Showing 153001 words to 156000 words out of 300844 words

Chapter 52 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2064

cewa yana wani guri ba.

Yana zuwa gida mai gadi ya sake tambaya, ya kuma maimaita masa abinda ya gaya wa Sumayya, sai ya duba gurin motoci da kansa ya tabbatar babu motar da suka tafi da ita Abuja, daga nan ya tafi part din da Adam yake kwana tare da sauran yaran gidan ya tambaye su duk duka ce basu ganshi ba. "Kuma wayarsa bata shiga" wani daga cikin su ya kara jaddada masa. Sanda ya bar part din kansa har juyawa yake yi yana jin jiri, abubuwa sunyi masa yawa, ga mutane duk inda yayi kowa yanaso yayi masa gaisuwa kowa yana so yayi masa magana. Haka ya samu ya dan zauna kadan a cikin mutanen da suke jiransa sannan ya tashi ya shiga gidan sa yana jin kansa yana tsananin sarawa. Menene yake faruwa a rayuwarsa? Hussain, Fatima and now Adam? Me ya samu Adam? Ko shima yayi accident ne a mota kuma babu wanda ya ganshi? Dan suma su Ruqayyah dan ita ta rayu ne ta nemi taimako ba dan haka ba da zasu iya kwana daya ko biyu ma ba tare da an san inda gawawwakin su suke ba.

Ya dauko wayar Hussain wadda da ita yake amfani yanzu ya kira number din Jabir. "Please ka sa a binciko motar da muka tafi da ita Abuja jiya, I will send you the plate number din yanzu" Jabir yace "lafiya? Ta bata ne?" Hassan yace "ba ta motar nake ba, ta yaron da yake cikin motar nake".

Har dare babu labari, har gari ya waye babu labarin Adam. A lokacin hankalin Sumayya ya kai makura gurin tashi, ta gaya wa inna halin da ake ciki ita kuma ta gayawa Baba wadanda a take suka fara addu'ar Allah ya bayyana shi. Suna cikin jajantawa da kuma tunanin zuwa suyi reporting gurin police Hassan ya shigo dakin asibitin. Ya gaishe su yana kallon Ruqayyah da take bacci dan jiya ma sam bata samu baccin kirki ba. Baba yace "Hassan da kokari da kayi zamanka ai" ya danyi murmushi kadan, sai ya kalli Sumayya yace "bai kira ba?" Ta gyada kanta kawai tana kallon wayar hannunta dan number dinsa cewa akai tana dialing, kamar jan charbi ta mayar da kiran number dinsa daga jiya zuwa yau. Baba yayi musu sallama ya fita sai Inna tabi bayansa. Ya zauna akan kujera yana kallon Sumayya yace "za'a ganshi insha Allah kinji?" Ta gyada kai tana kokarin mayar da hawayen idonta. Allah kadai yasan yadda take ji a zuciyarta, sai yanzu ta san zafin batan mutum da ake cewa gwara kaga gawarsa a gabankaakan ace ya bata baka san halin da yake ciki ba. Tun jiya babu abinda take yi sai sake sake na irin halayen da yake ciki, maybe yayi accident ya mutu babu wanda ya ganshi, maybe masu garkuwa da mutane ne suka kama shi yana hannunsu, maybe yana can yana neman taimako kuma babu wanda zai taimaka masa. Ta fara hawaye, Hassan ya jingina da jikin kujera yana kallon ta. "Ki daina kuka fa, zai dawo gurinki indai yana raye I promise you this kinji?" Ta gyada kai amma hawayenta yaki tsayawa, she just can't get it through her head cewa Adam ya bata, ya za'a yi ya bata kamar wani thing ba mutum ba?

