Showing 147001 words to 150000 words out of 300844 words
mana?
Ta samu gefen gado ta zauna kusa da kafafuwan Khadijah tana cigaba da kiran number din Hassan da Hussain amma duk babu wanda ya dauka. Ta gaji ta tashi ta daga window tana hangen titi ko zata hango tahowar su amma babu alamar su.
A lokacin ne taji an rusa ihun kuka da muryar Nafisa, taji wani abu ya tsirga mata tun daga kanta har tafin kafarta. Taji wani irin daci a makwogwaron ta. Sai taji sautin kukan Nafisa yayi mata kama da sautin kukanta a lokacin mutuwar Alhaji Aminu uban ƴaƴan ta.
Khadijah da take kwance ta mike da sauri ta tafi dakin Nafisa tana hardewa, a hanya suka hadu da Zulaihat itama tana dosar dakin Nafisa. A dai dai lokacin Aunty taga tsayawar ambulance a kofar gidan. Ta sandare a gurin tana kallo aka bude gate aka shigo da ambulance din sannan akayi packing aka bude baya, taga police sun fito, sannan taga Hassan ya fito amma bata ga Hussain ba sai taga an turo gado da wani abu da yayi kama da gawa akai. Ta saki labulen sannan a hankali ta zame ta zube a gaban tagar.
Hassan yabi gawar Hussain da kallo ya tabbatar an shiga da ita ciki sannan ya juya gurin limamin unguwar su da ya biyo bayan motar rasu. Ashe har sun samu labari sun zauna jira. Hussain mutumin kirki.
Liman yace "dare yayi yanzu, sai dai yayi kwanan keso sai da safe ayi masa sallah" Hassan ya gyada kai kawai. Liman din yace "da assuba zan tura aje makabarta a haka kabari, yanzu kuma zan sika a siyo likkafani, sai asa lokaci saboda yan uwanku su sami sallah" sai Hassan ya girgiza kansa yana kallon garden din gidan, inda tun suna raya suke yin shuke shuke shida Hussain har suyi rigima in wani ya tabata wani yace "anan za'a binne shi, a cikin garden din mu. Nayi masa alkawarin zanke zuwa kabarinsa kullum ina masa addu'a. Anan za'a binne shi a kusa dani"
Wannan littafin na siyarwa ne, idan kin ganshi a wani gurin na sata ne, in kina so ki karanta halaliyar ki kiyi min magana ta WhatsApp through wannan number 08067081020
Sorry about the typos please
Mai sharing littafi, bana ganin ki Amma *Allah* yana kallon ki kuma na barki da shi.
*Hidden Strength*
Sumayya yau bata tashi daga school ba sai da akayi kusa kiran sallar magrib. Ta gaji likis saboda yau sun safe suke lectures babu kakkautawa, dan yau sau daya taga Adam shima briefly yazo wai zasuyi sallama zai je Abuja tare da oga Hussain. Tana murmushi tave masa "kwana nawa zakuyi?" Yace "yau zamu dawo" tace "yau zaku dawo din shine harda sallama?" Ya langwabe kai "kika sani ko kawai so nake yi in ganki shine na fake da sallama" ta dan rufe fuska da mayafi, ya kama mayafin yana leka fuskar. Ta rufe idonta "ka bari fa" yace "ni ba zan bari ba, kallon fuskarki ma yanzu na fara" ta kwace mayafinta tana kara rufe fuskar dashi, yayi murmushi yace "kinsan wani abu?" Ta girgiza kai, yace "so nake in mun gama semester din nan inyi wa oga Hussain maganar mu, so nake a fara maganar auren mu tun yanzu ba wai sai mun gam school ba tunda kinga ai ina da aikina kuma ina samun kudi ba laifi, tunda na fara aikin kuma nake tarawa ba wani abin nke yi dashi ba. In nayi masa Magana nasan zai yi min jagora a maganar auren insha Allah"
Sai taji ranta yayi mata dadi, zuciyarta tayi fari tas, yace "kin amince da hakan?" Ta gyada kai tana murmushi, still fuskarta a boye, ita da ace amimcewarta kadai ake bukata da zata iya auren Adam ko da bashi da wannan aikin, koda sadaki kadai zai bayar babu lefe babu komai, thats how much take son shi. Da zasu rabu ya jaddada mata "you know I love you right?" Ta danyi murmushi tana kallon cikin idonsa ta gyada kai, sannan kuma kamar ba zata yi magana ba sai tace "and I love you too".
