Showing 219001 words to 222000 words out of 300844 words

Chapter 74 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2105

hada kai suka yi gaba daya su biyar din suna kuka kamar rayukan su zasu fita. Baya jin da ace labarin mutuwar Ruqayyah aka kawo musu zasu yi irin wannan kukan kuma su shiga irin wannan tashin hankalin ba, sai yaji cewa ba su yake tausayawa ba, Ruqayyah yake tausaya wa, in dai har iyayen ta zasu iya yin irin wannan kukan su zubar da irin wannan hawayen a kanta baya jin tana bukatar wasu sauran alhakin dan rusa rayuwar ta. Hakkin iyayen ta ma kadai ya ishe ta.

A gidan ya bar Sumayya yace ta kwana tare da iyayenta ta kwantar musu da hankali, daga nan gida Alhaji Kabiru ya je, ya yi packing a kofar gidan sannan ya kira wayar sa ya gaya masa yazo. Ba'a jima ba sai ga shi ya fito da kansa yana murmushi tare da yi masa iso kan cewa ya shiga cikin gidan, shi kuma sai yaki shiga. Yanayin fuskarsa ya katsewa Alhaji Kabiru murmushin sa, dan ko makaho ya shafa fuskar Hassan yasan hankalin sa a tashe yake, yace "lafiya kuwa Hassan? Da fatan dai duk iyalin lafiya lau suke?" Hassan ya shafa fuskarsa yana jin ina ma dai bai zo ba? Ina ma dai ya bi maganar Sumayya ya bar police sun zo sun gaya masa amma sai yaje jin in yayi haka kamar bai kyauta ba, kamar honouring din Alhaji Kabiru zaiyi by telling him by himself.

Yace "iyali duk suna nan lafiya Alhaji. Nazo ne in sanar maka da cewa an samu labari, akan Amina" Alhaji Kabiru yayi shiru yana kallon sa, ya kasa cewa komai dan yanayin Hassan ya tabbatar masa da abinda yake gayawa kansa kullum cewa Minal bata raye, kawai dai rashin ganin gawarta ko kuma wani abu da zai tabbatar masa da haka ne yasa har yanzu yake dan saka rai kadan. Jin yayi shiru yasa Hassan ya kara da cewa "sai hakuri Alhaji, Allah yayi mata rasuwa tun a ranar data bar gida".

Alhaji Kabiru ya rufe ido yana jin information din yana sinking sai kuma ya bude yana kallon Hassan da yaji kamar zaiyi kuka yace "bismillah Hassan, mu shiga ciki sai kayi min bayanin yadda ka riga ni samun wannan labarin" Hassan ya gyada kai, da yaso suyi magana briefly amma ganin yanayin alhajin ya saka yaji ya kamata yayi masa bayanin komai dan duk da cewa Minal ba mace ta gari ba ce ba amma still matarsa ce kuma dansa ne ta tafi lahira dashi a cikin ta.

Kwana biyu bayan nan Hassan bisa jagorancin police suka raka Alhaji Kabiru, baban Minal da kuma yayyen ta guda biyu zuwa inda kabarin ta yake.

Shirye shiryen zuwa court ake tayi daga dukkan bangarorin uku, bangaren Hassan, Fatima, da kuma Ruqayyah da har yau take tsare a asibitin ƙwaƙwalwa a bisa kulawar yan sanda. Sai dai sun samo mata maganin baccin ta kullum tana sha tana yi bacci kadan kamar yadda dama a gida kadan din take iya yi.

An samo mata lawyers har gida uku amma duk babu wanda yayi mata, sai a karshe bayan ta kwana biyar a hannun police sannan aka samo mata wanda yayi mata. Barrister Lukman.