A lokacin Ruqayyah ta bude ido, ashe tun shigowar Hassan idonta biyu ta rufe idon ne tana jin abinda suke cewa, ta yi kokarin mikewa zaune, Hassan yayi saurin taimaka mata yana yi mata sannu ta zauna tana kallonsa tace "Adam din Finally ya tafi kenan" yace "me kike nufi Finally ya tafi?" Ta danyi murmushi tace "wai da kun dauka zama zaiyi? Me naji kna cewa? A gabasa fa Hussain ya mutu kuma ka bashi mota kace ya taho Abuja, yanzu wannan motar idan ya siyar da ita ba yayi arziki ba, ai kawai ku fitar da ran ganinsa kawai na san ya debi rabon sa ne ya kara gaba" ran Sumayya ya baci, ta taso kan Ruqayyah da sauri "kar ki kara! Kar ki kuma alakan ta shi da sata ko cin amana, ba halinsa bane ba, motar banza motar wofi, ana tunanin ima mutum yake kuma wanne hali yake ciki ke kina zancen mota? Wacce irin zuciya ce a kirjinki Ruqayyah?" Hassan ya dafe kansa yana jin kamar zai tsage, sai Sumayya ta ja da baya tana jin babu dadi tayi masa hayaniya aka Sannan ta juya ta bar dakin da sauri tana hawaye, a ranta kuma tana Allah wadai da halin Ruqayyah da har after all what happened zata iya fadar abinda ita kanta tasan karya ne akan wani, wanin ma kuma wanda ake tsammanin yana cikin matsala.

Bayan tafita Ruqayyah ta bi ta da kallo sannan ta dawo da dubanta kan Hassan tace "kayi hakuri da halin Sumayya, tana da problem musamman in akaxmce akan wannan stupid yaron ne, ga gaskiya kiri kiri amma ba zata ganta ba, yaron nan ya saci mota ya gudu, period" Hassan ya girgiza kai yace "you are wrong Hassana, bana jin gudu wa yayi, you need to see yadda hankalin sa ya tashi a lokacin da Hussain ya rasu, he gave me support and a shoulder to cry on. Da yana son ya saci mota da tun da yake gidan zai sata, keys din Hussain duk suna hannunsa ko ni lokuta da dama a gurinsa nake karbar key din wasu motocin, in yana son ya dauki mota ya gudu da tuni ya dauka ya gudun" Ruqayyah tace "to ai lokacin yasan mai motocin yana da rai, yanzu kuwa yana ganin sun zama kayan gado shi yasa zai kwashi rabonsa" yayi shiru yana kallonta kawai yana lura da yadda ta ambaci gadon. It never occurred to him cewa kayan Hussain sun zama na gado ba, shi komai na Hussain ne a gurinsa duk kuwa da xewa tun kafin Hussain ya bar duniya ya mallaka masa rabin duk abinda ya Mallaka. Sai kawai ya girgiza kansa a ransa yan aiyana rigimar da zasuyi da Ruqayyah duk sanda ya gaya mata kudurin da ya yanke a zuciyarsa na abinda zaiyi da duk abinda Hussain ya bari. But he has already made up his mind tun kafin Hussain din ya bar duniya.

Yau ma sai da ta sake yi masa maganar fita waje, ya kira Doctor din yazo a gabanta suka yi magana yayi masa bayanin problem din da yake tunanin ya samu kafar da kuma solution din daya yanke. "jijiyar ce ta rike ba wani abu ba. We can treat her here, duk abinda za'a mata a waje zamu yi mata anan ma in dai har ta bamu dama" Hassan yace "babu problem, just do your best but in kunga akwai problem sai ku fada da wuri dan musan abin yi. Kana ganin zat warke ai ko?" Doctor din yayi murmushi yace "ras kuwa. In no time zata cigaba da amfani da ƙafafuwan ta. Garin accident din ne kashi ya bude a hips dinta sai jijiya ta shiga ciki, wannan yasa ta zata ita motsa kafar voluntarily ba sai dai in ta saka hannu ta motsa ta. Manually zamu fito da jijiyar daga cikin kashin sai mu daura mata belt a gurin mu barta tayi healing shikenan" Hassan y gyada kai cikin gamsuwa yace "shikenan Doctor" Ruqayyah kuma sai tace "amma Doctor ba tunda akayi accident din bane ba ta rike, nayi amfani da ita sai daga baya ta rike" Hassan yace "kinyi amfani da ita? Ina kika je?" Ta dauke kanta tana kallon gefe tace "na.... Ammmm naje nayi......na dan zagaya ina neman network zan kira ka" ya kalli Doctor din yace "to kaji, she used the leg after the accident" doctor yace "I can't say me ya faru gaskiya, it maybe sanda take tafiya ne, ko kuma wannan ciwon da taji, but hoton mu bai nuna mana komai a keg din ba shi yasa mukayi tunanin daga hip bone be, but zamu sake dubawa".

