Showing 222001 words to 225000 words out of 381117 words

Chapter 75 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

1991

feeling? Ya tambayeta daga nan tsaye ya kame
 Alhamdulillah da sauqi ta bashi amsa
Sake tambayarta yayi fuskanshi na nan yanda take a kame  meke damunki?
Saurin sauke kanta kasa tayi tana jin yanda kirjinta ke yin lugude, pat pat, Bakinta na karkarwa ta soma magana  ciwon kai da zazzabi
Juyawa yayi ya nufi hanyar fuce  get ready muje asibiti
Cikin sauri ta katse shi tunawa da maganar ammah  noo basai naje asibiti ba, ammah ta bani magani I m okay now
Ba tare da ya damu ba yace  okay
Yana kaiwa nan ya fuce daga dakin, saurin dafe kirjinta tayi ta zauna saboda wani jiri jiri daya soma dibanta, saida ta dauka kusan minti ashirin a zaune saiga salima ta shugo da tray a hannu da ammah ta aikota dashi don tasan amra ba lallai ta sauko ba saboda yanayin jikinta, plates da bowl biyu ne akan tray din daya pepper soup din gizzard da liver ne a ciki sai kuma fruits da ammah tasa salima ta yanka mata,
Da sallama salima ta shigo  oh yau ashe za ayi ruwan sama da kankara kin Tashi da wuri adda Wai, nikam adda Anya wannna barcin naki na lafiya ne kuwa? Kodai zamuje asibiti
Banza amra tayi mata don ba surutun ta ne agabanta ba yanxu, confusion din dake kanta ma ya isheta don gaba daya ta kasa gane yanda akayi ciki ya zauna a jikinta bayan doctor yace babu shi.
Ajiye tray din salima tayi a gefenta tace  gashi ammah tace na kawo maki, wannan special treatment dun da ammah ke baki yana bani mamaki ta karashe tana kama habar Bakinta, dafe kai amra tayi ba tare da ta kalleta ba tace  dan Allah salima kije kawai, ni ciwon kai surutunki ke sani Wallahi, Ki tafi da wannan abun ma banason cin fruit kawai zaki barmin ta karashe tana nuna mata plate din gizzard. Da mamaki salima ke kallonta, kafin ta tabe baki  uhm Toh shikenan,
Daukan plate din salima tayi ta bar mata bowl din fruit ta fuce daga dakin tana mamakin yanda gaba daya amra ta sauya kamar ba ita ba.
Salima na futa ta janyo plate din fruit ta fara ci tana tunani harta cinye tass ba tare da saninta ba, gaba daya jin tayi tana son karasa don haka ta zari hijab dinta ta sauko kasan, yau kusan sati kenan rabonta da saukowa kasan kullum tana kunshe a daki, anatse take tafiya harta shugo kitchen din, ammah ce sai salima a tsaye suna Dora lunch, da mamaki duka suka juyo suka kalleta, ammah ce Tayi saurin cewa  shugo daughter ya kika tsaya
Karasowa amra tayi kanta a kasa  ammah ke da kan a kitchen?
 Ay naji sauqi sosai daughter, dole na sauko Kar ayki yayi ma anty salima yawa dariya ammah tayi tana kallon salima, amra ma dan murmusawa tayi don ta gane dalilin kiranta da anty da tayi, kallon bowl din hannunta ammah tayi Ganin ta shanye tace  Masha Allah, kina buqatan wani abun? Ko a sake yanka maki wani fruit din
Girgiza mata kai amra tayi tace  Zan yanka
 Ah ah bazaki yanka ba, kije ki kwanta ki huta, salima zata kawo maki yanxu
Kallonsu kawai salima keyi tana kallon ikon Allah, tabe baki tayi ashagwabe tace  ni gaskia ammah wannan nuna kulawa da kikeyi ma adda yayi yawa Wallahi ni kwata kwata ba a yimin haka
Dariya ammah tayi ta wuce gaban fridge ta zaro bunch of different fruits ta ajiye akan island  haba mutuniyar, bakiga addan taki bata jin dadi bane?
Karban wukan da ammah ta dauko salima tayi tace  Bari na yanka bana son kina son wahala, Amma dai gaskia ammah nima adunga kula dani haka I m jealous
Rankwashi amra takai mata tare da hararta, da sauri ta kauce tana mata gwalo, dariya ammah ta dunga yi masu kafin ta tsagaita  oh Allah kuma kuna yin yar saqo da saquwa kenan, yanxu dai daughter ki wuce sama karki biye mata ta wahalar dake

