Showing 87001 words to 90000 words out of 381117 words

Chapter 30 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

1982

ba auren gaske bane wannan, auren yarjejeniya ne fa, how can I just give him my body bayan nasan ina samun abunda nake buqata shima ya samu abunda yake buqata shikenan kowa zaiyi hanyanshi and beside kinga na kusa gama housemanship dina 
  hmmm babe kedai kawai abar maganar 
Dariya haifa tayi kafin ta cigaba   talking of yarjejeniya, shi ya fada maki me yake buqata ne? 
Shuru amra tayi don all this time bata taba tambayanshi mey yake buqata ba daga wajenta da har ya amince ya aureta, gyara zaman wayanta tayi a kunnenta kafin tace   ban tambayeshi ba, and baice komai ba,but babe me kike tunanin zai buqata daga wajena sbd im very sure ba haka kawai ya amince ya aureni ba don na samu citizenship ta karkashinsa 
  babe time is not on our side, ina ganin ki tambayeshi kiji mey yake buqata daga wajenki kinga yanxu yanda kuka fara zama topic of discussion a cikin headquarters saidai ina tsoron kinsan yanda zance zaita yawo 
  haif nibazan tambayeshi ba tunda baice komi ba, 
Basu wani dade da hiran nasu ba ta sukayi sallama.
Tana aje wayan ta lumshe idanunta tana tunani kalaman haifa, tunanishi ne ya fado mata da moment dinsu tare, tabe baki tayi kafin tace   ina tausayin matarda zatayi rayuwa da wannan mutumin da baka gane mashi 
Shanye tunanin tayi har bacci ya kwasheta, bata wani dade da baccin ba wayanta ya soma ruri, da sauri ta janyo wayan don baccin nata baiyi nisa sosai,tayi picking, cikin muryan bacci tace   allo  tare da sauke nunfashinda ya sashi runtse idanunshi sosai don ya jishi ne har cikin tsakiyan kanshi
Shuru taji daga chan bangare saida ta sake maimatawa kafin ya sauke ijjiyan zuciya da nunfashi a tare wanda ta jishi har kwakwalwarta, bude idanunta tayi sosai ta zare wayan daga kunnenta ganin unknown number yasa ta maida wayan kunnenta ta sake tambaya   hellowww 
Jin anyi shuru ya sata tsaki don bata kaunar abunda zai katse mata baccin ta, bata kaiga kashe wayanba yace   did you just hiss  
Gabanta ne ya fadi don bata taba tsammanin kira daga wajenshi ba kwata kwata, mikewa tayi zaune kamar yana gabanta ta sauke kanta kasa tace   ?m so sorry bansan kaine ba 
Shuru yayi chan kasan maqoshi yace   baki iya& . 
Bai karasa ba ta tari nunfashinsa   ina wuni ya aiki 
murmushi yayi sosai don yanda ta fada saiya bashi dariya, guntse dariyan yayi yace   is everything okay over there, do you need anything 
bata gama mamakin daya bata ba da tambayoyinshi ya sake jefo mata wata   is there anything suspicious around you 
?
tsintar kanta tayi da murmushin da bata san dalilinshi ba tace   alhamdullilah, everthing is okay 
jin shurun yayi yawa yasa itama tace   hows your health? 
baiyi tsammanin tambayn nata ba saidai kuma yaji dadin tambayar   alhamdullah  ya amsa mata ataqaice kafin ya kashe wayan, jin alamun ending call din da yayi ya sata tabe baki tace   ikon allah 
aje wayan tayi gefenta ta cigaba da baccinta.
?
Kwanan su amar goma cip wajen training ya samu kiran gaggawa daga highest attained rank na army gaba daya, cikin kwanaki goman nan abubuwa da dama sun faru ciki kuwa harda wanda yayi preparing kanshi, ranar da zai dawo ya riski abubuwan da suka bashi mamaki sosai don baiyi tunanin hakan ba, ciki kuwa shine ya gano da hannun hammam dumu dumu cikin waenda keson rufe zancen suspect din da aka kama, yanda ya gano hakan kuwa shine, tun bayan tafiyarsa training hankali alif shuraim wato baban hammam ya tashi wanda yasa hammam amfani da duk karfin da yake dashi a cikin headquters don ya toshe maganar saidai abun ya faskara sosai, daman already an karbo shi susupect din daga hannun officials din da suka kamashi, lokacin da zancen yazo kunnen alif cewa yaron yana hannun army hankalinshi ya tashi sosai sanin waye general a yanxu da sun kasa samun abunda zasuyi using don suyi amfani dashi yanda suka saba akan sauran da suka karbi mukamin har sukayi retire ko suka bar aikin gaba daya,ganin basuda wani option dole sukayi amfani da abubuwan da suke dashi don ganin sun ci nasara akanshi, abunda yafi bama amar mamaki shine yanda kiri kiri babu wani kwana kwana amininshi wato abokinsa ya futo ya nuna asalin shi waye, a day before ranar da za ayi mashi kiran gaggawan kiran hammam ya shugo wayanshi, baiyi expecting call dinshi a wannan lokacin ba.?