Doctor din yana fita ta fara mita "kaji ko? Basu ma sani ba, basu ma san aikin su ba. Wannan mutanen babu abinda zasu iya yi min, idan kai ba zaka iya hakura da abinda kake yi ba ka taho mu tafi ba ni ka barni in tafi ni kadai" ya mike yana kallon ta, baya son ta kara masa wani tension din akan wanda yake ciki already yace "in zuwa karshen satin nan basu tsayar da matsaya ba zan nemi Doctor din da zai duba ki a waje sai ku tafi tare da Sumayya" tayi murmushi tana bayyana jin dadin ta tace "yauwa. Ko kaifa. Allah ya kaimu" ya juya ya fita yana lura da yadda bata ce masa a dawo lafiya ba, sai kuma ya tuna cewa har yanzu bata yi masa gaisuwar Hussain ba ballantana ta Fatima.

Ranar sadakar uku gidan gaisuwar ya cika har ma yafi ranar da akayi jana'iza cika. Dan yan uwan Fatima ma duk anan suka zo aka hada akayi musu addu'a tare, sannan aka fito da dukiya akayi ta bayarwa sadaka da niyyar Allah ya kai ladan kabarin Hussain da iyalinsa. A ranar saida Hassan ya karar da kudin da yaje cikin account din Hussain kaf, amma yayi noticing amount din dan yasan ba shi kadai ne yake da gadon Hussain ba. Kuma sadakar da yayi irin wadda yasan Hussain yana yi ce da Hussain ya kan ce

"Da ka tara mutane da yawa ka basu abu kadan wanda wani ma a kudin motar komawa gida zai karar da abinda ka bashi gwara ka tara mutane kadan ka basu abinda in suka lallaba shi kum Allah ya sa ka musu albarka zasu rabu da talauci"

Hussain baya taba kyautar abu kadan. Shim Hassan haka yayi. Bayan an watse ne wajen laasar sannan ya samu ya tafi asibiti gurin Ruqayyah. Yauma Sumayya ce a wajenta, suka gaisa ya zauna yana lura da irin ramar da Ruqayyah tayi yace "kin rame da yawa. Hope ba wai har yau ba kya iya cin abincin ba?" Ta girgiza kai tace bacci ne bana iyawa. Tsorata nake yi duk dare."

Haka ne, tun da Ruqayyah tazo asibitin bata iya bacci, in fact she is even scared of closing her eyes dan in banda gawawwaki babu abinda take gani. Gawar Minal, ta driver. In kuma tayi bacci mafarkin Hussain take yi, a very angry Hussain, abinda bata taba gani ba sanda yana raye amma yanzu a mafarkin ta tana ganin tsananin fushi a fuskarsa kuma yana binta kamar zai hallaka ta. Bata fada wa Sumayya ba, ta dai gaya mata tana mafarkin gawawwakin Fatima da ta driver a irin yana yin data gansu lokacin mutuwar su kuma Sumayya tagawa wa Inna Ade ita kuma ta bata adduoi kuma tayo mata rubutun da zai bata kariya daga tsorata. Dan sun san cew tsorata ce tayi. Sai dai kuma a mafarkin nata sai taga kafarta tana motsewa har sai ta koma irin ta jarirai sannan sai ta fadi tana kukan jarirai a haka har abinda ya biyo ta zai cimmata. Tayi kokarin yin addu'a akan hakan, tana so ta roki Allah ya yaye mata abinda yake damunta amma sai taji t kasa, me zata ce wa Allah a cikin addu'ar tata? Menene uzurin ta na aikata abinda t aikata? Duk wani link da take feeling a tsakanin ta da ubangiji idan tana addu'a a da yanzu jinsa take yi ya yi cutting, kamar ubangiji baya dubanta, bata son kuma tayi tunanin abinda hakan yake nufi dan amsar tunanin nata ba zaiyi mata dadi ba.

