Showing 165001 words to 168000 words out of 300844 words

Chapter 56 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2102

zai fara karantawa amma in yaji abin da bai kamata ya karanta bane ba zai fasa karantawa sai ya kona shi.

A zauna akan study table da yake can gefe ya kunna lamp din gurin sannan ya fara karantawa.

Dear baby ....

A hankali yake bin handwritten rubutun Hussain yana karantawa har ya gama page din farko ya bude na biyu, a lokacin ne ya fahimci wasiyya ce Hussain ya rubuta zuwa ga abinda Fatima zata haifa. Sai ya rufe diary din yana jin hawaye yana sauka a gaban rigarsa ba tare da yasan lokacin da suka fito daga idanun sa ba. "Yah Allah, kai ka barwa kanka dalilin da yasa wannan abin ya faru, ya Allah ka bani zuciyar dauka".

Bai kuma bude diary din ba saboda baya jin zuciyarsa zata iya daukan abinda yake ciki, musamman idan ya tuna da cewa shi wanda ya rubuta din bai san cewa wanda ya rubutawa ba zai zo duniyar ba ballantana har ya girma har ya karanta. A dakin ya kwana ranar, amma sai ya kasa daukar komai kamar yadda yayi niyyar daukan very personal abubuwan Hussain. Da safe ya tashi yayi sallah a dakin sannan ya dauki diary din ya je karshen sa ya rubuta date din da Hussain ya rasu sannan ya bude safe box din Hussain, wadda su biyu kadai suka san code din ya saka a ciki ya rufe. For some unknown reason sai yaji yana so ya ajiye diary din, duk da cewa a zuciyarsa yana jin komai dadewar mutuwar Hussain ba zai iya karanta wa ba.

Bayan ya koma part dinsa ya shirya sai ya dauki hanyar kano shi kadai. A kan hanya ne ya yanke hukuncin zai saa sake bincika masa kwararren likita guda daya wanda Ruqayyah zata ke gani amma kuma zai gaya mata da kakkausar murya cewa shi kadai zata ke gani babu chanji, sai su jira kuma suga abinda hali zaiyi.

Yana zuwa gurin likitan dayake dubata ya fara zuwa, dama sunyi waya tun kafin ya karaso, sai likitan yayi masa bayanin cewa sunyi iyakacin kokarin su wajen ganin cewa sun fahimci inda ciwon Ruqayyah ya dosa amma basu fahimta ba, in sunbi ta nan sai kuma suga wani abu daban. "Sai dai in zaku gwada wani asibitin kuma ko kuma ku fitar da ita waje" Hassan ya gyada kai yace "haka ne, mungode sosai. Allah ya saka da alkhairi" daga nan bai kara komai ba.

Yana zuwa gurin su Ruqayyah ya tarar sun shirya, sai dai wai tun da assuba Ruqayyah taki saka hearing aid dinta taki yiwa Sumayya magana duk da ita Sumayyan bat san laifin da tayi mata ba. Shima ya yi kokarin yi mata magana amma ta dauke kanta gefe taki kula shi duk da tasan magana yake yi mata. Tunda yaga haka sai ya rabu da ita suka gaisa da Sumayya wadda already har ta saka hijab dinta tana ganinsa ta dauki jaka, dama duk zaman asibitin ya ishe ta. Sai ya daukar mata daya jakar ya juya kallon Ruqayyah yace "mun tafi" yasan ta fahimci abinda yace, kamar ba zata tashi ba kuma sai ta yunkura ta tashi tana kokarin gyara karfen da aka saka mata a kafa, sai ya ajiye jakar hannunsa ya durkusa yana gyara mata sai ta ture hannun sa, a idonta yaga hawaye ya taru sai yaji babu dadi a zuciyarsa, tabbas ita din abar tausayi ce. Ya dago kai yana kallon ta cikin ido yace "am sorry" ta fahimci abinda yace daga motsin bakinsa, sai ta dauke kai ta mike tsaye ta fara tafiya tana jan kafa har ta bar dakin.

Ya juyo yana kallon Sumayya wadda itama shi take kallo fuskarta da alamun tausayi, tace "kayi hakuri, haka take very edgy. Yau kuma tafi kullum zama worst" ya gyada kai yace "ke zan bawa hakuri ai, zama da Ruqayyah a irin wannan yanayin nata sai ke din. I was selfish dana tafi na barki da ita. Ya kamata ace na zauna tare da ku" tace "babu komai, ai kana kokari ma tunda ba wai baka zuwa bane ba kullum kana kan hanya, sannan kana da abubuwa da yawa a gabanka" yaji dadin fahimtar sa da tayi sai ya dauki jakar itama ta dauki tata suka fita tare, suna hango Ruqayyah har ta danyi nisa, Hassan ya kara sauri dan ya kamota, tare suka isa gurin motarsaya bude mata ya sake kokarin taimaka mata wajen shiga amma taki karbar taimakon nasa ta shiga ita kadai ta zauna tare da rufe idonta.

