Showing 261001 words to 264000 words out of 300844 words
ta da irin kallon da yasa ta sandare a inda take a tsaye "I hate the sight of you" ya fada da karfi "kar ki kara tunanin kin haifi ɗa mai kama dani. Hanyar da duk nabi kar ki yarda ki bita ballantana ki hadu dani har kiyi kokarin kirana da sunan danki. You are not my mother" sai ya juya da sauri ya fita.
Abdullahi, Abdulrahman da Abdulrahim suka bi shi a baya suna kiransa dan su basu fahimci abinda yace ba, basu fahimci menene yake faruwa ba. Ruqayyah taji kafar ta guda daya ta kasa daukar ta duk da kujerar data rike, sai ta zame ta zauna akan carpet numfashin ta yana fita sama sama. She always dreamed of ranar da yayanta zasu shigo da kafafuwan su har cikin gidan nan su rungume ta su kira ta da mommy kamar yadda tayi bragging to Hassan sanda ya dauke su daga gabanta, she always thought tunda ta haife su ai ta gama musu komai, ta dauka a son will always stand for his mother no matter how bad she is, ta dauka wannan karin maganar ta uwa mafi uba ko da uban sarkine tayi applying to her, ta dauka......
Takun da taji ya saka ta dago kanta da sauri, twins dinta ne a tsaye a gabanta, and she wonders yaushe suka girma haka? Aminu ya durkusa kusa da ita, idonsa cike da hawaye yace "dazu da mommy tace mu shirya zamu shigo mu ganki mu gaishe ki, cewa muka yi ba zamu zo ba, kinsan saboda me?" Bata amsa masa ba, zuciyarta tana tuna mata da cewa ba ita suke referring to as Mommy ba, sai girgiza masa kai take yi, at least Hussain ta fahimci frustration dinsa dan tasan Adam da Fatima sun gama hure masa kunne a kanta, dama tasan dole ta samu problem dashi, amma not her gentle twins..
Sai Yusuf ya durkusa shima a kusa da dan'uwan sa yace "saboda bamu ga amfanin zuwa mu ganki ba, bama jin ko mun ki gaishe ki Allah zai kama mu da laifi" Aminu yace "da ana zabar uwa da ba zamu taba zaben ki ba" Yusuf yace "da ana chanja uwa da mun chanja ki" Yusuf yace "da ana goge memory da mun goge dukkan memoryn ganin ki da muka yi yau" Aminu yace "da ana un hearing magana da munyi unhearing labarin ki da muka ji" Yusuf yace "forget about us, kamar yadda kika riga kika yi dama tuntuni" Aminu yace "mu ma zamu manta dake ba zamu sake yin maganar ki ba ko da a tsakanin mu ne"
Tun da suke maganar take rarraba ido a tsakanin su inta kalli wannan sai ta koma ta kalli wancan, tana jin maganganun su tamkar saukar mashi a cikin zuciyarta, tana girgiza kanta tana cewa "no, no, no wallahi ba haka bane ba. Karya suka shirya dan su raba ni da ku, duk abinda aka fada muku karya ne ba gaskiya bane ba" ta saka hannu biyu ta rike kafafuwansu guda dai dai "babanku ne yayi min fin karfi ya raba ni daku, wallahi ina sonku, ni na haife ku fa, har nan ya shigo ya dauke ku yace ba zan kara ganin ku ba, shine kuma yanzu suka shirya magana dan suna ganin kunyi hankali zaku nemi ku dawo gurina. Ni na haife ku fa!" Ta fada da karfi a lokacin da suka mike sannan kuma a tare suka saka hannu suka cire hannayenta daga jikin kafafuwan su. Kuma ba tare da sunce komai ba suka juya zasu fita daga gidan. Ta sake kwallawa da karfi tana jan jiki akan carpet da manta ma da surgery wound dinta, "I am your mother" sai suka juyo a tare, Aminu yace "a gurin mu you are not, mun chanja ki da mafi alkhairi" Yusuf yace "mun chanja ki kamar yadda kika chanja mu da kudi" sai suka juya suka fice.
