiti kuma ya gani ah news.

Kula da ita sosai haifa tayi kamar yar uwarta ta jini, duk wani motsi sai haifa ta tambayi ko tana buqatan abu, har suka kwana uku tana kula da ita hartaji sauqi sosai, saidai yanxu ta rage Magana sosai sbd damuwa tayi mata yawa sosai akan batun su salima.

Haka suka karaci wannan kwana ukun sannan washe gari suka shirya suka koma aiki, babu wani aiki sosai sbd ana shirin yi hutun karshen wata, haka yasa basu wani dade ba suka dawo gida, washe gari ma haka suka karaci zamansu sannan suka fito, ganin shuru shurun amra ya fara yawa yasa haifa ta jata zuwa yawo, saida suka zagaye wurare da dama wanda yasa tadanji dadi sosai don damuwarta tadan ragu sosai.
'?('***Auren Katin Kasa ***('
'?
(Unexpectedly fallingd'?
Story and written by:
QueenMarh=?x?

Paid book =???
52

Salima kuwa azaman da sukayi ita da salim rashin lafiya sosai suka dunga yi, don sunyi wata irin rama sosai, salim kuwa kamar wanda ya samu qanjamau, don yanxu mama rabi ta daina aiki dalilin danta daya samu aiki a wani company babba ya saya mata gida da duk wani abunda zata buqata, haka yasa yace tabar aiki tunda girma yazo mata sosai.
?
Hakanan badan taso ba tabar aikin, don zataso ta zauna kodan su salima da salim wanda ta kasa fahimtar meysa ake wulaqanta su aka maidasu kamar prisoners agidan.

Dalilin tafiyar mama rabi yasa aka kawo wata rita, wadda ta sha rayuwar bariki ganin rayuwa ta juya mata yasa ta nema aiki kuma ta samu acikin gidan.

Rita irin mugayen yan iskan gari ce, ita ba musulma ba ita ba Christian ba, kuma baqar muguwace ita hakan yasa tasu tazo daya da khady don ta iya tafiya da yanda mutane sukeso, haka yasa khady ta bata umarnin daina bawa su salima abnci sau uku saidai sau daya arana, ganin hakan khady keso yasa taga banza ta samu, duk wani abu da ake basu na buqatu saita hana su irinsu sabulun wanka, da maclean wanda ake ajewa don yan aiki.

Yau kusan watanni Kenan rabon da suyi wanka da sabulu, duk sunyi baki sun dawo kamar aljanu, babu wani kuzari ajikinsu, wannan wahalar tasa cutar salim tashi gadan gadan, gashi babu magani ita kanta salima ciwon cikin nan dai qara gaba kawai yake, duk dare saidai tayi kuka ta godema Allah, yanxu basuda wani gata sai Allah, an raba su da yar uwarsu da karfi da yaji.
?
Abuja Nigeria& ..
Hankali atashe Amma ta mike ta fara zaryar tsakanin dakinta da parlor, jiran fitowar aman kawai take, kusan rabin awa kafin ya fito hannunshi rike da kwalba da alamu abuge yake, gabansa ta karasa tana kokarin kama hannunsa ya buge shi yace   uban waye wannan zai taba ni  hawaye ne suka cika idon Amma hankali atashe ta fara Magana   aman meysa kake son salwantar da rayuwarka, aman wannan ba rayuwa bace mai kyau..tana kaiwa nan hawaye na zuba akan kyakyawar fuskarta wadda take sak da amar, matsowa yayi dab da ita zaiyi Magana Kenan sai amai sharr ajikinta, runtse ido tayi ta tallabeshi tana bubuga bayanshi harya gama sannan ta kwala ma yar aiki kira tazo, ahankali lantana tazo sannan ta umarceta data share wajen, ahankali ta dagoshi daga jikinta sannan ta jashi har dakinsa ta kwantar shi, toilet ta shige ta debo ruwa a bowl ta fara share mashi jikinshi da towel saida ta gama tsaf sannan ta tashi, cikin layi ya jawo hannunta ya rungume kamar za a kwace mashi hannun ya fara sambatu   mummy karki tafi, mummy ki yafe min, wallahi banida karfin ikon abinda ya faru dake, daddy daddy& .   da sauri kuma ya lumshe idonshi bacci ya daukeshi.. zare hannunta tayi ahankali sannan ta mike ta rage mashi sanyin air con ta fito aranta tana mamakin me aman ke nufi da abinda yake shirin fada don da alamu abu na damunshi sosai don harda kwalla yake zubdawa, ganin bata da mai bata amsa yasa ta? kawar da zancen kawai ta wuce kitchen.

