Showing 219001 words to 222000 words out of 347251 words

Chapter 74 - Ibtissam Book Two Complete Hausa Novel

Mrs Lee   

21 Oct 2025

1473

tana komawa  bangaran su bata shiga cikin d aki ba dan tasan su Eshaal zasu yi mata tsiya . Balchony ta wuce kai tsaye sabida yadda kanta yake neman tarwatsewa , ta rasa tunanin mai zatayi a cikin zuciyarta . Anwar da ta bawa izinin ya turo ko kuma Sauban da kowa yake supporting?  Ya Allah ka kawo mun mafita  , ta fad a a fili kafun ta nufi d akin su , tana shiga suka soma yi mata guda  An kusa d aurawa ta zama matar Yaya Sauban , hararar su tayi tana shigewa toilet , tasan idan ta biye musu zasuyi ta jan zancan ne  .


********
 Daki ne mai duhu sosai da mutum bazai iya tantance ko ina bane sabida yadda ?wajan yake da dubu ko hannuwanka bazaka iya gani a ciki ba. Sautin muryarsa ce take fita ta ko ina cikin tsananin  bacin rai da har cikin muryarsa ana iya jin ta .
 Ta yaya hakan ya faru ? Sun shirya ? Mai hakan yake nufi kenan? Ba zan yadda da wannan abun ba , a yau d innan ba sai gobe ba , dole ku mutu kowa ma ya mutu, dole ku mutu , taya zan  bata shekara 22 da biyu a banza? Cikin  kan kanin lokaci su ruguzamun shiri na ?  , yana kai  karshe maganar ta sa sai wani sautin fashewar abune yake tashi ta ko ina a cikin d akin alamar fashewar, kamar wani tsohon mahaukaci haka yake ihu cikin tsananin  bacin rai da tashin hankalin da yake fita har cikin sautin sa .

*******
Abla tana idar da sallah wanka tayi cikin wani blue silk d in kayan bacci yar guntuwa da bata bi zuwa gwiwar ta ba sai dogon gashin kanta da ya gyara sosai ta tufkeshi, yadda rigar take shara shara yasa ta saka wata doguwar ba kar riga a kanta, bata yi kwalliya ba amma sosai tayi kyau musamman lipgloss d in da ta saka akan lips d inta sai shinning yake sosai.?

? ?Tunanin gyara masa d aki ne ya fad o mata a cikin ranta .  Dan murmushi ta saki bayan ta yanke hukunci zuwa ta gyara masa bedroom d insa kafun ya shigo cikin d akin ita kuma sai ta dawo nata d akin.?

