Showing 27001 words to 30000 words out of 300844 words

Chapter 10 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2031

dakin take chocking mutane".

Hussain da kansa ya hada wa Hassan ruwan wanka sannan kuma ya taimaka masa yayi wankan yadda ruwa ba zai taba sannan suka fito ya kuma taimaka masa gurin shiryawa a tsanake ya saka kayan da Safiyya taje gida ta dauko masa. Sannan suka kuma saka shi ya sake cin abinci duk da cewa da kyar yake hadiya saboda yuwansa yana yi masa ciwo sosai.

Hassan yace "ina fita daga nan zan fara shirya mana tafiya waje, gwara muje can a duba ka sosai" Hassan yace "ni da zaka bi ta tawa da ka bar maganar tafiyar nan. Babu abinda doctors din mu nan nan ba zasu iya bafa, wadansu daga cikin su fa su suke aiki a can din" Hussain yayi murmushi cikin rada yace "ai ba dan asibiti nake so mu fita ba, dan ka samu ka huta ne sosai. Anan yan dubiya da yan jaje ba zasu barka ka huta ba" Aunty ta dago kai daga zubawa Khadijah abinci tace "me kake cewa?" Ya shafa kansa Yace "babu komai Aunty, cewa nayi abincin yayi dadi sosai".

Daga baya ne Hassan ya basu labarin duk yadda lamarin ya kasance, briefly ya gaya musu irin zaman da yayi a hannun kidnappers din da kuma yadda suka yi jiya. Hankalin Aunty ya tashi jin Salisu ne a ciki, yammatan suka fara masifar sai sunci ubansa, Hussain yace "wanne uban nasa zaku ci bayan ubansa yana lahira? Shi kuma yana police station daga can za'a kai sji court sannan a wuce dashi prison, me zakuyi masa wanda Allah bai riga yayi masa ba? Daga nan Hassan ya basu labarin haduwarsu da Ruqayyah da yadda ta saka rayuwarta a cikin hatsari dan ta taimaka masa. Duk jikinsu yayi sanyi sosai, suka kuma jinjinawa kokarin ta. Aunty tace "tabbas alamu sun nuna cewa yarinyar ta kirki ce, tunda bata san ko kai waye ba, zata iya kasancewa kai mugu ne da zaka iya cutar da ita ko ahalin gidansu. Wannan shine taimako na gaskiya, ka taimaka wa wanda baka da tabbas din shi zai taimaka maka" Hassan ya gyada kai yace "tabbas, tunda ba sani na tayi ba ballantana muce tayi ne dan ta samu wani abu a gurin mu" duk sauran suka amince amma banda Hussain, har yanzu maganar bata kwanta masa na, yace "tunda naji kace talakawa ne sosai ina ganin abinda za'a yi in mun dawo sai a kira babanta a samu wani abu mai kyau a bashi, yadda zai samu jari, ko kuma ita a bata scholarship tayi karatu" Hassan ya girgiza kansa yace "ba haka za'a yi ba, aurenta zanyi, sometimes money is not always the solution, kudi in muka basu zasu iya karewa amma aure, hada jini, babu yadda za'a dawo dashi baya"

Hussain yace "exactly my point, babu yadda za'a yi undoing aure, ko an rabu tambarin yana nan, shi yasa ya kamata ayi dogon tunani da dogon nazari kafin ayi shi. What if suna da wani aibu, wani ciwo ko wani tambari marar goguwa? What if da akwai wani hidding halinta ko na iyayenta wanda ba'a sani ba? What if a cikin rescue mission din nata akwai wata hidding agenda da bamu sani ba?"

