Showing 174001 words to 177000 words out of 300844 words

Chapter 59 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2111

hannun masu shi ku zauna tare" wannan yasa inna ta mike dan tasan aljannar ta tana tattare da bin umarnin mijinta kuma tasan wannan wata sabuwar hanya ce daya biyo da ita dan ganin Ruqayyah ta dawo kan hanyar dai dai. Amma a ranta tana tunanin abinda Ruqayyah zata zaba, tsakanin su iyayenta da yanuwanta da kuma dukiya.

Kafin Inna ta kai bakin kofa Sumayya ta fito daga dakinta ta riga ta fita, duk tana jin maganganun da Baba yayi har maganar bada ita ga Hassan da yayi taji amma ba wannan ne a gaban ta ba yanzu, abinda yake gabanta shine tana so taga Ruqayyah, tana so ta gaya mata abinda yake zuciyarta face to face. A cikin Napep din Baba suka tafi, babu wanda yayi wa wani Magana a cikin su har suka je gidan, direct part din Hussain suka dosa dan sun san tana can kamar yadda Hassan ya fada. Ai kuwa a can din suka same ta rashe rashe a palon Fatima tana ta wasada yaranta kamar bata aikata komai ba. Sai dai ganin su da yanayin fuskokin su ya saka taji zuciyarta ta tsinke, wato Hassan karar ta ya kai gida ko? Zai zo ya same ta ne.

Tayi kokarin mikewa, "Inna sannu da zuwa. Ban san zaku zo ba ai. Ga guri zauna" Inna tace "a ina zan zauna Ruqayyah? Akan kujerar da ba taki ba? A cikin dakin da ba naki ba a kuma gidan da ba naki ba? Me kika mayar da rayuwar ki ne Ruqayyah? Yaushe lalacewar ki har ta zama haka ban sani ba?" Ruqayyah ta bude baki zata yi magana sai kuma ta rufe, bata jin ko ma menene zata gayawa Inna zata fahimta tunda ita duk bata san komai ba a game da jin dadin rayuwa ba.

Sai Inna Ade ta mika mata takardar da Hassan ya rubuta mata tace "gashi inji mijinki" ta karba amma bata bude ba, a zuciyarta taji ta san menene a ciki, sakinta Hassan yayi, wayo threats din ta baiyi ba kenan tunda har ya sake ta, wato taje ta fadi duk abinda zata fada kenan yake nufi ko? Lallai kuwa zaiyi nadama mai girma. A can kasan zuciyarta taji sunan bazawara ya karu akan sunan kurma kuma gurguwa. Duk sunayenta ne ita kadai. Sai kuma taji wata magana da tafi sauran zafi a gurinta. "Baban ku yace ki taso ki biyomu mu tafi gida tare, tunda can shine gidan uban ki ba nan ba. Yace kuma kar ki sake ki dauki ko chokali a cikin gidan nan tunda ba ubanki ne ya siya ba" Ruqayyah ta zaro ido waje tana girgiza kai, zuciyarta tana kaduwa, ba zata iya ba, after all what she went through ba zata iya yin asarar duk wannan dukiyar data samu bayan ta aikata abubuwa da yawa kafin ta same ta ba, biyu bau kenan, noo ba zata iya ba. She can't imagine ta koma gidan su da zama, gurguwa, kurma, bazawara kuma talaka? Impossible.

Inna Ade ta maimaita "ki tashi ki dauko mayafin ki mu tafi Ruqayyah. Ki duba ki karanta ki gani saki uku mijinki yayi miki" Ruqayyah bata motsa ba, Inna tace "Baban ku yace in baki taso kin biyo mu gida a yanzu ba, babu shi babu ke har abada, babu ni babu ke har abada, babu ke babu yanuwanki har abada ko kuma har sai kinyi nadamar abinda kika yi kuma kin nemi yafiyar duk wadanda kika batawa sannan muma zamu yafe miki".