Har yanzu, har bayan ta wuni sir a makaranta ta dawo gida a gajiye da yunwa da ƙishirwa amma bata daina jin kaifin kallon da yayi mata a jikinta ba. Tana cin abinci tana zuba murmushi ita kadai, tayi sallah tayi wanka ta fito tama shiryawa Inna Ade ta shigo tana kallon ta. "Ke kuma fa kike ta farin ciki kamar anyi miki albishir da kujerar makka? Au ashe ba kinje, dan haka ba lallai ne ma kiyi farin cikin da kike yi yanzu ba" samayya tayi dariya, "haba Inna, farin ciki ma kuwa ai har marar misaltuwa zanyi in za'a mayar dani in sake ganin Ka'aba. Amma dai duk son da nake yiwa komawar in dai aka bani a yanzu sai dai in baki ko Baba tunda ni na sauke farali" Inna ta zauna a gefen gado tace "to gaya min abind yake saka ki wannan farin ciki haka"Sumayya ta zauna a kusa da inna tana kare mata kallo. Cikin yan shekarun nan da suka dawo gidan nan baba kuma ya samu aiki duk Inna ta chanja, jikinta ya murmure sosai babu wannan muguwar ramar fatarta tayi kyau tayi haske, kyawunta ya sake fitowa sosai. Sai Sumayya tace "kawai dai ina duba rayuwa shine naji raina yayi dadi sosai. Ina duba halin da mutanen da nake tsananin so suke ciki misali ku Iyaye na, Ruqayyah, kannena da sauran su duk kowa yana cikin rayuwa mai kyau sai naji zuciya ta tayi dadi sosai" Inna tace "banji kin lissafa da Adam ba" Sumayya ta sunkuyar da kai, Inna tace "ko shine da sauransu din?" Sai Sumayya ta rufe fuskarta, a dai dai lokacin wayarta tayi kara, ta bude idon ta tana kallon bakuwar number din da bata sani ba sannan ta dauka a hankali tare da sallama "Assalamu alaikum" daga daya barin taji muryar Ruqayyah "Sumayya nice, yar uwarki Ruqayyah ce. Accident muka yi ni da m.......... nida Fatima, Allah ya musu rasuwa ita da driver. An tafi dani asibiti ni kuma"
Sumayya ta zaro ido cikin tashin hankali "accident? Mutuwa? Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Ya kike Ruqayyah me ya same ki ke? Wanne asibitin?" Ta jera mata tambayoyin cikin tashin hankali. Ruqayyah tace "da sauki. Asibitin da nake haihuwa. Ki gaya wa su Inna" sai ta kashe.
Inna Ade da dama tun da taji Maganar accident ta mike tsaye tana kallon Sumayya tace "me ya samu Ruqayyah? Hatsari suka yi?" Sumayya ta gyada mata kai already hawaye yana zuba a idonta tace "hatsari sukayi wai Fatima ta mutu. Allah sarki Fatima. Innalillahi wa inna ilaihir rajiun" ta fada tana neman hijab dinta. Sannan suka fito palo tare da Inna ita kuma tana nemna waya ta kira Baba ta gaya masa zasu tafi asibiti gurin Ruqayyah, a lokacin ne shi kuma baban suka shigo sun dawo daga masallaci tare da Suleiman. Sulaiman yana goge hawaye, Sumayya tace "kunji labarin kuma ko? Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Allah yaji kan Fatima" Baba yace "wacce Fatima ce kuma ta rasu? Mu yanzu ake gaya mana mutuwar yaron nan dan uwan Hassan. Hussain. Yanzu aka kawo gawarsa daga Abuja"
Sumayya ta dora hannu aka Baba ya daga mata hannu, "kar kiyi, ba da haka zaki nuna wa Ubangiji godiyar ki daya baki rai shima ya bashi rai sannan ya ƙaddara saduwar ku a duniya ba" Sumayya ta sauke hannnun tana sheshshekar kuka, Inna Ade tana tayata. Sannan Inna ta gaya musu kiran da Ruqayyah tayi musu da sakon data sanar dasu. Nan take suka shirya gabaki dayan su suka hau Napep din Sulaiman suka tafi asibitin.
