Showing 288001 words to 291000 words out of 347251 words

Chapter 97 - Ibtissam Book Two Complete Hausa Novel

Mrs Lee   

21 Oct 2025

1446

face d inta tana juyowa wajan sa  Ni ai bakayi mun laifi ba  ta  karasa maganarta tana ja masa hancin sa cike da d an mugunta , shima hannu yasaka zai ta ba hancinta tayi saurin  boye fuskarta a jikinsa tana dariya  kasa  kasa . Hugging d inta Big Boss yayi kafun ya furta  What s your biggest fear? Yana fad a mata hakan sai taji zuciyarta ta buga da  kirfi tsoran wani na shiga cikin zuciyarta da bata san ko na mene ne ba . Cikin sauri ta d ago fuskarta tana kallan tasa da ya d auke  My Biggest fear? Ta  kara nanatawa , kansa ya jinjina mata a wannan karan maimakon ya amsa mata  Bana so ka tafi ka barni , baba so kayi nesa dani, just don t leave me alone , sai kuma cikin muryar kuka ta furta  I can t leave without you ,?
?  Ya Allah ! Shine abunda ya shiga cikin zuciyarsa , so yake yayi controlling kansa amma tana san fallasa abunda ke cikin zuciyarsa , shiyasa bai tsaya ba ya d auketa gabaki d ayan suka nufi toilets tana hannunsa.

***** Suna fitowa daga wanka tare suka shirya abunsu, zai fesa turare ta furta  wait  zata matsa ya hanata sai turaren da ajje ya d auki irin nata ya saka  Yanzu fa? Ya fad a yana kallanta , da  yan yatsu ukun ta yayi masa alamar perfect tana d age masa gira . Girgiza kansa yayi kad an tare da pecking d inta  I want to go somewhere now , naje ko karna tafi ? Yadda yayi maganar Abla ba shiri ta soma dariya sai kuma ta tsaya  Nima please zanje wajan su Fanan kaji? Lumshe mata idanuwa yayi kafun ya furta  karki dad e amma , let s go , da haka suka fito daga da kin har suka fito part d in , hannun su sar ke da na juna . Part d in su Ammi suka nufa lokacin Abbi na cikin falourn shida Ammi , cikin sauri Abla ta zare hannunta , tana nufar Abbi.  Aby barka da rana  , kallanta Ammi tayi  sannu masu Abby mu kuma ko oho ko? Allah yasa wata yarinya tace tanasan abu , marairaice fuska Abla tayi tana kallan Abby  Rabu da ita , kina da Abby wa ya isa ya ta ba mun ke, ko me kike so just tell me zan sa a kawo miki  cikin sauri ta furta  Dagaske ? Kansa ya jinjina mata yana murmushi , ita shaf ta manta tare da Big Boss suka shigo  Abby zansha Ice cream da Youghurt  kallan side d in a Big Boss yayi ganin yadda ya murtuke fuskarsa , zuru zuru tayi da idanuwa ganin kallan da ya jefa mata , cikin sauri ta furta  No ! Abby na fasa bana sha , an hanani shan abu mai sanyi , Ammi ce ta kalli Big Bo_s  Rabu dasu Son, ka zauna mana  , girgiza kansa yayi  No Ammi , zance wani waje yanzu , amma idan na dawo zan zo nayi dinner . Uncle I m off . Ya fad a yana juyawa . Kallanta Uncle yayi  Daughter jeki raka mijin ki maza a sanyaye ta mi ke ta fito itama lokacin har ya shiga mota antayar, tana ganin motocin sun soma tafiya taji hawaye suna sakko mata , hannunta duka biyu ta saka ta rufe fuskarta zata juya a guje Big Boss da ya fito daga motar ya ri ko hannunta  Becareful , ya fad a a hankali, cikin sauri Abla ta kallesa  Sunshine am sorry kaji bai amsa mata ba sai hawayen da ya g?e mata  bana san kuka fa , bana hanaki shan kayan sanyi ba ? Mai yasa kike so Uncle ya siya miki? Cikin sauri ta girgiza masa kai  Bazan sha ba I promise , na dena , hancinta ya d an dalla  okay fine , ki koma ciki yanzu  , kanta ta jinjina masa a hankali zata juya ya kuma tsayar da ita  list anything you want amma banda kayan za ki da sanyi  . Shiru tayi sai kuma ta furta  kad an fa nake so , yawwa sai capri-sun ?
? ? ? okay fine Bobo zasu kawo miki, take care , kanta Abla ta jinjina masa, sai da yaa wucewarta tukunna ya shiga mota suka bar wajan shima .?
? ? ?Abla tana shiga falourn ta furta  Ammi na Harararta Ammi tayi ? wannan ne kuma baki isa ba , da kika shigo wajan Abbyn ki kuka nufa , dan haka nima babu ruwana dake  , kamar zatayi kuma ta furta  Abby , waje ya nuna mata  Don t worry , tana kishin mune, don t mind her  , murmushi sosai Abla tayi , mi kewa Ammi tayi ta nufi kitchen , sai kuma ta dawo d auke da wani bwol ne kyau da spoon  gashi ba daban halin ki ba  , ta fad a tana mi ka mata had in zogalan da tayi mata , Abla har da  yar dariya lokacin da ta amsa tana godewa Ammin, spoon d in farko Abby ta kaiwa baki , sai ya girgiza mata kai  Please Abby . Ta fad a tana mi ka amsa spoon d in , ba musu ya bud e bakinsa ta saka masa spoon d in zogalan, yana soma taunawa ya furta  ?daughter you have sweet hand , kinji yadda d and anan ya banbanta? Dariya Abla tayi tana satar kallan Ammi da ta share su, da kansa Abby ya kar bi zogalan yasoma bata a baki, sai da tac1 sosai tukunna ya  kyaleta . Abla ta dad e a sashen su tana hira da su Abbu , har saida akayi sallar azahar bayan tac1 abinci ta g?d? wajan su Fanan , da tun da ta doso wajan ta soma jin  kamshin turaran da ake musu gyara dashi, tana shiga tayi saurin jan baya tana toshe hancinta  idan  kamshin ya ragu zan dawo but not now  , ta fad a tana fita daga d akin da sauri . Su Fanan kuwa yau ba  karamin gyara suka shaba , dan sosai su Hajy Noori suke gwangwaje su.