Hawaye suka fara bin fuskar Ruqayyah, ta kama hannun Inna "Inna dan Allah ki fahimce ni kije ki fahimtar da Baba, ni ba zan iya komawa waccan rayuwar ba saboda yanzu ba zan iya yin irinta ba, na saba da wannan rayuwar, ga kuma nakasa da ta same ni, inna da wanne zanji? Da nakasa ko da saki ko kuma da juya min baya da kuke kokarin yi? Dan Allah ki fahimce ni Inna, kudin nan da nake fafutukar samu ai ba wai dan ni kadai bane ba, dan kune gabaki daya, yadda muka sha wahala a baya nake so muji dadi a gaba, zuwa aikin hajji duk shekara, su Zunnur su tafi kasar waje suyi karatun su a can su zama likitoci, Sumayya sai mijin data zaba zata aura, mazan ma ai kudi suke bi kamar yadda matan suke bin kudi" Inna ta kwace hannunta tana kukan takaici tace "ban taba tunanin abinda na haifa a cikina zai yi wannan tunanin ba, kina son Sumayya ta samu miji kuma kika korar mata yaron da yake sonta? Kika yi sanadiyar da yanzu yana can a hannun ahlul kitabi suna kokarin mayar dashi addinin su? A hakan kike sonta, wannan ce taki soyayyar?" Ruqayyah tayi sauri ta kalli Sumayya,bita ta manta ma ta gaya wa Hassan wannan maganar, dan bata yi niyyar gaya masa ba saboda baya son abinda zai bata tsakanin ta da Sumayya dan tana ganin ko duk duniya zasu guje ta Sumayya ba zata taba guje mata ba. Amma yanayin data gani a fuskar Sumayya ya saka taji zuciyarta ta tsaya da bugun da take yi.

Inna tace "na tafi Ruqayyah kamar yadda babanki ya fada zabi ya rage naki. Ko ki biyo ni ko kuma ki cigaba da zama ki cigaba da rayuwa amma ba tare da mu ba. Kuma babanki ya bawa tsohon mijinki damar yayi miki duk abinda yayi niyyar yi miki babu ruwansa, ko da kuwa abinda zaiyi mikin yana nufin ya hada ki da police ne" ta juya zata tafi sai Ruqayyah ta kuma kamo hannunta tace "dan Allah inna kiyi hakuri, ki rokar min Baba ya bani lokaci muyi magana da Hassan komai zai dai dai ta. Dan Allah Inna baku san wahalar da nasha ba kafin in samu kudin nan baku san irin abinda nayi ba kafin in samu kudin nan bazan iya hakura dasu ba tare da nayi iyakar kokari na ba" Inna ta kuma kwace hannunta tana goge hawayen ta tace "abinda kika yi ai duk tsohon mijinki ya gaya mana, lokaci kuma mun baki lokaci daga yanzu zuwa sanda zamu bar gidan nan ki dauko mayafin ki mu tafi tare, in baki yi haka ba kuwa to na gaya miki abinda zai biyo baya kuma da gaske muke" ganin Ruqayyah bata da niyyar tahowa ya saka Inna ta kama hannunta tana janta zata fitar da ita da karfi amma Ruqayyah taki fita, ganin Inna tana kokarin jin ciwo ya saka Sulaiman ya kama hannunsu ya raba su sannan ya ja Inna ya fita da ita tana ta kuka, aka bar Ruqayyah itama da take kukan tana kiran Inna da kuma Sumayya da tun da suka shigo take tsaye tana kallon su. Sai bayan fitar su sannan Sumayya ta matso gaban Ruqayyah, Ruqayyah tayi sauri ta rike hannunta tace "Sumayya kibi bayan Inna kije kiyi musu bayani yadda zasu fahimta, kudin nan fa har dasu za'a ji dadinsa, su bani lokaci in samu in yi Magana da Hassan ni na san abinda zan gaya masa komai zai dawo dai dai" Sumayya tace "kin tuna da ranar nan? Ranar da na yi miki warning cewa ki fita daga harkar Adam?" Ruqayyah tace "zamuyi wannan maganar daga baya, yanzu maganar Inna da Baba sunyi fushi dani akeyi akan maganar da Hassan ya gaya musu ba tare ma da sun tsaya sunji nawa side din ba. Kije ki basu hakuri kice zanzo gidan zamuyi magana sosai" Sumayya tace "kin tuna warning din da nayi miki ko baki tuna ba?" Ruqayyah ta ce " ta tuna kince kar in kara, na daina yanzu ba shikenan ba?" Sumayya tace "da nace kar ki kara dai kika ce in kin kara mai zanyi miki? To yanzu zan baki amsa" Ruqayyah tana tsaye tan kallon t da mamaki tace "me zaki yi min?" Sumayya tace "babu ni babu ke har abada. Shine abinda zanyi miki" daga nan ba tare da ta kara cewa komai ba ta juya ta bar palon.

