Showing 87001 words to 90000 words out of 300844 words
forming a fuskarsa, yarinya ce Ruqayyah in ma laifin tayi kamata yayi ya gaya mata abinda tayi din ballantana shi yanzu ya fahimci babu laifin da tayi in banda fadar laifin Hussain. Wannan ne laifinta. Kamata yayi ya gaya mata cewa baya so a fadi laifin Hussain ba wai yayi fushi da ita ba.
Ya zagaye hannayensa a kugunta yana dora goshinsa akan nata, idonsa cikin idonta da yake cike da kwalla "am sorry Precious ki daina kuka kinji. Nine ko?" Ya kama kunnensa daya da hannu daya ya ja yace "wannan Hassan din baya jin magana tunda ya sa matarsa kuka" ta dan yi dariya kadan sai ya goge mata hawayenta yace "baki yi min laifin komai ba kinji? Raina ne kawai ya baci. Kema kiyi hakuri akan maganar drivern nan kinji? A hankali zanyi wa Hussain baya ni yadda zan gamsu da dalili na na korar sa" ta kwantar da kanta a wuyansa tana jin dadin kamshin shower gel din da yayi amfani da shi tace "ni na bar maganar ma ai, ina fata ne kawai kar Hussain ya gane when it is too late. Damuwa ta kawai ita ce kai mijina, ina tsoron kar drivern nan ya raina ka" Hassan ya danyi dariya yace "it is never going to happen kinji. Kar ki damu akan hakan" ya dagi fuskarta yana kallo yace "mutane suna tsokana ta wai ina kyallin angonci, they should come and see yadda fuskarki take haske kamar wata zahra" ta kwace fuskarta tana sake mayar da kanta cikin wuyansa, yace "daga ni to Madam in tashi in shirya" ta makale kafada "naki din. Kamshin ka dadi" ya kyalkyale da dariya yana komawa da baya yana kwanciya akan gadon, ta bi jikin sa ta kwanta itama, ya rufe ta da hannayensa yana sauke ajjiyar zuciya.
Hussain daga gurin Aunty shima nasa part din ya tafi. Part din gimbiya ya zarce ya shiga har cikin Bedroom dinta amma bata nan, sai ya dauki waya ya kira ta, ta masa tace masa tana gym, ya fita ya tafi can. A can ya same ta ta kunna slow music kan treadmill tana tafiya da dan sauri kadan, bata ji shigowar saba, shi kuma yayi amfani da damar gurin tsayawa yana kare mata kallo a cikin gym wears dinta yana lura da jikinta yake motsawa tare da kowanne motsin ta, gashin ta data tubke guri daya yana kwance akan kafadarta guda daya, bakin ta yana motsawa a hankali tana bin wakar da take tashi a gurin.
Ya danyi gyaran murya kadan sai ta juyo da sauri tana kallonsa, sai kuma tayi masa murmushi tayi amsa alamar ya taho da hannunta. Ya zo ya tsaya a gefenta yana kara bin jikinta da kallo, fuskarta ta nuna alamun jin kunyarsa, yace "what are you doing?" Tace "getting in shape for the honeymoon" yayi dariya, "wa ya gaya miki ana fafe gora ranar tafiya?" Ta bata rai "to ni bana son in munje kaga turawan da suka fini shape mai kyau" ya dora hannunsa akan plat cikin ta yace "ni ban taba ganin baturiyar da take da shape daya kai naki ba Fatima, in kuwa akwai to babu wadda nata ya wuce naki" ta harare shi tace "in akwai kuma fa" yayi dariya yace "bazan kalla ba, kona kalla ma ba zan gani ba" tayi masa murmushi tana slowing down har ta tsaya sannan ta kashe machine din, ya jawo towel a gefe yana goge mata jiki yace "daga gurin Aunty nake, Hassan fushi yake yi dani" ta juyo tana kallon sa tace "akan me?" Sai ya bata labarin abinda ya sani a game da Adam. Sai kawai yaga tayi dariya, ya bata rai "au dariya kike yi min ma ko?" Tace "ba kai kadai nake wa dariya ba, ku biyun nake yiwa dariya da har kuka biye wa Ruqayya. Ruqayyah fa? Ruqayyah ai yarinya ce, sa'ar Zulaihat ce fa aka ce. Yarinta ce take damunta bawani abu ba kuma shima kansa Adam din da kuke magana a kansa yaron ne shina. Ni kasan abinda bake tunanin ya hada su? Irin abin yaran nan ne ko shi yace yana sonta tayi turning dinsa down sai ya koma kan kanwarta ko kuma ita tace tana sonsa shi kuma yace kanwar yake so. Shine suke holding grudges. Amma hakan bai kai ta saka a kore shi ba. Abinda Ruqayyah take bukata yanzu shine guidance, tana bukatar wanda zai koya mata abubuwan da suka danganci zama da miji zama da mutane da sauransu. Wannan zai taimaka mata wajen girma. Shi yasa na sage akan muyi tafiyar nan tare saboda mu samu damar bonding ni da ita, I have so many things to teach her" ya bata rai yace "wato da ita za kiyi bonding ba dani ba ko?" Ta zagaye hannayenta a wuyansa tace "kai ai kaine ginshikin komai, kowa kaga na kula albarkacin ka yake ci" yayi murmushi yana kallon cikin idonta yace "you know I love you right?" Tayi murmushi "and I love you too".
Tun ranar da Baba ya bawa Sumayya damar ta gaya wa Adam yake zuwa gidan daukan karatu ta kira shi a waya da niyyar sanar masa, sai dai abinda ya gaya mata akan ganinsa da Ruqayyah tayi da kuma abinda yake tunanin zata aikata ya saka taji jikinta yayi sanyi ta kasa gane a wanne bari na zuciyarta zata saka maganar, tasan kuma tsaf Ruqayyah zata iya sakawa a kori Adam daga aiki vabu abinda yayi mata zafi da future dinsa da hakan zaiyi destroying ko kuma tunanin inda zaije, in dai har birinta zai cika ita bata tunanin kowa. Washegari kuwa sai gashi ya kira ta yana gaya mata cewa an kore shi din, amma kuma an sake daukan sa wani aikin. Ya bata labarin yadda suka yi da Hassan da kuma yadda sukayi da Hussain, sai ta taya shi murna sosai musamman daya gaya mata Hussain ya sake bashi sabuwar offer of employment wadda albashin daya rubuta masa ya fi na wanda Hassan ya rubuta masa. Sai dai kuma a wani bangare na zuciyarta tana jin rashin dadin sabanin ra'ayin da aka samu a tsakanin tagwayen. Tasan irin shakuwar dake tsakanin tagwaye tunda ita ma sune, sai tayi addu'ar Allah ya tsayar haka. Daga nan kuma sai ta shigar masa da maganar Baba "albishirinka" yace "goro, Baba yace ya bani ke?" Tayi dariya "haka nan kawai sai Baba ya baka ni ba tare da ka tambaya ba? Sai kace wata riga?" yayi ajjiyar zuciya yace "haka ne, to meye albishir din?" Tace " nayi wa Baba maganar karatunka, ya amince kake zuwa gidan nan shi da kansa zai koya maka karatun Alkur'ani da duk littattafan addini" yace "WOW my Sweet Sumayya lallai wannan babban albishir ne kika yi min. Nagode Nagode" tace "nima na gode da ka amince cewa zaka ke zuwa ɗin" yace "kinga duk abinda ban gane ba sai in kira ki kizo ki kara min bayani ko?" Tace "no. Babu ruwana. Baba yayi fadan cewa nayi saurayi ban sanar a gida ba. Ruqayyah ce ta gaya masa abinda yake tsakanin mu" yace "to menene a tsakanin mu ɗin" tayi shiru, yace "ki fada min mana inji. So nake ki fada da bakin ki" tace "nima bansan sunan abin ba" yace "in gaya miki?" Tace "ina jin ka" yace "it is called Love. Ni dai abinda nake feeling a raina kenan, ina ji a zuciya ta cewa ke na ke so, da ke nake so inyi tafiya cikin rayuwar duniya har zuwa