Showing 252001 words to 255000 words out of 300844 words

Chapter 85 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2053

shirin sa.

A Kano kuma a ranar tun safe Gimbiya Asma'u take tare da Gimbiya Fatima a sashen ta tana debe mata kewa tare da kokarin ganin ta saka ta nishadi, which ya zama a banza dan da kyar take samun amsa daga Fatima. Ta lura da yadda ta ke ta kallon wayarta from time to time kamar mai jiran wani abu. Amma abin bai zo ba. Sai Asma'u tace "ki kira shi mana, in bai kira ki ba ai ke sai ki kira shi. It doesn't matter waye ya kira wani first" Fatima ta bata rai "waye kike magana a akansa ne wai? Waye yace miki ina son wani ya kira ni ko ina jiran kiran wani?" Asma'u tace "Allah ya baki hakuri. Wai kawai naga kina ta kallon wayarki ne shine nayi tunanin haka"

But a zuciyar Asma'u ta san abinda Fatima take missing, in normal circumstances yanzu dan zaman da sukayi din nan da Fatima ta kira Adam ko kuma shi ya kira ta, ko kuma da yanzu ta ambaci sunan Adam sai ba adadi. Anan ta fahimci menene matsalar Fatima, ba wai umarnin da aka bata bane yake damunta, rashin Adam ne yake damunta, but she is struggling to keep it aside, for a reason best known to her.

Asma'u bata tabbatar da zargin ta ba sai da Adam ya kwana uku a Kaduna babu waya, at least not to Fatimah but ya kan kira Asma'u yace ya kira ne su gaisa, duk da ita a ranta ta san Fatima yake nema shima. Bata san me ya faru tsakanin su ba amma tasan suna yaudarar kansu ne kuma sun dauki hanyar da ba zata bulle dasu ba. Tayi kokarin communicating da Fatima amma taki bata fuska, tana ganin ita kanwarta ce ba zata yi magana irin wannan da ita ba.

A lokacin da Adam yayi sati a Kaduna, a ranar ya kira Asma'u ya tambaye ta idan Fatima ta koma Dubai ko kuma tana Nigeria, sai ta gaya masa tana nan, ya tambaye ta idan ta san sanda zata koma, sai ta ce masa babu rana. Wannan yasa shi ya yanke shawarar zai koma can din, tunda aim dinsa shine yayi nesa da ita tunda ita ba zata koma ba shi zai koma. Bai san zata taho ba dama shi yasa ya taho. Sai Asma'u ta fadawa Fatima abinda Adam din yace mata.

A ranar ne kuma Fatima ta gama yanke shawarar ta bayan gabatar da istikhara da tayi, bata son bata lokaci tunda tasan cewa ko da shekara zata bata babu abinda zai chanja a cikin zuciyarta. Dan haka taje ta samu Hajiya Ummah da amsar ta. "Umma a sanar da Takawa cewa ni bani da zabi na mijin da zan aura, bana jin kuma zan iya zaba din kamar yadda ya umarce ni. A gaya masa na bar masa zabi, a zaba min duk wanda yake ganin ya dace, ni kuma nayi alkawarin yi muku biyayya"

Daga baya Takawa ya kirata ya nuna mata jin dadinsa tare da sa mata albarka da tabbatar mata da cewa ba zata yi dana sani ba, ta dawo daki ta kwanta, sai ta dauko wayar ta ta nemo number din Adam ta tura masa message. "Am sorry" an jima kadan yayo mata reply "am sorry too".

Tana nan a kwance Asma'u ta shigo ta zauna tana kallon ta tace "yanzu naji ummah tana gayawa hajiya abinda kika ce a gaya wa Takawa" Fatima ta mike zaune tana jingina bayan ta da jikin gado tace "eh", Asma'u ta bata rai "kin san kuwa abinda kika yi? Ba dan kar inyi miki baki ba da sai ince Allah yasa ya aura miki daya daga cikin dagatan sa sai inga ta taurin kai" Fatima tace "ke, baki da kunya? In ma wa zai aurawa ni ina ruwanki? Uba na ne shi fa kuma ya san abinda ya dace dani, ya ma fini sanin abinda ya dace dani. Bani da zaɓi, to menene laifi na dan na bashi zaɓi?" Asma'u tace "kina da zaɓi mana, kina son Adam, no matter what you said babu wanda zai yarda cewa ba kya son sa, ke kadai ce baki sani ba, maybe kuma kin sani kawai kina dannewa ne saboda wani dalili da ki ka barwa kanki. Amma zan gaya miki cewa kin yi rashin miji dan bana jin zaki samu irinsa ko mai kuwa zaben da za'a yi miki, dan babu wanda ya sanki kamar shi, babu wanda zai dauki nauyin ki kamar shi, babu wanda zai saka ki farin ciki kamar shi. Babu......"

