Showing 168001 words to 171000 words out of 300844 words
ko wuka zai saka mata a wuya ba zata fada masa abinda tayi dan ta samu dukiyar da yake kokarin rabarwa ga mutanen da ko sanda basu taba dagawa dan ganin samuwar dukiyar ba, bayan ita sai data....sai data...., Ko a cikin zuciyarta bata fadar abinda tayi ballantana a fili, ballantana a kunnen Hassan. Amma wannan hanyar daya dauko ba mai bullewa bace ba, she deserves that money, ba zata yi biyu babu ba, ba zata taba barinsa yayi mata wannan tozarcin ba, za kuma tayi komai dan ganin baiyi abinda ta gani a idonsa cewa ya gama daukan niyyar yi ba. In tace komai tana nufin komai.
Ya saki fuskarta jin bata ce komai ba. Ya yi taku biyu baya yana kallonta yace "akwai abinda kike boye min. Me kika sani wanda ni ban sani ba? Me kika aikata?kina son kudi na sani, ba kya son in bayar da kudin nan na sani, amma ina so ki san cewa kamar nayi na gama ne, ke matata ce, responsibility dina ce kuma zanyi iya kacin kokari na na ganin cewa na kula da ke na sauke duk wasu nauye nauyen ki da yake kaina. Amma dukiyar Hussain, no"
Ruqayyah tace "ni kuma zanga ta yadda zaka rabar da ita din, tsakanin ni da kai dan halak ka fasa, wallahi in dai ina numfashi ba zaka bayar da ko da kobo a cikin kudin nan ba, saboda kudin nan is as much mine as it is yours saboda ni matarka ce uwar yayan ka ce" bai ce mata komai ba sai ya juya yana kokarin barin dakin, shi duk inda tashin hankali yake yanzu baya baya yake yi dashi ba wai dan yana gudun mutuwa ba sai dan yana gudun wahala, yana gudun ya zama responsibility a gurin wadanda suke responsibilities dinsa saboda shi kansa yasan ciwo yana daf da kama shi indai rayuwa ta cigaba da tafiyar masa a haka.
Ta bi bayansa da kallo tana daga kafarta da kokarin zuwa ta tari gabansa, ta manta ma da problem din kafarta, jin kafar taki responding ya tuna mata da cewa kafar ta daina aiki wannan kuma ya kara tunxura ta tace "wallahi baka isa ba Hassan, wallahi baka isa ba kayi kadan wallahi. Wallahi sai dai ka zaba ko Hussain din da baya duniya ko kuma ni da yayana da muke da rai kuma muke da hakki akan ka. Wallahi ba zan taba barin ka ka aikata abinda kake da niyyar aikatawa ba, wallahi....." Karar rufe kofarsa ya ankarar da ita cewa ya fita ya bata guri.
Ta zauna tana rusa kuka kamar wadda aka aiko mata da labarin mutuwar Baba da Inna a lokaci daya. Dan yadda take ji a ranta bata jin ko daya daga cikinsu ne ya tafi zata ji wannan bakin cikin. Yaran ta da suka gaji da jiran ta saka musu riga suka fara wasan su a kasa ta kalla, duk mafarkan ta tana hango yaran a ciki, tana hango cewa sun girma cikin dukiya da wadata ba irin yadda ita ta girma cikin talauci da kunci ba. Duk dan su take yi, shi kansa Hassan din da yake ta wannan firirita dan shi take yi dan shine zai zauna akan kujerar da take fighting for ba wai ita ce zata zauna ba. Shi wanne irin mutum ne mai zuciya kamar dutse? Da wani irin rikakken ra'ayi kamar dangin firauna.
Sai taji a ranta tana missing Minal, da tana nan da yanzu ta dauki waya ta kirata ta gaya mata problem dinta amma Minal bata da rai a yanzu kuma babu wanda ya sani sai ita kadai. Ta goge hawayenta tana tuno da yadda gawar Minal tayi a cikin mota da yadda kaurin konewar gawawwakin ya cika dajin, sai taji a hancin ta kamar tana shakar kaurin a yanzu. Tayi sauri ta girgiza kanta dan it has been very hard for her to keep that secret to herself sannan kuma Hassan yace duk wannan a banza? Gaskiya ba zata yiwu ba. So yake tayi biyu babu? Bayan ta tafka kuskuren da ita kamta tasan zai taba lahirar ta dan ta sami duniya shine zai ce duniyar ma ba zata samu ba? Wato babu duniya babu lahira kenan!
Hassan yana fita daga dakin ya dafe kujera saboda yadda yake jin bugawar zuciyarsa yana kara gudu sosai kamar zata fito daga kirjinsa, yana jin kalaman da Ruqayyah ta bi bayansa dasu amma kuma baya son ya koma su cigaba da rigima akan dukiyar Hussain. Dukiyar da babu abinda zata kara musu gabaki dayan su. Shin wannan ita ce matar da ya zabawa kansa? Ita ce kuma uwar daya zabawa yayan sa?
