Showing 330001 words to 333000 words out of 347251 words

Chapter 111 - Ibtissam Book Two Complete Hausa Novel

Mrs Lee   

21 Oct 2025

1466

da wuri na tashi nayi duk abunda nake bu kataryi, lokacin har na samu nayi waya da Sofiyya duk da kasancewar bana samun su Farooq a waya , sosai hakan ya d aga mun hankali. Na jima a d aki na , dan a lokacin ko part d in Mama bance ba . Lokaci d aya abunda ya faru a kwanakin baya ya soma mun yawo cikin zuciya da  kwa kwalwata, dan duk abunda naji a wancan ranar na mantashi , sai cikin ikon Allah da lokaci d aya komai da komai ya fad omun a cikin rai.?
? ? ? ??
? ? ? ? A ranar gabaki d aya tunanin mafita na somayi , duk yadda nayi tunanin abun ba abune mai sau ki ba. Gabaki d aya hankalina a tashe yake, lokaci kawai nake dubawa sabida zuwa na  kara tabbatar wa kaina abunda naji.?

? ? ? ? Karfe 6:22pm na dare , Ana idar da sallah , Ammu da take zaune akan dadduma ta mi ke cikin sauri, dan sosai take san dare yayi, ko hankalinta zai fi kwanciya . Harta wayar hannunta bata d auka ba haka ta fito daga d akinta zuwa hanyar da ta sababi wanda yake da mahad i da duka gidan .?
? ? ? ?
? ? ? ? ? ?Cike da fargaba da abunda zata ji ta soma addua cikin zuciyarta , duk da hakan kuma duk lokacin da ta soma addu a zataji jikinta na zabura yana rawa rawa wani lokacin. Kai tsaye hanyar ta nufa , gabanta sai faman fad uwa yake , har ?ta  karasa zuwa inda take san zuwa.?

Almost 2 minutes tana tsaye a wajan bataji motsin kowa ba , ko alamar akwai mutumi a cikin d akin. Jiki a sanyaye ta juya zata koma. Caf taji mutumin ya soma magana cikin zafin rai.  Kona san zawo mana matsala? Akan me baku cika aikin akan lokaci ba .  Kungiya tana bu katar jinin yaranta, da s?ne kawai zan  karfafa burikana su cigaba da ?1ka. Dole na kashe  ya yan Safreena da abunda yake cikinta  , cikin  bacin rai da zabura , Ammu ta tura  kofar d akin, da ita kanta batasan lokacin da tayi haka ba .  Dakin duhu ne dashi sosai sai wani jan haske na kendir da aka kunna ja zagaye da wani ba kin spider .Ammu batasan lokacin data furta  Azubillahi minash& . Sai kuma murya ta ta ma kale sabida sha kar da akayi mata . Lokaci d aya hasken d akin ya bayyana , mutumin ne a tsaye a gabanta, jikinsa sanye da wasu ba ka ken kaya , ko hannunsa ba a iya gani baantana fuskarsa ,hannu Ammu ta saka zata yaye masa abun fuskarsa ya wanke ta da mari tare da hankad ata kan gadon da yake gefen wajan.?

? ? ?  Mai yasa bazaki barni na cika burina ba cikin salama ? Mai yasa bazaki cikamun buri na ba ?. Tabbas yanzu ke  yar  kungiyar spider ce , wadda dole sai kinyi sadaukarwa kamar yadda kowa yake yi.  Ya yan ki!  Ya yan ki da kike so zaki sadaukar wa  kungiya idan kikai wani gigin kuskuren kuma zata shafi har da mijin ki . Mai yasa kike da taurin kai ? Bayan ga dukiya mai d unbun yawa da zaki samu, zaki mulki duniya cikin lokaci  kalilan. Idan mazan kike so, zaki same su. Yara hud u? Yara hud u kawai zaki sadaukar dan ?1kar muradi na da naki kamar yadda nima na sadaukar da rai kuma nake san sadaukarwa. Kanta Ammu ta soma girgiza masa tana kuka  Mai mukai maka da muka cancanci wannan abun? Wane ne kai? Laifin mai mukai maka? Mai yarana sukai maka da kake san kashe mun su ? Kaji tsoran Allah . tsawa ya daka mata lokacin da take cewa yaji tsoran Allah. Cikin  bacin rai da ya ziyarce shi ya nuna ta da yatsa  Dole kiyi sadaukarwa kamar yadda akeyi. Kwana biyu, kwana biyu kawai kike dashi dan cika wannan aikin , jinin  ya yan muke so , idan baki kawo zuwa lokacin da na saka ba , ki tabbata daga ranar kinyi bankwana dasu.  a zabure Ammu ta mi ke tsaye , yadda ta mi ke mutumin gabaki d aya baiyi tunanin wani abu ba. ?A tunaninsa tsoratan da tayi da maganarsa ne yasa ta mu ke tsaye , amma sai ya ga sa banin hakan, a bazata Ammu ta saka hannu taja hular kansa, gabaki d aya fuskar mutumin ta fito waje. Dafe  kirjinta Ammu tayi ganin fuskar wanda ya fito , lokaci d aya jikinta ya soma rawa , bakinta ya soma karkarwa  Mammmmmmm shine abunda take fad a , dan ko maganar ta kasa . Ran mutumin ne ya  baci sosai cikin sauri ya fesa mata farin abu a fuskarta dan shi kansa bai yi tunanin bud e fuskarta zatayi ba . Ammu tana bud e idanuwanta ya ja ta a  kasa tare da fito da ita yana janta har zuwa dai dai  kofar da zai sadata da part d inta . Wani  karamar wu ka ya d auka tare da cutting hannunta kad an ya d ibi jinin hannunta tare da barin wajan.?