Hassan yace "shi yasa nace zan aureta, ni Hassan, bance Hussain ya aure ta na. Ko ma menene a tare da ita it will be my burden not yours"

Suka tsaya suna kallon kallo

Aunty tayi tagumi tace "zaku tsaya in yi magana ne ko kuma ba kwa bukatar jin ta bakina? Yanzu ku shirya ku tafi inda zaku je ku huta din kar a dame ku. Kafin ku dawo zan nemi gidan inje da kaina inyi musu godiya daga nan zan ga yarinyar zan kuma ga iyayenta, sannan zan san abinda za'a yi musu" ta juya tana kallon Hussain tace "su kuma wadanda baka son su zo su dami dan uwanka yanzu zanyi musu yawa su zo su ganshi, tunda ya bata suke garin nan kuma babu yadda za'a yi ace an ganshi kuma har ya bar kasar ba tare da sun ganshi ba. Daga nan ta dauki waya ta fara sanar wa da jama'a, kafin laasar Asibitin ya cika da yan dubiya da jaje.

Washegari gimbiya tazo da safe, bayan ta duba Hassan ta kuma zuba masa lafiyayyen girkin data shiryo masa tun daga kano wanda duk masu ruwa ruwa ne yadda zai ji dadin hadiya, duk kamewar Hassan sai daya yaba mata da girkinta sannan yayi mata godiya. Daga nan sai suka fita ita da Hussain tana tayashi shirye-shiryen tafiyar su shida Hassan. Sai da suka gama komai sannan ya kaita airport shi kuma ya koma gida.


Two Day's Later

Ranar Monday, kwana daya da tafiyar Hassan da Hussain India inda Hassan zai ga likita kuma zai samu ya huta sosai. A ranar ne su kuma su Ruqayyah bayan sun taso daga makaranta as usual Ruqayyah ta fito daga taxin tana mita. "Allah kaɗai ne yasan irin gajiyar da nayi wallahi. Yunwar da nake ji kuwa ina jin zan iya cinye abincin da akayi a gidan mu gabaki daya" Sumayya ta fara kokarin fitowa tana kuma zaro Naira dari a aljihun rigarta. Ta juya tana mikawa drivern sai taji yace "ki bata, ta sayi awara ta kara akan abincin dan ya ishe ta" tayi dariya yayin da Ruqayyah ta juyo da niyyar juye wa mai maganar kwandon bala'i, suka yi ido huɗu da drivern ranar nan. Ta bude ido tare da cewa "kutumelesi! Dama motar ka muka shigo?" Ya daga kafada kawai yana murmushi, ta juya gurin Sumayya da take dariya tace "da haɗin bakin ki muka shigo motar sa ko? Ya akayi ban gani ba?" Sumayya tace "nima sai da muka shiga sannan naga shine, nayi kokarin nuna miki ke kuma kina can kina yiwa yarinyar data taka miki kafa bala'i dan haka na rabu dake kawai" Ruqayyah ta kalle shi taga har yanzu murmushi yake yi sai taji tamkar ta kama kyakkyawar fuskarsa ta goga ta akan kwalta. Ta juya ta bar gurin tana maganganu kanana kanana.

Adam yace da Sumayya "sister dinki drama queen ce" ta gyada kai tace "sosai. But she is not as bad as she always acts" yace "Allah yasa, dan nasan ke kullum tare mata zaki ke yi, kullum kina side dinta ko?" Ta sake gyada kai tace "yes, bayan Inna da Baba bani da wanda ya kaita. Komai zafinta dole ita din tawa ce, she is a side of me that I can never get rid of. In babu ita to babu ni kuma ba zan........." Ya daga mata hannu "bla bla bla. Naji, amma nasan kinsan cewa bata da kirki, wannan side of her din kinsan dashi fiye da kowa" ta fito daga mitar tana kara mika masa kuɗin hannunta "ga kudin ka Adam. Mun gode" ya jefa mata murmushi "ki siya wa sister dinki awara, tunda ta riga ta gama debe wa abincin gidan ku albarka ko zata cinye ba zata ko shi ba" ta rufe masa kofar sannan ta jefa masa kuɗin ta window ta juya tabi bayan Ruqayyah ba tare data kuma cewa komai ba. Ta sani, tabbas tasan Ruqayyah bata da kirki amma kuma it hurts her in taji wani ya fada, kullum tana wa Ruqayyah addu'a, kuma bata taba barin tayi wani abu marar kyau ba tare data yi kokarin gyara mata ba. Kuma sosai tana ganin gyaran, gashi nan ta fara chanzawa, gashi nan ranar nan har ta kusa rasa rayuwarta saboda taimakon wani Allah.

