Showing 333001 words to 336000 words out of 347251 words

Chapter 112 - Ibtissam Book Two Complete Hausa Novel

Mrs Lee   

21 Oct 2025

1477

Yaya ki fad a mana ko wane ne wannan mu sanshi dan Allah, Indai a cikin mu yake , ko a kasin hakan  , kallan Ammin tayi sai kuma ta girgiza kanta  zan fad a muku , zan fad a muku koma wane ne , amma kuyi mun wannan alfarmar zuwa bayan sallar isha i, sannan inasan kuyi mun al kawari anan maganar zata tsaya har zuwan sallar isha  I, nayi muku al kawarin sanar daku ko wane ne  , gabaki d aya amince wa sukayi da hakan, dan tunda tace zata fad a to tabbas zata fad an. Lokaci d aya familyn ya sake dun kulewa waje d aya , farin ciki da annashuwa ne yake yawo a gabaki d aya a halin gidan. Ji suke kamar an musu wani babban albishir, dan bazasu ta ba mantawa da wannan ranar ba .
? ? ? ? ? ?
? ? ? ? ? ?**** kiran sallar magrib ne yasa gabaki d aya mazan suka wuce masallaci, suma matan suka tafi  bangaran su danyin sallar magrib, kowa burin sa bayan sallar isha i tayi sabida susan ko wane ne wannan da bayasan farin cikin su. Su Baby gabaki d aya part d in Mamy suka wuce tare da triplets da kuma Mamyn. Mamy kuma tayi hakan ne dan ta basu waje su d an tattauna kafin anjima tayin.?

****** Suna komawa ruwan wankan Mamy ta soma d orawa . Tana idar da sallar tayi mata wankan jego sai su Triplet da Hajiya Falmata tayi musu wanka tare da shirya su . Lokacin da Abla zata shayar dasu sai da ta gama mitarta tukunna , tanayi tana hawaye sabida zafin da take ji. Gabaki d aya ukun saida ta shayar dasu. Ita kad ai sai faman kunburi take , Sunshine take jira kawai yazo. Kallan yadda suke hannun su Baby tayi ,  Uhmm ai wallahi bazaku cire mun Nono ba haka kawai. Sunshine yazo ya siyo muku madara ko kuma na je na d akko ta kitchen a dinga ba ku." Ita kad ai sai faman mita take a cikin zuciyarta ganin har lokacin breast d inta basu dena yi mata zafin ba . Gashi duk abunda ta saka a wajan sai ruwan nono ya ji ka mata rigarta.

*******
? ? ?Ana idar da sallar Isha i gabaki d aya suka kuma taruwa a falourn Abbun. Banda Didi da Mama da basu san da Meeting d in ba , dan ko da kowa ya koma part d insa d azu babu wanda yayi maganar gashi daman kusan kullum a d aki suke zaune shiyasa babu wanda yayi tunanin sanar musu , gudun kar wani abun ya d aga musu hankali.?

Gabaki d aya suna falourn, Big Boss da Bobo ne kawai babu sai Sauban, amma hatta su Hajiya Sa adatu suna falourn. Kallan su gabaki d aya Ammu tayi tana tunanin yadda zata soma yi musu bayani , wanda tasan ba lalle ne zuciyar su ta amunta da hakan ba . Sai a yanzu take jin tsoran sanar dasu , dan har cikin zuciyarta bata bu katar abunda zai kuma ruguza family d inta , bata da wani mafita sai na fad a musu gaskiyar lamari.

? ?  Bansan yadda ko wannan ku zai d auki yanayin nan ba . Da ace akwai wata hanyar bayan wannan da , da ita zanyi anfani dan hankalin kowa ya huta . Yadda tayi maganar kamar tana tsoran sanar musu ne Abbu da tuntuni baiyi magana ba ya furta  Wane ne Safreena?  Dan kallansa Ammu tayi , tunda taji ya ambaci sunanta ta san tabbas abun ba  karami bane , da gasken gasken yana san san1n koma wane ne .?
? ??
? ? Ajiyar zuciya ta sauke mai d an  karfi  Akwai Underground ko? , yadda tayi masa maganar tana kakkauce idanuwanta daga nashi yasa ya d an murmusa ba tare da kowa ya lura da hakan ba .  Akwai.. shine amsar da ya fito bakinsa .  Dan shiru Ammu tayi kamar mai tunani kafun ta kallesu  Nan zamuje , zasuyi magana ta furta  Anan ne zaku samu amsar tanbayoyin ku gabaki d aya  , ta  karasa tana kallan su gabaki d aya .
? ??
? ? ?Babu wanda ya musa mata acikin su suka mi ke gabaki d ayan su. Suna shirin fita Big Boss ya shigo falourn, bai ce komai ba ya wuce wajan Triplets d insa , shiyasa itama Ablan ta fasa fita ,  Let s go  cewar Abbu yana bin wani  bangare daga cikin part d insa, suma duka suka biyo sa , zuciyar su gabaki d aya har bawa take da sauri da sauri , babu wanda zuciyarsa bata girgiza ba sabida tashin da ya soma ziyartar su. A yadda suke tafiyar ne zai tabbatar wa da mutum a cikin yanayin da suke ciki.