******* Ammu tafi 2 hours kwance a wajan kafun ta farka . Ganin inda take a kwance yasa cikin sauri ta mi ke tsaye tare da wucewa part d inta . Dan hankalinta ba  karamun tashi yayi ba . Abbu da yake Uk ta soma kira ba ai picking ba , kafun ?ta soma kiran su Uncle Isma il da Ammi , suna lokacin wayar su duk dai ta ki shiga . Lokacin da tayi  ko karin kiran su Farooq sai bacci ya d auketa a d akin ta s?lale kan gadon kamar wata mara rai , ga tsohon cikin da yake jikinsa .

Wannan shine rayuwar da nayi ba tare da sanin kowa ba . Rayuwa mai cike da  kunci da ba kin ciki, bani da yadda zanyi, bani da hanyar da zan ku butar da yara na . Duk lokacin da nayi  ko karin hakan sai wani abu ya faru. Zuciya ta gaf take da kamuwa da ciwo. Yara na kullum suna cikin zuciya ta , bansan mai mukai musu ba da mukai deserving wannan hukuncin amma tabbas sun cutar damu sama da yadda mukayi tsammani, mun nuna musu so da  kauna amma kuma s?ne suke san ganin bayan mu _abida hassada da wani  kuduri da yake cikin zuciyar su.

Ana cikin wannan yanayi su Farooq suka dawo gidan , dawowar su kuma ba  karamun tayar mun da hankali yayi ba shiyasa lokacin da na gansu nayi mugun tsorata , fargaba ya kamani, bansan da zuwan su ba , da babu abunda zaisa na yadda da su . Nayi  ko karin kiran Abbun su , shima baya picking dan kamar bani kad ai suke cutarwa ba, har dashi da halayen sa suka canza . Kullum baya zama sosai a cikin gida, sannan ko ya zauna sai ya dunga ke bewa shi kad ai.

A lokacin da sukazo waje na ba kamar da ba sai naji tsoran halin da zasu shiga idan suka zauna. Duk yadda naso su koma basu koma ba, duk a tunani na fad an da nayi musu zai sa su koma aushe ba hakan bane. Part d in su suka koma ba tare da sani na ba.?