Asibitin da aka kai Ruqayyah dana shine asibitin da suke zuwa, dan hka suna zuwa ba tare da wani matsala ba aka karbe ta aka bata taimakon gaggawa kafin karasowar likita. Kafin likitan yazo su Baba sunzo, sun kuma ji dadin yadda suka ganta complete ba tare da ta rasa wani abu na jikinta ba a hatsarin da ita kadai ta fita da rai. Wannan babban abin godiya ga Allah ne. Bayan likitan yazo yayi mata complete check up sai ya fahimci ko karaya bata dashi sai tarkade a hannun ta na hagu wanda ita Ruqayyan ma bata san dashi ba sai kuma ciwon da taji a cinyarta, wanda karfe ne ya soke ta a gurin. Amma problem din shine complain da take yi cewa kafar ta makale, ta kuma fadi cewa farkon data tashi tana iya motsa ta amma yanzu ta kasa. Sai doctor din ya rubuta mata hoto da za'a yi mata a kafar da safe yadda za'a fi ganin komai. Daga nan ya barta aga yanuwanta.
A gurin su ne ta kuma tabbatar da labarin mutuwar Hussain. Ita kuma tana kuka tana basu labarin mutuwar Fatima "tunda na tashi dama na fahimci cewa ta mutu, nayi nayi kokarin in fito da gawarsu daga cikin motar ita da driver amma na kasa, ga wuta kuma ta kama" sai ta rufe fuskarta tana rusa kuka Sumayya tana taya ta. Tace "wuta ta kone su kurmus. Ance ma ba za'a iya dauko gawawwakin su ba sai dai a binne su a can" Sumayya ta share hawayen ta tana tuno kyakykyawar fuskar Fatima, sai kuma ta kara karfin kukanta data tuno da tsohon cikin da Fatima take dauke dashi. Dai kuma Hussain, ta tuno ganinta dashi na karshe sanda taje gidan ta hadu dashi. Cikin barkwanci irin nasa yace "Sumayya kin kuwa san gimbiya ta tsohon ciki ne da ita?" Tayi dariya Tace "na sani mana, na shiga ai mun gaisa" yace "to ki je gida ki fasa bankin ki ki tattara kudaden ki ki sayi lace dan yayi ki kai wa tailor yayi miki dinkin zamani dan suna ne za'a yi shi irin wanda ba'a taba yin irinsa a garin kaduna" sukayi dariya gaba daya. Yanzu gashi babu shi babu matar babu dan. Duniya labari, duniya zancen banza, duk wanda ya dauke ta gurin zama tabbas yana tare da babbar nadama.
Baba ne yace da Inna Ade tazo su tafi gidan mutuwar, Sumayya kuma da Sulaiman su zauna a gurin yar uwarsu a asibiti gobe sa je suyi musu gaisuwa. A gidan mutuwar ne suka tarar da abin mamaki, layin gabadaya a cike yake da mutane maza da mata daga lunguna da sakuna na garin kaduna, wasu a zazzaune wasu a tsatstsaye kowa yana addu'ar samun rahama ga Hussain da iyalinsa saboda Hussain yana da wata al'ada ta kyautata wa duk wanda ya hadu dashi dan yana cewa
"ita haduwa kaddara ce, rabuwa dole ce. Duk mutumin da ka hadu dashi a rayuwa to kayi amfani da wannan damar wajen kyautata masa dan babu tabbas din zaku kuma haduwa, ko baka bashi komai ba kayi masa magana mai dadi, ko baka yi masa magana mai dadi ba kayi masa murmushi dan shima sadaka ne"
Cikin gidan kuwa da Inna ta shiga dakunan duk a bude suke kuma duk da mutane a ciki duk kuwa da cewa yan Gombe basu karaso ba, kowa kuka, musamman ma'aikatan gidan da suke ganin ba zasu kuma samun wani uban gidan kamar Hussain Aminu Abdullahi ba.