Tana kallonsa taji cewa yayi mata, so smart looking, sannan ga record dinsa na cewa baya loosing case no matter how bad it is sai yabi ya warware shi, bai damu da ko client dinsa yana da gaskiya ko kuma bashi da gaskiya ba, abinda ya damu dashi shine yayi winning ya kuma keeping reputation dinsa na cewa baya loosing case. Kudinsa yana da tsada sosai, amma tasan idan tayi nasara to yaci kudinsa dan kudin are nothing compared to going to jail and loosing everything. Dan haka ta zauna ta tsara masa duk yadda take so al'amurra su kasance, making sure cewa shi kansa da yake lawyer dinta bata fada masa gaskiyar magana ba amma shi ya gane cewa she is guilty ita ma kuma tasan ya san bata da gaskiya. Amma sai ya gyada kai yace "this is a piece of cake. Consider it done".

A bangaren su Hassan sun hada kai sun shigar da single kara da sunan Fatima, sunyi staring dukkan charges din da suke accusing Ruqayyah with, sannan sun shirya dukkan shaidun su suna ji a ransu cewa Ruqayyah bata da hanyar kubucewa wannan shirin nasu.

Ba'a saka da nisa ba shari'ar saboda ta manya ce, aka saka rana, rana tazo sannan aka zauna zaman court, kowa ya hallara har da miji da kuma yan uwan Minal wadanda suka zo da ganin an yi serving justice for Minal. Alkali ya shigo aka tashi sannan ya zauna kowa ma ya zauna a gurin sa. Lawyers din Fatimah gida biyu na Ruqayyah guda daya, aka gabatar da kara sannan alkali ya bayar da da umarnin aka shigo da Ruqayyah, jikinta sanye da kayan marasa lafiya, hannunta da ankwa.

Aka karanta wa Ruqayyah charges dinta guda biyu. Na farko zambo cikin aminci, inda ta boye mutuwar kawarta tayi replacing dinta da mutuwar matar kanin mijinta dan mijinta ya samu gado ita kuma ta samu daga gare shi. Na biyu salwantar da rayuwar jaririn dan Fatimah. "How do you plead?" "Not guilty" ta fada direct.

Daga nan sai Lawyer din mai kara guda daya ya tashi ya fara bayani, ya dauko labari tun daga kan rasuwar Hussain, tafiyar su Fatima a mota da Ruqayyah da Minal da kuma accident din da suka yi a hanya. Zuwa kiran da Ruqayyah tayi wa Hassan da wayar Fatima ta gaya masa cewa sunyi accident kuma Fatima da driver sun mutu, zuwa karyar da Hassan ya kamata tayi akan bata san inda Minal take ba sannan kuma da karyar data sake yi dan rufe waccan karyar.

Ya kira wo shaidar sa ta farko Hassan yazo yayi bayani dalla dalla na yadda suka yi da Ruqayyah a waya har zuwa yadda yaga kayan baby a motarta da abinda tace masa, sannan kuma ya dora da mugayen furucin da tayi akan Hussain wanda har ta dalilin haka ya datse igiyoyin aure tsakanin su.

Shaida ta biyu mijin Minal yazo ya fadi abinda Minal tace masa sanda zata bar gida sannan kuma Maman Minal ta bayar da shaida akan abinda Ruqayyah ta fada sanda taje tambayarta game da Minal, tana bayani tana kuka. Sai kuma aka kirawo Sumayya tabbatar da cewa a gabanta ne akayi maganar.

Daga nan sai mai gabatar da kara ya cigaba da bayanin yadda shekaru suka tura ba tare da kowa yasan cewa Fatima tana raye ba sai yanxu da ta dawo gida da kanta sannan aka san cewa va ita aka binne ba, Minal ce. Ya kira Fatima a matsayin shaida ta gabatar da kanta sannan tayi bayani yadda tafiyar tasu ta kasance da kuma yadda Minal ta gaya musu labarin mutuwar Hussain a hanya. "Wannan shine kawai abinda zan iya tunawa. Daga wannan maganar ban kuma sanin inda kai na yake ba sai dana farka na ganni a imo State" sai ta dora da labarin abinda ta sani na daga zamanta a gidan su Adam da irin taimakon da Adam yayi mata har ta dawo cikin hankalinta zuwa dawowar su gida.