? ? ?Sabida yadda na tashi hankaline da tsoratar da nayi labour ya kamani mai tsanani wanda yasa na fice daga hayyaci na, bani da wani  karfi ko tunanin kiran wani dan ya temaka mun. Bansan mai ya faru ba daga lokacin , sabida yadda komai ya juyemun idanuwansa suka soma dishi dishi. Shigowar wasu mata guda biyu ne yasa nayi  ko karin bud e idona. Nani kawai na gane da haka komai ya faru , nasan tabbas a lokacin haihuwa tazo mun. Inaji ina gani na haihu a cikin d akin. Naso na g?d? da Baby na alokacin amma sai suka soma dariya.?
? ? ?
? ? ? ? Dariyar da ta samo silar lallacewar komai na a halina, bansan a wana hali  ya yanta ma suke ciki ba. Bansan wana irin rayuwa sukai ba.?
? ? ? ??
? ? ? ? ?Hankali da tunani na basu tashi dawowa daidai ba sai lokacin da na tsinci kaina a cikin  kungiyar spider d in su . Shiru Ammu tayi sabida batasan tuno wa da irin azabar da tasha a hannun su . Babu wanda ta kalla a cikin falour sai hannunwanta .  Sun  kulle ni kamar ba mutum ba , sun azabtar dani kamar bazan rayuwa ba sabida rayuwar ahalina. Sun saka tsanata a cikin ? ya yan da na haifa duk sabida muradin su. Inasan nayi kuka sosai kamar kowa amma na kasa hakan. A ranar da na fara tsuntar kaina a wajan nasha wahala sosai, kullum burin su rayukan wad an da basuji ba basu gani ba . Bansan wana irin burika suke san cin mawa ba . Abu d aya nasani , rayuwa ce mai cike da ba kin ciki mai  kunci , wanda sanar daku kalar wahalar da nake ciki bashi da anfani ko mahimmanci a wannan lokacin . Shekarata hud u a wajan suka kama Isma il , wanda nasan abunda suke  ko karin yi akai na ne suke san yi akansa. Shiru Ammu tayi , dan yanzu sosai take jin zafin hakan a cikin zuciyar ta . Bata kuma cewa komai ba ta mi ke zata bar wajan.
? ? ? ? ?
? ? ? ? ? AMMU shine sunan da ya daki kunnanta . Cikin sauri ta juyo hannunta har yana rawa, Little da Prince ta gani a tsaye , lokaci d aya kuma suka kuma maimaita kalmar  Ammu da dole sai da Ammu ta samu waje ta zauna sabida jiri jirin da ta somaji. Cikin sauri Prince da Little suka  karaso wajanta, hannunta Little ya kama yana  kara maimaita  Ammu .  Dago da idanuwanta Ammu tayi da suka soma tara hawaye . Murya a sha ke ta furta  Mai kuka ce ? a karo na uku suka kuma maimaikon  Ammu.. hawaye ne ya soma sakko mata a idanuwana , cikin sauri Little ya saka hannu ya g?e mata hawayen mata , shi kansa kukan yake yi, ga Prince da shima hawayen yake yi. Abla da su Baby gabaki d aya kuka suke musamman Abla da ta fi kowa saurin kukan. Tunda ta soma magana Bobo yake kallanta , ko  yan yatsun hannunsa ya kasa motsawa , idanuwansa sosai sukayi tsantsan ja sabida  bacin rai, Abbu babu abunda yake nanatawa sai  innalillahi wa  inna ilaihi raji un, jinsa yake kamar ciwan zuciyarsa zai kuma tashi. Ammi ma kasa magana take sai kukan da take , gabaki d aya cikin falourn babu wanda baiyi kuka a cikin su ba .?
? ? ? ? ?
? ? ? ? ? ?Little da Prince sosai suka ri ke mata hannu kamar ance za a kwace masu ita . Gashi gabaki d aya an rasa mai magana a cikin su, ?Little tunda ya d ora kansa a laps d inta yake kuka . Murmushin ya ke kawai Ammu tayi hannunta d aya akan gashin su, gabaki d aya nauyin da takeji tsawan shekaru a cikin zuciyar ta ne ya soma raguwa . Shau ki da san ahalin ta s?ne suke yawo ako wana bargo da numfashin da ke tattare da rayuwarta . Farin cikin kasancewarta da  ya yanta yafi komai yi mata dad i a cikin zuciya . Ji take dama zata kasance a haka tare da su.  Dago kansa Prince yayi kad an karaf suka sauka akan Big Boss da yake shigowa falour, cikin sauri ya zare hannunsa daga na Ammu yana ja baya, a hankali ya furta  Yaya Big Boss  shima Little na jin haka ya zame hannunsa cikin nata yana mi kewa tsaye . Kallan yadda suka rabuta da ita tayi,lokaci d aya itama ta kuma da Big Boss da ya shigo falourn. Shima Bobo kallan Big Boss d in yayi yana jiran ganin reaction d insa , dan gabaki d aya kamar babu wani laka a jikinsa haka yake jin kansa .?
? ? ? ? ? ?