Fatimah tana juya kanta tace "ba zaki gane ba Asma'u ba zaki gane ba" Asma'u ta rike hannunta tace "ba zan gane ba tabbas saboda ban saka irin takalmin da kike tafiya dashi a yanzu ba, amma na san cewa akwai matan da suka rasa mazajensu kamar irin yadda kika yi, wasu ma sun fi ku dadewa tare, wasu ma akwai ya'ya a tsakanin su da mazajen da suka rasa amma kuma they eventually moved on. Mutuwar miji ba yana nufin karshen rayuwar ki bane ba, va yana nufin kiyi ta denying kanki happiness duk da cewa kina zagaye da happiness din ba. Ba yana nufin cewa zuciyar ki ba zata kuma karbar wani a matsayin miji ba. Adam yana sonki duk mun sani kuma kema kina sonsa duk mun sani, me yasa ba zaki bawa junan ku dama ba?

Fatima tace "Asma'u, bawai dan kaina naki zaben Adam ba, dan farin cikin sa ne, na gaya masa, na gaya wa Ummah, ban san me yasa duk kuka kasa fahimta ta ba" Asma'u tace "duk mun fahimce ki, amma hujjar bata gamshe mu ba, kin san abinda nake tunani? Kina so ne kiyi wa Hussain biyayya bayan rai, ki hana kanki farinciki saboda ke a ranki kina tunanin in kika yi auren soyayya zai zamanto kamar cin amana ga Hussain. Kin san kina son Adam shi yasa kike kokarin hana wa kanki shi. Kin san zaki samu farin ciki da Adam shi yasa kike gudun sa. Amma kinsan wani abu? Hussain da zai dawo zai yi farin ciki idan ya ganki cikin farin ciki ba zai kuma damu da wanda ya saka ki farin cikin ba. Bara kuma in tuna miki wani abu, yadda kika yi moaning mutuwar Hussain haka zakiyi moaning rabuwa da Adam, koma fiye da haka, saboda sho Hussain ba kya ganin sa shi kuma Adam zaki cigaba da ganin sa tunda yanzu kamar dan gida yake a gidan nan".

Fatima tayi shiru a ranta ta san gaskiya Asma'u ta fada mata, tana kuma tunanin halin da already take ciki na rashin Adam a cikin kwanakin nan, menene zai faru da ita nan gaba? Sai kuma ta sake neman wani excuse din "Asma'u, Adam yayi min karami" Asma'u cikin tsokana tace "Adam din? Are we talking about the same Adam? Ni wanda na sani giant ne" Fatimah ta kwace hannunta tana kai mata duka tace "ba wannan nake nufi ba" Asma'u tayi dariya, tana jin dadin yadda taga kamar Fatima ta fara saukowa tace "to me kike nufi?" Tace "tsakanin mu babu tazara sosai ta shekaru, ni farko ma na dauka na girme shi sai daga baya na fahimci cewa wata takwas ne kawai ya bani, kuma......."

Asma'u tace "kin manta Sani na gidan wambai da akayi bikinsa kwanaki? Wata biyu ya bawa matarsa, and they are so in love with each other. Age is just a number my sister. Age baya determining halayya ko maturity. Ita halayyar mutum da ita ake haifarsa sai dai abubuwan da mutum yayi facing a rayuwa su zasu kara ko su rage yanayin halayyar sa, maturity kuma yana da dangantaka da ilimin mutum da kuma exposure dinsa, ilimi ina nufin na cikin kai ba wai na takarda ba. Ni kuma banga wanda Adam ya rasa ba a cikin wadannan. Ko kuma maybe dan yana Igbo ne?"

Fatimah tayi mata dakuwa, sai kuma suka yi dariya tare, ita mantawa ma take yi da tribe din Adam dan bama ya yin yaren nasa in dai ba haduwa yayi da wani Igbo din ba yana kuma son ya nuna masa shi Igbo ne ba. Ko da yan gidansu va sosai suke yi ba sunfi yin English, ko suyi hausa. Asma'u ta mike "inje in fada ince kin chanja shawara?" Fatima ta zaro ido "nooo, kar ma ki gwada. Na gama magana ai. Ba kuma zan chanja magana ba not to Takawa. Bakin alkalami ya riga ya bushe" sai ta koma ta kwanta

Babu wanda a gidan yaji dadin hukuncin Fatima amma kuma babu wanda zai iya tunkarar Takawa da magana biyu, ta riga ta bashi amsa, zabi kuma yana gare shi a yanzu.