Bayan wannan kuma a duk lokacin da taji shiru babu maganganun mutane, sai taji kunnuwan ta sun cika da kukan jariri, kukan jaririn data ajiye a kofar orphanage.

A dole kullum ake yi mata allurar bacci, amma even with allurar baccin haka zata yi ta yi tana tsorata tana komawa tana dada farkawa har gari ya waye.

Amma ba zata gaya wa Hassan wannan ba. "Bana iya bacci ne mijina" ta maimaita tana kallonsa. Ya gyada kai "ki yi kokari ki cire abinda yake ranki kinji? Na san ba zaki manta ba, babu yadda za'a yi ki iya mantawa amma ki rage tunanin abin kinji? With time baccin ki zai dawo kamar yadda yake da" ta gyada kai kawai a lokacin da aka bide kafar aka shigo,suka juya ga aki daya. Maman Minal ce ta shigo tare da sallama, fuskarta jeme jeme kamar wadda ta kwana tana kuka. Ruqayyah ta kware da abincin da ta saka abakinta, Hassan ya tashi da sauri ya bata ruwa tasha yayinda Sumayya take yiwa maman Minal barka da zuwa tare da nuna mata kujera. Ta zauna duk suka gaishe ta, Ruqayyah ma ta gaishe ta ba tare da ta hada ido da ita ba. Sai matar tace "ya hakurin mu yaran nan? Allah yaji kansu yayi musu rahama. Ni naji labarin rasuwar amma ban dauka hatsari ne aka yi ba, ashe har da ke Ruqayyah a cikin accident din, Allah ya bami Lafiya" suka ce ameen, sannan tace "daga gidan ai nake, naje inyi muku gaisuwa kuma in tambaye ki labarin kawarki" Ruqayyah tace "ammmm....... ban ganta ba, ban san inda take ba. Ina nufin ba ta zo ta duba ni ba"

Maman Minal tace "baku yi waya da ita b kuma?" Ruqayyah tace "babu waya a hannuna ai, ta kone tare da.......tare da mota" Maman Minal ta share hawaye tace "kawarki yau kwanan ta uku rabont da gida. Ta tambayi mijinta zata je kasuwa ta karasa siyayyar kayan haihuwar ta, tunda ta fita shikenan. Anyi neman, duk inda muka san tana zuwa munje amma babu ita babu alamun ta." Sumayya ta yi salati "mun shiga uku, abinda ya same mu kenan kuma? Allah in laifi muka yi maka Allah mun tuba ka yafe mana" Ruqayyah ta dauke kai gefe "ban ganta ba Mama. Na kwana biyu ban ganta ba" Maman ta bita da kallo sannan tace "amma mijinta yace tace masa gidan ki zata zo tare zaku tafi kasuwar. Har tace masa a can zai je ya dauke ta da daddare, kafin yaje daukanta ne akayi wannan rasuwar kuma da yaje ya tarar gidan a cike da mutane. Ya kura wayarta kuma a kashe" Ruqayyah ta kuma girgiza kanta tace "batazo ba gaskiya, ni ta jima ma rabon da tazo gidana" ta karasa tana kallon Hassan wanda ya tsare ta da ido yana lura da rashin gaskiyar da yake rubuce a fuskarta.

