Showing 369001 words to 372000 words out of 381117 words

Chapter 124 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

2052

suka gaisa gaisuwar mutunci kafin ta soma magana  daman na buqaci gani Ka ne saboda inason muyi wata magana,
 Toh hajiya Ina sauraronki ya bata amsa kai tsaye
 Dama maganar Salima ne da Aman,
Dan Gyaran murya tayi kafin ta cigaba  Aman maraya ne , nasan kasan tarihin gidan nan basai na dago zancen ba,& .Baban aisha Ina neman ma dana Aman auren yarka salima, Ina fatan zaka amince da hakan
Murmusawa labaran yayi kafin ya kalleta yace  hajiya ai kece uwarta kume kece ubanta, komai yana hannunki, Duk zabin da kikayi mata nayi naam da shi, fatan mu Allah ya sanya albarka a cikin wannan
Murmushin jin dadi ammah tayi sosai tace  Nagode Nagode da wannan karamci baban aisha, Allah ya saka da Alkhairi
 Hajiya babu godiya Ay tsakaninmu Wallahi duk abunda kikace hakan za ayi Insha Allah
& & .



Saturday morning& .
Anatse take saukowa daga stairs, sanye take da Riga da skirt daya kamata sosai chip chip fuskanta fayau sai dan kohl data saka a a idanu ta, anatse take saukowa zuwa kitchen,
Kofar kitchen din ta bude, tana bude wa tayi turus ta tsaya Ganin tsaye yana kokarin hada tea a mug,yanda take kallonshi bai shima yake kallonta kafin ta kauda kanta gefe, ganinshi a kitchen din baisa taki karasowa ba don haka ta wuce hanyar pantry ta dauko noodles guda biyu da kwai biyu kafin ta fito, lokacin data fito yana tsaye Har lokacin ya zuba mata idanunshi yana sipping tea din hannunshi, fuskanshi tarr alamun bai dade da Tashi, kallonta ya dunga yi daga sama Har kasa Yan ajin kaunarta da shaawar ta yana double a kanshi, tayi mashi kyau sosai fatarta sai sheki takeyi don sai yanxu ya samu damar yi mata kallo kurulla sosai tundaga sama Har kasa, her body da yanda take komai a natse babu hayaniya is driving him crazy& .
Gyaran murya ya danyi Har lokacin yana kallonta bayan ya sauke mug din daga bakinshi yace  good morning beautiful, Har kin gama gudun Nawa?
Dan tsayuwa tayi chak daga dauraye tukunya dake hannunta tayi bata juyo ba haka zalika bata ce mashi Tak ba,
 Me zaki dafa mana ya tambayeta yana ajiye mug din hannunshi kan granite din dake kan table din kitchen,
Nan ma bata ce mashi ci kanka ba saima cigaba da abunda takeyi tayi, ganin haka ya sashi cewa
 Wifey bazaki kulani ba?, Wai har yanxu hukuntanin akeyi haka? Ya kamata a yafemin haka nan mana, Wallahi nayi regretting Duk abubuwan da nayi abaya
Yana kaiwa nan ya soma takowa inda take, Lola in tana tsaye a bakin plate cooked gas tana kokarin daura pot din akan plate din,
Murmushi kawai tayi don tasan daman abunda yake so kenan, yayi mata dadin baki saboda ya samu kanta cikin sauqi toh kuwa hakan bazai taba faruwa ba, Duk a tunanin ta taba ta zaiyi, abun mamaki kuwa sai taga akasin haka don yana zuwa dan da ita bai taba ta ba ya dan tsaya daga bayan nata yace  I know what you re thinking right now, inason ki san cewa bazan Kara takura ba sannan bazan fasa baki hakuri ba because I mean it, I want us to work this out, please..
Yana kaiwa nan ya wuce ya ajiye mug din kan sink kafun ya fuce daga kitchen din
Yana futa amra ta tabe baki tabi bayanshi da kallo Har fuce babu abunda yake Raya wa a zuciyar ta sai  hmm tanan Ka bullo kuma, Wai ni zaiyi ma dadin baki, idan har kaga na sauko da wuri ba sunana aisha ba
Tana gama tunanin nata ta juya ta kunna gas din.
Koda ta gama dafa lafiyayyiyar indomie din parlor ta dawo ta zauna ta kunna tv, sai a lokacin ta lura da nan ma an sauya komai ba dakinta kadai ba don komai dake dakinta saida aka sauya zuwa sabbi daga kan gadon zuwa carpet da sauran abubuwan dakin, nan ma parlor an sauya komai zuwa sabbin kuka wanda suka fi wanchan kyau sosai,
Gyara zama tayi ta fara cin indomien saida ta cinye tass ta rage kwai daya don ta cika cikinta sosai kafin ta mike ta wuce kitchen ta wanke plate din da mug din daya sha tea kafin ta dawo kitchen din ta zauna& .