Duk su biyun babu wanda ya rintsa da niyyar bacci, haka ma Sumayya, a ranar itama bata samu tayi bacci ba tana ta bitar abubuwan da suka faru a ranar musamman maganganun mai gadin gidan su Adam, abubuwan daya fada sun nuna cewa akwai chance mai karfi na cewa Adam yana hannun iyayensa, wata kila sun jima suna bibiyarsa suna gudun kar ya fahimta ya sake gudu kamar yadda ya gudo daga Kano, suna binsa a baya da niyyar kidnapping dinsa idan sun ganshi shi kadai a haka har Allah yasa suka samu nasara ranar da Hussain ya mutu suka kama shi a hanyar Abuja, mai gadin yace matar da ta aiko musu da sakon inda Adam yake a gidan da Adam din yake aiki take, kuma duk gidan ita tana ganin babu wanda ya damu da wanzuwar Adam a gidan kamar Ruqayyah tunda har furta hakan tayi da kanta. Sai dai kuma ita kanta Sumayya tana fatan kar hakan ta kasance domin kuwa abinda zai biyo baya ba zasu taba jin dadin sa ba daga ita har Ruqayyah. Tana so tayi bincike dan ta san gaskiyar abinda ya faru amma tana ganin abune mai wahala ta samu amsar ta ta hanyar bincike dan bata san ta inda zata fara ba sai kawai ta samu kanta da addu'ar idan Ruqayyah ke da hannu Allah yasa tayi Confessing da bakinta dan wannan shine kadai solution, kuma kamar kullum tayi wa adam addu'ar samun guidance daga Allah.
Washegari Hassan bai bari ma sun hadu da Ruqayyah ba ya fita daga gidan da wuri saboda yau ne zasu yi pricing duk komai da komai na Hussain including motocin sa, da kuma gidan sa, sai dai kuma a ransa yaji yana son ya cire gidan nasa ya fasa siyar dashi. So yake sai ya gama pricing komai sannan zai gaya wa Aunty kafin ya siyar duk da yasan abin bazaiyi mata dadi ba amma yana saka ran in taji dalilinsa zata yi masa kyakykyawar fahimta kuma zata kara masa kwarin guiwa. Shi dai kam yayi damara baya jin akwai abinda zai saka ya fasa kudurin sa. Ruqayyah tana hango fitarsa itama ta jawo kafarta ta fito palo tana amsa gaisuwar da masu aikinta suke jera mata, sai kuma ta kira daya daga ciki ta aika ta gurin aunty tace taje tace in ji ta ta bata key din gidan Hussain, tun jiya ta yanke hukuncin abinda zata yi. Ta gurgunce ta kuma kurumce sabida babu yadda zata yi tunda wadannan Allah ne ya aiko mata dasu, kaddara ce, amma ba zata talauce ba kawai dan wani son zuciya irin na Hassan.
Aunty tayi mamakin aiken dan tasan Hassan yana da spare key din gidan Hussain a hannunsa kuma Ruqayyah tana son budewa a gurimsa zata karba ba a gurinta ba. Taso ta aika a tambayi Ruqayyah abinda zata yi da key din amma sai ta fasa saboda ita macece mai jan girmanta sosai bata son shiga abinda zai zubar mata da kima a idon na kasa da ita, ta kuma san yaran zamani da rashin kunya. Sai kawai ta dauko key din ta bawa yar aikin.