Sunkuyar dakai amra tayi cikin jin kunya tace  Toh ammah kafin ta juya ta nufi hanyar futa daga kitchen din, kallonta ammah tayi harta fuce daga kitchen din kafin wani tunani yazo mata,  daughter!! Daughter!!! Zo
Salima ce ta ajiye wuqar ta nufi hanyar futa kitchen ta tsaya daga bakin kofar tace  addaaa kizo ammah na kira tana kaiwa nan ta juya cikin kitchen din ta cigaba da yankan fruits.

jiki a mace amra ta juyo don Har takai stairs, dan saukowan nan datayi da tsayuwar datayi gaba daya taji ta fara galabaicewa jikinta ya fara mutuwa, daman tana jin haka sai barci gaba daya tama manta da maganar ciki da ammah tayi mata akan shike sata barcin don yabi jikinta,
Da sallama ta sake shugowa kitchen din, ammah na ganinta ta soma magana anatse  sorry dear Har kin gaji ko? Ungo wannnan ki kaima Muhammad, na manta tun dazu ya buqaci akai mashi
 Ah ah ban gajiba bari nakai mashi amra ta amsata tana Karban mug din da ammah ke miqa mata tayi da yake turiri sosai kafin ta juya ta fuce daga Kitchen din, harta fuce ammah na kallonta tana karantar yanayin ta sosai saboda bayanin da zatayi ma doctor insunje asibiti akan yanayi ta, kana ganinta kasan she s so excited, fara ar fuskarta taqi yankewa kwata kwata, babu abunda take sai godiya ga Allah da kuma fatan abunda take tunani ya tabbata insunje asibiti dukda ta tabbatar da hakan a nata hasashen.
Anatse take tafiya harta shugo part dinshi, kamshin parlor ne ya bugeta don parlor ya dau sanyi sasai wanda taji lokaci guda cikinta ya hautsina, saurin toshe hancinta tayi ta wuce bedroom dinshi cikin sassarfa, tana bude kofar ta shige ta sauke wata nauyayyan ajiyar zuciya saboda kamshinsa daya bugeta wanda ya sata jin cikinta ya lafa, Har wani dadi taji ya ziyarceta aranta, tana bala I son kamshin musamman a yanxu.
Bin dakin nashi tayi da kallo, it s been long ta inda ta tako da kafarta ta shugo tun bayan last day din da suka dawo tare daga asibiti bayan yayi mata korar kare Inda tayi alqawarin bazata sake takowa ba tazo Inda yake harya daukota ya kawo ta, babu abunda ya sauya adakin, it s still so clean kamar yanda yake, ko ina fess fess gwanin ban shaawa, baya cikin dakin ta tako gefen bedside ta ajiye mashi mug din, saukan ruwa ta ji a kunnenta nan ta gane yana cikin toilet kenan m, har zata fuce daga dakin ta dawo bakin gado ta zauna tana jiran fitowa shi dinta bashi sakon ammah, tana nan zaune Har kusan minti goma bai fito ba, ga wani irin barci dake fusgarta sosai, zungudawa tayi kadan tayi kwanciyarta nan take barci ya kwasheta anan kan gadonshi,ba tare da sanin ta ba.