karshenta. Dake kuma nake so in tashi a can muyi rayuwa wadda bata da karshe a aljanna" tace "ameen, Allah ya amsa" yace "to ke kuma fa? Fada min menene a zuciyarki" ta danyi murmushi tana nuna jin kunya duk da ba tare suke ba tace "nima haka" yace "ke ma me?" Tace "duk abinda kace, nima irinsa" yayi dariya yana jin yana kara sonta a ransa yace "ki fito ki bude baki kiyi magana, in ba haka ba ba zan fahimta ba" tace "to zan gaya maka wata rana" yace "wacce rana kenan?" Tace "nima ban sani ba" yace "to shikenan, zanzo gobe sai ki gaya min a kunnuwa na inji" tace "hold it. Baba yace in ya kara gani na tare da kai sai ya zane ni" ya bude ido zuciyarsa tana bugawa yace "what? Saboda me?" Ta danyi dariya tace "yace sai ka nemi izninsa tukunna. Sai ya yarda ka ke ganina sannan zaka cigaba da gani na" ya yi ajjiyar zuciya yace "yau zan tashi da dare inyi sallah in nemi Allah ya dora ni akan sa. Kar ki damu, in na samu yadda nake so a gurinsa I will show you love the Igbo way".
Kamar yadda Adam ya fada, ranar sai da yayi sallar dare saboda samun courage da kuma neman nasarar fuskantar Baba. Ya nemi iznin Hussain, wanda yake ta shirye shiryen washegari zasu tashi zuwa honeymoon dinsu sannan ya tafi. Ya fada wa Sumayya ta sanar wa Baba da zuwansa da haka shima Baban bai fita ba ya zauna ya jira shi. Da yaje ya aika aka fadi cewa yazo, Zunnur ya fito yace ya shigo, yana ganin sa ya fahimci kanin su Sumayya ne, dakin su ya kai shi sannan ya gaishe shi ya amsa yana tambayarsa sunansa. Sannan Zunnur ya koma cikin gida ya gaya wa Baba zuwan sa. Baba ya fito ya same shi a dakin.
Adam ya mike tsaye saboda jin shigowar Baba, kansa a kasa, sai da Baban ya zauna sannan shima ya zauna a kasa, Baba ya miko mada hannu amma sai ya ki bashi nasa hannun sannan ya durkusa ya gaishe shi. Duk wannan yayi practicing tun safe, zamansa da hausawa ya saka ya koyi dabiun su da abinda yake dai dai da abinda yake akasin haka a gurin su.
Baba yace "Husaina tace min kana so kayi karatu tare damu hakane?" Adam yace "haka ne Baba. Ina son yin karatu saboda ni... Saboda ni...." Baba yace "ta gaya min ko kai waye. Shi yasa nace kazo kayi karatun, zamu baka baka ilimi dai dai iyakacin abinda Allah ya bamu. Naji tace kana aiki, nima ina yi, dan haka zamu tsayar da lokaci wanda zamuke yin karatun" Adam yace "Nagode Baba, nagode sosai"
Baba ya cigaba da kallon shi, yana nazarin sa yayin da shi kuma Adam din yake ta lissafin ta yadda zai shigo da maganar Sumayya. Yana kuma jin idon Baba akan sa kamar Baba yana jiran ya fadi wata magana. Sai yace "kuma Baba, dama Sumayya tace in gaya maka....." Baba yace " Sumayya ce tace ka gaya min ko kuma kai ne kake so ka gaya min?" Adam yayi saurin gyara wa. "Nine, ba Sumayya bace nine nake so in tambayeka dama in ka amince..... In ka yarda..... Ina so....dama Sumayya......" Baba yace "kana so zaka nemi auren Sumayya" Adam yace "eh Baba. Haka nake so in ce" Baba yace "me yasa kake neman auren Sumayya?" Adam bai yi in ina anan ba, yasan amsar direct ya fada "saboda ina son ta Baba" Baba yace "saboda me yasa kake sonta" anan sai Adam yayi murmushi, yasan wannan amsar itama. "Saboda kyawun halayyar ta Baba" ya tuno ranar daya fara haduwa da yan biyun a mota, yadda Ruqayyah tayi niyyar damfarar sa Naira hamsin har kuma tana yiwa Sumayyan warning akan kar ta tona mata asiri, tana so su had kansu suyi masa karya idan kuma yaki yarda suyi masa ihu su yi masa sharri, duk akan naira hamsin, amma Sumayya ta zabe shi, inyamurin direban taxi akan twin sister dinta. Ya sake maimaita wa "saboda kyawun halinta Baba" Baba yayi murmushi yace "kayi gaskiya, Sumayya tana da hali mai kyau, kuma ina son ya cigaba da zama a haka. Bana son ka zama dalilin chnazawar ta dai dai da kwayar zarra ne. Allah yayi muku albarka"