Gaysawa sukayi kamar yanda suka saba kafin ya soma Magana   dude, weve been friends for over 8years now, and don t be surprised with what I will be asking you now, inason ka cire hannunka daga research din da kake nasan ka gane me nake nufi 
Murmushi amar yayi don baiyi mamakin hakan ba kwata kwata,
  dude why, why are you doing this, koka manta abubuwan da kake kowa zaiyi considering din wannan as betraying army gaba daya why 
Dariyan yaqe hammam yayi yace   oh so ka san komai Kenan, then why did you pretend 
  yes na gane komai tun ba yanxu ba tun last general da kukayi threating ta hanyar using wani wrong doing dayayi achan baya, 
  So why did you pretend  hammam yayi saurin tabayan shi
  saboda na baka wani chance da benefit of doubt hammam why? Tell me why are you doing this tun chan baya kaike protecting dinsu kaida mutanenka, ka zama mai liken asiri, shin kayi tunanin outcome din hakan idan har gaskiyan cewa daga cikin the most secretive and hardworking officer kamar kai, mai kake tunani za ayi tunani idan aka gano cewa daga cikin masu kokarin protecting kasar gaba daya cikinsu akwai corrupted ones , im so disappointed dude   ,
Idanunun amar ne sukayi jaaa, yanda yake magana zaka gane hes hurt sosai,
  waye ke saka ka hammam, who are the empires, dude you need to wake up before its too late, this people are dangerous, they kill, they manipulate, they detroy a lot of family, shin kasan irin mutane nawa muke rawasa duk a shekara ta dalilinsu ta hanyar trafficking yara da kwayar da suke producing, kana da damar kawo karshen su, 
?
  I didn t call you to listen to all of that, just do as I say, stop the investigation if you don t you ll regret it  hammam ya fada ba tareda ya wani damu da abunda amar ke fadaba
?
Nunfasawa amar yayi kafin yace   do your worst  yana kaiwa nan ya kashe wayan, zuciyanshi zafi take mshi sosai, bai taba tunanin idan har yayi confronting hammam abunzai mashi zafi haka ba, ko lokacin daya gano komai game da sa hannun hammam wajen rufe duk wani hanyar samun evidence na kama kungiyar ba saidai yasan cewa akwai mastermind behind hammam din shima yana kyauta zaton manipulating dinshi akeyi wanda dalilin hakan yasa baita ba nuna mashi ya san komai ba don tun lokacin da yaje wani secret operation tare da m5 don kamo su ya gano cewa da hannun hammam.
?
Washe gari kuwa sakon gaggawa ya iso mashi wanda ya katse masu training din da ya kamata su gama cikin kwana hudu, koda helicopter ya iso daukan gaba daya freshers hardashi yayi mamakin ganin yanda security dinshi ya karu sosai, saiya zamana kamar criminal akazo dauka, bai kawo komai a ranshi ba don yasa ko baibada umarni ba dole yana da nashi security din, suna isa headquarters kuwa ya wuce direct inda ake emergency meeting security dinshi biye dashi a baya, tunda aka bude kofan shiga ya shige ba tare a wani tunani bay a zaune a kujeran dake tsakiyan wajen, daman yayi expecting hakan, saida ya sara masu don manyanshi ne sosai kafin ya zauna.
Wani solder ne ya matso ya aje mashi wasu papers a gabanshi kafin ya koma ya tsaya kyam,
  General Muhammad Taura 
  yes sir  yayi saurin amsawa
  mun samu labarin kana da sa hannu cikin illegal auren da kasan government din uae sun haramta hakan, wanda we believe kasan cewa hakan is not accepted a nan kasar, wannan gaskiya ne 
Kallon papers din gabanshi yayi ya som karantawa tsaf kafin ya dago yace   yes sir 
?
Daga daga cikin manyan ne su uku yace   did you know the consequences of that 
  yes sir  ya amsa babu tsror babu fargaba
  did you know that this will affect your job with no plead 
  yes sir ya sake amsawa
?
  did you know that this will ban you and your citizenship of the uae 
  yes sir ya kuma amsawa
Shuru wajen ya dauka kafin su cigaba
  we hearby declare you under suspension of favourable personnel action, youll be under our supervision for more investigation 
?