After like 10mins da kwanciyarta ya bude kofar bathroom, ya futo anatse kamar basarake, wani irin kamshi ne ke fita daga jikinshi mai kamshi dadi sosai at the same time ga tururin ruwan zafin da yayi wanka dashi, towel ne kawai a kugunshi, sai dan hand towel daya rike a hannunshi yana goge qirjinshi daya mummurde sosai, kwata kwata bai Lura da ita ba ya wuce gaban dresser ya fara Yan shafe shafen shi cikin class kamar wani mace, shafa chan goga chan, saidaya gama kafin ya nufi gadonshi don yana son yadan kwanta kona 2 hours ne don baiyi barcin safe ba tun bayan sallar asuba daya dawo daga masjid ya wuce gym.

Gaban switch na dakin ya wuce ya kashe ya rage bedside lamb kawai, dakin yayi duhu sosai don da hadari aka Tashi a garin daman abuja badai ruwan sama ba kullum cikin hadari ake ko ruwa haka garin zai hade sosai.
Juyowa yayi ya tako bakin gadon idanunshi a lumshe yana hamma.

Chak ya tsaya don saura kiris ya afka kan gadon saboda baiyi expecting dinta ba, don Yama manta when last ta shugo dakinshi da kafafunta, da fuskanta ya fara cin karo, da mamaki yake kallon yanda take barci hankali kwance, samun kanshi yayi da kallon fuskanta, Har lokacin he s surprised, ta kwanta ta tattare hijab dinta sama don harya harde mata wuyanta, kana Ganin ta kasan kwanciyar baiyi mata dadi ba but she s sleeping peacefully kamar wadda tasha wani abu, shuru ya danyi yana mamakin wannan wani irin barci ne haka? Bai kawo komai aranshi ba don haka ya dan harde hannayenshi a kirjinshi ya soma magana  Aisha!!! Aisha!! 
Tsit kake ji kamar da kanshi yake magana, sai fidda nunfashi takeyi akai akai kamar wadda aka shake, ganin nunfashinta na sama sama still tana barci yasa ya matso inda take kwance, Bakinta ta soma bude tana blabbering, Har lokacin barci na idanunta don ta rufe idanun gam, wajen wuyanta ta kama jiki a mace ta fara Jan hijab din  wayyo mamii.. wu..ya..na
Ahankali take furtawa don kwata kwata bai ji abunda take cewa ba saidai bin Bakinta yayi da kallo harya gane abunda yake cewa, cikin hanzari ya karaso bakin gadon ya sake kiranta  Aisha aisha!! Inaaa, bata jin shi, barcin ta kawai take tana surutai, Ganin tana kokari janye hijab din daga wuyanta ya gane damunta yake don haka ya zura hannunshi cikin hijab din da hannu daya Dayan kuma ya tallabo kanta gaba daya ya janye hijab din daga jikinta, yana cire wa ya sauke mata kanta ahanakli kan gado ya zame hijab din kasa, wani irin nunfashi ta sauke alamun samun relieve kafin ta gyara kwanciyarta tayi rub da ciki, dan yatsine baki tayi ta juya gefe saboda ta takura cikinta, Duk wannan juye juyen da takeyi akan idanunshi, gaba daya mamakin yanayin ta ya gama dabaibayeshi, wannan barcin baba lafiya bane ya fada aranshi, karshe dai tabe baki yayi ya maida idanunshi kan fuskanta, wani siririn hawaye ne ke sauko a fuskanta kamar tana mafarki, lokaci guda kuma yaji yana tausayin ta babu dalili, tana kashe mashi zuciya sosai ba tare da saninshi ba, yanxu ya gama yarda ya bata special gurbi a zuciyarshi, tayi mashi abunda bazai manta da ita ba, yanda ta nuna jajirce wajen ceto mahaifiyarshi bazai taba mantawa da wannan ba, saidai Har yanxu he s struggling akan karbanta a matsayin matar shi,he just feel like idan ya amince kamar ya cuceta ne, ko kuma he s being selfish saboda baya haihuwa,cause she s so young, tana da rayuwa anan gaba, idan ta zauna dashi a haka she will miserable ba kowa ne zai iya zaman auren da babu haihuwa ba,dalilin da yasa yaqi amincewa kenan da auren shiyasa tun farko da ya tabbatar babu cikinshi a jikinsa yaso ya saketa taje tayi aurenta tunda ita bata da matsalar komai.
Saurin dafe kanshi yayi yana tausaya mata haka kawai, yayi kokarin ya nunama ammmah manufarshi na qin karban auren ta amma ta kasa gane wa, saurin dafe kanshi yayi yana jin wani irin, dago da kanshi yayi da jajayen idanunshi ya kalleta kamar wani mai jin tsoro haka ya miqa hannayenshi ya fara gyara mata kwanciyanta zuwa jikinshi, ahankali yake matso da ita kamar kwai don baya son ta Tashi kafin ya janyo masu duvet ya rufa masu, tana jin kamshinsa na shiga hancinta cikin barci kuwa ta damkoshi sosai  uhm ina& .shon..wannan.. ta furta tana turo dan bakinta ahankali kamar mai rada cikin barcinta.
Akan idanunshi tayi haka wanda yasashi Saurin runtse idanunshi yanajin yanayin shi na sauyawa, gaba daya komai ya tsaya mashi chak, baiyi wata wata ba yakai bakinshi kan nata ya dan bata slow peck kafin ya zare bakin shi  mai bakin rashin kunya ya karashe yana sauke wani lausasan murmushi wanda ya Kara ma fuskanshi mahaukacin kyau sosai kamar bashi ba, lumshe idanunshi yayi har barci ya sauke shi mai dadi sosai.