***** Suna barin wajan Abla ta furta  Sannu da zuwa Sunshine  , bai amsa mata ba , sai alama da yayi mata da hannu alamar ta  karaso inda yake . Babu musu kuwa ta  karaso wajan bayan ta matso da abun Babies d in.  Me Mamy take baki ne ? Sai  kara  kiba kike fa.  Bata fuska Abl tayi  Ni babu wani abu da suke bani, idanuwanka ne suka maka gizo
 Dan zaro ido yayi kad an yana kallanta  My eyes ko? Okay ai nasan  kibar ki bari na sake dubawa  , yadda taga yana ta ba mata rigane ta d an soma dariya  No kay1 ha kuri Sunshine , na yadda nayi  kiba kad an, amma kai ma kashi kayi lukuti, har tumbi kayi fa . Kallan Cikinsa yayi sai kuma ya kalli nata .  Don t worry duk lokacin da Mamy ta bar mun ke zai koma . Waskewa tayi daga maganar da tayi , dan bata san amsar da zata bashi ba a wannan karan .
? Mai sunan Uncle Isma il ya d auka , kamar wanda aka mintsina, yana d aukansa ya soma kuka , a hankali ya soma jijjigashi ko zaiyi shiru , amma sai  kara bud e baki yake yana callara ihu, kallanta yayi ganin yadda ta  bata fuska  Feed him , ya fad a yana mi ka mata shi, kamar zatayi kuka itama ta furta  Ni ciwo suke mun, sai dai na had a masa madara a kitchen  , zata mi ke ya furta  Go back . Idanuwanta har ya soma tara hawaye , bai ce mata komai ba ya mi ka mata , ganin yadda ya d aure face d insa hawayen suka soma sakko mata , tana sawa yaran mama abaki kuwa ya dam ka har saida tayi wani  karar azaba . Lumshe idanuwansa yayi sosai yana sake bud ewa, ita kad ai ta san yadda suke mata ciwo, sosai ta soma kuka , tun tana hawaye har sautin kukan ya soma fitowa kad an. Ya dad e yana sha kafun ta cire masa lokacin har ya koma bacci. Zata kwantar dashi Beauty itama ta soma kuka , ganin kallan da yayi mata yasa itama ta d auketa ta soma bata , ita kad ai take kukan ta bai ce mata komai ba . Da ta gama bawa beauty itama sai da ta bawan mai sunan Uncle . Lokacin ta cika ta kumbura kamar zira take a ta bata ta fashe. Tana kwantar dashi ta mi ke zata bar wajan, amma ya hanata  Bakyasan shayar mun da yarana? Yadda yayi maganar cikin cool voice ne yasa ta sunkuyar da kanta  kasa , cikin rawar murya mai had e da kuka ta furta  Zafi suke mun sosai ai , ta  karasa tana fashe masa da kuka . Hugging d inta yayi yana tapping bayanta alamar lallashi  it s okay , zai dena kinji? We re sorry  d an turo bakinta tayi kad an tana hararar abun gadon nasu  kasa  kasa , har saida Big Boss yayi murmushi mai sauti da ya fito, dan sarai akan idanuwansa take hararar masa yaransa .?