Sumayya ta shiga baya shi kuma ya tayar da motar, sai Sumayya taga ya kamata tayi masa maganar da tunda tazo kanotake zuciyarta kawai dai bata son ta takura masa ne saboda ganin yadda abubuwa suka cunkushe masa, amma ganin dama tana so ta barta sai tace "yaya Hassan, dama tunda muka zo nake wani tunani" bai kalle ta ba yana kallon gabansa yace "wanne tunanin fa?" Tace "Adam. Nan ne garin su, ban sani ba ko kana da address din gidansu?" Ya dan kalle ta ta mirror yace "gidan su? Wai kina tunanin ya tafi gida ne? After what he went through kina tunanin zai juya ya koma gidan su kawai saboda Hussain ya mutu? Abandoning karatun sa? Abandoning you?" Ya danyi shiru sannan ya dora da "abandoning his religion?" Ta girgiza kanta "no, Adam ba zai taba yin haka intentionally ba. But what if he was forced to go? Maybe iyayensa somehow sun samu labarin inda yake kuma suka zo suka dauke shi forcefully, ina nufin what if he was Kidnapped by his own family?" Hassan yayi shiru, tabbas maganar ta abin dubawa ce, jin yayi shiru sai tayi ajjiyar zuciya tace "nasan hakan is not possible, sorry for bothering you, kawai dai hausawa sunce idan rakumin ka ya bata har cikin kuratandu kake nemansa" bai ce mata komai ba sai taga yayi setting wani address a Google map sannan sai yayi u turn kamar yadda map din ya nuna masa, da sauri tace "ina zamuje?" Yace "let's check out gidan nasu mu gani" taji wani irin dadi a ranta dan tana ji a jikinta cewa ko da ba'a samu Adam a gidan ba za'a samu wani hint na inda yake.

Ruqayyah tana jin su suna maganganu sama sama amma bata fahimtar su sosai, amma kuma tana so ta san me suke magana akai sai dai kuma duk su biyun fushi take yi dasu, gani take yi kamar basu damu da samun lafiyar ta ba dan har wani murna taga suna yi cewa an sallame ta daga asibiti duk da cewa ko kama hanyar warkewa bata yi ba. Sai ta dauko handbag dinta ta dauko hearing aid dinta ta saka dan taji abinda suke cewa sosai. Sai kuma taji sun daina maganar sai dai taga chanji a yanayin Sumayya kamar tana murna da wani abu, sai kuma ta lura da cewa motar ce take guiding Hassan zuwa inda zasu je. A haka har suka je kofar wani gida suka tsaya, yayi horn sai ga mai gadi ya fito ya tsaya yana kallon motar da alamar rashin sani a fuskarsa, sai Hassan ya fita ya tafi gurin sa, Sumayya tana hango su suna maganganu amma bata jin mai suke cewa sai ta tashi ta fita itama dan zuciyarta ba zata bari ta zauna a mota tana jira ba bayan zata iya samun labarin daya shafi Adam idan ta fita. Tana zuwa taji Hassan yana yiwa mai gadin kwatancen Adam yana cewa shi suke nema, friends dinsa ne. Sai taji mai gadin yace "Joseph?" Da sauri tace "eh shi" sai ya girgiza kansa yace "about five years kenan rabo na da in ga Joseph. Tun daya musulunta ya gudu ya bar gida ban kuma ganin sa ba" Hassan yace "kuma baka da ko labarin inda yake? Ba ka ji masu gidan suna fadar wani abu daya shafe shi ba?" Yace "banji suna fada ba. Amma kusan wata hudu da suka wuce a guy came here yana gaya min wai yasan inda Joseph yake a Kaduna, nace zan shigar dashi gurin mai gida amma sai ya ce shi ba zai shiga ba, yace wata ta turo shi ya fada anonymously, kamar tana son helping parents din ne su same shi" Hassan ya kalli Sumayya wadda itama shi take kallo sai yace "ko zaka iya gaya mana address din daya gaya maka please? Maybe ko zamu same shi acan din? Neman da muke yi masa mai muhimmanci ne sosai" sai mai gadin ya tsaya yana kallon su da alamar rashin yarda, sai Hassan ya zaro kudi masu yawa ya bashi yace yayi cefane, kamar ba zai fada ba kuma sai ya fada, address din gidan su Hassan. "mutumin yace wai aikin driver yake yi a gidan" Hassan yaji kansa ya dau zafi, yana iyakacin kokarin ganin bai nuna tashin hankalin sa a fili ba yace "kuma ka gayawa parents dinsa?" Mai gadin ya gyada kai "sosai. Sun jima suna nemansa, suna sonsa sosai" Hassan yace "yanzu masu gidan suna ina?" Mai gadin yace "mai gidan watansa biyu rabonsa da nan, Madam kuma da yara three weeks ago suma suka bishi, sun tafi state din su, imo".