Salima na gama yankan fruit ta wuce sama don takai mata, tana hawa sama taga wayam, bakin toilet dinta ta tsaya tace  adda??? Kina toilet ne? Ga fruits din
Jin shuru yasa ta cewa  adda! Still babu response, da sauri ta Bude kofar nan ma wayam, haka nan ta juya ta sauko kasa ta wuce kitchen, ammah dake sauke tukunya tana ganin ta shugo hannunta dauke da bowl din fruit din data futa dashi tace  ah ah ya kika dawo dashi ko bata so ne?
 Ammah naje ban ganta ba, na duba ko ina
Dan shuru ammah tayi kafin ta dan murmusa tace  ajiye mata a fridge zata sha anjima
Gaban fridge salima ta bude ta saka bowl din don itama sai a lokacin ta tuna taje wajen ya Muhammad, dariyar keta ta danyi kafun ta dan basar saboda ammah na wajen.

Suna cikin shirya abuncin warmer Aman ya shugo kitchen din yana hamma, da sallama ya karaso ya gaishe da ammah kafun yace  ammah!!! meysa kika shugo kitchen ya kamata ace kina hutawa ne saboda baki gama recovering ba
Murmusa ammah tayi ta kalleshi cikin kulawa tace  son na samu sauki fah, kuna shagaltani da yawa shiyasa naqi biye muku kaida son, Ay gwara na fito saboda na dunga exercising jikina, bayan wannan ma my baby tana buqatar helping hand tunda ku bakwa taimaka mata
Ta karashe tana kallon salima dake smiling kamar mimi kafin ta kalleshi ta watsa amshi harara, shima hararar ta yayi, ammah na kallonsu tana murmushin jin dadi sosai,  wannan mara kunyan babu wanda zai taimaka mata
Ya fada yana kallon salima yana zabga mata harara
Turo baki salima tayi ta rike kugu ta kalleshi  niba Mara kunya bace yaushe nayi maka rashin kunya ?
 Bani kika yima ba, baby na kikayima wani irin maqoqon baqin ciki ne ya turnike ta Har batasan lokacin datace  ah ba baby ba Ka manta feeder ce
Kallonsu ammah tayi kamar tohm and jerry yanda suke ma junansu,  nidai aurar daku zanyi na huta inkunje chan saiku karata ba a gida ba
Tabe baki Aman yayi ya bude fridge ya dauko ruwa yana shirin balle karfin yace  chapp ammah dawa zaki hadani? Wannan ? Badai niba ni inada wadda Zan aura
A harzuke salima ta kalleshi da idanunta da suka kawo ruwa tace  nima inada wanda nake so,
 Toh ya isa haka nan, kowa Zan bashi wanda yakeso tunda bakwa son juna,
Ammah ta fada fuskanta na nuni da she s serious, kallonta Aman yayi kafin ya dan sauke murya yace  nifa ba Yanxu zanyi auren bafa ammah
 Meysa ba yanzu ba ga dan uwana nan da matanshi, kaima aurar dakai zanyi very soon acikin shekarar nan ka fadama babyn taka anytime za a turo
Dan jim yayi kafin ya dan dago idanunshi nan take ammah ta kashe mashi ido daya,nan ya hasko abunda take shirin yi, dan murmusawa yayi ya soma magana trying to go along,  Toh shikenan ammah Zan mata magana, sai aje ayi tambaya ma kawai ya karashe ba tare da ya kalli inda salima ke tsaye ba,
Salima dai kafafunta gagarar daukanta sukayi don haka Tayi saurin fucewa tana hawayen takaici.