Karfe sha biyu daidai ya fito daga part dinshi, ahankli yake saukowa babu abunda yake sai kamshi, hannunshi rike da wayanshi sanye yake da kananun kaya as usual kamar koda yaushe, fuskanshi na nan yanda take,
Tundaga bakin stairs ya hangota a kwance akan doguwar kujera tana latsa waya hankali kwance,
Karasowa yayi har inda yake bata ba lura dashi ba don waya take daga kwance  salima meysa yake kuka? Kin bata abunci kuwa
Amra ta fada Har lokacin wayan na hannunta don ta saka wayan a speaker
Daga chan bangaren salima ta amsa ta  Adda Wallahi rigima ne, yanxun nan ammah ta gama bata abunci
 Kinbar ammah da hidimansu ko?
 Ah ah Wallahi, na dan shiga bathroom ne, kinsan yanxu mun koma part din ammah
 Ina hero s dina? Kai Wallahi I missed them so much, inason ganinsu Wallahi

Amar ne yayi gyaran murya wanda yasa ta waigo ta ganshi tsaye,  kinason akawo su ne?
Ya tambayeta, banza tayi dashi kafin tayi sallama da salima ta kashe wayar.
Bata kalleshi ba ta cigaba da kallon tv, Yan a Ganin haka ya dan hade rai don baya son yanda take banza dashi, idan zaiyi magana goma bazata ce mashi qala ba,
 Zan futa yanxu, zaki buqaci wani abun ne? Do you need anything? Ya tambayeta sounding very serious,
Tana jin haka ta dan dago ta kalleshi ,  bana buqatar komai
Tana karashe wa ta kauda kanta gefe
Yana ganin haka ya girgiza kanshi kafin ya dan tako inda fuskanta yake, abunda bata taba expecting ba a wannan lokaci, sai jin lips dinshi tayi a kumatunta both sides, saurin runtse idanunta tayi sosai don kamshinsa daya bugu hancinta hade da kamshin breath dinshi da suka bugeta,  take care of your self bazan dade ba Zan dawo yana kaiwa nan baima tsaya jin abunda zata ce ba ya fuce daga sitting room din, gaba daga amra sandarewa tayi, she can t lie wannan peck din ya shige ta sosai,
Harya fuce tana jin presence dinshi da tausasan lips dinshi akan kumatunta& ..


Tana nan zaune tana latsa waya tana duban hotunan da sukayi da triplets dinta lokacin birthday dinsu, babu abunda take sai murmushi musamman idan tayi playing videos dinsu, tana nan zaune saida lokacin sallah yayi ta mike ta wuce sama&