Abla tana sakkowa  kasan ta had u da Sauban da Bobo da suka shigo falourn yanzu. Tana gaishe su Bobo yayi saurin furta  ina Ammi da Mamy? A hankali Abla ta furta  Ammi tana part d inta , Mamy kuma ina tunanin tana d aki dan yanzu zan shiga wajanta . Tana kallan yadda suka wani saki ajiyar zuciya kusan a tare , Sauban ne ya furta  Sister s d inki fa? Yanzu ma reply tayi musu da suna sama , kallanta Bobo yayi  Sister can you do me a favor ? , kanta Abla ta jinjina masa da sauri ,  Called your sister for me , zan jira ki anan corridor d in kinji? Abla kamar zatayi dariya ta jinjina masa kai , Sauban kasa magana yayi sai  keya da yake ta  bawa  bari na kira muku su ta fad a tana juyawa .

Abla tana shiga d akin taga suna binta da idanuwa , kallan Eshaal ta somayi  kizo inji Ammi , bata bari sun bata damar magana ba tayi saurin fita , kallan juna sukayi sai kuma ta kalli jikinta ganin towel ne kawai, hijab d inta Fanan ta nuna mata  Ga hijab can , ki saka mana kawai kije ki dawo tunda Ammi ke kiran ki . Kanta Eshaal ta jinjina , bata kawo komai cikin ranta ba , ta fito daga d akin cikin dogon hijab d in Fanan. A kan step ta tarar da Abla , zatayi magana Abla ta soma tafiya sai da suka sakko tsakiyar Falourn tukunna Abla ta dafe goshinta  kash namanta aushe har da Baby Ammi tace na kira sai kuma ta kalli Eshaal ,  Ammi tana corridor d in can , kawai ki  karasa kar mu barta tana jira ni kuma bari na koma na kira Baby , ?toh kawai Eshaal tace mata tana nufar corridor d in , dan duk a tunaninta Ammin ce a ciki kamar yadda Abla ta fad a .