Ruqayyah bata iya motsawa ba, bata kuma iya cewa komai ba har taji sun tayar da Napep dinsu sannan yaji motsin bude gate din gidan alamun sun fita.

Sai bayan da su Inna suka bar gidan Baba sannan Hassan ya fito shima bayan Baba yayi masa doguwar nasiha akan yarda da kaddara da kuma mika lamura ga Ubangiji da neman zabinsa dan samun dacewa. Daga gidan Baba bai koma gida ba dan baya jin zai uya shiga gidan, sai ya tafi ya kama hotel ya zauna, ya kira Aunty ya gaya mata yana nan lafiya amma zai dan zauna a hotel kwana biyu, ita kuma Aunty sai ta dauka rigimar da suka yi da Ruqayyah akan tarewar da tayi a gidan Hussain ne ya saka shi yayi mata yaji, sai ta fara yi musu addu'ar samun fahimtar juna.

Sai da Hassan yayi sati guda a hotel din shi kadai. A cikin satin nan yayi abubuwa da yawa, na farko ya kara dawo da alakar sa da ubangiji, yayi Adduoi da dama akan rayuwarsa, ya nemi ubangiji yayi masa jagora ya bashi ikon cin dukkan jarabawowinsa, ya nemi zabin Allah a dukkan hukunce hukuncen da zaiyi a yanzu wadanda yasan zasu taba gaba ki dayan zuri'arsa kar karshen rayuwar su. A cikin satin yana daga hotel din ya yi abubuwa da yawa. Na farko ya siyar da share dinsa ta H and H kamar yadda yayi niyyar yi, sadakar nan da yayi niyyar yiwa Hussain sai ya yi ta babu fashi, abin mamaki sai Umar yayan Fatima wanda a lokacin shine yake tashen kudi a gidan sarkin kano ya siya. Sauran rabin kuma wanda shine na Hussain sai yasa aka kaiwa masana rabon gado suka raba, na Fatima Umar din ya sake siya, ya bawa iyayenta kudin. Wanda ya kasance nashi rabon kuma sai yace a barshi a cikin kamfanin a matsayin share.

Satin nayi daya fito sai yaji kamar duk wasu nauye nauye da yake jin su akan kafadar sa duk babu su kamar an dauke masa su. Yaji confidence a ransa, yaji a zuciyarsa kuma dukkan al'amuran suna warware masa da kansu.