Ana kaiwa Ruqayyah, tea kawai ta sha ta tattara yaran ta bawa nanny dinsu sannan ta debi sauran sai gidan Hussain, ita da kanta ta bude gidan ta shiga, ta tsaya tana kallon palon tare da sauke ajjiyar zuciya a ranta tana jin ta shiga kenan wallahi, ba Hassan ba ko Hussain ya dawo daga lahira bata jin zata fita ta bar masa gidan. Nan take ta saka yaranta suka fara aikin gwaran gida, ta gaya musu cewa sun dawo nan da zama kachokan, suka yi ta murna abinsu, sai kuma ta aika gidan Aunty tana kiran yan aikin Fatima da da suke gidan bayan mutuwar Hussain kuma suka koma gurin Aunty suke zaune a can tace su zo suma ayi aikin dasu tunda sune suka san duk wani lungu da sako na gidan. A haka ta ja kafarta da kyar ta hau har saman, sai dai ta tarar wing din Hussain a rufe yake na Fatima ne a bude tunda jiya anzo an debi kayanta, amma kuma sai taga kamar ba'a diba ba dan furnitures din duk suna nan sai few abubuwa aka dauka. Ta kira wata a yaran gidan ta tambayeta "ba'a kwashe kayan Fatima ba dama?" Tace "sunzo sun diba, amma sunce sunbar furnitures din duk wanda zai zauna a gidan yayi amfani dashi" Ruqayyah ta gyada kai, lallai ma mutanen nan wato su kudi ba komai bane ba a gurinsu, ita dai gaba ta kai ta gobarar titi a Jos, dan haka kawai ta bude dakin Fatima aka fara gyara, sai da suka gyara komai tsaf can wajan azahar sannan ta koma part dinta ta fara hado kayata tana bawa yaranta suna shigar mata dashi gidan Hussain, sai a lokacin ta dauki wayata kira Sumayya. "Hello Sumayya? Nace ko zaki taho ki taya ni aiki? Yau muna tare wa a sabon gidan mu" Sumayya tace "sabon gida? Wanne irin sabon gida kuma? Yaushe kuka yi sabon gida" Ruqayyah tace "bayi mukayi ba, gidan Hussain ne can zamu koma" sai Sumayya taji wani iri, anya kuwa bai yi wuri ba su koma gidan Hussain su zauna? Tasan ya zama gidan su amma dai ai ta dauka zasu bari mutuwar ta lafa sosai tukunna kafin su tare. Sai tace "Allah ya sanya alkhairi, amma ba zan samu damar zuwa ba saboda nima ina gyara dakina yau tunda na kwana biyu bananan". Sai Ruqayyah ta tabe baki kawai tace "shikenan, kwazo daga baya kuga sabon dakina" amma a ranta taji babu dadi, tana son duk sanda ta bukaci Sumayya tazo gurinta dan a lokacin ne take jinta fully satisfied.
Hassan bai dauko hanyar gida ba sai da biyar na yamma ta wuce, saboda yasan masifar Ruqayyah zai je ya tarar a gidan. Sun gama komai yau da lawyers dinsa da kuma sell agents, anyi pricing komai kuma dama tun jiya daya sanar da muradin sa na siyar da kamfanonin already har labarin ya iske manyan yan kasuwar kasarnan kuma sun fara nuna interest din su akai. Shi dama ya fi son ya siyar wa da yan kasuwa yadda zasu cigaba da running business din ta yadda babu wanda zai rasa aikin sa a cikin ma'aikatan kamfanonin, in suna bukatar service dinsa shima zai cigaba da yi musu aiki yana karbar albashin sa kamar yadda ya saba, idan ma kuma basa bukatar sa zai nemi wani aikin kuma yasan insha Allah ba zai sha wahala ba kafin ya samu in akayi la'akari da experience dinsa da kuma links din da yake dashi a cikin masu hannu da shuni na kasar nan. Sannan kuma a account dinsa yana da kudin da yake tunanin zasu rike shi daga yanzu zuwa lokacin da zai samu aikin.
Gurin Aunty ya fara shiga kamar yadda ya saba, ya gaishe ta sai yaga fuskarta da damuwa, bata bashi abinci ba kamar kullum saboda ta san matarsa ta dawo, sai shi ya kira Zulaihat yace ta kawo masa, ya fara ci sai Aunty tace "Hassan ya akayi baka gaya min yau zaku tare a gidan Hussain ba? Ai da sai in tura wadannan yaran su taya ku shirya kayan ku ko? Ko ba haka ba ma fadar ai tana da dadi akan ace sai dai inji a gurin yan aiki" ya ji abincin bakinsa yana kokarin shake shi, da kyar ya hadiye shi ido a waje yace "tarewa kuma? Gidan Hussain kuma?" A take Aunty tabbatar da abinda take zargi, Hassan bai san abinda Ruqayyah tayi ba kuma dama tayi tunanin haka dan babu yadda za'a yi Hassan ya aikata haka ba tare da ta sani ba dan shi Hassan baya taba yin komai sai ya tuntube ta first.
Chokalin hannunsa ya ajiye sannan ba tare da yace komai ba ya mike da sauri ya fita daga gidan. Sai kuma Aunty taji babu dadi a ranta ta ji kamar ta hada shi da Ruqayyah ne.
Yana shiga gidan ya hango kofar part din Hussain a bude ga mutane suna ta kai komo, da sauri ya shiga ciki ransa a matukar bace, yaran da ya tarar a palon kasa suka fara matsawa suna bashi guri saboda ganin yana yin sa, yace "ina take?" Suka nuna masa sama da sauri, ya hau da sauri yana hada stairs guda bibbiyu a lokaci daya sannan ya doshi wing din Fatimah dan yasan na Hussain a rufe yake. Bai taba shiga ba saboda duk haduwar da suke yi da Fatima a part din Hussain ne ko kuma a palon kasa sai ranar daya ganta a gym, yayi sauri ya kawar da tunanin daga ransa dan bama ya son tuno abinda ya faru a ranar. A can kuryar Bedroom din Fatimah ya tarar da Ruqayyah tana zaune akan gadon da ba nata ba hannunta rike da wata yar karamar box din da ba tata ba tana jera wasu kaya a ciki, gefenta Hussain karami ne yana kwance so innocently yana tsotsar hannunsa.