Ta tarar da Ruqayyah tana kokarin shan kwana, har yanzu mita take yi amma kuma daga dukkan alamu ba wai mitar mai taxi take yi ba kuma, mitar wani abun ne na daban.

"Mutane yanzu basu san a kyautata musu ba, shi yasa taimako yake da wahala, in ka taimaka ma babu abinda zaka samu" Sumayya ta kalle ta tana girgiza kant cikin takaici tace "shi taimako in dai kayi shi dan Allah ai baka bukatar komai daga gurin wanda ka taimaka wa" Ruqayyah tace "ko godiya? At least dai ai yazo yace min thank you for saving my life ko?" Sumayya tace "Rukee kenan. Kina kallon dai yadda aka fitar dashi daga gidan mu cikin jini, na tabbatar asibiti za'a wuce dashi kuma na tabbatar har yanzu yana asibitin, bai kamata ace har kin fara mita ba, kuma ai yayi miki godiya tun kafin ya bar gidan mu" Ruqayyah tace "wacce godiya yayi min? Ni me yace min ma in banda kira kamar tsohon makaho, 'Hassana" ta fada cikin kwaikwayon muryar Hassan, Sumayya tayi dariya ita kuma tayi tsaki, "bai san yadda na tsani a ce min Hassana ba, Baba ne kawai yake fada shima kuma dan babu yadda zanyi dashi ne".

A lokacin suka sha kwanar gidan nasu, abinda suka gani a kofar gidan ya saka su taka burki cikin mamaki, suka rike hannun juna, Sumayya ta rada wa Ruqayyah "ga mutumin naki nan yazo godiyar" Ruqayyah tace "ni Companyn sa nake so ya bani daya".

Manyan motoci ne guda biyu a kofar gidan, irin motocin da ba a kan kowanne titi su Ruqayyah suke ganin irin su ba. Ga kuma wadansu bakaken mutane masu bakaken kaya da bakaken tabarau a tsaye a gaban motocin, twins din suka rakube suka wuce su suka shiga gidan suna masu hada baki gurin yin sallama.

Babbar tabarma ce wadda Ruqayyah ta tabbatar aro wa aka yi daga gidan su Minal a shimfide a tsakar gidan, akan ta akwai wata mata wadda idan gaskiya za'a bi zata iya girmar Inna ade amma a kamanni zata iya cewa Inna ade ta haife ta. Kana ganinta kasan cewa naira ta zauna mata. A tare da ita akwai yammata, su biyar reras, wadansu farare wasu bakake. A gaban su da tray shima da aka aro a gidan su Minal aka siyo pure water mai sanyi guda goma aka zuba akai.

Daga gefen su karamar tabarma ce wadda tasu ce ta gida, akanta Baba ne tare da Inna Ade fuskokin su dauke da faffadan murmushi. Gabaki daya jama'ar gurin suka amsa musu sallamar. Inna Ade tace "yauwa, gasu nan ma sun dawo" Aunty tana kallon yan biyun da suke karasa shigowa tsakar gidan tace "tubarkallah masha Allah, ashe suma yan biyu ne?" Inna Ade ta sunkuyar da kanta tana murmushi. Hassana tace "Kai! Amma fa kyawawa ne, wacece takwarar tawa?" Inna Ade ta dago tana kallon ta tace "kuma yan biyu ne?" Hassana tace "a'a, ni suna kawai naci, yayyen mu maza ne dai yan biyun. Shi wanda kuka taimaka shine Hassan, akwai hussainin sa".