Ikon Allah ne kawai ya dawo da Sumayya cikin mota, bata iya zama ba sai ta zauna ta fara kuka a hankali. Hassan ma da ya shigo bai yi wa kowa magana ba sai ya tayar da motar yayi reverse suka bar gurin. Sai a lokacin Ruqayyah tayi magana "ina kuka je wai? Kun fita kun barni a mita ni kadai, ne kuka yi? Ta juyo tana kallon Sumayya tace "ita kuma wannan mai aka yi mata?" Babu wanda ya amsa mata a cikin su, sai Hassan ne ya kalli Sumayya yace "ki daina kuka Sumayya, farin ciki ya kamata kiyi, ko babu komai munsan cewa yana da rai yana kuma da lafiya, kar ki manta maganar mai gadin da yace suna sonsa sosai? They will never harm him" Ruqayyah ta sake cewa "wai waye kuke maganar sa?" Hassan yace mata " Adam" tayi sauri ta kalle shi idanuwa a bude, yace "yes, gidan iyayen sa ne nan, kuma muna suspecting wata ce daga gida ta aiko gidan su ta fadi inda yake, dan haka muna tsammanin iyayensa ne suka dauke shi" Ruqayyah ta dauke kai gefe tana kallon titi, trying so hard ta boye tashin hankalin ta, ta jima tana juya maganar sannan tace "at least yanzu zaku ragewa kanku damuwa saboda, he is in the safest of places for him. Yana tare da iyayensa".

Har suka je Kaduna babu wata maganar kirkin da suke yi a tsakanin su, gidan sa ya zarce dasu direct kuma suka tarar already Aunty ta aiko an yi duk gyare gyare-gyaren da ya kamata a yi a cikin gidan, har abinci an kawo musu an ajiye a dining. Suka ci abinci suka yi wanka sannan sai ga su Aunty sun shigo sun duba Ruqayyah. Daga baya kuma sai ga Inna Ade da Baba dasu Sulaiman, Baba ya barsu a gidan bai dawo daukarsu ba sai dare, a lokacin ne kuma inna Ade ta saka Ruqayyah a gaba da nasiha saboda ta fahimci ta sauki maganar ciwon nan da zafi sosai. Sumayya kuwa jin su kawai take yi tana tunanin maganganun mai gadin nan, kalmar wata mata ta tsaya mata a zuciya, wacce matar? Kuma wai a gidan take. Wacece ita? Tunani da yawa yana crossing mind dinta amma sai ta kawar dashi, no, it can't be, her sister can't be that cruel da har zata raba ta da happiness dinta saboda selfish reason dinta. It can't be. Idan haka ta kasance zuciyarta ba zata iya dauka ba, idan haka ta kasance babu ita babu Ruqayyah, har abada.

But she is going to find out, zata yi bincike da kanta saboda bata son tayi zargin yaruwarta........

Sai dare Baba ya dawo ya dauke su gaba ki dayan su har Sumayya suka tafi gida. Bayan sun tafi ya rage Ruqayyah da Hassan da kuma yara su guda uku. Shi yayi wa yaran wanka yana jin missing dinsu a ransa ya fito dasu ita kuma ta fara shirya su da kayan baccin su suna tayi mata gwaranci da alama sunyi missing dinta sosai. Sai ya jawo kujera ya zauna yana kallon su yana jin dadi, ta daga kai tana kallon sa tace "mijina. Nace wai yanzu tunda ba zan iya shiga jirgi zuwa kasar waje ba, why not kayi min kokarin yadda za'a yi shi doctor din yazo nan ya duba ni?" Ya nade hannunsa a kirjinsa yana kallonta yana mamakin ta, yace "yazo nan ya duba ki? Da wadanne kayan aikin? Da wannan kudin kuma zan iya hayar likita kamar wannan yazo har Nigeria ya duba matata?" Ta tsaya da abinda take yi tana kallonsa Tace "ban gane ba? Kai fa kace min zaka yi duk iyakacin kokarin ka kaga na samu lafiya, I am just trying to hold you to your promise" yace "haka na fada kuma haka zanyi, amma abinda kike fada is not possible" tace "not possible? A gurin ka? Kar ka manta fa yanzu fiye da rabin abinda Hussain yake dashi sanda yana da rai ya zama naka" sai ya mike tsaye yana kallon ta yace "tunda kince haka let me tell you plans dina duk da ban gaya wa kowa ba yet. Nayi putting up H and H gabaki dayan ta for sell, already har ance dangote ya fara tayawa, zan siyar da komai, in nace komai ina nufin komai including gidan nan da muke ciki da motocin da Hussain ya bari duk zan siyar, za'a fitarwa da Fatima gadonta a kaiwa iyayen ta, za'a fitar dana sisters din mu a basu abinsu sannan sauran zanyi sadaka dashi, gaba dayansa, da fatan Allah ya kai ladan kabarin Hussain".


