Showing 132001 words to 135000 words out of 300844 words
alkawarin da wannan malamin duban yayi mata "zaki yi kudi fiye da kudin da kike saka ran zaki yi" tayi tsaki "banza makaryaci" ta fada a fili. "Allah yaso ban bashi ko kwandala ta ba" ta dawo daki ta tarar Hassan ya fita ta koma tayi kwanciyar ta ta na jin duniya duk tayi mata kunci, me yasa ne duk plan din data shirya sai ya wargaje ne wai? Ita har yanzu fa ko quater din abinda take so bata samu ba. Wata zucuyar ta gaya mata ko dai tayi giving up ne ta koma school irin na Sumayya tayi karatu ko zata samu aiki ta dan kara wani abu? Tayi tsaki, kuma shikenan yadda ake ganin ta kuma sai aga ta koma makaranta? Wanda ma bai san cewa bata yi jami'a ba shikenan sai ya sani.
A haka har magrib tayi, dama yanzu tun dawowar su ta dawo da cook din su ta da ta cigaba dayi musu abinci saboda tana laulayin ciki, twins kuma shekaran jiya taje ta kaiwa su inna tsarabar su ta barsu a can zasu dan kwana biyu. Dan haka a daki take wuni sai dai ta fita taci abinci ta dawo, wani lokacin kuma abincin ma a daki ake kawo mata taci abinta takwanta. Balle yau da bata so taga fuskar kowa dan tana jin duk wanda ya kula ta zata iya rufe shi da masifa ko da kuwa babu laifin da yayi mata. Starting from Hassan dan da yasan haushin sa da take ji yau din nan da ko inda take ba zai dosa ba.
Tana zaune a kan sallaya ya shigo ya tsaya yana kallonta a ransa yana jin ba dadi akan irin yadda tayi reacting to labarin samun saukin Hussain. Baya son ya yadda da abinda kwakwalwar sa take gaya masa akanta. Yace "ki shirya in an jima zamu je gurin Aunty, ta shirya mana cin abinci na musamman dan murnar abinda ya samu Hussain" ta mike daga kan sallayar tana kallon sa "cin abinci na musamman? Saboda me? Saboda matar mai kudi ta samu ciki ko kuma saboda yar sarki ta samu ciki? Ni sanda na samu nawa cikin ko shan ruwa na musamman ba'a shirya min ba balle cin abinci, kai ni ko magana ta musamman ba'a gaya min ba" ya karaso tsakiyar dakin yana kallonta yace "da ni da Hussain duk daya muke a gurin Aunty, da ke da Fatima duk daya kuke a gurin Aunty, Aunty kuma uwa ce a gareni dan haka ina so ki san maganar da zaki fada a kanta. Ba kudin Hussain ko matsayin Fatima ne yasa zamu taya shi murna ba, ba kuma cikin jikin Fatima zamu yi celebrating ba, samun lafiyar Hussain zamuyi celebrating saboda ba wai abu ne common ace mutum yayi Cancer briefly ya warke ba, warkewar sa shine abinda zamuyi celebrating" ta cire hijab dinta tana ninkewa tana huci "eh dama ai kai kowa yana da muhimmanci a gurinka banda ni, ban isa in fadi magana akan kowa ba sai kace kar in kuma amma ni duk abinda za'a yi min mai baka gani, duk irin wariyar da ake nuna min kai baka gani" yaji bacin ransa yana karuwa, yace "dan Allah Ruqayyah kar ki bata min rai bayan ina cikin farin ciki, can't you at least pretend to be happy ko dan in shiga cikin yan uwana cikin jin dadi? Menene problem dinki ne wai? Yanzu rashin son da kuke yiwa Hussain har ya kai baki damu da samun lafiyar sa ba" ta ajiye hijab din ta hau kan gado ta kwanta tace "tunda bata maka rai nake yi it will be better idan banje gurin ba, kar in cigaba da bata maka ran acan ma. And ina taya Hussain farin ciki da samun lafiyar sa, kawai dai am not in the mood for celebration ne" ta ja bargo ta rufe har fuskarta.
Haka ya juyo ya fito daga dakin ya shiga nasa ya shirya ya fito, ko kallon dakinta baiyi ba ya fita ransa duk babu dadi, shi duk ba haka yayi tsammanin auren sa zai kasance ba, shi ba haka yayi tunanin matar da ya zaba a cikin matan duniya zata ke treating dinsa ba, shi ya saka ran total submission daga gurin matarsa yadda zata faranta masa shima kuma ya faranta mata. Bai taba tsammanin yarinya karamar daya dauko daga cikin talauci ya kawo ta cikin daula zata raina abinda yake dashi take kuma mayar masa da magana aduk lokacin daya fadi wani abu ba, bai dauka young and innocent hassanar sa zata iya fadar bakar magana akan Hussain ba ballantana Aunty.