Maman Minal tace "na shiga uku ni Hauwa. Yarinyar nan ita ta shiga da tsohon ciki? Innalillahi wa inna ilaihir rajiun" Hassan yace "Allah ya bayyana ta. An kai cigiya gidan radiyo?" Maman Minal tace "mijinta ya kai, har hoton ta duk yakai a gidajen talabijin" Sumayya tace "Allah sarki Minal. Kai duniya. Allah ka bayyana mana inda wadannan bayi naka suka shiga" Maman Minal ta mike tana cewa "dan Allah, idan kunji wani abu ko kunga wani abu ku gaya mana. Duk wanda yake da saka hannu a cikin batan yarinyar nan insha Allahu ba zai gama da duniya lafiya ba. Ni na san saka hannun makiyane dam anga zata haihu" sai kuma ta saka kuka "wayyo yata, Allah kar ka basu ikon cutar min da yata".

Duk sai da zuciyoyin su suka karye, Sumayya tana tayata kuka. Tana fita wayar Hassan tayi kara. Ya daga yana sauraro sannan yace "shikenan, gani nan zuwa" ya mike yana kallon Sumayya yace "anga motar da Adam ya taho da ita" ta mike itama tana dafe kirji. "Shi kuma fa? An ganshi?" Yace "an kusa dai" ya jura zai fita ta tari gabansa tace "me suka ce, dan Allah ka fada min" yace "a hannun wasu mutane aka kama motar, sunce wai tsintar ta suka yi a gefen hanya babu kowa a cikinta kuma da key a jikin ignition, da kuma waya ta a ciki, they may be lying, zanje gurin yanzu za'a kara tambayar su dan a tabbatar" ta rufe fuskarta da hannunta shi kuma ya wuce ta ya tafi.

Gurin police ya fara zuwa, yaga wadanda aka ga motar a hannunsu amma su sun dage basu ga Adam ba. Ya barsu a hannun police din ya koma gida yace a cigaba da bincikar du sai sun fito da shi. Yana zuwa gida ya shiga part dinsa ya hau saman sa ya dauko spare key din motar Ruqayyah ya sauko, tun sanda suke magana da maman Minal yasan da akwai wani abu da take boyewa kuma jikinsa ya bashi abin yana cikin motar ta. Dan a ranar tace masa zata je kasuwa, kuma ance Minal tace zasu je kasuwa tare.

Ya bude kofar motar ya shiga ciki yana ta dube dube bai ga komai ba, sai ya bude booth, idonsa ya sauka akan manyan ledojin kaya, ya saka hannu ya bude a hankali sai idonsa ya sauka akan kayan babies da tarkacen kayan haihuwa. Ya koma da baya yana dafe kansa yana tunawa da maganar Maman Minal "siyayyar kayan haihuwa zata karasa".

Tabbas Ruqayyah tayi masa karya.


*First Wave*


Ya mayar da booth din ya rufe yana jin ciwon kansa yana karuwa. Tun sanda tana magana yasan karya take yi, amma baya so ta karya ta ta sai ya tabbatar da cewa karya take yi din, wannan shi yasa ya bincika motar ta dan yasan cewa in dai sun fita tare da Minal to kuwa zai iya ganin shaida a cikin motar tata. Ya juya yana kallon gate zuciyarsa tana gaya masa ya koma asibiti ya tuhume ta akan karyar da tayi masa amma sai ya fasa, ya rufe motar ya koma cikin gida dan magrib ta gabato. Sai da yayi wanka sannan ya tafi masallaci aka yi Sallah yare da gabatar da Adduoi ga Hussain da iyalinsa sannan shi kuma ya shiga cikin gida gurin Aunty wadda har yau take kwance babu lafiya, jiya ma sai da aka mayarda ita asibiti saboda jinin ta daya kuma hawa, wannan ya sa ya kuma jaddada cewa babu zaman makoki dan ta samu ta huta, da yayi yayi da ita akan a mayar da ita asibiti tayi zamanta acan inda zata ke samun kulawar likitoci kuma ba za a dame ta ba amma taki,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login