Showing 171001 words to 174000 words out of 381117 words

Chapter 58 - Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

2035

salima ta goge hawayen da takeyi kanta akasa, ammah na ganin haka ta karso gefen gadon su da take zaune tace   my dear kukan menene wannan?  ammah ta fada tana kallonta   are you okay?, baki da lafiya ne 
Dan dagowa salima tayi tana kokarin danne hawayen dake shirin zubo mata tace   barka da dare ammah na, kaina ne ke ciwo 
  shine kike kuka? Kodai an maki wani abun ne?  ammah ta shefeta da tambayar tana kallonta don gano abunda ke damunta, kauda kai salima tayi tace   babu komi wallahi, ciwon kai ne ammah 
Murmushi ammah tayi ta kalleta   kodai kunyi fada ne keda mutumin naki  ammah ta fada tana kallonta tana murmushi, da sauri salima ta kalli ammah don tayi mamaakin jin abunda ta fada, saurin sunkuyar dakanta tayi kasa, ba tare da ta amsa tambayar da ammah tayi ba, mikewa ammah tayi kafin tace   zaku shirya ne ma, 
  kinsha magani?  ammah Ta sake tambayarta
Girgiza kai salima tayi tace   ah ah, amma zan sha yanxu, inada panadol 
  okay, ki fara cin abunci kafin kisha maganin, allah ya sawaqe  ammah ta fada tana futa daga dakin zuwa dakin ta.


Karfe tara da rabi daidai ya shigo gidan,babu kowa a sitting room, sai karar tv dake aiki, direct ya wuce bedroom dinshi kai tsaye, kayan jikinshi ya fara ragewa kafin ya wuce bathroom, anatse yayi wanka ya fito daure da towel cikin kamewa, yan sahfe shafen shi yayi, kafin ya wuce cikin closet dinshi, short ya zaro da jellabiya, agaggauce ya shirya ya janyo wayarshi daketa faman ringing babu kakkautawa ya fuce daga cikin bedroom din, hanyar stairs ya bi ya fara takawa cikin kasaita, har ya hauro saman, ya wuce dakin ammah,da sallama ya shuga bedroom din ammah, a tsaye ya taddata gefen wardrobe tana shirya kayan wanki da aka kawo daga laudry, juyowa tayi ta kalleshi fuskanta dauke da murmushi   har an dawo babana, 
Kallonta yayi cikin so da kaunarta ya karaso dakin ya zauna bakin gadonta   barka da dare ammah, 
  barka son, ya aiki? You look stressed kardai ka wahalar da kanka fa 
Ammah ta fada cikin kulawa tana karasowa inda yake zaune, kallonta yayi yana tausayinta sosai yace   ammah bakice komai game da daddy ba 
Fuskanta ne yadan chanza tayi shuru, saida ta dauka yan seconds kafin ta soma Magana cikin natsuwa  toh me zance son?, duk abunda ya faru shiya jefa kasha a ciki, ni na dade da zargin yana miyagun ayyuka, 
Murmushi amar yayi ya riko hannunta ganin tana neman shiga damuwa yace   please ammah karki sama kanki damuwa, daman na tambaya ne don naga baki ce komai ba akan zancen sa 
Riko hannunshi tayi cikin nasa itama tace   bazan saka damuwa araina ba akan mutumin da bai san damuwar kowa ba saita kanshi, ni yanxu kaine damuwa ta son 
Yasan inda ta dosa don haka yayi saurin kauda zancen ta hanyar cewa   inajin yunwa 
da ammaki ammah tace   yau da kanka kake neman abunci?  & .dariya ya danyi yana mahaifiyar tashi cikin kulawa yace   im craving special coffee dinky ammah na  
  oh kaida dada bansan waye yafi wani son coffee ba, allah ya jikanshi da rahama  ammah ta fada still fuskanta dauke da murmushi, jikinsa ne yayi sanyi sosai, tunawa da wani abu, anatse ya miqe yace   ammah kisa yarinyar nan ta kawo min bedroom,I will be so busy this night, zanyi rounding up duka investigation dina nan, I have to report back to office soon 
Murmushi kawai ammah tayi tana wani tunani kafin tace   bari za a kawo maka yanxu 
Yana fucewa yaci karo da salima da plate din abunci a hannunta tana shirin shiga bedroom dinsu, kallonta yayi suna hada idanu ta sauke nata don ta tuna lokacin da yayi mata Magana akan cin abunci late,   babu gaisuwa  ta tsinkayo muryashi don yana gab da sauka kasa, anatse tace   sorry ya muhammd, ina wuni ya officee 
  lafiya  ya bata amsa ataqaice kafin ya sauka kasan zuwa bedroom dinshi, yana wucewa salima ta sauke ajiyar zuciya tana hamdala, kafin ta shige daki.