Adam ya gama zamansa na sati guda a gida a cikin daki a kwance, ko duba Ruqayyah da kuma gaida Hassan da yace zaije yayi baiyi ba daga kwanciya sai tashi. Har sai da Baba yace ko za'a kai shi asibiti ne da ya fahimci bashi da lafiya kawai boyewa yake yi. Amma sai yaki, ya nuna cewa shi tafiya ma zaiyi, zai koma Dubai ne saboda ana bukatar sa a inda yake aiki. Har ya shirya da nufin washegari zai taho kano yayi sallama kuma ya wuce Dubai, sai Baba yace ya dakata zasu taho tare, yana so yazo yayi gaisuwa a gurin mai martaba, dama bai taba zuwa ba.

A dole ya jira shi ba dan yaso ba sai da ya kara kwana biyu sannan suka shirya suka taho tare da Baba da Sulaiman da Zunnur. Sanda suka zo ana zaman fada ne, kuma fadar ta cika sosai, suka shiga sukayi gaisuwa, sai Adam ya fahimci kamar dama jiransu akeyi. Sai kawai ya ji an fara gabatar da daurin aure, a cikin sigar yaji an ambaci sunansa, baba ne kuma waliyyin sa, sai kuma yaji an ambaci sunan Fatima a matsayin matarsa, sai kuma ya ga Baba ya dauko kudi dubu hamsin ya mika a matsayin sadaki, aka karba aka kuma shafa fatiha.

Bayan an gama ne mai martaba sarki ya fara jawabi "ya ta Fatima ta bani damar in zaba mata miji, ni kuma na zaba mata wanda nake ganin yafi kowa cancanta daya aure ta. Wannan hukunci na ne da na yanke ina kuma fatan wannan aure zai zamanto kamar mabudin cigaba da ire iren wadannan aurarrakin a tsakanin al'ummar mu. Ina fatan al'umma zasu yi kwaikwayo da abinda nayi su jawo mutane irin Adam jikin su su kuma aura musu ƴaƴan su idan bukatar hakan ta zo. Wannan wani abu ne da zai kawo mana cigaba sosai a cikin addinin mu da kuma zaman lafiyar kasar mu. Ina fatan wannan zai kara wa kwarin gwiwa ga duk wadanda ba musulmi ba wadanda suke da niyyar shiga musulunci, ina kuma fatan sauran kabilun da ba hausawa ba wannan auren zai saka su fahimci cewa dan muna yin magana da mabanbanta harshe ba yana nufin muna da banbanci ba. Dukkan nin mu mutane ne, dukkanin mu kuma yan Nigeria ne, dukkanin mu daya ne"


*The New Couple*

Adam yana jin dukkan abinda ake cewa amma zuciyarsa tana ta gaya masa cewa ba shi Adam din ake nufi ba, wani ne daban. Wani Adam din ne mai irin labarin sa aja daura masa aure da Fatima, amma ne ya shigar da Baba cikin maganar? Ta yaya akayi Baba ya tsaya a matsayin waliy har da bada sadaki? Sai kuma yaga mutane suna ta miko masa hannu suna yi masa Allah ya sanya alkhairi, wasu su dan buga kafadar sa cikin alamun taya murna fuskarsu. Baba ma sai murna yake shi ma kuma ana taya shi murnar, haka su Sulaiman ma.

Wannan yasa ya fara tunanin to ko shi Adam din ake nufi ne? Amma kuma sai yaji tunanin hakan bai saka ya as excited as he thought he would be a duk ranar da Fatima ta zama ta sa ba. Tunanin sa daya shine, Fatima bata son shi, ta gaya masa da kanta tace ba zata iya aurensa ba, kuma yanxu dakunnen sa yaji Mai martaba sarki yana fada cewa shi ta bawa zabi, shine ya zabi Adam din ba wai ita bace ba, as far as he knows ma maybe bata ma san da zancen daurin auren ba kamar yadda shima bau san da shi ba. Wannan ya saka ya janye jikinsa daga cikin mutane, yanalura da yadda ake ta buga tambura da busar kakaki da sarewa, kowa cikin murna amma banda ango.

Dakin da yake a matsayin nasa ya tafi ya shiga ya rufe kofa, daga nan ma yana cigaba da jin kide kiden da yake tashi a cikin gidan, daga cikin gida kuma ya ji an rangada guda, ya san ko bata sani ba ma yanzu ta sani and she will hate him, zata ga kamar shiya matsa aka aura mata shi duk da ta gaya masa bata son sa. Shi kuma gwara ya haura da aurenta akan ya aure ta bada son ranta ba, dan farin cikin ta shine burinsa, ko da kuwa nata farin cikin yana nufin rushewar nasa ne.

Ya dauko wayarsa yana jujjuya wa yana lissafin ko ya kira ta ya gaya mata bashi ya nemi aurenta ba? If she knows him as well as he thought then tasan baya karya, musamman akan abu mai muhimmanci irin wannan. Ya danna kira layin wayarta for the first time in ten days, ya saka a kunne yana zagaya dakin yana jin yadda wayar take kara amma ba'a daga ba, ya sake kira haka har sai da yayi kira sau biyar. A lokacin ne kuma aka zo ana knocking kofar da ya rufe.

