Showing 21001 words to 24000 words out of 381117 words

Chapter 8 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

1957

naso na Makara, ki sakko kawai yanxu yanxun nan,  ..jin haka yasa ta jawo jakanta ta maqala a hannunta sannan ta zaro flat shoes din ta suma farare kal sannan ta sa kai ta fuce bayan ta kulle kofar, tama manta da chanza rigar da taso tayi, & anatse ta karaso har gaban moton haifa, budewa tayi sannan ta shiga haifa ta jasu zuwa private loung din, tafiyan minti ashirin sukayi suka iso, tunda shuka shigo compound din gaban amra ya dunga faduwa, ahankali ta dunga karanto adduoi don she s so nervous, hannunta haifa ta jawo suka wuce ciki tana ce mata   calm down babe, don t be nervous kinji, just put your trust in Allah komai zaizo mana da sauki,  jin haka yasa amra dan daidaita natsuwarta sannan suka shiga ciki, wurin is so peaceful babu hayaniya kwata kwata, don wajen kamar bangare bangare ne, dukda da mutane amma ba ajin maganganun mutane saidai yan sautika kadan kadan,wajen da sukayi reserving suka shige suka zauna, nan aka kawo masu starter na chai tea mai kamshin dadi, suna nan zaune wajen minti biyar kafin suji sallamar matar, atsanake ta zauna suka gaisa cikin mutunci kafin itama a kawo nata chai din, tataunawa suka dan fara yi kafin su hammam su karaso.
?
Hammam ko yama manta bai sanar da amar ba da wuri, hakan yasa yayi saurin wucewa gidanshi, direct sama ya wuce cikin dakin amar, lokacin yana kwance yana bacci hankali kwance, har gaban gadon hammam ya karaso sannan yace  kai gayen nan dan iska ne, baccinshi ma yake hankali kwance da karfe daya na rana, jin an yaye duvet dinshi ya sashi saurin bude idonshi da bacci bai gama bari ba yace   what the hell is this hammam,  & hammam baiko tanka mashi ba yace   get ready we re going out, yau zaka ga bride dinka  ..jin haka yasa amar doka tsaki yace   get out please zan kimtsa  ..jin haka yasa hammam mikewa ya wuce wajen kofa yace   nasan halinka yanxu saika kai wajen awa kana wanka kamar kifi, dan allah karka bata mana lokaci  ..yana kaiwa nan ya fucewarshi zuwa qasa don ya jirashi ya kimtsa..ganin ya fuce yasa ya yaye sauran duvet din dake jikinshi, ya sakko da kafanshi ya sanya bathroom sleepers ya miqe tsaye, babu komi jikinshi sai wani dan mininin shorts wanda ya zaune mashi dam kamar pant na maza, kirar jikin shi ta futo sosai kamar giant, miqa yayi wadda ta fidda duk wani karfafan gabbanshi da jijiyoyin su, anatse ya wuce bathroom, wanka yayi na kusan 30mins kafin ya futo ya wuce closet room, ahankali ya zaro riga da wandonshi marasa nauyi kollon black, da shorts farare da inner vest, ahankali yake abubuwan shi kamar mace, kamar kullum yauma saida ya yi ruwan turare kafin ya sanya kayan, kayan sunyi mashi masifar kyau, ko ina zamzam, saida ya gyara sajen fuskarshi wanda ta cika sosai don bai saisaye ba a kwanakin, sai sheki suke yi baki sidikkk, ahankali ya futo bayan ya saka wani tsadadden loafters dinshi shima baki sannan ya bude glasses drawers dinshi, ahankali ya zaro wani hadadden bakin glass ya aje shi gefe sannan ya shimfida sallaya ya gabatar da sallar dhuhur saida ya idar sannan ya miqe ya dauko glasses din ya sanya a idanunshi, wayoyinshi ya jawo ya sanya a aljihunshi ya fara fitowa Har ya saukko kasa, duk wannan shirin da yayi ya dauka wajen awa daya yana yi, hammam na ganinshi ya soma cewa   shege, wannan wankan duk saboda zakaga bride din naka ne  ..amar ko baima kalleshi baya wuce hanyar fita da sauri hammam ya buyoshi sannan suka wuce a motor hamman.