Godiyar Allahn da yayi shine duk sun san tana fama da laulayin ciki, duk da dai sai da da yawa daga ciki suka yi korafin ya kamata axe ta daure ta dan leko ko na yan mintuna ne ta koma. Dole ba da son ransa ba yayi musu karya yace ai jikin ne ya matsa mata sosai. Sai yayi ta sha'awar Hussain yadda Fatima take makale dashi tana jinyar sa shima yana jinyar ta, a tare suke rige rigen serving junan su abinci , sai yayi tunanin shi yaushe rabon da Ruqayyah ta zauna ta zuba masa abinci? A table yake zuwa ya tarar mai girki ta ajiye ya zuba ya ci ya tashi ya tafi. Ko sanda tana girkin ma bata iya jiransa sai ya dawo daga office cin kayanta take yi in ya dawo yaci shi kadai.
A cikin kwanakin da suka biyo bayan nan abubuwa duk sun kara tabarbarewa Hassan, Ruqayyah gabaki daya ta kara rikice masa ya kasa gane kanta gabaki daya, har sai da wata zuciyar ta raya masa cewa ya je ya kai karar ta gurin Baba amma sai ya fasa ya saka ta a gaba da nasiha duk da dai cewa shi bai san laifin da yayi ba. A cikin wannan yanayin ne akayi bikin Safiyya da Jabir, a matsayin Hassan na babban yayan amarya sannan babban abokin ango amma haka yayi bikin duk babu dadi saboda cikin gidan sa babu dadi, saboda bai yi dace da mace ta gari ba.
Bayan hakan ne Minal tazo mata ziyara. Suka shige cikin dakinta suka zauna Minal tana cewa "kai Ruqayyah wannan dakin naki ai yayi datti da yawa, kwanan ki nawa rabon da ki share shi?" Ruqayyah tace "wannan kuma matsala ta ne. Ke dai ki zauna a nan dan yallaban gidan nan ya xe baya son mu'amala ta dake kuma dama kwana biyun nan ba dadi muke yi dashi ba" Minal tace "mijin naki ne ba kwa dadi da shi? Lallai sannun ki da aiki, in dai ta nine ya kwantar da hankalin sa in baya son inzo gidan sa ba zan kuma zuwa ba dan nima ina da gidan mijina ba wai a titi nake ba" Ruqayyah tace "ke ba akan ki bane ba, ni din ce dai kawai duk zuciyata babu dadi kwana biyun nan. Kinsan matar gidan nan kuwa ciki ne da ita?" Minal tace "wacce matar gidan? Aunty?" Ruqayyah tayi dariya tace "ke yar iska ce Allah. Auntyn ce zata yi ciki dan baki da kunya. Gimbiyar gidan nake yi miki magana matar dan goten kaduna" Minal ta bude ido "to fa babbar magana. Ni da nake ta saka ran ta hanyar rashin haihuwar ta ne maganar Malam zata tabbata" Ruqayyah tace "ke dai bari, abin nan ba karamin daga min hankali yake yi ba wallahi, musamman ace ta haifi namiji shikenan fa mu da dukiyar su daga hange sai leke sai harara daga nesa, duk yayan da zan tara zasu yi ta bin yayanta ne a baya kamar yadda mijina yake bin mijinta a baya" Minal tace "ki zo mu koma Ruqayyah, kina bukatar taimako, rayuwarki tana cikin matsala sai an hada miki da addu'a. Kinga fa ni yanzu albishir din da na zo inyi miki shine ciki ne dani, idan kinga yadda Alhaji, mahaifiyarsa da yan uwansa suke nan nan dani sai kinyi mamaki, ita fa uwargidan nasa da suke cewa matar so yanzu babu son duk ya dawo gurina da abinda yake cikina. Tana nan kamar zata mutu kullum kofarta a rufe" Ruqayyah tace "Allah Minal? Yanzu ciki ne da ke? Kai amma na taya ki murna wallahi Allah ya raba ku lafiya" daga nan sai ta bata labarin nata cikin itama suka taya juna murna suka cigaba da plans din su na yakar mutanen da suke gani a matsayin makiyan su.