Bai je gida ba sai daya je office ya aiwatar da duk abinda ya riga ya yanke hukuncin zai aiwata, sannan ya tafi gida. Direct part din Hussain ya tafi inda yasan acan ne zai samu Ruqayyah. A can kuwa ya same ta, tana dakin nan mai zanen sarauta tana feeding Hussain. Yana shiga ta dago kai tana kallonsa, idon ta kamar zai fado kasa, ta ajiye feeder a gefe cikin rawar murya tace "da gaske nake wallahi, duk abinda nace zan fada sai na fada wallahi. Har kafata, zan ce su suka shanye min kafata a gurin accident din suka mayar dani gurguwa" ga mamakin ta sai taga yayi murmushi ya samu guri ya zauna yana facing dinta yace "say whatever you want to say, do what ever you want to do. Hussain yana kabarin sa kuma duk maganganun ki ba zasu taba hurting dinsa ba dan he is out of your reach. Ko mutane sun tsine masa tsinuwar su ba zata taba yi masa komai ba saboda shi Ubangiji yasan gaskiya and that's all that matters. In ma da akwai wanda abinda zaki fada zai yi hurting to nine, ni kuma zuciyata yanzu ta zama ta karfe babu abinda zai iya hudata balle ya dame ni" ta sake jawo little Hussain jikinta tace "ba zan fita ba, wallahi ba inda zanje, ai na haihu da kai dan haka I deserve something" sai ya gyada kai yace "haka ne, kin haifa min yara har gida uku sune kuma dalilin da yasa ba zan kira police yanzu su fitar da ke daga gidan nan ba, kuma sume dalilin da yasa nazo gurinki yanzu zamuyi magana" sai ya tura mata takardu gabanta yace "wannan takarda ce, na riga na saka hannu nayi komai akan cewa na baki dukkan abinda na gada na daga dukiyar Hussain. Share ce mai tsoka a kamfanin H and H. Ba'a siyar da kamfanin ba yana nan kuma a yanzu kece kike da share mafi girma a ciki, na kuma nema miki manager da zai runga gudanar miki da komai yana saka miki kudadenki a cikin account dinki" ta bude baki tana kallon sa sai kuma ta kalli takardar, ya mika mata ta karba da sauri, sai shi kuma ya saka hannu ya dauki little Hussain, ta kalle shi tace "me kake so to? Tunda kace baka damu da in yi shiru ko inyi magana akan abinda nace zan fada dangane da Hussain ba" sai yace "yayana nake so. Babu ke babu su, shine deal din" ta zaro ido "yayan nawa? Ni fa na haife su ta yaya zaka ce babu ni babu su?" Sai ya daga kafadar sa yace "zabi ya rage ya naki kuma, ko ya'ya ko dukiya, in baki yarda ba zan karbi takardata kuma zan saka a fitar min dake daga gidan nan ki tafi duk inda zaki je sannan kuma zan karbi yayana ta karfi, kinsan ina da karfi najiki dana aljihu, kuma a iyakacin sanin da nayi Baba da inna sunce babu su babu ke, zabi ya rage naki" ta fara kuka tana kallon Hussain tace "Hassan baka da imani" yayi murmushi yace "bana jin akwai wanda ya kai ki rashin imani Hassana. Wannan shi yasa zan raba ki da yayana saboda ke din macijiya ce mai dafi, bana son ki shafa wa yayana mugun dafin ki" tace "yayana ne nima ai, kuma ko ka raba ni dasu dole wata rana da kansu zasu neme ni" yace "tabbas haka ne, but before then sun mallaki hankalin kansu sun samu tarbiyya mai kyau"

A lokacin twins suka shigo dakin da gudu sunji labarin daddy ya zo, suka rungume shi sai yace "ku je maza Nanny ta hada muku kayan ku, ku gaya mata zamu je unguwa daku" suka fita da sauri suna murna. Ruqayyah ta dafa bango ta mike tsaye tana kallon sa, ya tako zuwa gabanta, ta mika hannu zata karbi Hussain sai ya matsar dashi gefe yace "for the sake of our children, for the sake of your parents, ina fatan watarana zaki dawo kan hanyar dai dai ki gyara kurakuren ki" ta kara sautin kukan ta. "Yanzu Hassan abinda zaka yi min kenan? Dan nakasa ta same ni? Wato na gama yi maka amfani kenan ko? Kaci moriyar ganga ko?" Ya gane abinda take kokarin yi, so take ta saka yayi feeling guilty kamar shine mai laifin ba ita ba. Bayan shi gani yake yi ba karamin adalci yayi mata ba.