****** Su Ammu kuwa tafiy suke suna ratsa doguwar haryar da suka bi, Ammu da Abbu na gama su kuma su Mamy suna bayan su jikin kowa a sanyaye . Dan tsawan lokacin su a cikin gidan basu san da wannan hanyar ba . Basuyi tafiyar munti 3 suka  karaso Inda  kofofin kowa  bangare yake . Sai a lokacin Ammu ta kalli Abbu , a sanyaye ta furta  Kamar yanda tsarin underground d in wancan yake haka wannan ma d akunan suke? Kansa Kawai ya jinjina mata yana  kare mata kallo. Yana jin yadda tayi ajiyar zuciya . Kallan  kofofin da suke jere wajan ta  karayi, sai ya  kara tuno mata da shekarun baya lokacin da ta shigo wajan nan. Jiki a sanyaye ta cigaba da tafiya suma kuma suna binta a baya, sai da suka wuce  kofa biyar a ta shidan ce ta dakata kafun ta d aga hannunta zuwa handle d in, bakinta d auke da Addu a .
? ?Dai dai lokacin da d an  kungiyar spider yake  ko karin cakawa wani abu mai kamar jini jini wu ka . A tsorace Ammu ta d an ja baya tana ihu kad an sabida yadda abun ya tsorata ta . Cike da tsananin firgici da tsantsan razani ya jiyo da fuskarsa da a wannan karan take a bud e ba a rufe ba , mutanan da ya gani ne ya matu kar girgiza masa zuciya . Mutuwar tsaye Abbu yayi a wajan, yana  kara jingina da bangon d akin sabida mugun jirin da ya so kayar da shi. Cikin rawar murya da hawayen da suka soma fito masa ya furta  MAMA? rai a  bace Mama ta kalle su duk da yadda jikin ta ya soma rawa wu kar data yar tayi  ko karin d auka Ammu tayi saurin ball da ita ta shige  kar kashin gadon d akin. Kamar yadda His Excellency ya shiga tsananin tashin hankali haka su Mamy suka shiga sosai, hawayenta Mamy tayi saurin goge tana kallan su Baby  Ku wuce part d ina ina nan zuwa  , duk da ba_u san ko wane ne ba haka suka wuce ganin yadda su Mamyn duk suke hawaye . Abbu kasa tsayuwar yayi ya zame  kasa yana fashe wa da kuka  Mama?kece kike  ko karin ganin bayana ? Nasan hakan ba gaskiya bane Mama, na ro ke ki dan Allah ki  karyata Safreena , kice ba gaskiya take fad a ba. Kallanta itama Safreena tayi da idanuwanta da suka gama ji ke wa da hawaye sosai. Su Uncle Adam da su Uncle Kabeer kasa magana sukayi gabaki d ayan su sai kallan Mama da suke hankali a tashe. Juyawar da Ammi zatayi taga Abby baya wajan. Cikin sauri ta wawwaiga amma baya wajan , da sauri sauri tabi hanyar da suka biyo ko zata ?same sa .?
? ?
? ? ?Abbu kasa kuma cewa komai yayi sabida yadda yake jin zuciyarsa kamar ana caka masa wu ka ta ko ina . Uncle Adam ne ya furta  Mama dan Allah kice ba ?haka bane , wannan maganar ba gaskiya bace , Mama kina san a halin nan , dan Allah kice mana ba haka bane Mama , Dan Allah  shima yana  karasawa cike da kuka . Duk kuka ko wannan su yake dan ko magana ma sun kasa yi sabida tsananin tashin hankali. Abbu kamar wanda ciwo ya soma kamashi ya furta  Tun bayan mutuwar mahaifiyar mu , ke?e kika zama tamkar uwa a gare mu. Kin kula damu kamar  ya yan cikin ki, idan ni da nake babba zaki yi mun haka , mai yasa zakiyi wa 0smail? Ya nuna miki so sabida ke kad ai yake kallo a matsayin mahaifiyarsa , ya nuna miki  kauna da tsantsan biyayya, Mama mai yasa muka cancanci hakan daga gare ki? Kasa  karasa maganar yayi sabida  kwarewar da yayi, lokaci d aya jini ya fito masa a bakinsa . Da sauri Ammu ta ri ko hannunsa  Dan Allah karka kuma cewa komai, ka bari likita ya dubaka , Dan Allah karkayi mun musu , girgiza kansa yayi kad an , sai kuma ya saki murmushin da yafi kuka tsananin a zaba da  kuna a cikin zuciya . Kallan su Uncle Adam yayi da suka kasa magana gabaki d ayan su , amma a hankali Ammu ta taimaka masa ya mi ke , shima da wani irin jiri kamar wanda yake  ko karin ?fad uwa . Juyawar da zasuyi Mama ta rarumi wata wu ka zata cakawa Abbu, cikin sauri Abbas ya hankad asu gefe a  ko karin taimakar su , wai wu kar