Showing 222001 words to 225000 words out of 300844 words

Chapter 75 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2055

an ajiye miki shine a gaban ki" ta mike tana kallon sa tace "ba wai rashin ganin laifi bane ba, Ruqayyah tana da laifuffuka da dama amma wannan bayanin na likita, likitan da ni da kai ne muka kai ta gurinsa ballantana muce hada baki suka yi. Ya kamata mu sauko mu fahimci abin sosai. Sannan kuma ga shaidar da Adam ya bayar, mu jira please mu ga abinda Shari'a zata yanke sai ya wuce ta ya dauki key din mota ya fice daga gidan. This is the first time da yayi nata fushi irin haka.

A palon gidan Ruqayyah, tana zaune a wheel chair dinta daaka kawo mata bata nan, Lukman yana zaune a daya daga cikin kujerun palon yana ta kokarin kwantar mata da hankali "wannan shaidar ba zata yi amfani ba, shi da kansa yace he is not sure a gaban alkali da sauran jama'a, he is a fool to even come out and say something sannan yace he is not sure" Ruqayyah tayi shiru tamkar bata jinsa, hankalin ta yana can wani guri daban daga alama ta shiga zurfin tunani, sai ta juyo tana kallon sa tace "yaro ya bata, and definitely someone is responsible for batan sa, a yanzu kuma ni kadai ce suspect, and I don't like that, ina son kayi creating another suspect din in an koma court" ya jima yana kallonta, tabbas maganar ta gaskiya ne amma tayaya zai creating another suspect kuma?

Yace "ban gane ba" ta fara bubbuga yatsunta akan hannun kujera fuskar ta kamar an aiko mata da sakon mutuwa tace "that stupid Igbo guy, wanda yake ikirarin ya ganni da baby, make him take the fall" yace "how?" Tace "anyi accident, Minal da driver sun mutu, ni na fita daga cikin hayyacina Fatima kuma ta kama hanya ta bar gurin. Adam shine mutum na farko daya fara ganin ta, ita kuma ba zata iya tuna lokacin da suka hadu din ba ballantana ta tuna in da ciki a jikinta lokacin ko kuma babu. Make the judge believe cewa da ciki a jikinta Adam ya dauke ta."


As always, forgive the typos..........


*The Lone Cat*

Yayi shiru yana kallonta, yana mamakin shaidanci irin na Ruqayyah, wato shi shine lawyer amma ita itace mai lauya magana zuwa yadda zata yi serving interest din ta. Tabbas, abinda ta fada zai kara wa shari'ar su light amma kuma bashi da wata shaida da zaiyi proving maganar kamar yadda suka wadancan lawyers din basu da yadda zasuyi suyi proving cewa Ruqayyah is guilty, duk lalube cikin duhu suke yi, kuma yasan ko yayi abinda Ruqayyah tace ko bai yi ba Ruqayyah will go free, na farko saboda babu wani takamaiman shaidar cewa ta aikata abinda ake zarginta da shi, na biyu kuma ga statement din doctors na cewa she is mental unstable, sannan shi kansa Adam da yayi ikirarin ya ganta ko da ace ya tabbatar da cewa ita din ce wannan statement din na doctor ya hau kan shaidar sa, ko da ta dauki babyn za'a yi ruling out as ta aikata laifin a cikin hauka.

But then, that will make the judge mark her as dangerous, dole kuma zai saka ayi isolating dinta ko a gidan mahaukata saboda a kare sauran al'umma daga gareta. Dan haka Maganar ta akan Adam zata taimaka musu sosai, in suka nuna wa judge cewa zai iya kasance wa shi ua aikata laifin shi yasa yayi wannan maganar against Ruqayyah dan ya kara rufe nasa laifin, wannan zai sa alkali ya rushe shaidarsa ko da kuwa basu yi proving cewa shi yayi din ba.