Wuraren karfe uku suka isa cikin private loung din, anatse suka fito atare, gyara zaman glasses dinshi yayi sannan ya zura hannunshi daya cikin aljihun wandonshi, dayan kuma ya rike wayansa, yana dannawa,..tafiya suka soma yi har suka shiga cikin loung din, sanin inda akayi reserving yasa hamman tunkarar wurin direct shi kuma amar biye dashi abaya, anatse hammam yayi sallama, wanda haifa ne kawai ta iya amsa wa tana dagowa domin ganin waye na bayan hamman din, anatse suka kutsa kai suka zauna akan carpet din loung din, amar wanda tunda suka shigo bai ko bi ta kan kowa ba hankalinshi nakan waya. Itako haifa suman zaune tayi ba ita kadai bama harda matar dake tare dasu, amra kuwa bata san me ake ciki ba don gyagyadi ta soma, inda ta dan dafe da jinkin bangon wajen, ahankali wani sanyayan kamshi ya fara shiga cikin hancin, da kyar ta fara bude idanun ta suka sauka kan wanda ko a mafarki bata tsammanin zata taba hada wurin zama daya dashi ba, bude baki tayi galala kamar wadda ke shirin Magana, shiko oga baimasan tana yi ba, yadai san inda ya zauna yana fuskantar mutun,..haifa ce ta tattaro nata natsuwan sannan tace   greetings to general sir  .. baiko dago ba bare ta saka rai ya amsa, ita ko amra ta kasa cewa komi ma, kallon da tayi mashi da farko ta kawar dakai bata kuma gigin yin wani ba.

Cikin tsoro matar ta gaishesu don sarai ta son su kuma tasan muqamin su,amma batayi tsammanin sune wanda suka amince da wannan abin ba, haka yasa ta kame kanta don kartayi laifi.

Hammam ne yayi gyaran murya sannan ya soma Magana   wannan abokina ne kuma ogana amar, wanda duk nasan kun sanshi, general amar,shine wanda zakuyi yarjejeni  ..ya nuna amra wadda a tsure take hankali tashe, sannan ya cigaba,  kamar yanda na fada maku last time shima yana da nashi buqatun, kamar yanda ke amra kike buqatan katin kasa wanda zai taimaka maki ki samu kema kuma zaki taimaka masa. & & ..

Jin abinda hammam ya fadi yasa yayi saurin dagowa don kallon hammam din, wai zata taimaka mashi, shi sam word din da yayi using bai mashi ba, akasin hakan yasa idonshi bai kaiga zuwa kan na hammam ba ya sauka akan ta, zaro ido yayi sannan yace   who s she?  da sauri ta dago kai ta kalleshi, ganin yanda idonshi ya cikata da kwarjini yasa tayi saurin saukewa, shiko kallonta ya tsaya yi na wajen minti goma kafin ya kalli hammam yace   I m asking who s she  ..don harga Allah yana jin kamar ya taba ganin fuskar tata, amma ganin gwara ya samu tabbacin ita dince yasa ya sake tambayan..  she s amra, she works in headquarters with haifa, she s the lady that took your sample the other day  ..jin hakan yasa ya tabbatar da ita dince din dai, wannan mai rawar kan ayanda ya maqala mata Kenan,..ganin yanda amar ya sauya lokaci guda ya sanya hammam cewa   mrs lily can you start your job now  & anatse matar ta soma cewa   okay sir..sannna ta zaro wata doguwar paper daga cikin jakanta sannan ta soma bayani ..  na farko dai duk yanda nayi tunanin abin zaizo da sauqi sakamakon yanda kuke da mukami babba abin zaiyi wuya, na farko dai dole kunsan marriage consent group saisun yi research akanku domin dukkan ku bayan kasarnan bane, but tunda oganku soja ne babba anan kasar wadda government ta bashi katin kasa dalilin haka, amma ita sanin itama yar kasar da yake ce dole saisunyi bincike sosai wanda ina tunanin hakan zaizo da sauqi idan har sukayi pretending suna son junan su sosai, na biyu kuma auren ne, dole yanda addini ya tanadar haka za ayi shi don auren sunna ne tunda ku musulmai ne kuma dole saida waliyy dinta wanda ku zaku nema wanda kuka yarda dashi don yayi hakan kuma ya rufa maku asiri, don for sure marriage consent group saisun buqaci wasu bayanai daga wajenshi harma binciken sirri saisunyi, na uku kamar yanda kuka sani bayan aure saikun dauka wata biyar atare kuma gida daya don marriage consent group suna yin zuwan bazata don ganin yanda zaman takewanku yake, na hudu dole saikunbi duk wani rules dana rubuta acikin paper dinnan kafin akaiga filing form din application na katin kasa, don ana daura aure za ah baku papers na application for her sbd shi& ta nuna amar, ..sbd shi aikinsa ya bashi katin kasa.
Tana kaiwa nan ta miqa masu papers din, kowa ya karba banda amar wanda zuciyar shi ke tururi, haka kawai, don shi wannan abin kamar kaskantar da kanshi yake.

