Showing 177001 words to 180000 words out of 300844 words

Chapter 60 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2093

amsa mata sannan ta gaishe da Hassan, itama tana lura da lalacewar daya sake yi. Sai da suka tafi sannan Aunty tace masa "ina jin ka, wanne dalili ne ya saka zaka raba uwa da yayanta ka kawo min su har da jariri?" Ya gyara zamansa yace "Aunty abubuwa da yawa sun faru wadanda baki san su ba, akwai abubuwa da yawa wadanda ban fada miki ba, kuma nayi haka ne saboda ina gudun bacin ranki musamman a yanzu da lafiya bata ishe ki sosai ba, kuma a yanxun ma ina so ki yi hakuri kar ki tashi hankalin ki akan duk wani abi da xan gaya miki, ki sani, tashin hankalin ki ba zai chanza komai ba tunda hannun agogo baya taba dawowa baya, da yana dawowa dana dawo dashi na chanja abubuwa da dama, da na chanja wasu choices da nayi a rayuwata. Amma kwantar da hankalin ki zai taimaka sosai wajen kwantar min da nawa hankalin, zai taimaka mana wajen hada kai mu samar da matsaya a lamarin mu"

"Abu na farko da bamu gaya miki ba shine tun lokacin da Hussain ya a da rai, tun lokacin da aka sanar dashi surgery din sa was not successful sai ya raba H and H biyu ya bani rabi, tunanin sa a lokacin shine kar in ya mutu Fatima ta haifi namiji ya kasance bamu da komai a cikin dukiyar sa, ban fada miki ba tun a lokacin saboda bana son ki san cewa Hussain bai warke ba"

"Abu na biyu da ban fada miki ba shine na siyar da rabin H and H, share din da Hussain ya bani tun yana da rai"

Aunty ta bude ido "ka siyar? Saboda me? Wa ka siyar wa? Me zaka yi da kudin?" Bai ce komai ba har tayi shiru tana mayar da numfashi sai ya kuma cewa "Aunty dan Allah kar ki tayar da hankalin ki, zan miki bayanin komai" sai data jera ajjiyar zuciya sannan tace "ina jinka" ya cigaba..

"Umar ne ya siya, yayan Fatima. Dalilin dabyasa na siyar kuma saboda tun a lokacin da Hussain ya bani nayi alkawarin in har ya kasance bai rayu ba to ni kuma ba zanci wannan kudin ba, zanyi masa sadaka dasu ne"

"Abu na uku da nayi ban gaya miki ba shine an raba gadon Hussain. Bana so in gaya miki dalilin da yasa na sa ayi rabon da gaggawa saboda bana so ki tashi hankalin ki har sai nayi solving problem din. Problem din kuma shine Ruqayyah" ta bude ido "Ruqayyah kuma? Menene hadin Ruqayyah da rabon gadon Hussain?" Sai kuma ta tuno da tarewar da Ruqayyah tayi a gidan Hussain, sai tayi shiru, sai ya dauko mata labari a nutse cikin hankali ya gaya mata duk abinda Ruqayyah tayi da wanda tace zata yi, da kuma shi abinda yayi. Aunty tayi mamaki kwarai da gaske, maganar kuma ta taba ta sosai musamman iƙrarin da Ruqayyah tayi na tarwatsa sunan Hussain, Hussain din da baiyi mata komai ba a rayuwarta dai alkhairi, amma yadda Hassan ya bi da maganar da matakin daya dauka ya saka tashin hankalin nata bai tsananta ba. Tace "tabbas Ruqayyah tayi asara Babba, tabbas rabata da yaran nan shine abinda yafi dacewa dan kamar yadda kace ita din guba ce, ita kuma halayya naso take yi sai wanda Allah ya tsare" Hassan yace "haka ne, wannan yasa na datse igiyoyin aure na da ita, duk ukun" Aunty ta dafe kai tana salati, yace "kiyi hakuri Aunty, bana jin zan bar duk wata alaka tsakani na da wadda zata iya yiwa Hussain wannan sharrin. Yaya Allah ya riga ya bani tare da ita, amma zanyi iya kacin kokari na wajen nesanta su da ita duk da cewa ba zan iya chanja musu uwa ba" Aunty ta jimanta abin, ita iyayen Ruqayyah take ji, mutanen kirki sai dai sunyi asarar haihuwar Ruqayyah. Amma kuma ta fahimci dalilin da yasa Hassan ya bar mata kudin daya gada daga Hussain tare da gidan Hussain din da take haƙo, wannan kadai zai koya mata darasin rayuwa, ko da badan ita ba ko dan ƴaƴanta dole zasuyi fatan Allah ya shiryeta.