Labarin Mutuwar Fatima ya dira tamkar kibiya a zuciyoyin iyayenta, yanuwanta da masoyansa ta. Nan take masarautar kano ta hargitse kowa kukan rashin Fatima musamman da suka ji irin mutiwar da ake tunanin tayi. Wai ko gawar ta ba zasu gani ba, wai ko sun gani din ma ba zasu gane taba saboda ta zama gawayi. Fatimah dai ta su, Fatima da suke ji da Ita tamkar kwai ita ce ta mutu kuma wuta ta kone ta. Wannan wanne irin tashin hankali ne?
Mai martaba sarki duk da cewa ya dimauce ya gigice da alhinin mutuwar yar tasa amma duk da haka sai ya hada kan ya'yansa maza gabaki daya suka hau jirgi a daren suka tafi Abuja. Da assuba suka yiwa gawar da suke tunanin ta yar uwar su ce sutura tare da ta driver aka yi musu sallah sannan aka binne su a gurin da suka mutu. Daga nan kuma sai ya juyo ya koma kano dan fara karbar taaziyya daga mutanensa, yayan sa kuma ya tura su Kaduna dan su halarci jana'izar Hussain wadda aka daka karfe goma sha daya na safiyar asabar.
Abinda yake bawa kowa mamaki a gidan gaisuwar shine Hassan. Da kansa yayi wa gawar Hussain wanka ya kuma suturta ta tare da taimakon limamin gidan tun cikin dare. Kallonsa kadai idan kayi ya isa abin tausayi amma zuciyarsa tana tsaye. Yana zaune a gaban gawar yana yi masa addu'a kamar yadda cikin gidan da wajen gidan yake cike da mutane da suke masa addu'a har gari ya waye. A lokacin yan Gombe suka karaso, dangin maman su da dangin babansu. Da gari ya waye ne Hassan ya kira Aunty, wadda duk ta gama fita daga hayyacinta, tare da dukkan yan uwansu mata su biyar yace su zo suyi sallama da Hussain. Kuka suke suna karawa, haka yahada su ya rungume duk a jikinsa in ya share hawayen wannan sai ya share na wannan yana cewa "ku daina masa kuka kuyi masa addu'a, ku ringa cewa innalillahi wa inna ilaihir rajiun zaku ji sanyi a zuciyoyin ku" sai daya kaisu sannan ya dawo ya kama Aunty da kyar ya daga ta ya tafi daita itama. Suka zagaye gawar Hussain suna ta karanta masa suratul ikhlas suna maimaita wa, yadda suke kallon Hussain a kwance a cikin likkafanin sa duk sai sukaji duniyar gaba ki daya ta fita a kansu, suna tuno da sutturu irin na Hussain wanda baya saka kaya idan ba na zamani ba, komai nasa latest ne, in kuwa akayi wani design din to ya daina saka wancan design din. Amma yanzu gashi da brand din kaya irin wanda ake sakawa tun dubunnan shekaru da suka wuce, babu safa ballantana takalmi, babu agogo da sauran kayan adon maza, sai dai in suka kalli fuskarsa sai suji dadi a ransu, yayi kyau irin wanda bai taba yi ba koda kuwa yayi ado da kwalliyar. A hankali suka daina kuka suka cigaba dayi masa addu'a tare da sallamar bankwana, ban kwana na har abada, ban kwana na sai a lahira kuma ba dai a duniya ba dan haduwarsu a duniya ta kare. Sai dai ko bayan sun daina kukan ma in suka tuna da Fatima sai su sake wani, a lokacin babu abinda ba zasu bayar babko da kuwa kawunan sune, babu abinda ba zasu iya yi ba idan za'a dawo musu da Fatima da abinda yake cikinta. Musamman Khadijah wadda tun zuwan Fatima gidan ita ce suka fi shakuwa akan duk sauran, kullum suna tare, tasan irin son da Fatima da Hussain suke yiwa cikin Fatima ta kuma san irin shirin da suke yi na taryar sa, ashe ba mai rayuwa bane ba, ashe ko numfashi bashi da rabon shaka a duniya.