Idan kun shirya komai na maganar auren sai kuyi fixing date, most preferably Friday, don kamar yanda na rubuta cikin list din dole saiya zamana kansu a hade yake, don za ayi masu tambayoyi sosai idan marriage consent group sunzo game da kansu, kamar ita za a tambaye ta akanshi, idan har tayi kuskuren rashin amsa koda kuwa abincin da yafi so ne to fa zai jawo matsala babba.
Matar na kaiwa nan tayi masu sallama akan idan sun yanke shawara saisu kirata don ta fara planning yanda zata hardada masu eveidence na cewa sun dade suna soyayya.
Kallon haifa hammam yayi sannan shima ya zaro wata paper daga aljihunshi sanna ya mika mata da pen yace   let her sign the contract  & miqa mata haifa tayi, ta dauka wajen minti biyar tana juya paper hankalinta baya kan rubutun ma, da kyar tayi signing hannunta na kakkarwa, tana gamawa ta miqa masu tayi excusing kanta zuwa restroom.
'?('***Auren Katin Kasa ***('
'?
(Unexpectedly fallingd'?
Story and written by:
QueenMarh=?x?

Paid book =???
65-66

Kallon haifa hammam yayi sannan yace, I can be his walyy because I m his only best friend, so about her I don t knw what to do, and its risky to hire someone,  & kallonshi haifa tayi sannan tace  habibi I have a solution to that, I ve told abuuh about everything so I m sure he will help us out insha ALLAH..jinjina kai yayi, suna nan zaune amar ya miqe abinshi ya wuce motor don yanxu kam sai yanda hammam yayi kawai, donshi bayajin zai iya yin wannan abu haka, baya son stress kwata kwata, bayan wannan ma yama za ayi ya hada kwanciyar aure da wannan qanqanuwar yarinyar salon ta raina shi, don kallon yar shekara 15 yake mata gaba dayanta.

Motor haifa suka shiga itada amra wadda zata fara sauke amra kafin ta wuce gida, tunda suka shiga cikin motor babu wanda yace qala tsakaninsu, ganin shurun yayi yawa yasa haifa cewa   babe, naga tunda su hammam suka zo shida general baki ce komi ba, nasan hankalinki ya tashi game da duk wannan yarjejeniya, but babe ya zamuyi, wannan ce kawai solution, idan kinga bazaki iya ba kuma sai mu hakura a nema wata mafitar  & dago kanta tayi ta kalli haifa sannan tace   haifa ni tsoronshi nake ji, kinajin dai yanda kowa ke fadin bashida kirki a office, ni tsoro nake ji.  & juyowa haifa tayi ta dan kalleta kafin ta maida idonta kan driving da take tace   indai akan wannan ne amra, inason ki kwantar da hankalinki, all abinda ya kamata kiyi focusing akai yanxu shine yanda zaki samu ki karba katin kasa don ki taimaki qannenki, duk wani abu da zai biyo baya ki manta shi for now, just focus kinji babe  & jinjina kai amra tayi sannan tadan kwantar da kanta jikin window motar.
?
Hammam na sauke amar baima tsaya yabi ta kanshi ba don yasan idan har ya mashi Magana yanxu bazasu kare da sauki ba hakan yasa ya kira house boy din amar ya bashi papers din yarjejeniyar don ya kai mashi yayi wucewan shi gida ranshi fess, shiko goga yana wucewa cikin penthouse dinshi baima bi takan dinner ba ya wuce sama don ya samu ya watsa ruwa, koda ya fito jellabiya yasa sannan ya tada sallah, ya dade sosai akan sallaya yana rokon Allah akan abubuwa da dama kafin ya miqe ya wuce closet ya chanza kayansa zuwa na bacci, white pjs riga da wando wanda ya haska fatanshi sosai ya saka wannan yabi lafiyar gadonshi yah hau ya kwanta ya jawo duvet dinshi.
?
Amra kuwa kwanan zaune tayi, hankalinta duk baya jikinta, yanxu wannan mai wuyan sha anin ne zata aura?, tashin hankalinta ma saida ta karanta wannan papers din da matar nan tace shi zasuyi don proving cewa auren soyayya sukayi don idan har auren wanda yake da katin kasa zakayi dole sai anyi dogon bincike sosai, hankali atashe take kallon papers din, abinda yafi tsaya mata shine, dole zasu zauna gida daya daki daya for months sannan dole yasan komai akan abubuwan da take so da wanda bata so, sannan dole saisunyi pretending suna son junansu sosai shida ita.
?
Washe gari yayi shirin shi cikin kaki ya fito, breakfast yayi wanda Pablo ya shirya mashi akan dining table, sai da yaci ya qoshi ya miqe don wucewa office, nan yasa Pablo ya fito mashi da briefcase da laptop dinshi, anatse yake tafiya har ya zo gaban g-wag dinshi da? m-5 yayi parking a compound din, zama yayi abaya sannan Pablo ya miko mashi papers hade da laptop da brief case din ya aje agefen shi,baima bi takan paper dinba sannan suka wuce headquater.