Rayuwa ta cigaba da tafiya ba tare da kowa yasan cewa Hussain ba wai warkewa yayi da gaske ba, hatta Hassan bai san cewa ciwo yana cin Hussain kadan kadan ba, itama kuma Fatima saboda tana fama da nata laulayin cikin sai ta gaza gurin fahimtar changes din da yake samu. Ciwon ciki ne yafi damunsa mostly idan yaci abinci amma sai ya boye yaki yarda fatima ta gani. Duk sanda kuma baya jin ciwon hakan keeping wide smile a fuskarsa wanda yake boye damuwar da take cikin idanuwansa, amma duk da haka damuwar bata boyu ga Hassan ba, tambaye shi "wai kai me yake damunka ne?" Sai yace "ni babu abinda yake damuna, maybe idonka ne yake nuna maka hakan" "babu wani ido na, gashi nan har ramewa naga kayi? Are you sick or something?" Hussain ya daga kafada yace "babu wani abu, gajiya ce kawai, aiki yayi min yawa ina bukatar hutawa. Ga kuma marar lafiya ina da ita a gida" ya fada yana murmushin dan ya kawar da maganar amma Hassan bai yarda ba, sam zuciyarsa bata yi masa dadi da yanayin na Hussain.
Baya son abinda zuciyarsa take fada masa akan yanayin na Hussain amma kuma dole ya kamata ya bincika wannan angle din ko dan ya samu nutsuwar zuciya. Wannan ya sa ya tura sako zuwa ga doctor din Hussain, ya roki sanin health status din Hussain duk da cewa yana tunanin ba zasu bashi ba amma kuma ganin cewa ya tura sakon ne da same email da ya fara registering Hussain sai ya saka ran samu. Sai da aka kwana biyu sannan sai ga phone call daga doctor din.
Yana office ne a lokacin, yaga number da code din India sai jikinsa ya bashi doctor din ne tunda bashi da business da wani a India kuma yana saka ran ji daga doctor din. Sai dai kuma sai yaji yana tsoron dauka dan bai san abinda zaiji ba, da kyar dai ya hakura ya dauka ya kara a kunnensa yare da cewa "Hello" doctor din yace "are you Hussain aminu's brother?" Hassan yace "yes, I am" sai ya fara fada "then why are you not bringing him back to hospital? He should be in the hospital right now taking treatment" Hassan ya runtse idonsa yana jin tamkar wukake doctor din yake soka masa a kirjinsa yace "but he said the operation was a success" doctor yace "no it wasn't, and we told him that. You should bring him in again, he is .... ....." Hassan bai karasa jin maganar doctor din ba ya saki wayar hannu sa ta fadi kasa.
*Kuyi hakuri babu yawa, bana so in barku jira babu dadi shi yasa na baku a haka, tomorrow's episode will insha Allah be longer and more action packed*.
Wannan littafin na siyarwa ne, idan kin ganshi a wani guri na sata ne, in kina so ki karanta halaliyar ki kiyi min magana through WhatsApp ta wannan number din 08067081020
*The Accident*
Ko bi ta kan wayar ta sa da ya yar bai yi ba, bai kuma kula da mutanen da suke tambayar da ko lafiya suka gandhi a rikice ba, kokarin sa kawai shine ya ganshi a gida ya ganshi a gaban Hussain kuma ya yi convincing dinsa su tafi asibiti. Ko parking bai kammala ba ya fito ya rufe kofa ya doshi part din Hussain dan yaga Adam ma'ana Hussain yana gida kenan.
Yana shig ya samu daya daga cikin yaran Fatima "ina Fatima take? Me gidan yana ciki?" Ganin Yadda hankalinsa yake a tashe ya sa ta rude "gimbiya bata nan, sun fita dazu ita da Aunty Khadija, amma yallaban yana ciki banga saukowarsa ba....." bai jira ta karasa bayanin ta ba ya wuce ta ya haura sama da sauri ya nufi wing din Hussain. A palo ya same shi a kwance akan doguwar kujera da diary dinsa a gabansa, idonsa a rufe, hannun daya akan cikinsa dayan kuma akan diary din. Motsin shigowar Hassan ne ya saka shi bude idonsa da sauri. Sai kuma yayi kokarin mikewa zaune yana dan cije lips dinsa amma kuma fuskarsa da murmushi "hey, gidan mijin aure ne fa kake shigo min kai tsaye, ko baka san ni mijin aure bane ba?" Hassan ya share shi ya nufi diary din kamar zai dauka sai Hussain ya riga shi, a tura shi bayan sa yace "sirri ne na gaya maka" Hassan yana kallon sa yana lura da yadda yake iyakacin kokarin sa na ganin yayi keeping straight face sannan yace "why? Me yasa zaka yi mana karya Hussain? Ko zaka yi wa kowa karya ni mai yasa zaka yi min Hussain? Why do you choose to suffer alone bayan ba kai kadai aka haife ka ba tare dani aka haife ka? Me yasa zaka ware ni when you need me the most?" Hussain ya dauke kansa gefe, ya fahimci cewa ya sani, sai ya girgiza kansa yace "what does it matter in na gaya maka din, babu abinda zaka iya yi min, babu abinda kowa zai iya yi min, wanda zai yi min komai na gaya masa na kuma roke shi ya bani lafiya, na saka kun taya ni rokonsa ya bani lafiya, tunda ka ga bai bani ba to lafiyar bat da alkhairi a gurina, shi kadai yasan me yake nufi da ni".