Tana futa amma ta kalleshi,  son!! Kaifa yanxu ba yaro bane, basai an fada maka yanda yarinyar kirki ke sonka ba, man up and stop all this childish act Ka daina wahalar min da yarinya, seat her down and talk to her in a cool manner, okay?? 
Kanshi a kasa ya amsata  Insha Allah ammah na
 Masha Allah, Allah yyi maku albarka baki daya
 Ameen ya yi saurin amsata kafun ya taimaka mata suka fito da warmers zuwa dining.

Salima na hawa sama tasha kukanta tana dana sanin shegen Jan aji data dunga yi mashi gashi yanxu ya kubce mata, son da take mashi bata jin yayi mata irin shi,  Wallahi yaya bazaka auri kowa ba saini ta fada tana hawayen takaici.

Bangaren su amra Basu farka ba sai wajen karfe uku na rana, shine ya fara bude idanunshi ya sauke su akanta, gaba daya ta nannadoshi kamar mage ta kudundune shi, saida ya dauka kusan minti biyar yana kallonta, kumatunta daya kara zama fluffy yajaa kadan kafun ya kauda kanshi ya soma kokarin zame jikin shi daga nata ahankali.
Kokarin riko towel dinshi yayi saidai yanda ta kwanta a jikinshi dole saidai ya bar towel din, haka kuwa yayi ya akai towel sun don baya son tashin ta,juyawa yayi ya dan tsaya yayi miqa jikinshi na murdewa sosai, ahankali ya soma tafiya majestically, daidai nan ta bude idanunta da sukayi luhu luhu karaf ta sauke su akan naked bodynshi daga bayanshi zuwa ga ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????structure dinshi, da sauri ta runtse idanunta don batayi expecting Ganin haka ba daga tashinta daga barci, kamar munafuka haka ta soma bude idanunta akaro na biyu ta sauke akanshi lokacin har yakai wajen kofar bathroom zai shige, kasa sauke idanunta tayi daga kallon jikinshi, he s so hot, skin dinshi fari tass babu tabo, ga kirarshi so sexy, saida ya shige bathroom ya dawo hayyacinta ta sauke ijiyar zuciya kafin Tayi saurin mikewa ta gyara towel dinta dake neman zamewa ta janyo hijab dinta ta zura shi ta fuce daga dakin cikin sassarfa don wata irin yunwa ce ta tashe ta daga barcin.
Cikin sassarfa ta hau sama don bata son amah ta ganta, saida ta shiga cikin daki ta sauke nauyayyiyar ajiyar zuciya tana haki kamar wadda za a kama, toilet ta wuce direct ta dauro alwala don an kira sallar la asar.

Bangaren salima saida ta shaqi kukanta son ranta kafin tayi wanka, tana futowa agurguje ta sauya kaya tayi sallah ta fito kasan jiki a mace, idanunta sun kumbura sosai alamun kukan datayi sosai,
Kasa ta sauko ahankali tana tafiya tunaninta ya gushe harta shiga kitchen , ganin ko ina tsaf yasa taji wani iri don tama manta aiki sukeyi ita da amah ta gudu sama saboda takaicin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login