Amar s& ..
Kwance yake, da laptop agefenshi, tunda ya tashi da asuba ya kasa komawa bacci anatse ya fara kallon laptop din wanda tun bayan asuba yake kallon screen din ya kasa gano clue kwata kwata, sake maimaita word din yayi MKS da sauri ya rufe system din kawai ya kasa gane me abin ke nufi amma yayi alqawarin duk abinda zaiyi saiya nemo ko wacce hanya ce don exposing wannan kungiyar ta mutun uku& ..mutun uku yana fadin haka aranshi da sauri ya dawo gaban laptop din ya bude sannan yace   m..k..s I got it now, da sauri yayi murmushi sannan ya wuce toilet, kamar kullum yauma saida yayi bubble bath sannan ya futo ya wuce closet dinshi ya fiddo da kayan da zaisa don yau baya tunanin saka kakin shi.

Anatse ya shirya cikin kayanshi farare tass riga da wando, kayan sunyi matuqar amsarshi, sai yayi wani irin kyau, anatse ya shiga lift ya sakko sitting room, kiran Pablo yayi a kawo mashi breakfast, bai wani ci da yawa ba ya fito ya wuce cikin white color ferarri shi wadda itama sai kyalli take don tsafta, anatse m5 ya fito ya sara mashi sannan ya bude mashi ya shiga suka kama hanya, haka kawai ya tsinci kanshi cikin farin ciki, har suka isa cikin headquarters, koda ya fito ya shiga ciki kowa mamaki yake yanda idan aka gaisheshi baya amsawa amma yau gashi yana masu murmushin da yake melting zuciyar matan wajen da yawa ciki kuwa harda hafiza wadda ta shigo domin diban sample din blood din senior officers, ganin yanda yake cikin farin ciki yasa ta yi alqawarin komai zai faru yau kam saita bayyana mashi sakon zuciyar ta, fucewa tayi zuwa asibiti fuskarta dauke da murmushi, tana shiga office dinta kuwa lokacin amra bata nan taje second patient check up, anatse ta samu waje ta zauna sannan ta cire dan kunnenta ta chanza zuwa na diamond sannan ta shafa red lipstick , daman abayane ajikinta mai budewa wanda tayi buttoning din ta sanna ta daura lapcoat, batako saka mayafin abayan ba saita riqeshi ahannunta , wayan ta kawai ta jawo sannan ta fito bayan ta dan feshe jikinta da turare mai kamshi, ahankali ta fara fita harta shiga cikin headquater sannan ta shiga lift zuwa office din general.
'?('***Auren Katin Kasa ***('
'?
(Unexpectedly fallingd'?
Story and written by:
QueenMarh=?x?

Paid book =???
53
Knocking ya fara yi saida aka dauka kusan 5mins kafin taji yace come in, ahankali ta bude kofan ta kutsa kanta ciki, azaune ta tarar dashi hakimce, waya maqale a kunnenshi, baiko kalli wanda ya shigo ba but yajiyo kamshin turarenta, ahankali yake motsa bakinshi kamar mai shagwaba yace   Amma I promise insha Aallah zanyi kokari ko kwana biyu ne zanzo nayi but for now aikin yayi min yawa  shuru ya danyi ya lumshe idonshi saida ya gama lallaba Amman shi kafin suyi sallama sannan ya kashe wayan.