Already har kansa ya fara aikin samun hanyoyin da zai bi ya haka ramin da zai rufta da Adam. Yace "that was excellent! Me yasa baki karanci harkar law ba? You would have make a good lawyer" ta kalleshi kawai, she is in no mood for jokes dan ranta a bace yake sosai. Komai ya tafi dai dai a court, wannan stupid Adam din ne yaso ya cika wa kabar ta ruwa. Tace "ka tafi kaje tayi aikin ka. I want to see that guy behind bars,I want to see yadda Sumayya zatayi reacting idan taga an kama shi, I want to see yadda Hassan zaiyi reacting to yadda Sumayya tayi reacting. I want to see idan da gaske ne suna son junan su ko kuma pretending kawai suke yi.

A haka suka rabu, ya tashi ya tafi ita kuma ta aika aka tabbatar mata da cewa bodyguards din da tayi hiring suna nan a gurin, tasan Hassan might try something on her shi yasa ta tanadi guards din, kuma there is a possibility that suna yan uwan Minal in basu yarda da jawabin Lukman ba, za kuma su iya zuwa suce zasu taba lafiyar ta dan tasan ba mutunci ne ya ishe su ba. Ita kuma ba lafa ba ballantana ta gudu idan sun zo, gwara ta nemi kariya.

Washegari aka sake sabon zama tsakanin Hassan, brothers din Fatimah da lawyers dinsu. A nan suka duba abubuwan da suka faru a court suka kuma fara planning next thing daya kamata su yi. Lawyen farko ya fara bayani. "I want to be frank with you, tun farko dama munsan ba zamu iya nailing dinta akan batan jariri ba, saboda bamu da shaida" Hassan yace "wacce irin babu shaida, kowa yasan ita ta dauke shi, idan ba ita ba to waye?" Lawyer yace "abinda aka sani da abinda za'a iya proving a court daban ne, babu eye witness, dan haka idan ba ita ce tayi confessing da kanta tace ta dauke shi ba, ko kuma ita Fatima ta tuna abinda ya faru ta fadi cewa ita ta dauke shi ba, to babu yadda za'a yi muyi proving ita ta dauka"

Dayan yace "dama laifin da muke saka ran za'a iya kamata dashi shine na chanja labarin mutuwa da tayi, saboda muna da isassun shaidu akan hakan, yanzu kuma wannan medical report din, wannan statement din na likita na cewa tana da matsalar ƙwaƙwalwa ya rushe duk shaidar da kuka bayar" Umar yace "yanzu kana nufin ba zamu iya yi mata komai ba kena?" Yace "yanzun wannan shaidar da Adam ya bayar ita kawai muke counting on, even with it, the worst she can get is a kaita gidan mahaukata, daga tayi shekara daya zuwa biyu zata ce ta warke shikenan ta dawo gida ta cigaba da rayuwar ta"

Hassan ya mike ya fara zagaye, "it is all my fault, it is all my fault" Abubakar yace "amma yanzu shikenan babu abinda za'a sake gwadawa?" Lawyer yace "zamu iya samun wasu shaidun da zasu bada shaida akan rashin kyawun halayyar ta da son kudin ta, yadda alkali zai san cewa zata iya aikawa haka saboda kudi, za kuma mu gwada yi mata tambayoyi muma a gaban alkali with hope na cewa zata yi subutar baki ta fadi wani abu da zai tona asirin ta. Wannan shine kadai hope din mu. Kuma zamu yi requesting a bamu dama mu kaita gurin doctor of our choice ya sake duba kwakwalwar ta ya rubuta nashi findings din"

Da wannan hankalin Hassan yadan kwanta kadan, sai ya zauna suka fara rubuta all possible mutanen da yasan zasu iya fadar halin Ruqayyah, shine na daya, sai Sumayya, zasu kuma nemo wasu daga cikin kawayen su na unguwa da kawayen da tayi haya da bikin su, sai kuma Adam. And they also need one more person, sai dai Hassan bashi da tabbas din zai yi magana. Baba.