Mikewa duk sukayi kafin ya sara masu suka fuce, kanshi ne ya soma sara mashi don baiyi tunanin abunzai kaiga haka ba idanunshi kuwa sunyi jaa sosai, sanin abunda suke nufi ya sashi wucewa securities din biye dashi har wajen da floor din da ake investigation daki ne babba wanda shi kadai ne a floor din an zagaye dakin da sound proof glass, saida aka amshi riganshi dake da rank dinsa a jiki ya zamana daga inner white riganshi sai dogon wandon army nashi hatta wayoyin duk sun amshe, zama yayi kan kujeran dake dauke da table din kafin ya dafe kanshi dake sara mashi, bayason tunanin komai hakan yasa ya dafe kanshi don samun sauqin ciwon kan dake damunshi sosai.
M5 ne ya shigo dakin tare da sara ma ogan nashi, dago rinannun idanunshi yayi ya kalli m5 kafin ya gayar zamashi ya fuskanceshi   have you done it 
Da sauri m5 yace   yes sir everthing is ready, and im sure she has arrived by now 
Resting bayanshi yayi kafin ya cigaba   in 2 days I will ban from the uae government, just as we planned, I have prep all the evidence through secretive portal,nayi linking dinka to the portal, don t take any action until you receive my alarm 
Kamewa m5 yayi kafin yace   yes sir  ya sara mashi ya fuce.
?
Tun baya fitar m5 babu abunda ke mikar dashi sai sallah da zuwa toilet a cikin dakin, koda aka kawo mashi abunci baima bi takan abuncin ba.
?
Bari mu leka amra&
Tun bayan tashin datayi da asuba ta tashi da fargaba, jikinta gaba daya yayi weak tana jin alamun kamar wani mummunan abu zai faru, wanka tayi hade da sallah kafin ta zauna nan kan sallaya hawaye na zubo mata don idan taji irin wannan halin tana alaqanta shi da qila wani mummunan abu ne ya faru da kannenta, wunin ranar tayi shi ne cikin sanyin jiki hade da ciwon kai mai tsanani karfe bakwai na dare taji karar door bell, mamaki ne ya kamata sosai hade da tsoron daya dirar mata babu zato ba tsammani, miqewa tayi sanye da hijab dinta har kasa ta wuce parlor, jin an sake danna door bell din ya sata saurin budewa, ganin m5 yasata mamakin zuwanshi a daidai wannan lokacin, babu wani bata lokaci ya gaisheta kafin ya mata bayani tafiyanta   maam, you will have to leave the country now 
Hankalinta ne ya sake tashi dan ta kasa gane me yake nufi dakewa tayi kafin tace   may I know why 
  in 24hour you ll be arrested for trying to get uae citizenship 
Hankali a tashe ta kalleshi tace   whatt, please explain to me the way I can understand kamin bayani yanda zan gane?, 
?
  we don t have time now, ma am, your flight is in 30 minutes, 
Juyawa tayi hankali a tashe ta koma dakin, hawayene ya soma gangaro mata a fuskanta wanda ta kasa gane dalili, meke shirin faruwa Kenan, bude closet tayi ta dauka bakin abaya ta saka kafin ta janyo karamin box dinta tayi ta zuba few kayanta a ciki kafin ta janyo laptop dinta da wayanta, fitowa tayi yanda tabarshi anan ta sameshi tsaye bakin kofar, karban box din nata yayi kafin ya rufe kofa tabi bayanshi, cikin motar yasa mata box dinta kafin ya bude mata ta shiga shima ya shiga suka wuce, abubuwa ne da dama ke yawo a kanta ciki kuwa harda general da makamin karatunta, kukane ya kufce mata mara dalili, wannan wace irin kaddara ce, ta kasa gane inda aka samu matsala, general ne ya fado mata rai yanxu shi wani hali zai shiga kenan, inhar ita kamata za ayi shi kuma aikinsa fa shida yake babban mutun a kasar kuka ne ya kufce mata hankali tashe ta kalli m5 tace   uhm please whats going to happen to him, dan allah ka fada min meke faruwa 
Cikin airport din yayi parking kafin ya zaro mata wasu takaddu ya bata hade da passport dinta ganin yanda take kuka ya sashi cewa   karki damu, he will be fine,ga passport dinky, ive made an arrangement, akwai motar dazai daukeki idan kun isa, sir will join you soon 
Innalillahi ta soma furtawa, dakyar m5 ya tausasa ta ya mata sauran abubuwan daya dace ya mata sallama ya tafi.