Tana shiga sai ta tarar da ba Ammi, duk a tunaninta Ammi tana can ?1k1 ne shiyasa itama ta nufi cikin, har kwanar da zatayi a wajen kawai taji an janyota, baki ta bud e zata  kwala ihu yayi saurin rufe mata bakin , dai dai saitin kunnanta ya furta  Ni ne a jiyar zuciya Eshaal ta sauke fahimtar ko wane ne , sai kuma bugawar da zuciyarta ta somayi da Sauri Sauri ganin yadda ya ri keta sosai gashi ko  kwa kw kwaran motsi ta kasa . Cikin sar kewar harshe ta bud e bakinta  ina.. ina wuni , Bobo bai amsa mata ba sai kallanta da ya tsaya yi hakan yasa gabaki d aya ta soma jin wani irin a jikinta . ? kinyi kyau ya fad a kamar wanda ake masa dole . Cikin sauri Eshaal ta furta  Ammi tana kira na..  kin sakinta Bobo yayi ganin tana  ko karin kawar da kanta gefe ya furta  Look at me   kin kallansa tayi kamar yadda ya fad a , ba zato ba tsammani ya saka hannunsa a  kugunta , a tsorace Eshaal ta d ago tana kallansa , jikinta har ya soma rawa , lips d inta sai motsi yake , hakan kuma ba  karamin jan hankalin sa yayi ba shiyasa ya  kara rungumota cikinsa , dan tun a ri ke war farko da yayi mata ya fuskanci babu kaya ajikinta . Eshaal kamar zatayi kuka ta furta  Ni ka sake ni, Ammi na kira na  , le kowa fuskarta yayi tayi saurin kaucewa ,  kara kallanta yayi ganin yadda ta tsorata  tsoran me kike ? Ko bakiji abunda Abbu ya fad a ba ? You re now my wife , I can do anything to you now, kamar haka , ya soma ri ke hijab d inta ,cikin sauri Eshaal ta ri ke hannunsa tana kallansa  kayi ha kuri please , sakin hijab d in yayi kamar yadda ta bu kata  na ha kura amma ki kunna wayar ki, if not yau a d aki na zaki kwana , and i mean it, kinji? Cikin sauri ta jinjina masa kanta  zan kunna , murmushi yayi tare da furta  Good Eshaal kamar zatayi kuka ta furta  Su Ammi sun hana mu fita kuma zasu iya zuwa yanzu kanshi ya jinjina mata tare da sakinta , babu shiri ta juya zata saka g?d? ya ri kota , d an zaro ido Eshaal tayi batayi aune ba ya had e lips d in su , a tsorace Eshaal ta soma kokawar  kwace wa amma  karfin su ba d aya ba , sai da ya sake ta tukunna ta saka g?d? ba tare da ta  kara waiwayo wa ba , shi kuma kasa motsawa yayi daga inda yake sai jingina da yayi da jikin bangon wajan yana lumshe idanuwansa.