Ta kifa kanta a carpet ta saka kuka mai karfi, dama haka iyaye suke ji idan dan da suka haifa ya gaya musu magana? Dama haka Inna Ade da Baba suka ringa ji a lokacin da take mayar musu da magana? Sai wata zuciyar take tuna mata da cewa abinda suka ji yafi wannan tunda su suka raine ta suka yi mata komai da yake hakkin yaya akan iyayen su, ita kuma haihuwar Aminu da Yusuf kadai tayi. Sai kuma ta dago kanta ta sauke jajayen idanuwan ta a kan Sumayya wadda tunda suka shigo take tsaye a guri daya hannayenta rike da na Amatullah da duk abinda akayi a gabanta ne.
Cikin dacin murya tace "Nagode Sumayya, kin karbe mijina kin karbe gidana kin kuma karbe yaya na. Tabbas Lukman yayi gaskiya da yace abu kadan kike jira ki ga bayana. I thought we are twin sisters, ina alkawarin mu na cewa we will always be there for each other? Ina alkawarin da kika yi na cewa you will always be by my side, ina ........" Sumayya tace "kin zubar. Duk abubuwan da kike tambaya ta ke kika zubar dasu da kanki. Mental problem ko not mental problem duk hali yake tarar wa, mijinki ke kika rabu dashi, yayanki ke kika zabi kudi a kansu, gidan ki ke kika fita daga ciki fa kafafuwan ki" sai ta ja hannun Amatullah zasu fita sannan tace "am still your sister shi yasa ma kika ganni a cikin gidan nan" daga nan ta fita da Amatullah wadda already har ta fara jero mata tambayoyin "ina ne nan! Wacece take kuka? Me akayi mata take kuka?"
Bayan sun fita Ruqayyah ta koma ta kwanta akan carpet tana cigaba da kukan ta, childhood memories din ta ne suke ta dawo mata tana tuno da irin shakuwar su da Sumayya ta irin alƙawarin da suka yiwa junan su. What happened? What has changed so much?. Kukan jariranta ya saka ta bude ido, saitin inda ta kwanta duk ya jike da hawaye. Tana jin nannies dinsu guda biyu da aka dauka na musamman dan kula dasu suka zo suka dauke su a inda bakin da suka zo barka suka ajjiye su. Sai kuma taji anzo an kama ta an mikar da ita an mayar da ita kan kujera, bata san waye ya mikar da ita din ba amma tasan dan tana biyan sa kudi ne ya taimaka mata ba dan Allah ba, ta san tayi loosing wadanda zasu taimaka mata dan Allah dan ita ma sanda tayi taimako ba dan Allah tayi ba. Twice.
*16 years Later*
Shekaru talatin kenan da mutuwar Hussain.......
Shekaru talatin da batan jaririn dansa
Rayuwa ta cigaba da tafiya, lokaci yana ta gudu kamar yadda kowa yasan cewa baya jiran kowa. Ko kana aikata alkhairi ko kuma kana aikata sharri shi lokaci babu ruwansa tafiya zai cigaba da yi kuma yana tafiya tare da adadin kwanakin da aka lissafa maka a duniya.
Ko wanne wayewar gari kuma tamkar dama ce da take gaya wa mutum yayi aikin alkhairi, kamar tunatarwa ce ta cewa kwanakin ka suna tafiya, damammakin ka suna karewa, change! repent! Amma kash, mai hankali ne kadai yake ganewa, mai hankali kadai yake chanja munanan halayensa da kyawawa a lokacin da ya gane, mai hankali ne kawai yake nadama a lokacin daya fahimci ya aikata zunubi kuma ya tuba ga ubangiji, mai hankali ne kawai yake neman yafiya ga wadanda ya zalunta a take a lokacin daya fahimci ya zalunce su din.
Ba zai jira sai nan gaba ba.......