Sai kuma Hassan ya mika mata wasu takardu daya fito dasu daga aljihunsa yace "ga wannan, kason su Hassana ne na daga gadon Hussain, ban siyar ba yana nan a matsayin share a kamfanin H and H wanda a yanzu yake a ƙarƙashin Umar da Ruqayyah. Zabin sune suyi duk abinda suke so suyi dashi" ta daga tana kallon rubuce rubucen jikin takardar, maganganu irin na lauyoyi da tasan ko ta karanta ba gane wa zata yi ba sai ta ajiye tana kallon Hassan tace

"kai kuma fa? What are you going to do?"

Ya rufe idonsa ya bude, wannan tambayar ta Aunty is a one million dollar question, me zaiyi shi kuma? Ina ya dosa a rayuwa? Ya girgiza kansa, "ban sani ba Aunty, a yanzu haka ban san menene matsayi na ba, ban san me zanyi next ba. Ki bani shawara dan Allah" sai tayi shiru tana tunani sannan tace "you need to start afresh, ka tattara duk tabbunan baya ka tura su bayanka ka manta dasu ka kuma rungumi gaban ka. Ba zaka iya mantawa da baya ba na sani amma ina so ka saka ta a wani bangare na zuciyarka wanda ba ko da yaushe kake bude gurin ba. You need to be strong for your children sake, for our sake gabaki dayan mu" sai ta mika masa takardar ta ya bata tace "ka karbi wannan ka kafa naka business din, forget about H and H, ka siyar da share din su Hassana suma, mun rasa Hussain da iyalinsa baki daya mun hakura babu abinda zai same mu dan mun rasa H and H" yace "Aunty wannan kudin yaran nan ne, in kuma suna da bukata fa? Besides, kuma kuma bukatar abubuwan amfani da yau da gobe, gidan nan yana bukatar maintenance, yara suna bukatar kudin makaranta, wannan kudin shine future din kowa, in na dauka na fara business dasu suka lalace yaya zamuyi kenan?" Sai tayi murmushi, wannan maganar daya fada exactly irin wadda ya fada ce shekaru goma sha uku da suka wuce lokacin da Hussain yake rokonta ta bashi gadon su ya shiga kasuwanci dashi, tace "Hassan kenan. Always the smart one. Muka bawa Hussain kudi ya kafa kasuwanci ma ballantana kai? Hussain din da yake kashe kudi tamkar wanda yake saka musu wuta ballantana kai da nake da tabbacin zaka adana su? Maganar yanuwanka kuma ina tuna maka cewa suma yanuwan Hussain ne kuma suna sonsa kamar yadda kake sonsa dan haka in suka ji abinda kayi da kudin daya bar maka murna zasuyi suji dadi, in kuma suka ji abinda ni kuma nayi da nasu kudin sai su kara jin dadi saboda kai ma dan'uwan su ne kuma suna son ka sosai"