ta cakesa sosai a baya . A rud e Mama ta ja baya tana saka ihu ganin abunda ya faru. Cikin sauri Abbu ya ri ke Uncle da yake  ko karin fad uwa  kasa , su Uncle Adam gabaki d aya kansa sukai hankali ya tashe , su Abbu suna  ko karin d aukanshi zuwa asibiti ya girgixa musu kai , ga jini da yake d an zubo masa a baki  Nasan bazan rayuwa Mohammad . ?Hukuncin abunda na aikata ne yake bina . Bani da wani za bi , bani da yadda zanyi dole nakeyi sabida gudun tsinuwarta, tace zata tsinemun idan banyi abunda tace ba . Kayi ha kuri Mohammad , nice na saka layar cikin falourn ka amma naji dad i sosai lokacin da Abla ta fasa base d in.. wani irin jan nunfashi ya kumayi, da  kyar muryarsa take fitowa  Mohamamd nine nake zuba maka maganin .. da take & bani a cikin& cof..fee d in.. ka, ka yafe mun& .Dan Allah ba dan hali..na & ba .. inaso kayi mun& alfarmar& ko bayan raina& zaka kular mun da Yasmeen da Bilal duk da & . Nasan inda yake za a kula dashi sosai& Sa adatu kuma na riga da na rubuta mata takardar sakinta& . Ka & ka & ka yafemun dan Allah  wani irin sha kuwa yake yi sosai , cikin kakarin murya, shahada Abbu ya soma karantawa cikin muryar kuka , su Uncle gabaki d aya suma shi suke fad a kowa yana kukan. Cikin ikon Allah Uncle Abbas yayi shahada kafun rai yayi halinsa , ga jini sosai da ya  bata Abbu da su Uncle .
? ? ?
? ? ? Suna cikin kukan ne suka soma jin muryar Mama  Kai ka kashe mun shi muhammad , kai ka kashe mun yaro na . Mai yasa duk lokacin da nayi yun  kurin kashe su sai wani abun ya same ni , mai yasa ?mai yasa  sai kuma ta soma dariya sosai tana tafa hannayenta. Tabbas kuncika  ya yan kaltoom, kamar yadda ta rabani da mijina , kamar yadda ya nuna mata so Haka kuka yanxu kuke yin hakan. Mai yasa duk yarana zaku fisu kud i da wadata? Mai yasa zaku samu d aukaka sama damu bayan mune ya kamata mu samu hakan. Sau da dama idan nayi  ko karin kashe ku sai kun  batamun shiri na , mai yasa ? Na kashe kaltoom dan cikar burina amma hakan kamar  kara da bawa kai na wu ka nayi  cikin rinannnun idanuwansa Abbu ya furta  Ke kika & kashe mana mahaifiya& ? Yadda yayi maganar sai ya baka tausayi, cikin halin ko in kula ta furta  Nice na kashe ta , nice nan na kashe ta sabida d aukaka da farin jini da ta fini, dan na samu zuciyar gabaki d ayan ku na d auki isma il dan na shayar dashi amma ko sau d aya ban ta ba bashi Nono na ba. Sabida na tsane ku Sabida yadda na tsani uwar ku. Bana bu katar ku, bana  kaunar ku a tattare dani . Nida  ya yana kawai nakesan mulkar komai amma a kullum riguza mun shiri kuke, zuwan shed anin fararan mutanan nan ( ta nuna Ammu) s?ne suka  kara  bata mun shiri lokacin da na so kashe su. Tabbas Kabeer nice na kashe Matar ka sannan nayi  ko karin kashe yar ka duk da banyi na sara ba, kai ma Adam kamar yadda matarka ta fad a , nice nan na kira ta sannan na saka ta kashe maka matarka, Nusaiba mijin ki ya so tonamun asiri , wanda babu wanda ya isa yayi wannan gangancin na barshi a raye. Cikar burina kawai ya rage yanzu wanda kuka ruguzamun komai . Ko sau d aya banyi nadamar abunda na aikata ba , banyi ba , banyi ba  ta  karasa tana kyal kyalewa da wani irin dariya . Sau d aya Abbu ya kalleta dan ya kasa cewa komai, mi kewa tsaye yayi duk da jirin da yake ji, haka Ammu ta taimaka masa ya soma tafiya , Uncle kabeer da Uncle Adam ma gawar Uncle Abbas suka lullu bawa abu dukda hakan kuma bata dena jini ba . Aunty Nusaiba ma cikin kuka tabar wajan, shi kansa Uncle Adam kasa binsu yayi Sabida baisan da wana irin ido zai kalle suba.?

**** Abbu yana fitowa falourn , y zu be  kasa baya motsi Sabida yadda ciwan zuciyarsa ya tashi, hankali a tashe su Baby sukayo kansan dan yanzu Suka gama kukan Abby da Big Boss ya fita


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login