***** A  bangaran su Baby ba haka Abla taje ta kira ta wai Mamy na kiranta , Hijab d inta Baby ta saka ta sakko  kasan tana d an wa ka  kasa  kasa abunta . Tana sakkowa ta tarar da babu Mamy , har zata nufi d akinta sai kuma wuce na su d akin , tuno a can tabar wayanta , tana shiga ta tu be hijab d inta tare da hawaye kan gado tana rufda ciki , ?dai dai lokacin da take  ko karin kunna wayarta, bata san da shigowar mutum ba sai ji tayi an zauna a gefenta, a rud e ta juyo, Sauban data gani a gefenta ne ya  kara tsoratar da ita , cikin sauri ta zabura zata mi kewa ya ri ko hannunta , hankad ashi tayi ta zata saka g?d? ya janyo baya tare da d ora ta kan gadon, tana  kasa yana samanta gudun karta g?d?, tsu ke fuskarta Baby tayi  Ni fa ba yar iska bace , kuma wallahi sai na fad a ka shigo mana d aki , d an waro idan sa yayi kad an Jin abun tace ? Mai yasa kika kashe wayar ki? Ya fad a yana kallanta ,  bata fuska Baby tayi sosai , Nidai ka sake ni bana so. Ta kuma fad a murmushi yayi mata yana sakar mata nauyinsa , Baby kamar zatayi kuka ta furta  wallahi kai da Allah, kasan dai ba kyau ko? Allah kuma .. katseta yayi ta hanyar furta  bakin ki baya shiru ko?  Dan murgud a bakinta tayi kafun ta furta  toh ka sake ni sai nayi shiru ko kuma na fad awa su Mamy ka matseni  murmushi yayi sosai akan face d insa , kafun ya saka hannu ya fusgi towel d inta , zatayi magana kuma ya had e lips d insu , a tsorace Baby ta soma zare ido ganin abunda bata ta ba gani ba , wani irin futsarin tsoro ne taji yana  ko karin sakko mata , bata gama rud ewa ba saida taga ya saka hannunsa akan breast d inta , da iya ragowar  karfin da yayi mata saura ta bige masa hannun tana kare  kirjinta , ganin ya ki sakar mata le be ta gantsara masa cizo, yana sakinta a guje ta shige toilet tare da saka lock , kwanta wa yayi akan bed d in yana maida nunfashi, tsokanar ya so yi amma sai gashi ta barsa da aiki, dan lokaci d aya ciwan mara ya saukar masa ,wani irin feelings na bu katar tane ya soma masa yawo cikin jiki, da  kyar ya iya saita , amma duk da hakan bai fita sai ya nufi sai tin toilet d in yadda zata jisa ,  ki kunna wayar ki, zamuyi magana anjima , if not abunda nayi yanzu wani daban zanyi anjima  yadda yayi magana kamar wani d an maye , a haka ya bar d akin, ita kuma Baby saida ta  kara kusan 10 minutes a toilet tukunna ta re ko zufa duk ta tarar mata a fuska , kamar zatayi kuka ta furta  wallahi Abla ke da Allah tunda iskanci daman kika kawo ayi dani ,ita kad ai sai mita take , tana  ko karin d aukar wayarta taji kamar har yanzu yana kissing d inta, inda ya zauna ta soma harara kamar ance mata zata ganshi a wajan.?

Abla kuwa tana gidan Baby sai ta g?d? d akin Mamy tayi zaman ta gudun ma kar ta had u dasu, ita kad ai sai faman dariya take cikin zuciyarta.

****** A d akin su Harry gabaki d aya kusan jiya basuyi bacci ba shiyasa ko da aka kira meeting suka  ki zuwa tsabar ba kin cikin da yake cin zuciyoyin su. Dadyn Harry sarai yana sane da abubuwan da suke , kallan su kawai yake kamar baisan sunayi ba , harta gyaran jikin da suka  ki tsayawa ayi wa Harryn duk ya sani, gobe kawai yake jira dan duk haukanta gobe sai ta tare a gidan mijinta .?

******
Ana sallar magrib Abla ta koma d akin da su Fanan suke , wani irin harara Baby da Eshaal suka soma yi mata , duk yadda taso ri ke dariyar ta sai da ta  kwace mata , shiyasa ta _akasu a gaba sai faman dariya take ,  kara  kuluwa Baby tayi ganin yadda take musu dariya, Eshaal ba a  kufule ta soma harararta, tsura musu idanuwa Arwa da Fanan sukai kafun su furta  wai me akai musu? Tunda suka dawo sai faman kukkun bura suke su biyu  kara kwashewa da dariya Abla tayi tana d aga hannunta sama  Nidai babu ruwana wallahi, kawai dai.. Eshaal ce ta tsayar da ita ta hanyar furta  Kawai dai me? Ido d aya Abla ta kashe mata tana d aga mata ido d aya , d auke idanta Eshaal tayi daga kanta ganin wayarta ta soma haske ,  My Love shine abunda ya fito a cikin wayar, tsoran kalamansa da ya fad a d azu ne ya saka ta d auki kiran, Daidai lokacin itama da Baby aka kira ta awaya , amma amaimakon ta d aga kiran sai ta saka ta a silent , kallanta Abla tayi  Mai yasa bazaki d auka ba? Share ta Baby tayi tana  kara tsuke fuskarta . ?Shigowar Mamy ne ya hanata Abla furta abunda tayi niyar furtawa  Kuna yin sallar isha i kuje ku kwanta dan za ayi ba ki and gobe da wuri za ayi muku henna da saloon kafun a tafi dinner okay ? Fanan ce ta furta  Dinner kuma Mamy? Ta mece ce ? Katseta Mamy tayi  idan goben tayi kin gani , kin dai ji abunda nace


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login