Baiko kalli inda hafiza ke tsaye baya soma gyaran murya yace   how may I help you? jin bai yi mata fada ba akan zuwa mashi office daya hanata ba yasa tayi saurin gyara tsayuwar ta sannan ta soma Magana cikin kwarkwasa   sir daman akwai wani Magana da nakeso nayi maka mai mahimmacin  ..jin hakan ya sa shi tsagaita abinda yake ya dago ya mata kallon ke har kin isa kizo gabana kice kinason Magana mai muhimmanci dani, shi mamaki ne ma ya cikashi sbd babu abinda ya taba hadashi da ita in banda lokacin da tayi mashi kallon da bayaso hakan yasa ya soma magana cikin harshen turanci da muryanshi mai dadin sauraro   okay go ahead  ..babu wani bata lokaci ta soma bayani   harga Allah nifa sonka nake sir, babu wani kwana kwana, kuma duk abinda kake buqata zan iya yi maka koda kuwa bada rai na ne  dariya ce taso kufce mashi anatse ya guntse ta sannan ya tamke fuska kamar baitaba dariya ba   so you even have the guts to come in my office without my consent and you think akwai abun da zanso a wajenki sannan kin tsaya agabana kina fadamin maganganun banza huh!........ya buga table din, ganin haka yasa hafiza saurin karasowa gaabanshi da sauri ta sanya hannu jikin lap coat dinta ta sabule ta sannan ta fara kokari cire rigar jikinta, baiko ankare ba ta yasar da rigar ta tako har gabanshi daga bra sai pant ajikinta, amai ne ya fara kokarin kakaro mashi, yama rasa mey zaiyi, wani irin azabben masifa ce ta tunkaro shi, runtse ido yayi don karta gane, itako duk atunaninta haqarta ce ta cimma ruwan don haka ta fara takowa daidai gabanshi ta duqo daidai saitin fuskarshi ta soma hura mashi iskan bakinta tace   harda wannan ma  , ta girgiza mashi yan nonuwanta kananu kamar ta roka aka sammata , bude idonshi yayi wanda masifa ta ciyoshi sannan yayi sauri hankadata wanda hakan yasa tayi tangal tangal ta fadi, da sauri ya miqe yace   get out before na illataki  hafiza da taurine kai kuwa tana miqewa kamar zata wuce sai ta dawo da gudu ta rungumeshi, azabure ya tsaya yana kallon ikon Allah, kankameshi tayi sosai tana shafa mashi kirjinta sannan ahankalin hannunta ya fara yawo a kasanshi ganin abun ya fara wuce gona da irin yasa ya jawo gashin kanta sannan yayi baya da ita ya kwasa mata maruka zafafa guda uku ajere tass tass& lokaci guda hafiza ta tayi hutun wucin gadi, saidata dawo sannan ya karan hankadata da table din shi, nan take goshinta ya fashe, ganin zai mata illa wanda shi sam cikin tsarin rayuwarshi babu dukan mace yasa yayi sauri jawo landline dinshi yace   get the car ready now!!  yana kaiwa nan ya kalli hafiza wadda fuskarta harta kumburo hawaye shabe shabe yayi saurin cewa   ki tattara qazantar jikinki da kayanki ki fice daga office dinnan, zan kyaleki ne kawai sbd ke macece badan haka ba da saina illataki don girman laifinki ba wanda zan iya yafewa bane, sannan kisama ranki cewa aiki anan kin gamashi har abada, I don t ever want to see your face, yana kaiwa nan ya fuce daga cikin office din nan ya wuce gida.

Hafiza kuwa takaici bakin ciki duk yagama cikata ga disgin da yayi mata hakan yasa ta tattara tarkacen ta, sannan ta shirya ta fuce fuu kamar iska, batama tsaya shiga office ba ta wuce motarta ta fusgeta tabar premises din gaba daya, tunda ta shiga mota take huci, bata taba tsammanin zai mata haka ba, ga dizgi ga wulaqanci babu abinda take cewa sai   you ll regret this, I will surely make u regret what you did amar yunus tauraaaa&

Amra kuwa tana cikin aikinta wayanta ya dunga ringing, saida ta gama duba patients kafin ta fito ta wuce office, zama tayi sannan ta fara kallon missed call din, ganin number Nigeria yasa tayi saurin kira don tunaninta kawai ya kawomata su salima ne, saida ta kira kusan sau biyu kafin adauka, anatse ta soma Magana cikin harshe turenci   hello please dawa nake magana  & rita kuwa ganin number kasar waje yasa tayi saurin cewa wrong number, kune masu kiran mutane mu dauka daga kasar waje ne ashe yan scamming ne  tana kaiwa nan ta kashe wayarta, amra kuwa cikin rashin jin dadi ta aje wayan gefenta sannan ta doka tagumi, babu wanda take tunani saisu salima, ko a wani hali suke, yanxu idan tace zatayi kokarin komawa gida karatun ta zai salwanta barema bazai yuwu.
'?('***Auren Katin Kasa ***('
'?
(Unexpectedly fallingd'?
Story and written by:
QueenMarh=?x?

Paid book =???

Chapter 54
Bangaren rita kuwa tana aje wayan ta cigaba da wanke wankenta, Allah Allah take ta gama ta tafi wajen khady domin kai mata sakon molly data bata ta sayo mata, wato itama yar hannu ce shiyasa take kokarin siyeta da abubuwan mayen, ita kuwa khady sauqi ne yazo mata har gida don yanxu rita ce aminiyarta don itake kawo mata komai kuma ita ke mata introducing abubuwa sabbi wanda hakan ba karamin dadi takeji ba.

Saida ta gama gyare gyare sannan ta aje wayan nata a daki tayi wanka sannan ta shirya cikin casual dressing dinta na kafirai, riga da mini skirt sannan ta fito ta wuce sama wajen dakin khady, saida kwankwasa mata kafin ta shige ciki, akwance ta tarar da ita, ganin rita yasa khady mikewa tana fadi   my girllll, hope todays molly is powerful  murmushi rita tayi sannan ta zauna gefenta tace   ma, todays molly is so powerful but the money high o,  jin haka yasa khady miqewa ta wuce wajen da take aje hand bag dinta, anatse ta zaro yan dubu dubu guda biyar sannan ta dawo gaban rita, hannu rita ta miqa ta karba, saida ta kirga kafin ta zaqulo yar takardar daga kwankwasonta ta bata, hannu na rawa khady ta fuzge sannan ta fara kokarin budewa, tana ganin molly tayi maza ta bude ta shaqa, wani irin bari jikinta ya fara sannan ta afka abakinta, ko minti biyar batayi ba ta lula, ruf ta fadi don wannan mai shegen karfi ce, ganin khady ta jeme yasa rita dariyar mugunta tace   shegun yara kunfi kowa iya kananun iskanci, iyayenku na daki kuma kuna daki kuna naku iskanci,  ahankali rita ta fara bude jakar khady, saida ta yasheta tass sbd tasan cewa idan har ta farka bazata tuna duk wani abu data aje ba, saida ta kwashe yan zobinan gold dinta sannan ta wuce drower dinta ta kwashi English wears dinta wanda suka mata sannan ta tattara komai waje daya ta dawo gaban khady ta kuma kecewa da dariya sannan tace   tunda har kin lula nima saina kwashi rabona, 