Wannan littafin na siyarwa ne idan kika ganshi a wani gurin na sata ne, in kina so ki karanta halaliyar ki kiyi min magana through WhatsApp ta wannan number din 08067081020


*The Fourth Wave*

Yana kallo rigar Yusuf da take hannunta ta zame ta fadi, yanayin fuskarta ya fara chanzawa from fair to bad then to worst. Har saida yanayin ta ya juya zuwa yadda bai taba gani ba, sai yaga gabadaya ta chanja daga Hassanar da ya sani ya kuma aura zuwa wata halitta ta daban wadda bai taba sani ba. Tabbas yasan tana son kudi, yasan ta boye masa cewa tana son kudi tun ranar da tayi subutar baki a gabansa ta gaya masa cewa shi bashi da komai dan uwansa yana da komai, amma bai taba zaton son da take yiwa kudi ya kai wanda yanayin ta zai iya wannan chanzawar a lokaci daya ba dan yace zaiyi wa dan'uwan sa sadaka da kudin da dan'uwan nasa ne ya tara da kansa ba wani ne ya tara masa ba.

Yana kallonta ta mike tsaye, har tana bude Yusuf da yake kusa da ita yana jiran ta saka masa riga, amma bata kalli yaron ba kamar ma bata san ta bige shi din ba tace "what? Me naji kace?" Ya rungume hannunsa yana kara studying dinta yace "abinda kika ji shi na fada, zanyi sadakar duk abinda Hussain ya bari da kuma share din daya bani kafin rasuwar sa ga mabukata, da fatan Allah ya kai rahama kabarin sa, thats how much nake son sa"

Idonta yaga ya kawo ruwa sannan hawaye ya fara zuba daga idon, ta bude baki ta mayar ta rufe, amma bai fita ba kuma bai daina kallon ta ba yana so ya karanta wani abu a idonta, yana so ya hango ko da burbushin yarinyar nan data taimaka masa ranar nan a idonta amma babu, she is totally gone.

Ta hadiye abinda ya hana ta magana sannan tace "love? Love kake cewa? That's how much kake son Hussain, Hussain da baya duniya bayan mu kuma gamu a duniya, what about us? Mu baka son mu? Ni da yayanka. In kai baka bukatar dukiyar mu ai muna bukata, ni da yayanka, ta yaya zaka kula damu? Ko dan na zama nakasashshiya shine kake saka ran zan fita inyi bara in samo abin bukata? Wannan shine abinda kake nufi?" Fada take yi tana magana da duk kan karfinta, daga inda yake yana kallon yadda jikinta yake rawa, yana kallon yadda rage yake burning a cikin idonta. Bai taba dauka zata dauki zafi irin haka ba akan kudin da ba nata ba. Sai ya tako xuwa kusa da ita yace "yayana da ke da kannena da aunty duk responsibility dina ne, zan kula daku koda dako zanyi a kasuwa, kudin Hussain shi ya tara bani ba and am sending it back to him, nima zan tara nawa zan kuma kula da ku da iyakacin arzikin da aka rubuta min, na yanke wannan hukuncin tun ranar da Hussain ya raba dukiyar sa biyu ya bani saboda in kula da kaina in kuma kula da aunty da yan uwanmu saboda yana gudun kar Fatima ta haifi namiji in kasa gadarsa, yes, that's how much he loved me. And....." Ta kwace hannunta daga nasa tana masa wani irin kallo, tace "rabin dukiyarsa? Ya baka? Amma baka taba gaya min ba a matsayi na na matarka?" Yace "yes, saboda banyi niyyar amfani da ita ba tun a wancan lokacin, dan haka nayi tunanin gaya miki bashi da amfani" ta dafe kanta da hannu biyu tana fitar da numfashi sama sama, Wato tayi spending time a matsayin matar ceo without her knowing, kuma da tasan da wannan maybe da bata yi abinda tayi har yake hanata bacci ba. Ta bude idonta tana kallonsa tace "da kasan abinda kayi da bakayi ba, da zan gaya maka abinda kayi da kayi nadama babba" ya bude ido yace "me nayi? Dan ban gaya miki kanina yayi min kyauta ba shine zanyi nadama? I don't think so" sai kawai yaga tayi wani irin murmushi ta kawar da kanta gefe sannan tace "lallai rashin sani kukumi ne" ya saka hannu ya juyo da fuskar tata yace "me kike nufi, what don't I know?" sai ta rufe idonta saboda bata son ganin cikin idonsa,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login