Kar ka manta, tabbas Hussain ne yake biya musu kudin makaranta amma kai kaine kake tsaye a kansu a matsayin babansu, tun daga sec sch dinsu har jami'ar su kai kace fafutukar samar musu kuma duk wani abu da ake bukata na uba kai kake yi musu, wadanda suka yi aurea cikin su kai ka tsaya musu a matsayin uba Hussain kudin kawai yake fitarwa. Kar kuma ka manta cewa Hassana da Safiyya yanzu duk aiki suke yi, aiyukan kuma da kai ne kayi fafutukar samar musu, nan zuwa karshen shekarar nan muke saka ran Khadijah zata karbi certificate dinta a matsayin cikakkiyar likita, Nafisa tana shekarar ta ta karshe, Zulaihat tana shekara ta biyun karshe, to menene kuma ya rage wanda suke bukata? Allah yayi mana komai Hassan, mun gode masa kuma mun gode maka kai da danuwanka, ko Hassana kadai a yanzu zata iya kula damu kafin business dinka ya kafu, tunda mijin da kai ka zabar mata bai rage ta da komai ba kuma salaryn ta mai kyau ne. Maganar house maintenance kuma bana jin muna bukata, motocin nan da Hussain ya tara mana duk ka hada kansu ka siyar ka kara jari, ka bar mana guda daya ta ishe mu kaga an rage kudin maintenance da kudin mai, an kuma rage drivers, driver guda daya ya ishe mu mai gadi guda daya. Ina da kudade a account dina da kuke bani kai da danuwanka a matsayin kudin kashewa, babu abinda nake yi dasu sai ajjiya, suma zasu yi mana wani amfanin, yaran nan gaba ki daya babu wadda bata da personal kudi a account dinta, mai muke bukata kuma? Wacce daga cikin niimar ubangijin mu muka raina?"

Sai ta mike ta hau sama, Hassan ya bita da kallo sai gata ta kuma saukowa dawani karamin box a hannunta ta ajiye a gabansa tace "gwala gwala-gwalai nane da Hussain yake siya min duk sanda yayi tafiya, yasan yadda nake son gold shi yasa yake siya min a matsayin toshiyar baki dan kar inyi masa fada. Ka bawa Jabir naga yana harkar gold ya siyar maka ka kara dasu" ya girgiza kansa yace "Aunty ai kina son kayanki ko?" Tace "eh ina son su mana, shi yasa na baka ai saboda nafi son ka akansu. Kuma nasan in kayi kafuwar da nake so kayi zaka siya min abinda yafi gold ma ba gold ba. A yanzu so nake kayi kafuwar da Ruqayyah in ta kalle ka sai ta sake kallonka. Allah ya sa maka albarka a cikin duk abinda zaka yi, na yarda dakai Hassan, na tabbatar nan da shekara mai zuwa sai ka kai gurin da kai kanka sai kayi mamaki ba mu ba".

Yayi shiru yana mamakin Aunty da irin tarin kyautatawar ta gare su shi da Hussain, ko uwar data durkusa ta haife su iyakacin soyayyar da zata nuna musu kenan. Ya dauki takardun da box din ya mike zai tafi sai tace "Hassan, abinda Ruqayyah bata fahimta ba shine da family da kuɗi akwai banbanci mai girma a tsakanin su, in kana tare da family dinka babu irin matsayin da ba zasu tallafa maka taje ba, shi kuma kudi baya taba siyawa mutum family, amma nan gaba kadan zata gane" ya gyada kai yace "insha Allah Aunty. Nagode sosai. Thank you for your understanding, thank you for believing in me".