Saida rita ta kwakuleta tass kafin ta fice daga dakin, khady wadda azaba ta fara dawo da ita daga cikin hayyacinta yasa ta fara aman wahala.
?
Bayan fitar rita kuwa salima tana ankare da ita hakan yasa tayi saurin wucewa cikin dakinta ta dauki wayanta sannan ta dawo dakin su, ahankali ta soma laluben number amra wadda ta rubuta acikin paper kafin akwace masu wayan data bar masu, hakan yasa tayi saurin lalubar number tayi dialing, kusan sau biyar wayan ba a dagawa hakan yasa salima ta fashe da kuka, tana cikin kukan taji karar kofar rita, hankali atashe ta mike tana labewa jikin kofar har saida rita ta rufe kofar dakinta, hankali atashe ta jawo wayan ta kashe wayan sannan ta wullata cikin drower, rita kuwa agajiye ta dawo daki bata bi takan wayanta bama ta kwanta abinta.

Washe gari duban duniya rita tayi ma wayan ta, amma bata samu ba hakan yasa hankalinta tashi sosai, ta koma dakin khady koda ta shiga bata sameta ba, haka yasa ta juya zata fuce jin kakarin amai yasa ta tsaya sannan ta wuce toilet din khady, zaune ta tarar da ita tana kwara aman wahala, saida rita ta taimaka mata tayi wanka sannan ta futo, ta kwanta.
Rita kuwa tsabar dariyar mugunta dake ciyo ta yasa tama manta da batun waya.

Kwana hudu Kenan rita na neman waya harta gaji ta shirgama khady karyay cewa saida wayar ne zata samu ta dunga karba mata molly, haka yasa khady ta shiga dakin mummyn su haj kareema, ta kwaso kudi masu yawa acikin drower ta lokacin haj kareem ta shiga toilet, saida ta diba mai isarta sannan ta futo ta wuce daki, nan ta tarar da rita tana jiranta. Duka kudin kuwa khady ta bata, batama tsaya kirgasu ba.
Rita kuwa dadi kamar zai kashe ta, tana komawa daki ta kwashi dubu biyar sannan ta boye sauran daman ranar zataje sayan groceries don haka tayi shirin tafiya da dubu biyar dinta don ta sayo sabuwar waya.
?
Salima kuwa saida ta jera kwana biyar tana kiran amra bata samunta don duk sai dare take samun yin wayan don tsoro takeji sosai kar akama ta tana wayan. Bangaren amra kuwa duk cikin dare sai an kirata da wannan number da matar tace wrong number, ganin hakan yasa tayi tunanin qila mistake suke suna kiranta, wanda yawancin kiran sai dare ake mata kuma lokacin tayi bacci.
?
Bayan kwana biyar salima kullum saitayi kiran number amra, yanxu tashin hankalinta charging wayan da yake neman mutuwa gashi tana tsoron zuwa dakin rita dauko charger don karta gane cewa itace da dauka wayan ta gashi jikin salim yayi wani mugun tsanani don yanxu abin nashi harda seizure idan ya fara saiya dauki wajen minti ashirin kafin ya dawo daidai.
'?('***Auren Katin Kasa ***('
'?
(Unexpectedly fallingd'?

Paid book =???

Chapter 55

Tunda salima ta tashi yau take tsoron daukan wayan don charging bazaikai mata dare ba zai mutu haka yasa tayi dialing number amra, lokacin da kiran ya shugo amra na tare da haifa suna duba patients, jin kiran yayi yawa yasa ta zaro wayan sannan tadan koma gefe ta daga ta fara Magana   hello who s this? .. jin an daga wayan yasa salima fashewa da wani matsanancin kuka tace   addaa adda nice ki kirani  jin muryar salima yasa amra saurin cewa   salima salima kece salimaaa   da sauri ta kashe wayan sannan ta sake kiran layi, da sauri salima ta dauka ta fashe mata da wani matsanancin kuka tace   adda nice, adda muna cikin mawuyacin hali, adda ki taimake


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login