Yana kokarin saita numfashin sa yace mata "me kike tunanin kina yi?" Ta juyo tana kallon sa sannan ta mike tsaye tace "sannu da zuwa mijina" yace "me kike tunanin kina yi? Wa ya baki izinin shigowa nan har da kwaso kaya? Ki zo ki fita daga gidan nan" tace "na shigo ne saboda gidan mijina ne, kuma fita ta ba yanzu ba, am here to stay. Idan kai baka so mu muna so ni da yayanka, zaka iya cigaba da zama a can gidan duk sanda kake bukatar ganin mu sai kazo ka ganmu anan. Amma mu anan zamu zauna" yace "ni nine mai gidan, kuma ni nace ki fita, ba'a nan nayi niyyar ki zauna ba kuma ba'a nan zaki zauna ba, ki fita ko kuma in saka a fitar dake. Na gama magana" ya fada dead serious, ya juya zai fita daga dakin sai tace "ni kuma ban gama magana ba, in fact, ban ma fara magana ba tukuna, in har kana ganin zaka iya sakawa a zo a fitar da matarka da yayanka daga cikin gidan ka bismillah. Amma ni ba zan fita ba kuma ba zan barka ka bayar da ko kwandala daga cikin kudin nan ba" ya juyo yana kallonta yace "and how are you going to stop me? Taya zaki hana ni yin abinda na yi niyya?" Itama ta juyo tana kallon sa tace "da ace kasan abinda nayi kafin in samu kudin nan da baka tambaye ni yadda zanyi in hana ka rabar da su ba" ya kara matsowa cikin mamaki yace "kika samu? Yaushe kika samu? Me kuma kika yi? What have you done?" Ta danyi murmushi tace "komai, from the beginning to the end" sai ya dakata a tafiyar da yake yi, a lokaci daya yana realising truth, tun farko ba shi ta aura ba dukiyar da tayi tunanin tasa ce ta aura, daga baya kuma da ta san ba tasa bace ba ta zauna dashi ne saboda tana tunanin zai samu, tana burin ya samu. Zuciyarsa tayi sinking a cikin kirjinsa, ji yayi kamar ta koma cikinsa ta bar kirjinsa. Cikin muryar da yaji kamar ba tashi bace ba Yace "me yasa kika taimaka min ranar nan? Me yasa kika yi saving rayuwata?" Sai ta sake wani murmushin, she hates breaking his heart amma yau ranar gaskiya ce, dole ta fada masa dan ya san dalilin da yasa zata aikata abinda ta riga tayi niyyar yi.
Tace "Baba yaje neman aiki gurinka, sanda aka sace ka sai ya bamu labari, shi ya dauka kaine mai kamfanin dan haka ce mana yayi kai ne mai H and H. Muna ta following labarin batanka saboda Baba ya damu da kai sosai, and then sai gaka a toilet din mu, daga yanayin ka da kayan jikinka nayi tunanin kai ne shi yasa na saka rayuwata a hadari na taimaka maka dan inaso ka rike taimakon da nayi maka a ranka kar ka manta, dan ina so ka biya ni. Na dauka wasu kudi zaka bani wanda zai fitardani daga talauci sai kai kuma ka yi Maganar aure na and I thought auren mais even better dan maybe abinda zaka bani din zai iya karewa amma in na aureka komai naka ya zama nawa. That's why I married you"
Ya dafe kirjinsa yana jingina da jikin bango dan ji yake yi kafafuwan sa kamar ba zasu iya daukarsa ba. Yana girgiza kansa yace "kina nufin ba kya sona Hassana? Kudina Kika aura bani ba Hassana?" Ta bata rai tace "I can't say gaskiya, ban sani ba ko zaman da muka yi da kai na fara sonka amma ban sani ba but abinda na sani shine bana son wannan sunan da kake gaya min, I hate it, kullum kuma ka gaya min raina baci yake yi" ya bude baki zaiyi magana amma sai ya kasa, his heart breaking into pieces, bleeding, kunnuwan sa har kara suke yi masa dan suna so su daina jin maganganun Ruqayyah amma sai ta cigaba da cewa "nasan heart dinka zata yi breaking kaima kamar yadda tawa tayi breaking lokacin da aka kawo ni gidan nan na fahimci cewa ba kai ne mai kudin ba, na fahimci cewa you are just your brother's puppet. But I thought zan iya juya ra'ayin ka tunda naga kana sona, I thought zan iya hada ka da brother din naka yadda zaka kwasar