Washegari da sassafe jirgi ya tashi da tagwayen maza tare da amaren su zuwa yawon cin amarcin su inda zasu fara ta Amalfi Coast, Italy. Kannen su gaba daya sunzo rakiyar su har Hassana da bata gidan, suna gab da tashi sai ga Adam ya kawo Sumayya, Sulaiman da Zunnur, suma sun zo yiwa yar uwarsu sallama. Kallo daya Ruqayyah tayi masa ta dauke kanta ta je gurin yan uwanta. Sai da jirginsu ya tashi sannan ya rakiyar tasu kowa ya kama gabansa.
Wannan littafin na siyarwa ne, duk wadda take so tayi mini magana through WhatsApp 08067081020
A cikin wata guda da suka yi a honeymoon dinsu, abubuwa da dama sun faru, na farko dai a wannan lokacin ne idanun Ruqayyah suka bude, a wannan tafiyar ne tasan kiyasin how much Hussain is really worth. Kudin data kiyasta kuma ba kadan bane ba, ta lura da duk inda suka je da mutanen da suka hadu dasu da kuma irin girman da mutanen suke bashi. Sunansa yaje inda ita bata taba zato ba. Irin hotels din da suke zama kadai ko a cikin mutanen kasashen ba kowa ne yake zama a irin wadannan gurin ba. Irin guraren da zata iya kira da aljannar duniya dan ita in tana lissafin aljanna a ranta irin haka take hasko wa. Duk kuma kalar dakin da Hussain ya kama musu shida Fatima to irinsa yake kamawa Hassan da Ruqayyah, daga nan kuma kowa zai shiga harkokin sa babu wanda zai takurawa wani sai dare sannan zasu hadu suyi dinner tare suyi maganganun su shikenan kuma kowa sai ya kama gabansa. Amma duk da haka Fatima sai da tayi kokarin ganin ta cika alkawarin ta, kullum takan ware wasu lokuta a cikin lokutan mijinta ta zauna da Ruqayyah. Kullum da akwai darasin da suke yi, tun daga kan kwalliya, dresssing, passion trend, tafiya, zama, magana da kuma harkar kula da miji musamman a gado. Da farko Ruqayyah taki bata hadin kai, tana ganin kamar wata hanya ce ta dauko dan ta kaskantar da ita amma daga baya bayan tayi waya da Minal sai ta fahimci wannan hanya ce da zata shiga gari itama. Tasan Fatima karshe ce a abubuwa da dama, dan haka in ta kiya daga gare ta kuma ta yi koyi da ita to kuwa tabbas in vata zama kamarta ba to kuwa zata zama a kusa da ita. Dan haka ta zage dantse ta bude kunnuwanta da kwakwalwar ta take koyon duk abinda Fatima take koya mata sannan tana lura da ita ta a kwaikwayon yadda take duk wani abinta. Amma ko sau daya bata taba gayawa Hassan abinda suke yi tare da Fatima in suka kebe ba. Daya tambayeta sai tace "hira ce kawai muke yi. Kullum labarin gidan sarauta da sarakuna kamar bansan xewa daga can take ba, ni na gaji wallahi. Bana so dai in daina zuwa kar taga kamar wani abu ne" shima kuma Hassan bai hana ta ba, saboda a lokacin ne yake samun personal time dinsa ya dan gudanar da wasu ayyukan office din ko kuma suyi maganar aiki shi da Hussain, musamman maganar da ta shafi bikin bude kamfanin da za'a yi da zarar sun koma Nigeria.