? ?Medium size hijab d inta ta d auka da ko hannuwanta basu gama rufewa ba ta saka sai turare da ta  kara fesawa d an kad an a jikinta .?
? Hanyar d azun ta sake bi kamar zata shiga d akin nan sai kuma ta fasa sabida bedroom d insa da take dan gyarawa .  Dan ajiyar zuciya ta sauke bayan ta shiga bedroom d insa , tsayawa  karewa d akin kallo tayi tana tunanin ta yadda zata fara gyarawa . Hijab d in jikinta ta cire duk da d akin ba wani datti yayi ba. Saban blanket take san fara shinfid a masa shiyasa ta nufi dressing room d insa , nan cikin ma tsaff yake sai  yar  kura kad an da baza a rasa ba shima sabida da d ewar da yayi ba a shiga ciki ba.?
? ? Wani saban white blanket ta d auka takai d ak1n sannan ta sake dawowa ta d auki na pillows d in. Tana jan su sai wasu papers suka tar watse a wajan. Ajje abun hannunta tayi ta soma kwashe papers d in. Sai data gama kwashewa duka zata mayar idanuwanta suka kai kan  karamun picture da yake jikin file d in hannunta . Sakin baki tayi sosai tana kallan hotan kai ganin hotanta wanda ita kanta bata san yaushe akayi saba sabida dad ewar hotan.  Ibtissam Isma il  , shine sunan da ta gani  baro  baro a jikin file d in.  Kirjinta ne ya buga da  karfi ganin hakan shiyasa ta soma bin file d in da kallo tana san fahimtar wani abu daga cikin file d in amma ta kasa fahimtar komai . Shiyasa ta samu waje ta zauna a gaban dressing mirror d in d akin tana fito da papers d in ciki d aya bayan d aya tana kallan papers d in jiki. Wani farar paper da take a ninke ta bud e har zata yar ganin kamar diagram ne a jiki sai kuma wata zuciyar ta sa ta fara karanta abunda yake jikin paper . Tsananin mamaki ne ya hanata magana sai  kurawa paper ido da tayi ko  kiftasu batayi, gabaki d aya abunda yake jiki sunan wajan da ta zauna ne tundaga gidan uwar karuwai , matar data tsinceta, fitar da ita daga nigeria da akai har  kasar da aka kaita kafin zuwan su America . Abla bata san dalili ba sai taji kamar hawaye na san sakko mata a cikin idanuwa na. Shafa wajan idan tayi jin hawaye a wajan da batasan yadda akai suka sakko ba , tana  ko karin gogewa wani hawayen ya sake sakko mata sabida tuna irin rayuwar da tayi a baya ne suka soma yi mata yawo cikin kwanyarta. A jiyar zuciya ta sauke kad an ?tana ajje paper d in kafun ta bud e na  kasan ta , ita gabaki d aya kanta ya soma kulle wa ne sabida kasa fahimtar papers d in menene .  Sofiyya
Shine sunan data gani a cikin babbar paper d in ciki daga  kasan ta aka saka Mother , sai d ayan side da aka saka isma il shima daga  kasan sa aka saka father , hannun Abla har rawa yake sabida yadda taji zuciyarta tana mata bugu da sauri sauri , bata san gasgata zuciyarta akan abun da take raya mata shiyasa ta  kara bin paper da kallo ganin tsakiyar ta anja layi sai sunan  Ibtissam  da ya fito sosai a wajan  kasanta an rubuta daughter. A zabure Abla ta mi ke tsaye ragowar papers din suna zubewa  kasa . Hawayen idanuwanta ta goge cikin sauri ta fito daga dressing room d insa bata tsaya  bata lokacin ba ta nufi  kofa zata fita, tana saka hannu akan handle d in shima yana bud e  kofar, saura kad an ta fad i  kasa yayi saurin ta ro ta , da mamaki yake kallan face d inta ganin hawaye  Crying? Ya fad a yana  kara kallanta , fisge hannunta Abla tayi daga ri kon da yayi mata , tsayawa kallanta yayi cike da mamaki , paper d in hannun ta Abla ta mi ka masa cikin rawar murya ta furta  Mene ne wannan? Ta fad a cikin kuka lokacin da ta ke nuna masa paper hannunta , kallan paper yayi tare da kallanta , zai ri ke hannunta tayi saurin jan baya  Tun Yaushe kake  boyemun gaskiya ?Mai yasa ? Kasan Itace ta bar ni tun ina  karama amma kasa na sha ku da ita ? Wacece ni? Su wane ne Iyaye na  , dafe goshinsa Big Boss yayi yana  kara step d aya itama tayi bata kad an  Let s talk please, stop crying zan miki bayani . Cikin kuka Abla ta furta  Bana so  . Tana fad an hakan tayi gefensa zata wuce ya ri kota, a zuciye ta zo zata fusge jikinta ya  kara ri kota, cikin kuka Abla ta soma ko kawar  kwace jikinta , ganin tana san zame masa ya ri keta sosai yadda ko  kwa k kwaran motsi bazata iya ba amma _ai ya sassauta mata yadda zataji zafi ba . Cikin kuka take furta  Ni ka sake ni na tafi, ka barni  . Hugging d inta yayi a jikinsa yana tapping bayanta  baki da lapiya kar mu soma haka yanzu please, ki manta komai , a zuciye yanzu ma ta fusge zata wuce ya  kara ri kota yanzu kam da gasken kokawar ta soma yi dashi tana san  kwace jikinta amma ya  ki bata damar hakan. Cikin kuka ta daddage ta gantsara masa cizo a hannu , duk da yaji zafin ciwan bai saketa ba haka ya zaunar da ita kan d aya daga cikin kujerun wajan. Gabaki d aya ta  ki tsayawa ta saurare sa balantana yayi mata bayan1n. Ganin yadda ta kesan fita daga hayyacinta ne yasa ya d an daka mata tsawa kad an da ya tsoratar da ita . Lokaci d aya ta nutsu, zai yi magana ta dafe jikinta da take ji kamar yana san murd a mata. Ba zato ba tsammani ya tsugunna a wajan  kafafuwanta tare da d ora kansa akan laps d inta.


MSSLEE
'?.


IBTISSAM
? ? ? ( A heart touching story of love and destiny)

Story & written?
? ? ? By
Mss Lee ??

?
? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?0812 044 4608


? ? TALLA!! TALLA!!! TALLAH !!!!!!!

SHIN KUNSAN WACECE HAJIYA NUSAIBA BR~B ZURU ?d'?