Shaida ta gaba shine Adam, shi kuma yayi bayanin rabuwar su da Hassan a Abuja zuwa tsintar Fatima da yayi a hanya ya kuma tabbatar da cewa babu ciki a jikinta sanda ya tsince ta da kuma kama shi da baban sa yayi ya tafi dasu ba tare da ya varshi ya sanar wa da yanuwan Fatima cewa tana gurin sa ba. Yayi bayanin uzurin sa na daukan wannan lokaci batare da yayi contacting yan uwan Fatima ba. "Mu duk mun dauka cewa ana nan ana nemanta, bamu san cewa an dauka ta mutu bane ba".

Daga nan sai daya lawyer din ya tashi yayi concluding da cewa "da wadannan shaidun namu muke fatan mai girma mai Shari'a zai duba ya tabbatar da cewa duk laifukan da ake zargin wannan baiwar Allah dasu ta aikata su, dan idan har bata salwantar da jaririn ba menene nata na boye mutuwar kawarta? Me yasa zata ce Fatima ta mutu bayan bata mutu ba? Mai yasa zata yi ta karya akan maganar?

"Mutum hudu ne suka yi tafiyar mai girma mai Shari'a, biyu daga cikin su suna dauke da juna biyu. Ga dai gawawwaki can an binne ta driver da mace mai ciki wadda a yanzu aka tabbatar gawar Amina ce, ga kuma Fatima ta dawo babu ciki babu da kuma bata da masaniyar abinda ya faru da cikin nata. Wanda ya rage mana kadai ita ce Ruqayyah, wadda ita kadai ce ta fito fes daga cikin hatsarin dan haka ita muke sauraro tayi mana bayanin inda abinda yake cikin Fatima ya shiga, da kuma dalilin da yasatace Fatima ta mutu bayan ga Fatima a gaban mu kuma da rai a jikin ta"

Alkali ya gama rubuce rubucen sa sannan ya dago kai yana kallon barrister Lukman yace "lawyern wadda ake kara, kana da abin cewa?"

Barrister Lukman ya mike yayi gaisuwa sannan yace "duk abubuwan da masu kara suka gabatar na yarda dasu, ban musa ba kuma ko kadan bani da ja a game dasu. Amma abin da zanyi bayani akai shine; menene dalilin da yasa Ruqayyah ta fadi wannan maganar, menene dalilin da yasa tace Fatima ce ta mutu ba Amina ba? Amsar itace, saboda abinda idanuwan ta suka gane mata kenan."

Kamar yadda wannan hatsarin yayi sanadiyar rayukan lawan driver da Amina da kuma abinda ke cikin Amina, ya kuma yi sanadiyyar daukewar tunani tare da mantuwa ga Fatima, haka yayi sanadiyar samun jirkicewar ƙwaƙwalwa ga Ruqayyah. Ruqayyah tana iya ganin abin da ba haka bane ba tace haka ne, kuma ita a idanun ta haka ta gani. Ruqayyah ta samu wannan matsala ne a gurin da hatsarin ya faru sakamakon buguwa da tayi da kuma irin horror din da tayi witnessing na kawarta aminiyarta tana ci da wuta tare da driver a cikin dajin da babu gida gaba babu gida baya. Wannan kadai is enough ya haukata mutane da yawa daga cikin mu. Wannan abin data yi witnessing ne ya saka kwakwalwar ta ta nuna mata cewa ba kawarta Amina bace ba, Fatima ce, sai kuma a cikin kanta ta shafe tunanin cewa sun taho tare da Amina a wannan tafiyar gabaki daya"

Gabaki daya yan court din sai suka koma kallon juna suna mamakin wannan rainin hankalin da wannan lawyern yake so yayi musu. Hassan zai mike Jabir ya rike shi ya hana shi tashi.