Karfe goma daidai amra ta bude idanunta kamar wadda aka tsungula, mamakin yanda akayi tayi barci a wannan lokacin tayi, tarr ta bude idanunta ta fara bin da kallo kafin ta miqe zaune bakinta dauke da salati, mikewa tayi ta wuce bathroom jin jikinta yayi weak sosai, wanka ta fara yi ta wanke bakinta kafin ta fito anatse, wani irin yunwa ne ya nuqurqusota, aggauce ta bude wardrop ta janyo doguwar riga mara nauyi ta barci ta saka, rigar takai mata har kasa tana da hula a baya, bata tsaya komai ba ta futo daga bedroom dinta ta sauka kasa don neman abunda zata sakama cikinta, hanyar dining tabi ta karasa, ganin an kwashe warmers dake kan dining din yasa ta wuce cikin kitchen anatse, bin ko ina ta farayi da kallo neat, tunanin abunda zata sama cikinta ta farayi, kafin ta yi deciding, bread dake ajiye a gefe rak ta jawo ta saka cikin toaster, cikin yan mintuna kalilan ta fidda toasted bread din ta bude fridge ta janyo avocado tayi mashing, tana gamawa ta hada da toasted bread din ta fito dining, zama tayi ta fara ci anatse, nan kasan shuru babu sound din komai.
Tana nan zaune tana tura toast a bakinta tana tunani harta cinye kusan slize biyar, saida tajita dam kafin ta mike ta maida plate din kitchen ta dauraye kafin ta wuce sama.
Bata dade da shiga daki ba saiga ammah, da sallama ta shugo cikin dakin sanye da hijab har kasa fuskanta dauke da fara a   daughter harkin tashi? Na shigo ay naga kinata barci 
Murmushi amra tayi kanta a kasa tace   barka da dare aammah, daxun ne kaina ya dan soma ciwo shine na kwanta banma san lokacin da barci ya kwashe ni ba 
Murmushi itama ammah tayi mata ganin ta fara sakin jiki da ita ta karso cikin bedroom din,   zauna daughter 
Zama amra tayi gefen gadon itama ammah ta zauna gefenta   baki manta da abunda na fada maki ba daxu ko? 
Dan sunkuyar dakai amra tayi tace   eh ban manta ba 
  yauwa, ungu wannan  ammah ta fada tana miqa mata wata kwalbar turare mai shegen kyau   ki shafa kafin ki tafi, yana da kyau mace ta kasance tana kamshi koda yaushe, 
Sunkuyar dakai amra tayi ta karba hannu bibiyu tana jin kunya sosai, ammah na ganin haka tace   daughter ki daina jin kunya ta, karki daukeni a matsayin sirika, ni uwa ce agareki, kuma zanyi kokarin ganin kin samu matsayi mai girma a wajen mijinki kinji, 
  in sha allah, allah ya saka da alkairi  amra ta fada
  baki daukeni uwa ba Kenan tunda kika godemin  saurin dagowa amra tayi kafin ta sauke kanta kasa tace   ba haka bane ammah 
  karki godemin daga yanxu, duk abunda uwa zatayi ma diya shi zanyi maki  murmushi amra tayi mata tana jin kaunar ammah sosai aranta, wannan itace uwa ta gari, mai jan kowa a jiki, ita kowa nata ne, bata kallon amra kwata kwata a matsayin suruka sai ya, shiyasa wayewa take da dadi.

  yanxu kije kiyi wanka ki shirya saiki tafi ko, akwai coffee daya buqata yana kan dining ki kai mashi, karkiji tsoron komai, ki cire tsoronshi a ranki  ammah ta fada tana shirin miqewa,   tohm  amra ta fada ahankali
  saida safe  amra ta fada ahankali kamar wadda aka zarema laka,
  Allah ya tashe mu lafiya daughter  ammah ta fada tana fucewa daga bedroom din fuskanta dauke da murmushin jin dadi.

Tana fita amra ta sauke wani nauyayyan ijiyar zuciya, gabanta na faduwa tama rasa me zatayi, wani irin tsoro ne ya durar mata, kwata kwata shes not ready to face him saidai bazatayi jayyaya da maganra ammah ba, tasan cewa ammah tayi hakan ne saboda ta daidaita.