HAJIYA ~ NUSAIBA DR~B ZURU

MAMALAKIYAR ZIMH ISLAMIC AND MEDICINE DAKE RINGH ROAD A KANO NIGERIA
Tazo muku da ingantattu ko sahihan magungunan mata masu inganci, ba anan kad ai ta tsaya ba har da na cututtuka da Turarukan wuta , Humra masu shegen  kaushi . Abun Alfaharin kuma tana bada sar1 cikin sau ki, sannan kuma suna aikawa duk inda mutum yake afad in duniyar nan.?

Duk wacce ta siya magungunan Hajiya Nusaiba Dr B zuru, taga be yi mata aiki ba tazo za a dawo miki da kudin ki .?


KA DAN DAGA CIKIN ABUBUWAN DA AKE SIYAR WA



1?? Hadin amarya
2?? Hadin mai jego
3?? Hadin sabon budurchi
4?? Hadin Kaza Yar Suddan
5?? zuma -Tsumi- Tabaje da sauransu
6?? Turaren Sandal ruuu& flastic Sandal
7?? Hadin Hawwi domin inganta zafafiyar kauna
8?? Hadin bagadad,kahlij,kajiji,gafgaf dasauransu
9?? Hadin humra soyaya dole ta matan aure da normal humra

DON SAMUN  kARIN BAYANI KU NE META TA WANNAN NUMBER KAMAR HAKA :?
? ? 08133647913?
? ??
? ?KANO NIGERIA?

LOCATION: RING ROAD BAYAN G0DAN MAN NAZARGO.

? ? ? ?SIYAN NAGARI MAIDA KU DI GIDA

PAID BOOK


BOOK 2?
? ? ? ? ?S_____ 41
? ? ? ??

Jikinta ne yayi sanyi lokaci d aya ,bata san mai yasa tayi hakan ba itama , bata san dalili ba duk da bata da tabbacin abunda take hasashe a cikin zuciyarta .Cikin sanyin jiki ta furta  Am sorry Sunshine  , bai amsa mata ba sannan bai motsa daga yadda yake ba, so take ta zame  kasa kamar yadda yayi amma bai bata damar yin hakan ba gabaki d aya. ? Am sorry Sunshine  .ta  kara fad a a sanyaye tanajin wani saban kukan na shirin  kwace mata . Kusan mintuna biyu yana a hakan kafun ya mi ke ba tare da yace mata komai ba ya nufi dressing room d insa, cikin tashin hankalin ganin yadda ya shareta ta bi bayansa , tun kafin ta  karasa shigowa ya kulle  kofar.?

? ?Direct toilet ya nufa yana sakar wa kansa ruwa mai sanyi, ko damuwa da ya cire kayan jikinsa ba yayi, tun da ya lumshe idanuwansa ko motsawa ba yayi abubuwa da yawa suna masa yawo cikin zuciyarsa . A waje kuwa tunda taga ya kulle  kofar ta zame a bakin wajan tana raira wani saban kuka. Tun tana kuka tana shash she kar ta har barci ya d auketa a wajan ba tare da sanin ta ba .?

? ? ?Kusan tsawan mintuna 15 kafun a bud e  kofar , ganin yadda kanta yake  ko karin zamewa  kasa yayi saurin tare ta , daman ba baccin dad i ne ya d auke ta ba shiyasa yana ta batan ta bud e ido cikin sauri.  Am sorry.. ta fad a cikin rawar murya kamar mai shirin sakin kuka , idanuwansa ya lumshe mata kusan tsawan seconds kafun ya furta  it s okay, let s sleep off , yana gama fad ar hakan ya d auketa gabaki d aya ya fito da ita daga d akin zuwa d akinsa na sama , ko ina na wajan dumm light ne har lokacin kuma bata dena tsoran duhu ba shiyasa ta ri ke hannun rigar tasa sosai tana kulle ido. Bata san ya akai ba sai jin ta kawai da tayi akan lallausan abu da ko musu bazata yi ba tasan a kan gado ya d orata,bud e idanuwanta tayi ganin yana  ko karin sauka daga kan bed ta ri ko hannunsa cikin sauri  Dan Allah ka fad amun dagaske sune iyaye na ? Kamar yadda na soma jin labarin su a cikin diary? Dagaske Yaya Lil d an uwa na ne ? Dagaske kai d in Yaya na ne ?  Dan jiyowa yayi ya d an kalleta kafun ya matso da ita kusa da shi  zakiyi farin ciki? Hawayen fuskarta ta goge cikin sauri tana jinjina masa kai, hannu ya bud e mata ba musu ta fad a jikinsa , cikin cool voice d insa ya furta  Yes they re your family  . Yana jin yadda ta sauke ajiyar zuciya mai  karfi, a hankali ta furta  Dagaske kai Yayana ne , Yaya Bobo , Yaya Prince , Yaya Little duk Yayye nane , ina sanku duka amma su bana san su tunda nima basa sona , basu ta ba zuwa sun dubani ba, basu ta ba bani abinci ba  .  Dan d ago da face d inta yayi yana kallan yadda face d inta ya  baci da hawaye  kinasan sanin  karashen labarin ko? A hankali ta d aga masa kai . Hannu ya saka ya goge mata ragowar hawayen fuskarta  Then I will tell you everything tomorrow amma sai kinyi mun al kawarin bazaki sake kuka yanzu ba. Kanta Abla ta  kara jinjima masa tana lafewa a jikinsa . A hankali ya soma tapping bayanta, tun tana sakin ajiyar zuciya har bacci ya d auketa a yadda suke, d an  karamun iska ya fesar a bakinsa bayan ya tabbatar da baccin ya d auketa .
? ? ?
? ? Tunda bacci ya d auketa ya koma kan sofa sabida karya tasheta . Shi kad an sai faman shan coffee yake cikin daran ga jijiyoyin kansa da suka fito rud u rud u sabida yadda yake jin matsanancin ciwan mara , tun bayan fitar sa lokacin da ya barta , amma idan ba fad a maka akayi ba babu Wanda ya isa ya gane hakan ko ta kan fuskarsa ,sosai yake shan coffee har ya d auko allura zai yi wa kansa sai kuma ya fasa sabida al kawarin da yayi mata . He don t want to force a irin wannan lokacin shiyasa bai ne metan ba . Gabaki d aya daran nan bai runtsa ba sai ana daff da kiran sallahr asuba tukunna baccin  barawo ya d aukesa akan sofa d in, shiyasa lokaci d aya ciwan kai ya saukar masa .?