Alkali yace "kana da hujjojin da zasu tabbatar mana da abinda kake cewa?" Lukman yace "of course" sai ya fara gabatar da shaidun sa, shaida ta farko shine likitan da a yanzu Ruqayyah take asibitin sa, wanda ya taho da file din Ruqayyah ya kuma yi bayani akan diagnosis din da yayi mata shekaru uku da suka wuce, "tabbas tana fama da extreme hallucinations wanda har ya kaita ga tayi overdose na sleeping pills danta samu tayi bacci, tun a lokacin na dora ta akan magunguna kuma har yanzu tana kan shan magungunan bata warke ba" Lukman yace "zaka iya fadar lokacin da kake tunanin ta hadu da wannan lalura ta gane gane?" Doctor yace "gaskiya ba zan iya fadar exact lokaci ba, amma dai nasan ba dashi aka haife ta ba samu tayi daga baya ta dalilin wani abu daya faru da ita" Lukman yace "kana ganin hatsarin mota tare da ganin wani abu na tashin hankali zai iya jawowa ta samu wannan matsalar?" Likitan ya tabbatar da cewa eh accident ko tashin hankali mai tsanani zai iya samar wa da mutum wannan cutar. Sai kuma ya sake yi masa wata tambayar, "shin accident zai iya sakawa wani memory na mutum ya goge daga kansa yaji tamkar abinda ya faru bai faru ba? Likitan ya sake amsawa da "ofcause, memory lost yana daya daga cikin mental problems din da ake yawan samu as a result of car accident"

Sai Lukman ya karbi file din ya mika wa alkali tare da cewa "wannan ya nuna cewa Ruqayyah, a matsayin ta na mutum kamar komai tana iya samun wadannan cutuka dana lissafa a baya" alkali ya bude file yana dubawa, duk maganganu ne irin na likitoci, a kasa kuma an rubuta "mentally unstable".

Sai shaida na biyu shine therapist dinta, shima yayi bayanin yadda take yawan yi masa complain akan cewa tana tsorata tana kuma ganin abubuwa wadanda ita da kanta tasan sauran mutane basa gani. Ya kuma kara bayani akan kadaicin da take ciki da kuma yadda mijinta ya sake ta ya auri kanwarta, da kuma yadda iyayenta suka juya mata bata. "Wannan dalilin zai iya sakawa ta zamanto har yanzu bata warke ba, saboda kadaici kadai yanaiya saka cuta ballantana dama ya tarar da cutar".

Shaida ta uku ita ce Luba yar aikin ta, tayi bayanin yadda suke jin tana ihu sometimes cikin dare, da yadda take kasancewa kullum cikin kadaici. Sai police suka bayar da shaidar yadda sanda suka je kamata ta bisu salin alin ba tare da jayayya ba, abinda Lukman ya kira da "innocent submission" hakan yana nuna cewa tasan tana da gaskiya shi yasa bata gudu ko ta yi tirjiya ba.

Ga mamakin su sai ya kira Sumayya ita ma a matsayin shaidar sa, ya tambaye ta ko a zaman sa tayi na jinyar Ruqayyah ta lura da irin wadannan alamomin a gurin ta? Sumayya ta amsa da "eh, tana tsorata cikin bacci kuma tana kasa yin bacci, sometimes sai anyi mata allura ko ta sha maganin bacci" Lukman yace "amma me yasa baku dauki abin da muhimmanci ba?" Sumayya tace "mu a gurin mu firgita ce saboda abinda ya faru da ita, mu a gurin mu abu ne da zai zo ya wuce" yace "amma ya wuce?" Tace "ban sani ba, bayan mun bar asibiti muka daina kwana tare, dan haka ban sani ba ko ta daina" yace "amma kinsan tayi kokarin kashe kanta ta hanyar overdose ko? Tunda an ce ke ce tare da mijinta, oh sorry mijin ki, kuka kaita asibiti" tace "eh mun kaita asibiti, amma daga nan ta nuna mana bata bukatar taimakon mu dan haka muka rabu da ita"