Auncle din su ma da aunties dinsu duk sun shigo sunyi sallama da Hussain, yaron da yayi achieving abinda mutum goma in aka hada ba zasu iya achieving ba. Shi mutum daya ne tamkar dubu. Mutum ne da su kansu sunsan za'a jima a dangi ba'a samu irinsa ba a arziki, alkhairi, kyautata wa da kuma yawan jama'a. Mutuwar Fatima itama ta daga musu hankali ba kadan ba, dan da tana nan da suna saka ran zata haifar musu abinda zasu ke gani suna tunawa da Hussain.
Abokan Hussain, abokan business dinsa da sauran abokan muamalar sa duk sunzo jana'izar sa, a ciki har da Sadiq wanda mutuwa ta riski Hussain a hanyar sada zumunci tsakanin su. Ya koka sosai da mutuwar abokin nasa kuma ya jinjinawa karfin hali irin na Hassan. "Ban san bashi da lafiya ba, bai taba gayamin bashi da lafiya ba. And his family, ohhh dear God. Fatima and His baby! Kullum sai sai ya bani labarin Fatima ta kusa haihuwa. Wannan mutuwar mutuwa ce da ba zamu taba mantawa da ita ba".
Karfe goma da rabi aka fito da gawar Hussain daga cikin gida, abinda ya saka yanuwansa suka kara rikicewa, Khadijah da Hassana suka zube a kasa. Sha daya dai dai aka yi masa sallah a cikin compound din gidan Aunty, amma mutane sun rufe gabaki daya titin unguwar har da bayan layin da cikin gidajen mutane, kowa yana so ya halarci zanazar Hussain saboda ya taba rayuwarsa in positive way. Dama shi alkhairi haka yake, in ka shuka shi to kuwa zai bika ne tun a duniya kafin ka je lahira, shima kuma sharri haka yake, babu yadda za'a yi ka shuka dawa ka kuma girbi shinkafa.
Hassan da hannunsa tare da taimakon Jabir mijin Safiyya, Saeed mijin Hassana, uncle Mustapha kanin Alhaji Aminu da Baba Amadu yayan su aunty suka saka Hussain a cikin kabarinsa akan barin sa na dama sannan fuskarsa tana kallon gabas, sai kuma aka jejjera itatuwa a saman gawar tasa aka kuma bi da kwababbiyar kasa aka lullube itatuwan tare da like duk gurin da yake da kofa. Sannan aka mayar da kasar da aka fito da ita daga gurin sai kuma aka yayyafa ruwa a saman kasar.
Sai aka durkusa kuma aka yi doguwar addu'a ga ruhin Hussain, masu kuka a hankali nayi nasu dauriyar zuciya nayi har aka shafa sai kowa ya fara kama gabansa. Hassan yana tsugune, tunda ya saka Hussain a cikin ramin ya koma gefe ya tsuguna yake kallonsa har aka rufe shi da itace ta daina ganin sa amma bai dauke idonsa daga inda yake ba, yana kallo aka gama komai aka kuma yi addu'a, ya daga hannunsa, duk da cewa kunnuwan sa basa fahimtar me ake cewa amma yasan addu'a ce akeyi ga Hussain. Yana kallo aka shafa shima ya shafa. Sai kuma yaga mutane sun fara tashi suna tafiya, na kusa dashi kowa in zai tafi sai yazo ya dan dafa shi alamar bada hakuri sannan ya wuce, a haka , a hankali a hankali har kowa ya watse, har aka barshi shi kadai tare da kabarin Hussain.
A hankali yace "Hussain. Amanar da ka bar min ta danka ban sami damar rike ta ba saboda shima ya biyo ka, shi da Fatima, ina fatan zai zamo mai ceto a