Bayan futar Amar daga larrics bai tsaya ko Ina ba sai taura estate don kusan kullum sai yazo gidan ya duba yayanshi, ya dade sosai a wajen su don sai wajen yamma likis ya futo daga gidan, yana futowa daga taura estate ya wuce shopping mall, don wunin ranar da amra yayi shi, sayyayyan kayan girke girke yayi mata ya karo wasu provisions din da yawa Duk wani abunda zata bukata Harda frozen namomi babu abunda bai sayo mata ba,
Saida ya shake motar da kayyayki kafin ya wuce gida, a hanyanshi ta zuwa gidan ma saida ya tsaya ya saya masu grilled chicken kafin ya wuce gidan, lokacin daya karaso gida Har anyi Kiran sallar isha I don haka ya bude bayan yasa securities suka shiga da kayayyakin saida suka ajiye komai kafin ya wuce masallaci.
Saida aka idar ya fito ya shige cikin gidan, lokacin daya shiga sitting room babu kowa a kasan don haka ya wuce sama ya watsa ruwa ya sauya kaya kafin ya sauko zuwa part dinta,
Knocking ya danyi fir a seconds, baiyi gangancin bude kofar ba saida ta tako da kafarta ta bude kofar, kallonta ya tsaya yi kafin ya kauda kanshi, sanye take da hijab Har kasa da alamu bata dade da idar da sallah ba.
 Muje kasa na kawo provisions inason muyi sorting dinsu
Kallonshi ta danyi for a seconds fuskanta babu wani fara a ta dan tabe baki kafin tace  Ina zuwa Tana kaiwa nan ta rufe kofar ta shige ciki,
Shima kasa ya sauko ya zauna akan kujera yana jiran saukowa ta.

Yan anan zaune saida ta duaka kusan minti ashirin kafin ta sauko, sanye take da Riga da wando na barci wanda yayi mata cif, kanta ta nade shi da hula hannunta ta rike wayanta dashi, babu abunda yake sai baza kamshi don da alamu wanka tayi kafin ta sauko tana saukowa kasan, tana karasowa Ind a yake ta tsaya kikam bata ce mashi komai ba,
Already tundaga kan stairs din ya hango ta kafin ya kauda kanshi, ganin harya karaso batace mashi komai ba ya sashi mikewa ya fara duban ledojin yana shugowa dasu kitchen, tana Ganin haka itama ta soma diban ledojin tana nufa kitchen din dasu, yana hangota kuwa yayi saurin amshewa yace  just wait for me inside the kitchen let me do the job of packing it
Yana kaiwa nan ya fuce daga kitchen din, da mamaki take kallonshi, Wai Anya kuwa? Kodai he s possessed ne? Ta tambayi kanta,, tana cikin wannan nazarin sai Gashi ya dawo da wasu ledojin, haka ya dunga fita yana shugowa dasu akan idanunta saida ya gama tass ya rike kugunshi yana kallonta  Wai ashe it s not an easy task, now it s your turn, saiki fadi abunda Zan tayaki
Kauda kai amra tayi bayan ta gama sauraron nashi bata ce mashi komai ba Har lokacin fuskanta babu yabo ba fallasa, haka ta fara bude ledojin tana sorting dinsu ba tare da tace mashi komai ba,  wifey let me help you out
Kai tsaye tace  ka barshi Zan ita ni kadai
 No bazan barki kiyi ke daya ba aikin da yawa zaki gaji, let me help you please ya karashe yana kashe mata murya wanda yasa batama san tace mashi,  okay Ka saka waennan a fridge
Murmushi kawai yayi don yanxu karantarta yake sosai yana Ganin abunda yake sosai don Ganin abunda yake so da how she react on abubuwan da yake mata.
Yau saiga General guda Ana sorting abubuwa a fridge da freezer, dukda ba magana take mashi ba yaji dadin yanda suke ayyuka atare yana taimaka mata Har suka gama sorting komai, tana wanke hannunta ta fuce daga kitchen din, shima hannunshi ya wanke a gaggauce kafin ya futo, lokacin harta kai stairs yayi saurin cewa  wait& ga grilled chicken na sayo
Dan tsayuwa tayi kafin ta dan juyo tace  na koshi saidai zuwa gobe
Tana kaiwa nan ta wuce sama abunta.
Ak hanata tafiya ba don haka ya juya wajen dining ya dauka kadan ya wuce dashi kitchen ya saka a cikin fridge don shima a koshen yake& .