Ba zai jira sai ya samu another chance ba...........
Saboda bashi da tabbas din zai samu wani chance din
Saboda tomorrow is never promised.
Komai zaka yi kayi shi a yanzu, dan today is what you have. Abinda kake dashi kuma dashi kake amfani
Yara sun zama manya, manya kuma sun zama magidanta, magidanta kuma sun zama dattijai.
Baba da Inna shekaru sun tura, Adam ya yi surprising din su da gina musu sabuwar makarantar islamiyya anan karshen layin da gidan su yake, aka dauki malamai da yawa da Baba a matsayin oga kwata kwata, Inna ma kuma sai ta roka aka bata ajujuwa a ciki da take koyawa matan aure karatu, wannan abin ya faranta musu rai matuka dan duk a rayuwar su babu abinda yake basu joy irin du koyar da ilimin addini.
Lafiya lau suke zamansu sai dan abinda ba za'a rasa ba saboda shekaru. Sai kuma Ruqayyah da har yau suke ganinta a matsayin jarabawar su da suka fadi, sai dai a matsayin ta na yarsu har yau basu fidda ran zata bude bakinta ta fadi laifinta ta kuma nemi yafiya.
Aunty ma tana nan duk da shekaru sunja mata amma tsabar jin dadin da take ciki ya saka hankalin ta a kwance yake tana rayuwa cikin tarin jikokin ta, ta kuma samu sabuwar dabi'a ta dauko yara yammata na cikin dangi su zauna a gurinta na dan lokaci kuma ta aurar dasu cikin bajinta da karamci. Bata yi aure ba duk da nacin da Hassan yayi ta yi mata har ya hakura ya barta.
Fatima da Adam har yanzu suna Dubai. A yanzu ma sun zama tamkar yan kasa a can Adam yayi kuɗi na gasken gaske saboda kwazon sa da kokarin sa a gurin aikinsa, da kuma zurfin da yayi a ilimin abinda yake aiki a kai. Babban jin dadin su kuma shine yadda suke tarairayar junansu cikin tsantsar soyayya, shakuwa, abota da kuma wayewa. Fatima har yanzu gap din da yake cikin memory dinta bai cike ba duk kuwa da irin doctors din da tayi ta gani har ta gaji ta barwa Allah ikonsa. Soyayyar Adam da kuma soyayyar yayansu guda hudu ya taimaka wajen rufe ramin da yake zuciyarta duk da dai ciki hollow ne, bata sani ba ko zai cike a duniya ko kuma sai a lahira? Kannen Adam duk sunyi aure, mamansa ma tayi, babansa ya mutu a imo da bakin cikin rashin family dinsa, brother dinsa is no where to be found.
Sumayya da Hassan komai zam zam, kamar yadda yaran sukayi alkawarin sun bar Ruqayyah haka suka yi, basu kuma waiwayenta ba duk da cewa katanga daya ce a tsakanin su dan suna ganin sun samu komai a gurin Sumayya a matsayin uwa. The boys are now men, Aminu da Yusuf sun gama duk karatun suke da burin yi a rayuwa, Aminu ya samu aiki a Abuja a NESREA, Yusuf kuma yana nan ya kamawa Baban sa harkar Real Estate da har yanzu Hassan yake kanta, yanzu kusan shi yake jagorantar komai sai dan abinda ba'a rasa ba da Hassan yake yi da kansa. Duk su biyun sunyi aure harda karuwar ya'ya ɗai ɗai.
Hussain yana gurin second parents dinsa har yanzu kuma kamar yadda yace zai gaji mai sunan sa haka yayi, kasuwanci sosai ya kafa kuma yake cigaba da kafawa a bangaren suttura, kasancewar garin da yake dama na kasuwanci ne sai ya samu budi sosai ta wannan bangaren. A yanzu haka yayi nisa gurin neman auren takwarar Fatima da sarki Umar yayi mata.