Ya bude suka hada ido da Abubakar da yake ta washe masa baki, ga kuma Sulaiman a bayan sa. Sai kuma wani dogari dauke da karamar jaka a hannunsa, Abubakar yace "ango kasha kamshi. Menene kuma na zuwa da rufe kofa haka? Common ka fito mu je za'a yi reception tare da bakin Takawa. Gaskiya muna binka bashi duk bamu san da maganar ba bamu shirya komai ba" Adam bai ce komai ba sai ya matsa ya basu guri suka shigo, dogarin ya ajiye jakar hannun sa ya mika gaisuwa ta musamman ga Adam sannan ya fita.

Sulaiman yana kare wa palon kallo yace "wow" sai ya zauna akan kujera yace "amma fa mu mun sani" Adam ya juyo yana kallon sa yace "What?" Sai yayi dariya "wallahi kuwa. Daga nan aka kira Baba shekaran jiya aka gaya masa yau za'a yi, shi yasa ya hana ka tahowa yace sai yau, shi ya nema yace zaiyi maka walicci, mu kuma ya kira mu muka taho tare" Adam ya dafe kansa "amma baku gaya min ba? Alkawari yace haka ne?"

Abubakar yayi dariya "ai gwara da ba'a gaya maka din ba da tuni ka bata wa mutane show, itama amaryar taka bata sani ba sai da aka daura, tana can tana halin nata, sai ka shirya shirin yin rarrashi" Adam yace "ya Salam" Abubakar yace "yanzu tashi ga kaya na taho maka dasu ka dauka ka saka ka fito a angon ka sak, mu kuma sai mu bude bakin aljihu muyi ta yi maka liki" Sulaiman yace "ni ko kamun ango ba'a yi ba, wai shin ma menene al'adun ku na aure a Igbo land!" Adam ya mike yana cewa "ba'a sani ba, nima ba sani ba, sai dai ku kama wani ba ni ba. Now park all your wahalas and all your likis and go, am not in the mood"

Abubakar yace "to va sako na bane ba ai, nima bani kayan akayi akace in kawo maka ka saka kuma ka fita gurin mutane, in kuma ka ki in je in gaya wa mai aiken cewa kace ba zakayi ba you are not in the mood" Sulaiman yayi dariya, Adam ya bata rai sannan ya dauki jakar kayan da yaron ya shigo da ita bai kara ce musu komai ba ya shiga cikin bedroom.

Bayan shigar sa Umar ya shigo shima tare da wasu cousins dinsu da kuma Zunnur, nan suka baje suna ta hira, Sanda ya fito gaba ki daya sai da suka tashi, complete set na jabba ne a jikinsa milk colour wanda ya dace sosai da hasken fatarsa kuma ya shiga da hular daya dora a kansa, agogon hannunsa da ya shiga da takalmin kafarsa wanda yake irin na sarauta (shambatse), fuskarsa kuma dauke da murmushi, sai dai zuciyarsa tana rawa dangane da wannan babban abinda ya same shi.

Suna fita guri ya kara rudewa da shagali, a cikin taron Hassan ya iso yana ta bada hakurin cewa yayi missing daurin auren "Baba ya gaya min ai tun jiya, da tare zamu taho kuma wani abu ya taso min da dole nace kuyo gaba, Allah ya sanya alkhairi Adam. Ina taya ka murna sosai" Adam da yaji nauyinsa duk ya kama shi yace "au kai ma ka sani kenan?" Hassan yayi dariya, "naso in fasa kwan ai, Baba ne ya hanani yana ganin cewa tun da aka boye maka anan din to akwai dalilin yin hakan. Tabbas nasan mai martaba ya zabe ka ne ya kuma baka auren Fatima saboda abinda ya hango a tare da kai. You really are a lucky man Adam. Am sure Fatimah will make you happy. She will be the best thing that happen to you"

Adam ya gyada kai "yes, am really lucky haka ne, but Fatima is not the best thing that happened to me, the best thing is Islam. It will always come first" Hassan ya gyada kai yana murmushi, tunda ya taho a hanya yake lissafin lamarin Adam da irin sa'ar da yake da ita a rayuwa, sai yanzu ya kuma fahimtar source of luck dinsa. Adam a ransa yai dadin daya kasance Hassan ya fahimci sarki ne ya hada aurensa da Fatima ba shi ya nema ba, duk da dai hakan is not completely true, amma tunda Hassan bai sani ba ai there is no need to tell him ko? A hankali tashin hankalin da yake zuciyar Adam ya fara rauzayewa yana komawa murna, it is going to be


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login