A ranar yayi waya ya bayar da kwangilar yin katanga tsakanin gidansa da gidan Hussain inda Ruqayyah take ciki. Washegari da sassafe suka fara aikin, shi kuma ya fita ya kaiwa Jabir akwatin gold din Aunty yace ya siyar masa, daga nan kuma sai ya tattara hankalin sa kachokan ya mayar kan harkar sadakar da yayi niyyar yi. Ba wai mutane ya tara ya rarrabawa kudin ba a'a sakawa yayi aka bincika masa ƙauyuka da unguwannin da suke fama da matsala ko ta rashin ruwa ko masallaci ko makarantar islamiyya ko harkar lafiya, wannan yayi tayi, abinda yasan zai zaman to sadakatul jariya ga Hussain. Boreholes an haka babu adadi, masallatai an gina an saka alquranai a ciki, an kuma gina islamiyyoyi da yawa an zuba duk littattafan addini an kuma dauki malamai, sai kuma ya koma asibitoci yana neman marasa lafiyan da ba zasu iya biyan kudin aiki ko siyan magani ba, duk da sunan Hussain, da fatan Allah ya kai rahama kabarin Hussain. Wannan abin da yake yi shi ya taimaka masa sosai wajan mantawa da Ruqayyah and all what she did, dan baya ma tunawa da ita sai yazo kwanciya bacci tukunna zaiyi ta juyi a gadonsa zuciyarsa tana kuna da kalaman ta wadanda har yau yake jin su tamkar mashi ne a kafe a cikin kirjinsa, tabbas ta riga tayi masa illar da ba zai taba warkewa ba. Yayi mata so iyakacin so ita kuma ta zalince shi iyakar zalinta.

Sai da abubuwa suka lafa sannan ya waiwayi Jabir da maganar gold, nan take ya dauko kudi da takardar lissafi tsaf na yadda ya siyar da kowanne, Hassan bai karbi lissafin ba kudin kawai ya karba yana jinjina yawan su, tabbas gwalagwalan masu matukar tsada ne, tabbas Hussain ne ya siye su.

Wannan kudin su ya hada da kudin gadon kannensa da suka bar masa, ya kuma hada da kudin da ya dade yana tarawa a banki inda yake ajiye rabin albashinsa na kowanne wata, jimillar abinda ya samu sai data bashi mamaki, amma sai dai har yanzu bai yanke shawarar abinda zai yi ba, shi ba Hussain bane ba, shi bai iya shiga abu sama ta ka ba, shi yafi gane ya zauna yayi tunani akan abu yayi bincike sannan yayi. Dan haka wannan karon ma haka yayi, yayi tunani yayi bincike yayi shawara sannan yayi addu'a. A karshe ya yanke shawara. Real Estate management.

Ya yanke wannan shawarar ne saboda fahimta da yayi cewar risk na asarar kudi a real estate market is very low, ko mutum bai ci riba ba to ba zaiyi asara ba in dai ba disaster ya hadu da ita ba kamar gobara, flooding da ire-iren su, ya gaya wa Aunty shawarar sa kuma ta amince da hakan ta saka masa albarka sai yaje ya sayi land babba, ya zagaye shi sannan ya fara gini, blocks guda shiga kowanne kuma sama da kasa, kowanne gida kuma three bedrooms da palo, tsarin gidajen kuma irin na zamani masu kyau da akayi da kayayyakin aiki masu nagarta, a cikin watanni shida ya gama komai, ya zuba duk abinda ake bukata a gidajen. Wannan itace estate dinsa ta farko wadda ya sakawa "Hussain Aminu Abdullahi Memorial Estate".

Ginin estate din nan sai daya lamushe duk tarin kudin da yake ganin ya tara dan har sai daya fara tunanin ya daga gidan sa ya siyar amma Aunty da sauran yanuwansa suka hana shi, suka sake tallafa masa sosai, daga mai siyar da sarkar ta sai mai siyar da motar ta a haka gini ya kammala. Suka shirya walima ta taya shi murna wadda aka hada tare da addu'ar shekara ta rasuwar Hussain, aka gayyaci yanuwa da abokan arziki aka hadu anan cikin Estate din aka gabatar da adduoi aka kuma ci aka sha aka gode Allah sannan aka zazzaga aka ga gidajen, a take aka fara kama hayar su, abin mamaki sati bai rufa ba duk an kame gidajen guda goma sha biyu. A ranar ne bayan an tashi Aunty ta saka shi ya mayar da Sumayya gida.

Babban kuma abinda ya jawo hankalin mutane kan gidajen bayan kyawun shine sunan da aka saka wa Estate din, kowa yasan Hussain Aminu kuma yasan taste dinsa bana banza bane ba.