********His Excellency kuwa bayan fitar Big Boss da Bobo anan Little da Prince suka zauna wajan sa , shi kansa tunda ya shigo bai sake mararin fita ba balantana yayi marmarin cin wani abu. Su kansu su Uncle lokacin da suka zo cin abinci ba  karamun mamakin rashin ganinsa sukai ba amma babu wanda yayi  ko karin shiga cikin sashen da ko kusa basa shigansa.?

? ? ? A d akinsa suka zauna Little da Prince na bashi labarin yadda suke a America da karatun su da komai da Yaya Big Boss suke masu sai da suka bashi labari. Babu abunda yake yi sai murmushi , bai ji dad in yadda suka zauna tsawan shekarun nan babu mahaifi ko mahaifiya a kusa da su ba . Amma a wani  bangaran yaji dad in yadda suka samu tarbiya wajan yayyin su tare da kulawar Uncle da bazai ta ba mantawa ba, dan ba kowa ne zai iyayi maka wannan halarcin ba.?

? ?Suma su Little babu Wanda yayi tunanin komawa d akin su , gabaki d aya su ukun akan gadon sa suka kwanta tun suna labarin har suka soma bacci. Murmushi His Excellency ya saki kosai ganin ko wannan su yayi bacci sai yake ganin su kamar Farooq da Abdul d insa da suka  kanana suma .?
? Bai kwanta bacci ba sai alwala da yayi, sosai yake nafila yana  kara godewa Allah da ya bashi irin ganin wannan ranar da bazai ta ba mantawa dashi ba . Ya dad e yana sallar kamar bazai idar ba . Sai da ya kwashe sama da kusan hour 2 yana nafilfu kafin ya tsagaita sabida  kafafuwansa da yaji suna  ko karin ri kewa. Blanket ya soma  ko karin gyara musu ganin yadda ya zame ga sanyin Ac da yake ratsa ko ina na cikin d akin. Cikin bacci Little ya bud e idanuwansa , a sanyaye ya furta  Abbu? Shafa kansa Abbu   Dan abbu ? Ya fara yana kallansa ,  kazo ka kwanta da mu ?please  , farin ciki ne ya bayyana akan fuskar sa sosai amma duk da hakan sai da ya  kara maimaita  zaka kwana dani? Kansa Little ya jinjina masa da hannu ya nuna masa tsakiyar su , ba musu His Excellency ya kwanta a wajan, hannunsa d aya Little ya kama , a sanyaye ya furta  Ina sanka Abbu , sai kuma ya lumshe idanuwansa ya cigaba da baccinsa , hannun nasa Abbu sunbata kafin ya furta  Nima ina sanka Auta na . A haka sukai baccin su ?rungume da juna kamar wasu abokai, lokaci zuwa lokaci yana sauke ajiyar zuciya sabida dad in baccin da yaji wanda ya d auki tsawan shekaru bai yisa ba tun bayan  batan su.?

***** Rashin fitowar His Excellency cin abinci kamar yadda ya saba


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login