Daga dan nesa su Ruqayyah suka durkusa suna gaishe da bakin. Duk suka amsa da fara'ar su. Aunty ta miko hannunta, ku zo kusa dani ku zauna kunji yayan albarka? Wacece hassanar a cikin ku?" Da sauri Sumayya ta nuna Ruqayyah itama Ruqayyah ta nuna Sumayya. Duk aka kwashe da dariya. Inna Ade tace "Ruqayyah ki amsa mana anayi miki magana" Ruqayyah ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da tsinke a kasa tace "na'am" Aunty ta taso da kanta tazo har gabanta ta ruko hannunta tace "zuwa nayi har gida inyi miki godiya Ruqayyah. Nagode Nagode Nagode, Allah ya biya ki da gidan aljanna" duk sukace ameen banda Ruqayyah da take murmushi kasa kasa tana boye fuskarta.

Aunty tace "Allah yasa wannan abu daya faru ya zama silar zumunci a tsakanin mu daku zumunci na har abada. Dan mu kam abinda kukayi mana ba zamu iya biyan ku ba, bamu da kudin da zamu iya biyan ku fatan da zamuyi kawai shine mu hada jini daku idan kun amince. Shine kadai sakayya".

Bayan baƙin sun tafi, Inna da Baba sun tafi rakasu mota su kuma su Ruqayyah sun shiga daki suna cire uniform dinsu sai Ruqayyah ta daga labule tana leken waje tace "ni banga ana shigo da kwalayen ba" Sumayya ta ce "wadanna kwalaye kuma?" Ruqayyah tace "kina nufin wai hannu rabbana suka zo mana gida? Sai pure water din mu da suka shanye?" Sumayya tace "ho! Rukee. Wai duk bayanin matar nan baki fahimta ba?" Ruqayyah ta saki labulen tana kallon ta tace "wanne bayani fa? Ni ban fiye gane dogon bayani ba nafi son in ga aiki a aikace" Sumayya tazo ta kama hannun ta tace "ni abinda na fahimta daga bayanin ta shine kamar tana neman aure ne a gidan nan. Kamar tana nema wa wannan mutumin da naji sun kira da Hassan auren ki".

Ruqayyah ta saki hannunta tana kallonta dalala da baki cikin mamaki, she never thought it possible, ta dauka yana da aure sannan da jerin manyan yammatan da suke rushing a kansa, bata taba tunanin mutane irin su zasu nemi hada zuri'a da irinta ba shi yasa dam bata gane bayanin ba. Ita jira kawai take taga an miko.

Sai ta kama rawa tana juyi a dan karamin dakin nasu, Sumayya tana dariya cikin taya yaruwarta farin ciki. Har sai da hajijiy ata kama Ruqayyah ta fada kan katifar su tana birgima. Sumayya tazo tana janye kayan shanyar su data debo tana cewa "ni daga mana kaya kar kiyi masu squeezing ki kara min wahalar guga" Ruqayyah ta jawo ta ta fado jikinta tana cewa "ke ta guga kike yi? Yar uwarki zata zama matar CEO na H and H amm kina damun kanki da guga?" Sumayya ta mike zaune tana dariya tace "zata zama kika ce, ba wai ta zama ba. In banyi gugar ba ai ba zaki samu kayan sakawa ba in CEO din yazo ganin ki" Ruqayyah ta mike tsaye tana kallon kanta, ta dauko mudubi ta kalli fuskarta sannan ta ajiye tana cewa "farko aiki zan saka shi ya fara bawa Baba, Babban aiki irin wanda hatta yan Zariya sai sun san yarsa tayi babban kamu. Sannan sai in saka ya rushe gidan nan ya gina mana wani, irin gidan Alhaji Kabiru sabon kudi wanda aka saka tiles har a jikin bango. Kuma ginin hawa uku nake so, kasa su Zunnur ne zasu zauna tare da abokansu da suke kwana tare a shagon Bala, hawana biyu kuma inna ade da Baba, hawa na uku ni da Sumayya, sai im saka ayi min personal balcony a can sama inda zan ke hawa ni kadai ina kallon kowa a kasa na, ina kallon duk unguwar nan a kasa na, ina kallon kaduna a kasa na. And that, will only be the beginning"


Wannan littafin na siyarwa ne, wanda yake so ya nemi wannan number
08067081020

Twelve : A Kind Suggestion
Sumayya da tun da Ruqayyah ta fara lissafin ta take tsaye a bayanta rike da kaya a hannu baki a bude cikin mamaki, tasan yaruwar tata tana da dogon biri amma bata taba sanin cewa burin nata ya kai tsahon haka ba sai yau.