The next morning& .
Da kanta ta Tashi ta wuce kitchen tayi masu breakfast, da farko cikinta kawai taso dafama sai kuma daga baya ta danji babu dadi don koba komai gidan shi take zaune don haka ta daga hardashi ta ajiye mashi a dining ta wuce sama zuwa dakinta.
Amar kuwa sai wajen karfe goma sha daya ya Tashi, wanka kawai yayi ya sauya kaya zuwa na zaman gida kafun ya fuce daga bedroom din,
Kamar kullum bai tsaya ko Ina ba sai kitchen ya hada tea ya fito, da mamaki idanunshi ya sauka kan dining data jera plates din abunci akai da flask sun ruwan zafi mai kyau, ahankali ya soma takowa fuskanshi dauke da murmushi ya soma bude plates din, English breakfast ne tayi pancakes da sausages sai oatmeal a cikin wnai bowl a gefe, saurin ajiye cup din tea din dake hannunshi yayi ya zauna ya fara cin breakfast din,
Shida baya cin abunci sosai sai gashi ya tashi da abuncin tass bai rage komai ba, yana gamawa ya dauka plates din da bowl din ya aje a kitchen, Har zai futo yaga ko ina clean don haka ya wanke plates sun da kanshi don baya son yana bata wahala& .

****
Zaune take a bakin gado tana yanke farcenta incoming call ya shugo mata, cikin hanzari ta dauka wayar Ganin sunan anty Madina,
Da sallama amra ta dauka wayar tace  anty Madina& & . Kun manta dani sai yau
 Sorry my dear Wallahi na shiga busy kwana biyu, na dawo fah, nazo yin wani aiki ne ammah Zan koma,
 Dan Allah kin dawo? Kai ammah naji dadi sosai amra ta amsa ta
Dariya Madina tayi kafin tace  Ay dazu na kira hajiya mu gaisa, take shaida min kin tare ma, Toh Masha Allah naji dadi kinyi abun arziki kenan? Na dauka zakiyi taurin kan maki ne
Dan turo baki amra tayi kamar taba gabanta  kai anty Madina, nidai yanxu yaushe zakizo?

 Ki tura min address din gidan Zan shugo gobe Insha Allah, Madina ta amsa ta daga chan bangaren wayar

 Toh shikenan anty Madina sai kinzo
Sallama sukayi kafin amra ta kashe wayar, ta cigaba da yankan faratan nata.

Karfe buyer na yamma ta sake saukowa kasan don dora dinner, sanye take da doguwar ri??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????gar atamfa tayi mata kyau sosai don yanxu tafi saka su sosai ba kamar da ba da take yawa saka doguwar rigar abaya,
Wayanta na gefenta ta kunna wata slow music mai dadin saurare don tafi kaunar sauraron irin wannan wakokin don suna bata nishadi sosai, haka kawai saita tsinci kanta tana murmushi idan tana sauraron wakar.

Anatse take komai bayan ta fidda veggies din da zatayi amfani dashi, cikin kwarewa take Sarrafa girkin nata tana dan takawa, gaba daya ta gama shagala a cikin wakar tana miming  love me like you do love love love me like you, touch me like you do touch touch touch like you baby