Kamar wata munafuka haka ta aje turaren kan dresser ta janyo zumbulelen hijab dinta akan rigar ta nufi hanyar futa, dan tsayawa tayi jimm ta juyo ta koma gaban dresser din, bude cover turaren tayi ta dan shaka a hancinta, turaren yana da wani irin karfi sosai at the same time yana da dadi sosai,beneath her breath tace   uhm akwai kamshi  tunani ta soma yi ko me yasa ammah tace ta saka kafun ta tafi part din, bata kawo komai aranta ba don haka ta dan zuba a tafin hannunta daya dan jan lalle a yatsun, tana zuba turaren taga its oily don haka tayi saurin murzawa a hannunta ta dake hijab din ta goga a jikinta, tana gamawa ta aje kwalban ta fuce daga bedroom din.
Kasan ta sauko ta wuce kan dining, nan taga flask din coffee dinshi akan tray da mug agefe sai zuma, daukan tray din tayi anatse ta wuce hanyar part dinshi gabanta na faduwa, knockin ta fara yi, jin shuru yasa ta bude kofar ta tsaya bakin kofar, sanyin ac ne ya daketa, da sauri ta fara bin parlorn da kallo,wayanshi ne kawai da laptop a kan couch sai wani dan d?cor blanket a gefe da alamun bai dade da barin wajen ba, ta dade a tsaye ta kasa yin komai sai sake sake take aranta tana tunani, tana nan tsaye sai gashi ya futo kai tsaye sanye yake da classy pjs dinshi riga da wando nabarci, farare tass, baima lura da ita ba daya futo don kanshi a kasa yake yana kokari buttoning rigarshi, saida ya dago idanunshi ya sarqe cikin nata, mamakin ganinta ya soma yi don ba ita ya buqaci ta kawo mashi coffee din ba, jiki na bari amra ta kauda idanunta daga nashi ganin irin kallon da yake mata,kauda idanunshi yayi daga kanta ya karasa inda ya tashi daga kan couch din
Yana zama ya dora kafanshi dake dauke da black sock kan daya ya janyo laptop dinshi ya daura kan cinyashi, ta gefen idanu take kallonshi, saida ta tsaida natsuwarta waje daya jiki a mace ta karaso har inda yake zaune ta aje tray din akan center table, tana ajewa ta danyi baya gefe tace   barka da dawowa, ina wuni ya aiki? 
Da mamaki ya dago ya kalleta, he s so surprise, shi mamakin ta ma yake ji, lokaci guda ta chanza from that stubborn girl to soft girl, murmushi ya danyi ta gefen baki tunawa da dalilin chnzawan nata,   mata are fake  ya fada a zuciyarshi
Wani irin banzan kallo ya mata yace   meya kawo ki dakina? 
Ya fada babu wasa a fuskanshi, sauke kanta kasa tayi murya chan kasa tace   ammah tace na kawo maka coffee 
Bai ce mata komai ba ya maida hankalinshi kan aikinsa, ya dauka kusan minti talatin yana aiki, tana tsaye a gefenshi ta kasa motsawa, kamar daga sama ya tsinkayo melodious muryanta   na saka maka coffee din 
Cire idanunshi yayi kan laptop din ya maida kanta yana kureta da idanu, tana ganin haka ta sauke nata kasa   wowww,& ashe kema baki da banbanci da sauran mata, youre so fake, why are you acting up?na buqaci abu daga wajenki ne? 
Kasa dago kanta tayi tana sauraron abunda yake fada, idanunta yayi jaa sosai hawaye na shirin zubo mata daman tasan haka zata kasance, shiyasa kwata kwata bata shirya ma fuskantanshi ba, saidai babu yanda zata iya daman tasan zai fadi hakan.
Shiko mamakin ta y agama cikashi don yasan duk wannan sauyin nata saboda ta gane shine ya taimaki yan uwanta, aduniya babu abunda ya tsana kamar mutun mai faking abu, ba haka ya santa ba, saidai yanda ta sauya lokaci guda abun na bashi mamki.
  what are you still waiting for?,  ya kafeta da idanunshi dake tayar mata da hankali, kasa cewa komai tayi sai hawaye, yana ganin haka yace   youre dismiss, zaki iya fita 
Ararrabe ta soma Magana   anan zan kwa&  
Kasa tsayawa ya ji me zatace yayi ya zabga mata wani kallo daya sa zancen nata ya maqale,   are you deaf?, you knw how I hate repeating my self right? 
Da sauri ta juya ta bude kofar parlorn nashi ta fuce tana hawaye, samun kanta tayi da zama a sitting room din kasa tasha kukanta harta gode ma, zuciyarta ta karaya sosai da alamarinshi, saidai ko sau daya bata kawo cewa zatayi giving up ba, ko me zaiyi mata da duk maganganun da zai gaya mata haka zata zauna dashi, wannan alkawari ne ta dauka ma kanta, da dade sosai a zaune tana saka wa tana warware har barci ya kwashe ta anan sitting room.
Shiko goga tana futa ya tabe baki ya cigaba da aikinshi, coffee dinma baisha ba saida yaji barci na neman dibanshi ya fara sha don hana barcin, sai wajen karfe biyu da rabi ya samu ya wuce bedroom dinshi ya kwanta.
Da asuba ammah ta futo ta wuce bedroom dinta, don hankalinta bai kwan taba data turata part dinshi, don definitely zai iya korota, saboda tasan halinshi, ganin bata dakin yasa ammah yin hamdala, ta wuce dakin su salima ta tashesu kafin ta fito, tana fitowata nufi hanyar bedroom dinta, bata kaiga karasawa ba ta juya zuwa stairs ta sauka anatse har zuwa kitchen, ganin koi a a kashe ya tabbatar mata da lantana bata tashi ba, bottle water ta deba guda biyu kafin ta fito daga kitchen din, kamar ance ta dago kuwa ta hango amra na yi miqa tana salati, baki abude ammah take kallonta don ita batabhango taba, ammah na ganin haka ta wuce sama ba tare da ta bari ta ganta ba, tana shiga bedroom kuwa ta zauna gefen gado tana mamakin ganin amra a kwance a sitting room din kasa, daman tasan za ayi hakan indai muhammd ne kafiya tayi mashi yawa sosai, girgiza kai kawia ammah tayi   zanyi maganinka kuwa, indai korar yarinyar nan kayi 
Ammah ta fada tana janyo ledar magungunan ta ta bude tasha na safe don daman dalilin saukanta kasa Kenan don ta dauka ruwan da zata sha magani, yawanci lantana ke kawo mata da asuba, saigashi saukanta yanxu da tayi yayi amfani don ba lallai ta gane cewa ya kori amran ba haka zalika tasan amra bazata fada mataba.