But sai baban ya bashi mamaki, yanayi masa bayani yace zaiyi, sai kuma Hassan yaji babu dadi, kamar cin fuska ne ga Baba amma kuma dole ce ta kama. Daga nan suka ci-gaba da shirye shiryen su musamman a bangaren tambayoyin da zasu yiwa Ruqayyah, da yadda zasu tsara tambayoyin yadda zasu rikita ta. Shima kuma Lukman a nasa bangaren yana ta nasa shirin tare da taimakon Ruqayyah wadda shi kansa mamakin yadda take tsara masa abubuwa yake yi, abubuwa irin wanda shi tunanin sa baya zuwa gurin.

A haka har ranar komawa court tazo, kowa ya hallara, duk witnesses din dasu Hassan suka gayyata duk babu wanda ya basu kunya dan kawayen Ruqayyah ma sunzo musamman da Hassan ya basu kudi.

Farko bayan alkali ya zauna an gabatar da kara sai aka shigo da Ruqayyah akan wheel chair dinta, aka saka ta a akwatin wanda ake zargi, tadaga kai tana kallon mutanen da suke gurin, ta fahimci cewa kusan kowa data yi mu'amala dashi at one point in her life, sai ta fahimci cewa tabbas akwai problem, duk wadannan mutanen, mutanen da suke important a rayuwarta, yau sun taru ne sun hada kai against her, ita kanta bata san sanda tayi reaching this stage ba.

Ta lura da Baba, Baban ta mahaifi yana daga layin farko a zaman court din, kallo daya yayi mata ya dauke kansa gefe, rabon sata ganshi tun ranar daya yi mata korar jare daga gidan sa kuma yace babu shi babu ita, a gurin aiki ma transfer ya nema daga kamfanin flour inda office dinta yake ya koma kamfanin sukari. Ta zauna tana binsu da kallo daya bayan daya, ta lura da yadda Sumayya taki yarda su hada ido, da yadda Hassan yake binta da mugun kallo mai cike da nuna tsana da kyamata. Shin dama soyayya tana zama kiyayya? Wai ba taji ance bakin daya furta so vaya taba furta ki ba? Ko nata case din daban yake ne?

Bayan an karanta abinda aka tattauna akai a zaman daya gabata sai alkali ya tambayi lauyoyin masu kara ko suna da wani abu da zasu kuma gabatar wa? A take suka mike suka gabatar da kansu sannan daya ya zauna daya kuma ya fito ya fara jawabi kamar haka "shaidun da lawyer mai bada kariya ya gabatar a wancan zaman da akayi suna kokarin nunawa ne cewa Hajiya Ruqayyah Yusuf tana da matsalar ƙwaƙwalwa, dan haka mu kuma a yanzu zamu nuna wa mai girma mai Shari'a cewa wancan claim din nata na karya ne. Abu na farko shine muna neman alfarma a bamu dama idan an tashi daga court zamu kai Hajiya Ruqayyah zuwa gurin wani likitan daban dan ya bamu second opinion akan lafiyar kwakwalwar"

Alkali ya ce ya amince, sai kuma lawyer ya sake neman alfarmar yiwa Ruqayyah tambayoyi. Aka bashi dama ya tafi gurin ta ya fara mata. "Farko zanso ki gabatar mana da kanki, suna da shekaru da kuma stage din karatu" sai tayi shiru tana kallonsa kamar bata ji abinda yace ba, kowa yayi shiru yana kallonta sai tace "magana kayi ne? Kasan ni kurma ce, bana ji sosai sai ka daga muryarka sosai".