Sai ya kira Hassan shima, kusan irin tambayoyin Sumayya ya maimaita masa inda Hassan din yace shi sam bai san wani mental issue a tare da Ruqayyah ba. "duk abinda ta fada, karya take yi. Saboda ita din tafi shaidani iya shaidanci, ta sani, tana sane duk abinda tayi kuma wallahi she will never go free, sai ta fadi inda ta kai jaririn nan dan babu wani tabin hankali da take dashi" Lukman yace "kai likita ne da zaka ce bata da tabin hankali bayan ga likita nan ya fadi cewa tana dashi?" Hassan yace "ni tsohon mijinta ne kuma uban ƴaƴan ta, na san duk irin abinda zata iya aikatawa...." Lukman yace "Tsohon mijinta kuma mijin kanwarta a yanzu, wannan shine dalilin da yasa ba ka fahimci cewa bata da lafiyar kwakwalwa ba saboda kana can kana bibiyar kanwarta a lokacin da ita kuma take struggling da lafiyar ta. Bayan ta rasa kafarta ta rasa kunnuwan ta ga kuma matsalar ƙwaƙwalwa da take damunta kai kuma sai kazo ka hada ta da saki uku ka raba ta da ƴaƴan ta sannan kaje ka auri kanwarta".

Lawyer din Hassan ya mike yace "objection my Lord, lawyen wadda ake tuhuma yana magana akan abinda bashi da dangantaka da abinda ya hada mu anan" alkali yayi wa Lukman warning sai yace Hassan yaje ya zauna, amma kuma a ransa ya samu abinda yake so, ya nunawa alkali irin rashin adalcin da Hassan yayi wa Ruqayyah.

Bayan Hassan ya zauna sai Lukman ya rufe jawabin sa da cewa "client dina ta rufe maganar mutuwar Amina tace Fatima ce ta mutu saboda haka idanuwan ta suma gane mata, sakamakon matsala ta tabin hankalidata samu a sanadiyar wannan hatsarin da suka yi. Sannan client dina bata da masaniya kwata kwata akan inda cikin Fatima ya tafi, dan ita sanda ta farka bayan anyi matsayi gawar Fatima ta gani tana ci da wuta. Ita ma, kamar kowa tayi tunanin Fatima ta mutu ne a ranar" ya yi gaisuwa ya koma ya zauna.

Kotu tayi shiru ana jiran alkali yayi magana sai Adam ya daga hannu yace yana da magana idan alkali ya yarda, alkali ya bashi dama ya sake fitowa ya tsaya yace "akwai abinda ban fada ba a cikin labarin dana bayar, ban fada bane ba kuma saboda ban tabbatar ba kuma bana so in bada shaida akan abinda ban tabbatar ba, bana so in tsaya a gaban Ubangiji saboda nayi shaidar zur" alkali yace "menene abinda baka fada ba?" Yace "lokacin dana taho daga Abuja a mota ina duban hanya ko zanga su Fatima, I saw something ta mirror, someone that looked like Ruqayyah was carrying something that looked like a baby. Dana juya kuma sai naga ban gansu ba sun bace a cikin bishiyoyi"

A take court din ta rude da hayaniya, alkali ya ajiye biron hannunsa yana kallon Adam yace "amma me yasa dazu baka fada ba?" Adam yace "saboda ban tabbatar ba, ta mirror kawai na gani dana juya kuma ban gani ba, bayan nayi gaba kadan kuma sai na ga Fatima"

Alkali ya yi rubuce rubucen sa sannan yace ya daga shari'ar zuwa sati mai zuwa inda zai yanke hukunci. Sannan kuma ya bayar da bail din Ruqayyah kamar yadda lawyer dinta ya nema.

A matukar fusace Hassan ya dawo gida, a ranar duk yadda Sumayya ta kai da iya kalamai da iya lallabawa amma ta kasa kwantar masa da hankali, "ta kashe dan Hussain, and she is going free" Sumayya tace "Habibi, bana jin Ruqayyah ta kashe jaririn nan fa, bana jin Ruqayyah zata iya kisa ballantana kisan jariri. Ya kamata mu duba possibility na kasancewar abinda lawyer din nan yake fada gaskiya ne, tunda akayi accident din nan Ruqayyah has not been herself, what if he is right?" Ya ture hannun ta daga jikinsa yana mikewa a fusace "don't tell me kin yarda da wancan rubbish din, don't tell me you love your sister so much that ba zaki iya ganin laifin ta ba ko da kuwa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login