Ya yanke hukuncin bata kudin ne saboda yana son ta fahimci wani abu a rayuwa, ta fahimci cewa kudi is nothing compared to love, ta fahimci cewa akwai abubuwa da dama wa'danda kudi basu isa su siya mata ba, idan ba haka yayi mata ba bazata taba fahimta ba, kuma no matter how he tried ba zai taba cire ta daga rayuwar sa ba ko da kuwa saki dubu yayi mata.

Bai kula ta ba sai ya fita yayi locking duk dakunan Hussain ya cire keys din ya saka a aljihunsa, ba dai babban gida take so da dogon bene da katon valcony ba? Gashi nan ta samu, ba dai H and H take so ba? Gata nan ya bata. Ya kuma barta da duniya.

Yana fitowa twins suna dawowa Nanny tana jan akwatin kayansu, yana kallon Ruqayyah ta jawo kafa zuwa bakin kofar dakin da take tana kallon su tana sheshshekar kuka. Har yaran zasu tafi gurinta sai ya rike su ya yaudare su da zancen ice cream suka sauka kasa da sauri, har sunje bakim kofa ya sake juyowa ya kalli Ruqayyah ya kama rails tana kallonsu, ta bude baki zata yi masa magana sai yayi sauri ya fita ya turo kofa.

Washegari da safe tana kwance duk da ba bacci take yi ba taji kara kamar ana gini, ta tashi da sauri ta ja kafa zuwa taga ta leka sai ta hango katanga ake ginawa ana raba tsakanin gidan Hassan da gidan Hussain, sannan kuma ana toshe karamin gate din daya hada gidajen gida biyu dana Aunty.


*Life Afresh*

Bayan Hassan ya rufe kofar gidan sai ya jingina da jikin kofar yana mayar da numfashi, tabbas shi kansa yasan zuciyarsa tana son Ruqayyah amma dole ya barta saboda shi dai bai taba haduwa da shaidanin mutum irinta ba, ba zai cigaba da zama da ita ba kuma ba zai bar yayansa a hannunta ba for his sake and for the sake of his children. Har cikin ransa yasan wannan hukuncin da ya yanke shine dai dai duk da wani bari na zuciyarsa yana nuna masa kamar bai yi wa yayansa adalci ba daya raba su da mahaifiyar su, sai kuma ya gaya wa kansa "ita ta zabi haka, ita ta zabar musu haka".

Gidan Aunty ya shiga dasu, wani yaro ya daukar masa akwatin da aka zubo musu kayansu. Aunty tana zaune palo tana kallon wa'azi taji sallamar sa, ta daga kai da sauri tana kallonsa rabe rabe da yara, cikin kwanakin da bata ganshi ba sai taga fuskarsa ta fada ciki, manyan idanuwan sa sun kara fitowa waje sannan fatarsa ta kara duhu. Tabbas bayan rashin Hussain akwai wani bakon al'amari da yake damunsa. "Allah ga dan marayan nan Allah ka tausaya masa" ta fada a ranta lokacin da yake zama a gabanta yana mika mata Hussain, Yusuf da Aminu kuma suka fara rige rigen hawa jikinta. Hassan ya gaishe ta ta amsa tana shafa kan tagwayen da tun da aka haife su take jin soyayyar su a zuciyarta tamkar irin son da tayi wasu Hassan sanda suna kanana.

Ta kalli akwatin kayan da aka ajiye a can gefe tace "gidan Sa'adatu zaka kai su ne? Ba kwanan nan suka dawo ba?" Yace "ba can zan kai su ba, nan na kawo su, anan zasu cigaba da zama" sai tayi shiru bata ce komai ba amma tana ji a jikinta cewa wani abin ya faru da ma'auratan. Sai tasa baki ta kira Zulaihat tace "dauki yaran nan ki tafi dasu sama zamu yi magana da yayan ku" Zulaihat ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login