Samun waje tayi a airport din, nan komai ya dawo mata kamar mafarki, tundaga lokacin data iso kasar, allah kadai yasan irin farin cikin da take ciki sai gashi yanxu kuma zata koma kamar mafarki take ganin komai, yanxu ya makomar karatun nata Kenan, me zata cema daddy idan ta koma, mai zata tarar idan taje chan, runtse idanunwata tayi hawaye na kwaranyo mata, gaba daya baifi mata wata uku ta gama housemanship din shima sbd extention data nema ne anan asubiti na haousemanship da takeyi na additional 3 months don ta don samu ta tara kudin da zata biya daddy bayan wannan ma gashi kuma yanxu komai ya juya, cikin yan mintuna akayi announcing jirginsu, mikewa tayi hawaye sharr a fuskanta harta wuce harabar jirgin, koda suka tashi tunani iri iri ne a ranta, yanxu makomar karatunta ma bashine damuwanta ba, sir general ne damuwanta, wani hali ta jefa shi, da career shi, idan har ita arresting dinta za ayi shi kuma fah, a wani hali yake ciki, koma wani hali yake ciki ita ta jefa shi tunda itace ta nemi taimakonshi daya ya aureta dukda sunsan illegal ne a kasar, idanunta ne sukayi jaa sosai, anya ta kyauta kuwa, tanajin kamar tayi butulci, tambayoyi ne burjik a kanta wanda ta rasa wanda zai amsa mata su, na farko ya akayi m5 yasan za ayi arresting dinta, ya akayi asirinsu ya tonu, sannan a wani hali yake ciki yanxu ganin babu mai bata amsosahin ta yasata fashewa da matsanancin kuka sosai har baccin wahala ya dauketa.
Sama sama ta dunga jin Magana akanta, bude rinannun idanuwanta tayi da sukayi jaa sosai kafin saukesu akan crew din dake tashinta,   ma, weve arrived 
Juyawa tayi ganin bbu kowa cikin flight din har garin ya waye yasata mikewa ta janyo karamin box dinta hade da laptop bag dinta da wayanta, takowa tayi ahankali tare da shaker kamshin kasar najeria, nan take komai ya sake dawo mata, runtse idanunta tayi kafin ta soma takawa gabanta na mugun bugu sosai harta futa daga harabar jirgin,saida ta tsaya ta gama clearing komai don daman daga dubai to Abuja ne booking din da m5 yyi mata,duban wayanta tayi da charge ya sauka kasa, rasa abunyi tayi don babu kudi kwata kwata a jikinta gashi booking daya ne daga dubai to Abuja, gashi bata taba zuwa Abuja ba balle tasan inda zatabi taje car park, futowa tayi daga cikin airport din inda taxis da motoci suke dagowa tayi nan idanunta suka sauka kan wani mutumi daya daga katon board da sunanta a jiki, tunawa da abunda m5 ya fada mata na cewa yayi making arrangement dinda zai kaita gida yasa tayi handala ta daga hannunta da sauri mutumin ya karaso gabanta tare da welcoming dinta, karban box dinta yayi kafin tabi bayanshi, idanunta a kasa yace   bismillah hajiya 
?
Dagowa tayi ganin zabgegeiyar motar dake gabanta, ba tareda wani tunani ba ta shiga baya yaja motar suka wuce.106-107
Unedited pageL'
Update& ..
Tun akan hanya driver ya isheta da surutun da ba gane kan zancen nashi take ba iyakacin ta uhm sai kuma murmushi, sam hankalinta baya jikinta karhse ma dai lumshe Idanunta tayi don wani irin ciwon kaine ke damunta sosai, tunda suka karyo kwanan layin ta bude idanuwanta, fadin tsaruwan anguwan ma bata lokaci ne don daga gani kasan anguwar manya ce bata kananu ba,ko ina fess fess babu hayaniya sai kamshi ciyayu da sukayi tsayi, idanunta ta soma rarrabawa har suka karaso wani hadadden estates mai suna LARICS ESTATE qasan kuma aka rubuta TAURA COM, jerin securities dake wajen ma abun kallo ne, bayan fargabar da take ciki saida tsoro ya durar mata ganin yanda wajen yake da tight security, babu bata lokaci driver ya fidda wani kati da alamu na company ne kafin suka bude gate din, yana kutsa kai kuwa komai ya dauke mata lokaci guda, ita data dawo daga kasar waje saita zama yar kallo, gidaje ne da aqalla bazai wuce guda goma ba don estate din bashida wani girma, idanunta ta sauke kan gidan da yake tunkara wanda ya gaji da haduwa tundaga waje, don yafi duk sauran gidajen dake cikin estate din, don shi kanshi gidan ma daga kan titin estate din kake hangoshi don yana da girma da tsayi, daidai gaban gate din din ya kara horn, wani armed security ne ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login