Amar dake saukowa daga sama tundaga stairs ya soma jin kamshin abunci ta daya bade duka gidan, daman da yar yunwar shi ya sauko kasan don haka bai tsaya ko Ina ba sai kitchen, lokacin daya shugo kitchen din turus yayi yana kallonta, wani irin murmushi ne ya kubce mashi akan kyakyawan fuskanshi lokaci data daga wooden spatula da take juya abunci dashi tana rausaya  love me like you do baby& .oh touch me like you do baby
Kama habar bakinshi yayi yana admiring dinta Har baisan lokacin da dariya ya kubce mashi ba, a furgice ta juyo don bata san da tsayuwar shi a wajen ba, bin kykyawar fuskarshi ta soma yi da kallo, inda yake shafa sajensa yana bitting lower lip dinshi harya shigo cikin kitchen din yace  daman jin iya waqa haka? Looks like you re enjoying your moment ki cigaba da abunki please Inason gani
Wata irin kunya ce ta luluba ta saidai da yake ita din Akwai kafiya don hakan ta matse fuska ta kashe waqar gaba daya ta fara kokarin futa daga kitchen din, saida tazo dab da Ind a yake ya sanya hannushi ya rike hannunta gentle ya soma magana anatse  oh noo please, saboda nazo ne zaki gudu? Bari na futa tohm ki cigaba da abunki yana kaiwa nan ya fuce daga cikin kitchen din.
Bun bayanshi tayi da kallo harya fuce kafin ta koma bakin gas cooker ta tsaya tana wani tunani& ..

Koda ta gama dafa abunci, a cikin warmer ta zuba mashi ta wuce dining ta ajiye mashi kafin ta wuce kitchen din, tana shiga ta fiddo da plates da serving spoon da cokali Harda juice mai sanyi a jug kafin ta futo ta sake jerawa a dining din, already an kira sallan son haka ta tattara kitchen din ta wuce sama, sabon wanka ta sakeyi kafin ta dauro alwala, tana futowa ta shirya a gaggauce ta zura hijab dinta ta fada kabbara, saida ta tsaya tayi sallar isha i tana idarwa ta mike tsaye ta janyo wayarta ta fuce daga dakin, anatse take saukowa kasa harta karaso wajen dining din,
Duban abunci da zai ishi cikin ta tayi tana gamawa ta nufi hanyar stairs, a daidai nan ya shugo cikin gidan anatse, daga nesa ya hangota harta wuce sama,

Shima bai hau saman ba saida ya tsaya ya ci delica dun data daga masu kafin ya wuce sama,
Part dinta ya fara tsayawa yayi knocking, tana budewa ya kalleta daga Sam shar kasa, sanye take da wasu silk kayan barci pink doguwar Riga, kanta babu wani dan kwali,
Skin dinta sai sheki yakeyi wanda yasa ya kasa duake idnaunshi akanta, saida ta kafe shi da ido tace  Yadai?
 Sorry uhm, Zan ita samun coffee please
Gyra tsayuwar ta tayi sai kawai wnai irin murmushi ya kubce mata kafin ta hade rai,  wato yana son yayi using trick dinshi na kai mashi coffee daki kenan? Lallai ma ya& 
Katse mata tunanin nata yayi ta hanyar cewa  idan zai samu ki ajiye min akan dining Zan sauko na dauka thanks wifey, goodnight
Yana kaiwa nan ya wuce sama, da mamanki take kallon shi harya bace mata da gani, meysa Yanxu Duk abunda taje tunanin akai bashi yake yi ba? Kodai wasa yake mata da tunaninta ne? What sort of game is he playing yanxu kuma
Haka ta tsaya tana tambayar kanta ganin babu mai bata amsa yasa ta rufe dakin ta wuce cikin bedroom din,
Daukan plate din data gama cin abunci tayi ta sauko kasa, within 5min ta hada mashi coffee a cikin mug, tana gamawa ta ajiye mashi akan dining kafin ta wuce daki ta rufe kofar ta ta kwanta abunta.

Amar dake tsaye a dakin sa tsawon minti goma yana zarya hoping zatayi tunanin kawo mashi daki saijin shuru yayi,
Murmushi kawai yayi yana tausasa kanshi don baya son takurata don haka ya sauko kasan da kanshi, yana zuwa kuwa ya tadda ta hada mashi coffee din ta ajiye kamar yanda yace, daukan coffe sun kawai yayi ya wuce sama yana cije lebe yana murmushi,

Washe gari sunday, baije ko ina ba yana zaune a gida, kwata kwata baima ganta ba yau da safe don bata sauko ba, yana shirin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login