? ? ? ? ? ?Ammu bata kuma ce musu komai ba daman tasan halinsa tun bayan zuba. Jiki a sanyaye tazo wucewa ta inda yake, da hannu d aya ya ri ko nata, shiyasa tayi saurin jiyowa tana kallansa .?
? ? ? ? ? ?
? ? ? ? ? ? Yanzu ma tafiya zakiyi kamar wancan karan? Yadda yayi maganar a fusge kamar bashi ba yasa Ammu taja hancinsa kamar yadda yakeyiwa Abla  Bazan ta ba tafiya na barku ba . Am sorry my son , am so sorry , can t you forget your mom? Shiru Big Boss yayi mata na  yan second ni , sai kuma ya juya side d in Ammi  Mu ha kura ? Ko mu rama? Da kuwa Ammi ta kai masa tana murmushi a lokaci d aya kuma tana g?e hawayen fuskarta.
? ? ? ? ? ?
? ? ? ? ? ? ?Hannun Ammu ya kama suka dawo cikin falourn har zuwa inda su Little suke a tsaye .?
? ? ? ? ? ?Gabaki d aya sai suka zuba masa idanuwa kowa yana jiran ganin abunda zaiyi. Ganin ko motsi sun kasayi ya furta  Wa zai fara hugging d inta  , da  karfi Little ya furta  Yes&  sai yayi hugging Big Boss , tare da hugging Ammu a lokaci d aya . Shima Prince hakan yayi duka su biyun yayi hugging d insu suna dariya  kasa  kasa .?
? ? ? ? ? ?
? ? ? ? ? ?  Idan kun gama sai a bamu ragowa  , cewar Bobo lokacin da shima ya ke nufo Inda suke . Murmushi Ammu ta saki tare da saka hannu akan kumatun ta .  Bobo na ya girma yanzu , hugging d inta Bobo yayi yana goge kwallar da take san tarar masa a idanu a fakaice .?
? ? ? ? ? ??
? ? ? ? kallan Big Boss ta kuma yi  That time I don t really meant to hurt you . That s the only thing i can do to protect you and.. hugging d inta shima yayi  it s okay . I just missed you, allowed me to hug you please  , yadda yayi maganar babu wanda ya jisa sai ita , sai kuma Bobo da yake kusa da su sosai duk da shima kamar wucewar iska haka yaji maganar . Hugging d insa sosai Ammu tayi tana sakin ajiyar zuciya . Ta ko ina iskace take ratsa gab banta , irin iskar da ta dad e bata sha ke irin ta ba , ji tayi gabaki d aya wahalhalun da tayi tsawan shekarun nan sun tafi lokaci d aya .?
? ? ? ??
? ? ? ? Idan kun gama hugging d inta sai muma ku bar mata ita haka karku karya ta cewar Mamy.  Dan murmushi su Bobo Suka saka , Big Boss kuma kallan matarsa da take kuka yayi, ga Babies d insa da suke baccin su hankali kwance . Hannun Ammu ya kama zuwa inda Babyn suke .?
? ? ? ?
? ? ? ?Kallan Babies d in tayi sosai , sai kuma ta kallesa shima , kansa ya jinjina mata  your grand children , mayar da kallan nata tayi kan su tana  kara  kare musu kallo , sai kuma murmushi sosia ya bayyana akan fuskarta  kama suke da maman su duka , an thank god , maman tasu kama take dani, ko daughter ? Ta fad a hakan tana kallan Abla . Cikin sauri Abla ta  boye fuskarta tana sakin dariya  kasa  kasa. Abbu sai kallan Ammu yake ko zata kallesa amma ta ki kallan  barin da yake sai cikin kuskure idan idanuwan su ya had u sai tayi saurin janye mata .?
? ? ? ?
? ? ? ? ? Mi kewa tsaye Ammi tayi jikinta duk yayi la a_ar , itama so take kawai taji tayi hugging  yar uwarta ko zataji sanyi a ranta .  Ina zakije ? Cewar Ammu tana kallanta . Hanyar fita Ammi ta kalla kad an kafun ta furta  zan fad awa su Didi ne  girgiza kanta Ammu tayi  Tell the truth, kinasan rungumata ne , kuma kinyi letti sabida jikoki na sun rugaki  ta  karasa tana kissing yaran d aya bayan d aya . Murmushi Ammi ta saki sabida ganotan da ?Ammu tayi.?
? ? ? ? ??
? ? ? ? ? ?Hankalin kowa ya kwanta a wannan lokacin. Kallan mutanan falourn tayi d aya bayan d aya , sai kuma ta saki murmushi tana d an girgiza kanta .?
? ? ? ? ? ? Nasan ko wannan ku akwai tar1n tanbayoyi a tattare dashi. Na sani , kowa yana san sanin ko wane ne mutumin nan da yake cutar damu, mutumin da ko wannan ku yake kalla a matsayin mutum. Bansan da wana ido zaku kalli abun ba , bansan ya zaku d auki abun ba . Amma babu yadda zanyi dole na fad a kowa yasan shi kafun su soma mummunan  kudirin su akan mu. Ta  karasa maganar tana kuma kallan su .?
? ? ? ? ? ?
? ? ? ? ? ?


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login