Yayi murmushi sannan ya daga muryar ya sake maimaita mata tambayar, ta amsa masa a takaice, sai yace "ranar goma ga watan december, shekaru biyar da suka wuce, kunyi hatsarin mota, ko zaki bami labarin yadda abin ya kasance?" Ta gyara zama tare da tattara hankalin ta guri daya kamar mai tunani sannan tace "abin duk a cukurkude nake ganin sa, na san dai a ranar munje kasuwa tare da Minal, sannan muka dawo gida, muna dawowa muka ga Fatima tana shiri zata tafi Abuja sai nace zan bita, muka shiga motar ta da driver muka tafi, mun kusa shiga Abuja sai Hassan ya kira ni yace mu koma gasu nan zasu taho suma, mun juya zamu dawo sai muka yi hatsari, ni bansan ya akayi ba, dana farka sai naga wuta ta kama motar mu ninkuma ina gefe a kasa, na leka cikin motar sai naga Fatima da driver sun mutu suna ci da wuta"

Sai ta rufe fuskarta tana kuka. Lawyer yace "ita kuma kawarki fa? Da kuka dawo daga kasuwa tare, tana ina?" Tace "ni ban ganta ba, ban san inda take ba, sai dana dawo sai naji ana neman ta wai ta bata ba'a ganta ba" yace "amma mijinki yace farko kin gaya cewa baki san inda take ba, kince kun dade rabon da ku hadu, daga baya kuma sai kika ce masa kun ajiye ta a hanya ta shiga taxi ta tafi gida" tace "eh haka na gaya masa, saboda bana so yayi min fada, shi fada ne dashi da yawan fushi da tsawa, kuma baya son Minal, baya son muna mu'amala da ita shi yasa ba boye masa dan banaso yayi min fada, amma ni ba zan iya tuna komai a game da Minal ba, ni dai nasan munje kasuwa mun dawo, shikenan abinda zan iya tunawa akan ta" ya gyada kai yace "to yanzu mu koma gurin accident din. Bayan kin tashi sai kika ga me?" Tace "naga Fatima ta mutu tare da driver, naga gawawwakin su suna cin wuta" ta sake saka kuka, yace "kinga waccan?" Ya fada yana nuna Fatima, Ruqayyah ta bita da kallo yace "wacece?" Tace "Fatima ce" yace "kuma ki ka ce kin ganta ta mutu, an bata mutuwa dama an dawo?" Ta dafe kanta, "ni ban sani ba, ni ban san ya akayi ba, ne dai abinda na gani kenan a lokacin ban san ya akayi bayan ta mutu kuma ta dawo ba".

Yace "Malama Ruqayyah, bayani ya nuna cewa kunyi hatsarin nan ne da misalin karfe biyar da rabi, ke kuma kin kira wayar Hassan ne da misalin karfe shida da rabi. Menene kika yi a cikin awa dayan da take tsakani?" Ta dago kai tana kallonsa, yace "baki ji ba ko? Bara in maimaita" sai ya kuma maimaita tambayarsa sannan ta amsa tace "uhm, ina ta yawo ne ina neman network din da zan kira shi, gurin bau network" yace "kina ta yawo, har na tsahon awa daya. Amma kuma a lissafi distance din da yake tsakanin inda motar ku ta fadi da titi bai fi tafiyar minti goma ba ko da kuwa ga marar lafiya ne, a cikin awa dayan nan duk baki zo titi ba? Tunda banji Labarin kin nemi taimakon a gurin motocin da suke wucewa ba, ko kuma kinzo titin ne kika sake komawa ciki? Tunda a ciki police suka dauke ki?"

Tayi shiri tana kallonsa, kwakwalwar ta tana aiki, ta gane me yake yi, so yake tace tazo titi ta koma, ma'ana yana so yayi proving maganar Adam na cewa ya ganta. Ta girgiza kai, "banzo titi ba. Ban iya tafiya mai nisaba saboda kafata taki takuwa sai janta nake yi" yace "kafarki ta rike shi yasa baki yi tafiya mai nisa har kin je titi ba?" Tace "eh" doubtfully, dan ta lura akwai magana a bakinsa, sai ya nuna bay yace "amma likitan daua fara duba ki bayan kunyi hatsarin ya tabbatar mana da cewa kin gaya masa cewa kinyi amfani da kafarki bayan kunyi accident, daga baya ne ta makale" ta kalli inda ya nuna sai ga doctor a zaune, ta dauke kai, lallai wadannan mutanen, ya maimaita "awa dayan da kika yi kafin ki kira Hassan me kika yi a cikin ta" ta dauke kai tace "ba zan iya tunawa ba"