Zuciyar Hassan ta karye ya durkusa a gaban Hussain tare da dafa gwuiwar sa yace "Hussain dan Allah kazo mu koma asibiti, dan girman....." Hussain yayi sauri ya rufe masa baki "mun gama maganar nan Hassan, na roke ka kuma ka amince, kayi min min alkawarin ba zaka sake mayar dani asibiti ba. Hassan likitoci ba zasu hana mala'ikan daukan rai ya dauke ni ba, kudina dukka ko zan karar dasu ba zasu kara min adadin kwanakin da aka kayyade min ba. Dan Allah Hassan kar ka tilasta min komawa asibitin nan, bana so in mutu a zagaye da likitoci da injina,bana son in karasa sauran kwanaki na a asibiti looking at faces din mutanen da basu da muhimmanci a rayuwata. Na fi son in zauna a gida tare da ku, tare da Fatima, nafi son inyi making use of my last days doing abinda zai amfani lahira ta ba wai neman lafiyar da babu wanda zai bani ita ba. Wancan aikin da akayi min na gaya maka na amince ne dan in faranta maka ba wai dan raina yana so ba" Hassan ya sake girgiza kansa "ba dan ni ba, yanzu kayi dan Fatima, dan abinda yake cikin Fatima" Hussain ya dauko diary dinsa yana budewa yana murmushi yace "Allah baya taba barin wani dan wani yaji dadi, ko babu ni nasan abinda yake cikin Fatima yana da uba, nasan ba zai yi kuka maraici ba, zai samu gatan uba a gurinka kuma a bangaren mahaifiyarsa ma ba zaiyi rashin komai ba".
Hassan ya zauna sosai yana kallon Hussain guiwoyin sa sunyi sanyi da suka kasa cigaba da daukan sa, ya runtse idonsa yana fatan hawaye yazo masa ko zaiji sanyi a zuciyarsa. A ransa yana addu'a "Allah in zaka dauki wani a cikin mu Allah ka dauke ni ka bar Hussain, Allah ka dawo da ciwon Hussain kaina shi ka bashi lafiya ya Allah. Allah kar kasa Hussain ya tafi ya barni Allah" ya bude idonsa sai suka hada ido da Hussain yana yi masa murmushi yace "don't cry bro, kar kabada maza mana, everything is going to be okay".
Babu yadda Hassan bai yi ba amma Hussain ya tubure yace shi babu asibitin da zai koma, babu aikin da za'a sake yi masa, kuma ya roke shi Allah da Annabi kar yabari kowa yaji cewa ciwonsa ya dawo. "Bana so inga hawayen su, ga halin da Fatima take ciki bana so in tayar mata da hankali" sai dai Hassan bai hakura ba sai da ya kuma kiran wancan doctor din yayi masa bayanin irin taurin kan Hussain da dagewar da yayi akan ba zai koma ba, sai doctor din yayi referring dinsu to wani oncologist din a nan Nigeria ya kuma bawa Hassan shawarar ya lallaba Hussain ya kaishi can "ko ba za'a yi masa aiki ba sai a bashi drugs din da zasu rage masa radadin ciwo, cos he is in pain right now, ina mamakin ma yadda har kace yan iya harkokin sa har yana boye ciwonsa, he really is strong". Hassan ya gyada kai yace "the strongest man I have ever known".
Likitan da aka hada shi da shi a Abuja yake da private hospital dinsa kuma ya kware sosai a aikinsa. Hassan ne ya shirya yaje asibitin, ya tarar already an aiko da record din Hussain da komai daga can asibitin dan hak kawai takardu ya ciccike sannan ya koma Kaduna ya fara yakin lallaba Hussain akan ya taho yaga wannan likitan. Da kyar ya yarda suka zo, da alkawarin cewa ba kwantar dashi za'a yi ba. Da daddare suka zo secretly saboda gudun sa idon yan media, Doctor din ya duba shi sosai, yayi masa hotuna sannan yayi masa prescribing drugs din da zasu taimaka masa wajen dulling pain din da yake ji. Amma Hassan bai ji yayi promising komai ba. Haka suka karasa kwana a hotel tunda Hussain yaki kwana a asibitin.
Da safe ne da zasu taho yake cewa "da akwai wani abokina Sadiq, dan sarkin Abuja ne ina jin baka san shi ba dan a wani zuwa da nayi London muka hadu dashi kuma bai taba kawo min ziyara ba nima ones na taba zuwa gidan su tunda shi ba mazauni bane ba. Amma we are very close a waya munsan affairs din juna" Hassan yace "to