Kudin da aka hada wa Hassan a matsayin kudin hayar gidajen sai yaga sun ishe shi siyan wani land din har da kafa foundation din wasu gidajen suma irin wadancan, dan ma dai abin ya hadu da bikin Khadijah wadda shi yayi mata komai da ya kamata uba yayi wa yarsa, sai kadan daga kayan kitchen wadanda ta siya da kanta tunda ta fara daukan albashi sannan kuma yanuwanta ma suka siya mata wasu.

A cikin shekara gudar nan Hassan went through a lot a zuciyarsa, yayi fighting sosai da soyayyar Ruqayyah, yayi fighting da impulse din da yake gaya masa ya shiga gidan da take ya duba jikinta, ya dai taba ganinta a bakin gate kamar tana so ta shiga gidan, tana jan kafa tana bin katanga, a take ya kira maigadi yace kar ya barta ta shiga, sai dai ganin nata ya taba zuciyarsa kuma ya gaya wa Aunty, tun daga nan dai yasan Aunty ta kan aika mata da yaran lokaci zuwa lokaci su ganta, bai taba tambayarsu ya take ba, bai kuma taba shiga shi ya ganta din ba.

Wannan kenan......

Sumayya, in ka ganta a cikin shekarar nan zaka kasa tantance wanene yafi shiga damuwa tsakanin ta da Hassan. Ta rame ta lalace ta fita daga hayyacinta, rashin Adam, tunanin halin da yake ciki shine yake hanata bacci, yake hanata karatu, yake hanata cin abinci, yake kuma hanata fara'a. Kowa ya santa ya san ta chanja. Tun a watannin farkon bayyanar gaskiya ta samu Inna Ade, wadda itama a lokacin duk ba'a cikin nutsuwar ta take ba saboda tunanin Ruqayyah. Ta zauna a kusa da ita tace "Inna magana nazo da ita dan Allah, ki daure ki dan saurare ni ko kadan ne" Inna ta juyo tana kallonta, bata jin dadin yadda yar tata take rauzayewa a guri daya tace "Sumayya wani abun kike so?" Sumayya tace "dama Inna akan maganar Adam ne, nace ko zaki dan yiwa Baba magana muji ko da akwai yadda zamu iya zuwa nemansa" Inna ta bude ido tace "nemansa Sumayya? A ina zamu neme shi? Kina ji dai Hassan yace yana tare da mahaifansa a can garin inyamurai, ta yaya zamu iya zuwa can mu neme shi?" Sumayya ta fara sharar hawaye, "ni zan iya zuwa Inna in kun barni, ko ku hada ni da Sulaiman, Inna dan Allah" Inna tana girgiza kai tace "Sumayya! Sumayya munsan kin damu da Adam kuma muma mun damu dashi, mun damu da musan halin da yake ciki, amma ba zamu barki ki tafi nemansa ba Sumayya, ko da a kusa yake damu ba zamu barki ki fita nemansa ba ballantana yayi nisa sosai, yana cikin mutanen da ba irin mu ba wadanda shiga cikin su zaiyi mana wahala" sai Sumayya ta kara sautin kukan ta, inna ta jawo ta jikinta tana lallashin ta "ba zan iya yiwa babanku maganar nan ba, ransa a bace yake har yanzu akan maganar yaruwarki, ga kuma alkawarin da yayi wa Hassan a kanki...." Sumayyan ta kwace jikinta, bata so ko zancen hadin su da Hassan ayi mata dan kullum so take ta gaya wa kanta cewa hakan ba gaskiya bane ba, in aka fada kuma sai taji yana so ya zama gaskiya. Tace "Inna Adam fa? Shikenan mun bar shi? Shikenan ba zamu taimaka masa ba?" Inna tace "Sumayya Adam jarumi ne, kuma islam ya zauna a zuciyarsa, bani da shakku a kansa, kuma indai har da gaske yana son ki yana kuma son auren ki zai samu hanyar da zai dawo zuwa gare ki. Shi yasan inda kike, ke kuma baki san inda yake ba dan haka shine ya kamata yazo


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login