Gida mai hawa uku, balcony, kallon kowa a kasa, lallai Ruqayyah ta wuce duk inda Sumayya take tunani. Tace "Ruqayyah? Duk wannan lissafin kawai dan babarsa ta nuna tana so a haɗa ku? Tun shi bai ce yana son ki ba tun baku fahimci juna ba ballantana ayi zancen auren har kin fara lissafin abinda zaki samu daga gare shi? Tabbas zaki fara ginin auren ki akan tubalin toka dan kuwa shi aure ana gina shine saboda Allah ba wai saboda abin duniya da ake burin za'a samu ba"

Ruqayyah ta juyo tana kallonta, ita lissafi take yi a zuciyarta ba ta san cewaa fili tayi maganar ba amma so what? Waye baya son kuɗi? Kowa fa aka bashi daɗin su zaiji amma mutane da munafurci sai suke nuna wa kamar basa so.

Ta hade rai tace "shikenan kuma yanzu Sumayya mutum bashi da ikon ya fadi a binda yake zuciyarsa sai a sako shi gaba da wa'azi? Ni banga aibu dan mutum ya nemi duniya at the same time kuma ya nemi lahira ba. Shi yasa ake addu'a ana cewa rabbana atina fidduniya hassanatan wa fil akhirati hassanatan......." Sumayya tace "kyakkyawar rayuwar ake nema ba wai kudi ba Ruqayyah, kudi ba shine farinciki ba, kudi ba shine abu mafi muhimmanci a rayuwa ba Ruqayyah. Happiness. Ka zauna cikin farin ciki shine abinda ake nema, wannan kuwa baya samuwa sai da wadatar zuci ba wai wadatar aljihu ba, the more kina samun kudi da more kina kara jin cewa ya kamata ki samu wasu, amma in dama baki saba dasu ba You will be contented with the little you have. Ni wannan shine abinda na fahimta, wannan shine abinda nake so. Wadatar zuciya. Kuma su kudi a fahimtata sukan kawo rabuwar kawuna ne a cikin iyali. Idan family da basu da kuɗi kamar mu din nan zaki ga sunfi haɗin kai ana haduwaa rufawa juna asiri but the moment kudi ya shigo ciki sai kiga an samu rarrabuwar kawuna musamman idan wani bangare ne ya samu kudin wani kuma bai samu ba. Ni abinda nake gudar mana kenan. Ruqayyah bound din da yake tsakanin mu yafi min gida mai hawa ukun da kike buri"

Ruqayyah ta jawo ta jikinta tace "my darling sister, ba kudi ba, babu abinda zai raba tsakanin mu, duk inda zanje a rayuwa duk matakin da zan taka a rayuwa you will always be by my side, family na will always be y top priority, shi yasa a lissafin nawa Baba na fara sakawa nasan yana wahala damu" Sumayya ta zame daga jikinta tace "how can I be always by your side idan kika auri CEO na H and H? Zaku tafi ne unguwar masu kudi ya gina muku gida mai hawa biyar. Ni ma kuma dole zanyi aure, yanzu misali in na auri....... Na auri..... Na auri Adam drivern taxi yaje ya kama mana hayar gidan kasa kinga ai mun rabu kenan, banbancin yayi yawa"

Ruqayyah ta kuma jawota tace "sai in saka mijina ya gina muku gida a kusa da gidan mu ya baku kyauta dan mu zauna tare" ta hade rai tace "kuma ba zaki auri Adam ba, kar ki ma kuma saka shi a misali" ta fita ta tafi yin alwala tana mita "na tsani wannan gayen wallahi, he is so arrogant and rude, gashi shi ba kowan kowa ba amma in yana magana kamar yafi kowa" tayi tsaki "inyamuri kawai.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login