Amma duk wannan abin Ruqayyah tana lura kuma tana sane da Hussain, ta lura baya kula ta amma idanuwansa yana kan ta, kamar wanda yake studying dinta, kamar wanda yake so ya kama ta da wani laifi. Sai dai ko da wasa bata taba barinshi ya kama ta da laifin ba, in tana gabansa tana jin kamar dalibi marar gaskiyar da yake gaban principal. Wannan yasa bata enjoying dinner din da suke yi tare duk kuwa da cewa abinci ne irin wadanda bata taba tunanin akwai abinci irin su a duniya ba.
Bayan sunyi sati daya a Amalfi coast, Italy, sai suka tafi.........daga nan sai Maldives sannan......... Anan ne Fatima tayi suggesting ahe a duba lafiyar Ruqayyah, dama tun zuwansu take lura da ita musamman wayan kwadayin da taga tana dashi, da farko ta dauka saboda bata saba wadannan ciye ciyen ba amma sai daga baya ta lura da cewa yafi karfin haka. Bata taba zama bata cin wani abu, jikinta ya murje sosai tayi kiba da fari, sannan kirjinta sun kara girma kamar ana hura musu aska. Girman kirjin ya saka Fatima tace akai ta asibiti. "Ruqayyah ki shirya gobe muje asibiti a duba ki" Ruqayyah ta bude ido kwakwalwar ta tana zama alert, wannan matar me take nufi? Tace "asibiti kuma? Dama an taba kai mai lafiya asibiti? Ni na dauka marar lafiya ne yake zuwa asibiti?" Fatima tayi murmushi tace "
Mr Careful
Hussain ya bi Hassan da Ruqayyah da kallo fuskarsa dauke da mixed emotions na shock da kuma tambayoyi kala-kala, har suka wuce shi suka fita suka bar kofa a bude, ya juya ya rufe kofar sannan ta juyo yana kallon fatima da take tsaye tana sheshshekar kuka. Tunda yake da ita tunda ya santa sama da shekaru hudu bai taba gani ko jinta tana kuka ba, bai san gaskiyar me ya faru a gurin ba amma sai yaji zuciyarsa tafi karkata gurin Fatima, yaji kukan ta har cikin ransa. Da sassarfa ya karasa inda take ta jawo ta jikinsa ya zagaye ta da hannayensa yana jin kukan ta yana karuwa. Bai lalllashe ta ba sai ya barta tayi kukan ta sosai ta gama. Tunda take a zata iya tuna ranar da aka yi mata tsawa ba, in ma an taba yi mata gaskiya bata sami ba ballantana hara akai ga daga mata hannu kuma akan laifin da bata san ta aikata ba. Ita da soyayya aka raine ta, im ma tayi laifi ana yi mata fada ne ta sigar lallashi da kuma nasiha, wani lokacin ma ba zata fahimci fada ake yi mata ba sai anyi mentioning laifin da tayi. Duka kuwa is totally out of the question, amma ita yau Hassan yake daga wa hannu, ta dauka marin ta zaiyi duk da cewa bata san me tayi ba, ya kuma kirawo ta da munafuka amma bata sam munafuncin me tayi masa ba, and above all yayi violating privacy dinta ya ganta a yana yin da in ba mijinta ba babu namijin da ya taba ganin ta haka a