Karfe goma kowa ya fito breakfast, jiki a mace amra ta sauko salima na gefenta suka karaso har dining suka gaida ammah, kafin kowa ya zauna, gaba dayansu daga salima har amra dukkansu jiki a mace kowa da abunda ke damunshi, ammah duk ta lura dasu don haka ya kauda kanta gefe batace komai ba don duk tasan damuwar su.
Aman ne ya fara karasowa dining din shima jikinsa yayi laasar saboda baya samun barci kwata kwata, damuwar salima tayi mashi yawa don ta daina kula shi kwata kwata, bata ma saukowa kasan don shi baya hawa sama saidai idan zaije ya gaida ammah, kiri kiri take avoiding dinshi taki bashi chance din fada mata side of his story.
Dagowa salima tayi idanunta ya sauka akan nashi,kauda kanta gefe tayi rai abace, shiko haka ya karaso kamar wani mara lafiya ya zauna agefe.
Duk ammah na lura dasu su duka, don taga yanda suka kalli juna kafin su kauda kai.
Anatse salima ta mike tayi serving din ammah kafin ta zuba ma amra da salim, tana gamawa ta nema wajen zama, dan dagowa yayi ya kalleta itama ta kalleshi tare da galla mashi harara, fuskan tausayi yayi yana dan daga hannunshi alamun bada hakuri, ammah na ganin haka tace   dear yau baza a zubama yayan bane? 
Dan dagowa salima tayi ta kalli ammah tace   shi yace karna zuba mashi  & da mamaki ya dago ya kalleta jin irin karyar da tayi, ammah najin haka ta dan murmusa ta maida hankali wajen cin abuncin ta,
Akarshe dai aman da kanshi ya zuba ma kanshi abunci, amra dai hankalinta baya kansu kwata kwata, sai juya cokali take a abunci ta kasa ci tana tausayin kanta.
Kamshinsa ne ya maidota daga tunanin data shiga,nan take hancinta ya shaida mata yana tafe don tundaga nesa ta jiyo kamshin, qin dago kanta tayi ta kalleshi har ya karaso ya jaa kujera ya zauna ya gaisheda ammah, su salima ma gaishesa sukayi ya amsa.
Kallon ta ammah tayi ganin yanda ta sauke kanta kasa   daughter bismillah 
Ammah ta fada tana kallonta, sanin abunda hakan ke nufi yasa ta mike ta jawo plate mai kyau ta zuba mashi, saida ta gama atsanake ta tura abuncin gabanshi, muryanta chan kasa kamar mai jin barci tace   ina kwana, bismillah 
Bai amsa ta ba haka zalika hart aje abuncin bai kalli wajenba, jiki a mace ta juya ta zuana a mazauninta.
Gaba daya breakfast din was awkward, don kowa yayi jugum sai karar spoon ne ke tashi, amar ne ya fara miqewa ya wuce bedroom dinshi follow by ammah, ammah na wucewa amra ta sauke ajiyar zuciya ta ture abuncin don tunda ta saka abuncin agaba tayi loma daya taji ya fita akanta, mikewa itama tayi ta wuce abunta, salim ma bai wani dade bay a mike, ya rage daga salima sai aman, itama bata san kowa ya watse ba don ta lula tunani, aman na samun chanze dinnan kuwa ya mike ya zagayo inda take zaune ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login