Suna isa cikin headquater ya wuce office dinshi m5 kuma ya biyoshi da briefcase dinshi da sauran abubuwan.
Lokacin da m5 ya shugo office din azaune ya ganshi ya dafe kanshi kamar wanda baida lafiya ganin haka yasa m5 cewa   sir are you okay?  ..jin haka yasa ya dago kamar bazaiyi magana ba chan kuma yace   I m okay, any update from the private investigator?  .. kallonshi m5 yayi sannan yace   yes, he s still on in  ..yana kaiwa nan yayi excusing kanshi ya fuce daga office din, anatse amar ya soma bude files dinshi, sanna ya jawo laptop dinshi, ganin papers tare da brief case dinshi ya sashi jawota ya fara karantawa, tunda ya fara karantawa ya jingina da kanshi yana wani tunani daga bisani kuma yayi tsaki ya aje paper din agefen, tunda ya ajeta bai bi ta kanta ba ya soma aikinshi atsanake, tuna abinda ya karanta ya sashi jawo landline din gefen shi yana tsaki, yayi dialing wasu code sannan yasa a speaker yace   come to my office  yana kaiwa nan ya kashe, ya jingine kanshi da chairs din da yake zaune ya lumshe idonshi kamar wanda kejin bacci,..yana nan zaune hammam ya bude kofan ya shugo, zama yayi yaa fuskance shi yace   whats the urgent call dude?  ..anatse ya soma bude idanunshi ya sauke shi akan hammam sannan yace   what s this?  ya nuna paper din, sannan ya cigaba   do you expect me to do all that is listed?, kana tunanin zanyi hakan ne just because ta samu katin kasa which kasan yin hakan is illegal  ..kallonshi hammam yake irin kallon kama raina min hankali, azafafe ya soma Magana   kai kaji matsalarka Kenan, kai kana tunanin idon tasan naka qudurin zata amince ne, let me tell you something da baka sani ba, abinda zakayi is the most selfish abu, na farko ciki zaka mata a shekarunta, sannan ta haife shi kai kuma ka amshe abinka, karaba uwa da danta, bayan wannan ma, rabuwa zakuyi after kowa ya samu abin da yakeso, baka tunanin wannan abun zai aje mata wani tabo da bazata taba gogewa ko mantawa ba eh?, to bari kaji amar, nayi niyar fada masu naka buqatar amma yanxu kuwa na cire hannuna, kaika fada masu da kanka, sannan idan kaga bazaka yi ba, let s not even waste our time, zamu iya cancelling yarjejeniyar fine,..yana kaiwa nan ya miqe azafafe ya fuce daga office din, amar kuwa harya fuce ya kasa rufe bakinshi don mamakin hamman, tsaki yayi kawai ya cigaba da aikinshi, sai wajen 5 ya bar office ya koma gida da tunani iri iri, at this point bashida wata mafuta, kuma gaskiyar hammam ne, yarjejeniya ce, tabashi abinda yake so shima ya taimaka mata ta samu abinda take so kowa yakama hanyarshi, da wannan tunanin ya kwanta.
?
AMRA kuwa ta cire komai daga ranta kamar yanda haifa tace, yanxu focus dinta shine kawai ta samu ayi auren ta karba katin kasa sannan a kunce auren.

Haifas res&
Haifa ce zaune kusa da abu, tana bare orange tana miqa mashi yana sha suna hirar uba da ya, saida ta tabbatar da ya bata attention din shi kafin ta soma Magana   Abu ka tuna kwanaki munyi Magana akan amra, to dama akwai wani da ke sonta kuma ya amince zai aureta, army officer ne, so yanxu kawun ta wanda ke ruqonta da siblings dinta yace bazai samu zuwa ba, so shine muke neman alfarma wajenka  ..kallonta abuh yayi sannan yayi murmushi yace   wani irin taimako Kenan haifa  ..kallonshi tayi fuskarta gwanin ban tausayi tace   abuh dan allah ka zama walyy na amra, bata da kowa wanda zai tsaya mata, daman shi uncle din nata ne to shima yace bazai iya zuwa ba  & kallonta sosai yayi sannan yayi shuru na yan mintuna yana nazari kafin ya soma Magana   if that s what you want I will gladly do that in sha Allah  ..murmushi tayi wanda ya fidda kyawawan hkoranta sannan tace  thank you abuuhhh ..

Dakinta ta koma sanna ta fara dialing number hamma, yana dagawa suka gaisa as usual ,sannan ta soma mashi bayanin yanda sukayi da abuh, shima yaji dadi sosai don komai yanxu yana zuwa masu da sauqi, sai next plan kuma suji amincewar both amar da amra.

Sunayin sallama tayi dialing number amra, lokacin tana kitchen tana dama oat, don wani irin yunwa ce ta tasota daga baccin data samu tayi bayan sallar asr, jin karar wayanta yasa ta wuce parlor ta dauka wayan daga kan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login