Ya juya ya na kallon alkali yace "ya mai girma mai sharia, magana uku kenan akan tambaya daya, tace tayi ta yawo tana neman network, ta ce kafarta ta makale ta kasa tafiya, sannan kuma tace ba zata iya tunawa ba".

Sai ya sake juyo wa kan Ruqayyah yace "tambaya ta gaba Malama Ruqayyah, kinyi furuci ga Hassan lokacin da kike a matsayin matarsa cewa da yasan abinda kika aikata dan ya samu gadon Hussain, da ba zai boye miki cewa Hussain ya bashi rabin dukiyarsa ba. Mai zaki iya cewa dangane da wannan maganar? Me hakan yake nufi?" Ta daga kai tana kallon Hassan wanda shima ita yake kallo a lokacin, sannan ta dawo da hankalin ta kan lawyer din tace "karya yake min, ni ban fadi haka ba, yana dai neman abinda zai kare kansa dashi ne saboda abinda yayi min".

Lawyer yace "menene yayi miki?" Tace "ya sake ni saki uku saboda na hadu da nakasa, sannan ya raba ni da yaya na kuma ya auri kanwata, twin sister dina" lawyer yayi murmushi yace "saboda kin samu nakasa, ko saboda halin ki? Saboda iƙrarin da kika yi na yin kazafi ga danuwansa daya rasu in bar baki dukiya ba. Idan ba haka ba zaki iya yi wa court bayanin dalilin da yasa ya baki kusan dukkan abinda ya mallaka bayan ya sake ki?" Tayi sauri tace "ya bani ne a matsayin toshiyar baki?" Yace "toshiyar baki na me?" Ta sunkuyar da kanta tace "na kar in ce ya sake ni saboda na nakasa".

Ya girgiza kai yace "wannan ai ba abu ne boyayye ba, kowa ai yasan ya sake ki tunda har ya auri kanwarki. Da haka ba zai baki wannan uban kudin dan ki boye abinda yake a bayyane ba. Ya baki ne saboda iƙrarin da kika yi na tarwatsa good name din Marigayin dan uwansa, wannan shine dalilin rabuwar auren ku ba wai dan kin nakasa ba, wannan kuma shine dalilin da yasa iyayen ki da suka haife ki da kansu suka sallama ki suka ce babu su babu ke har abada. Bana jin akwai wata nakasa da Da zaiyi wanda zai saka iyayensa su guje shi"

Lukman ya mike "objection my Lord. Lawyen mai kara yana kokarin yayi concluding akan abinda bai sani ba" lawyen Fatima yace "ayi min afuwa my lord, amma ba wai ni zanyi concluding ba, zan kira mahaifin Hajiya Ruqayyah, Malam Yusuf, shi zaiyi concluding da kansa.

Daga nan aka kira Baba, wanda ya zauna opposite Ruqayyah wadda ta rufe idonta hawaye yana zuba yana jika fuskarta sannan yana zuba a kan hijab dinta. Baba ya yi rantsuwa akan zai fadi gaskiya and nothing but the truth. Sai ya fara magana akan halayyar Ruqayyah tun dag tashin ta har zuwa girman ta da aurenta da Hassan, ya dora da bayanin abinda yayi sanadiyar rabuwar auren su "ni na roke shi da kaina na hada shi da Allah da Annabi ya sake ta, na kuma roke shi ya auri kanwarta dan ina yi masa fatan samun farin ciki tare da ita" ya cigaba da bayanin yadda ya aika har gida a gayamata ta dawowa da Hassan dukiyar sa ta dawo


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login