The three Abduls duk sunyi nisa a nasu bangarorin na rayuwa, Amatullah tana jami'a kuma bakin Sumayya ya karbu dan ba'a yi mata kani ko kanwa ba.
Kowa yana having good life, an excellent life, banda Ruqayyah.......
Komai na rayuwar Ruqayyah bai tafi mata dai dai ba a wadannan shekarun, yan biyun ta sun girma cikin dukiya da gata kamar kamar yadda take mafarki, tayi kokarin ta yi replacing din lost children dinta da su amma abin ya gagara, problem na farko shine gaba-daya tarbiyya yaran taki tafiya mata dai dai, musamman Sa'ad, tun yana yaro tantiri ne na karshe dan Ruqayyah tana jin duk abinda take tunanin tayi tun daga yarintarta har zuwa girman ta to Sa'ad yayi doubling.
Baya jin maganar ta ko kadan, ya raina ta karshen raini, zai iya gaggaya mata magana a duk lokacin da yayi niyya ba tare da ko kadan ya ji cewa bai yi dai dai ba, kuma a fahimtar Ruqayyah sai ta fahimci cewa Lukman ne mai daure masa gindi yayi duk abinda yake so. Sa'adatu ce mai dama dama, dama daman ta kuma shine tana son Ruqayyah tana kulawa da ita sosai da sosai dan duk wasu hidimomi nata a yanzu Sa'adatu ce take yi indai har tana gida. Abu daya da Ruqayyah take jin dadin sa shine yadda yaran suke tsananin kaunar junansu, ba'a taba daya daya ya kyale koda kuwa ita ce, ko fada tayi wa Sa'ad sai Sa'adatu ta nuna bacin ranta. Babban abinda yake bata mamaki a halayyar Sa'ad shine shegen son kudin sa, duk kuwa da cewa an wada ta shi da komai in abundance amma hakan bai hana shi ya saka hannu ya dauki duk abinda ta ajiye ko ubansa ya ajiye ba.
An saka su a makarantar kuɗi irin wadda Ruqayyah take ta mafarkin saka ƴaƴanta, amma kuma sai dai kan babu komai, duk uban kudin da ake zubawa a cikin makarantar amma babu abinda yaran suke fitowa da shi sai lalacewar tarbiyya musamman ta bangaren Sa'ad.
Sa'ad ya fara shaye shaye tun yana js class, sanda ya shiga senior class kuwa ya gama gwanancewa akan duk wasu munanan dabi'u da dukkan wata lalatacciyar tarbiyya. Hawan jini, ciwon zuciya babu wanda Ruqayyah bata dashi a yanzu, ba wai matsalar yaya bane kadai har data miji, yanzu ta kuma tabbatar wa cewa Lukman ba sonta yake ko kankani ba ya aure ta ne dan ya cigaba da juya dukiyar ta, sannan ya haihu da ita for security, dan zuwa yanzu ko magana mai dadi babu a tsakanin su kamar yadda babu komai tsakanin ta da dukiyar ta in banda ta saka masa hannu a takarda, abinda a ranta take tunanin shine kadai zaren da yake rike da su a tare.
And then one day......
Ranar da Sa'ad da Sa'adatu suka yi graduation na secondary school, a ranar ne Sa'ad din yazo kamar yadda ya saba ya jefi Ruqayyah da hoton wata sport car, a bayan hoton ya rubuta wani amount na kudi, tace "na menene wannan din?" Yace "ji nake yi kina gani, ko idon ya tafi ne shima ban sani ba? Kudi ne zaki bani" tace "me zakayi da wannan kuɗin Sa'ad? Wannan uban kudin me zakayi dasu?" Ya rike kugu, daga dukkan alamu a buge yake yace "kaji wata tambayar rainin hankali, yama zakiyi ki tambaye ni abinda zanyi da kuɗi? Kudi fa? To mota zan siya, sabuwar sport car din da ake yayi yanzu irin wadda yayan masu kudi suke yayi ita nake so inyi order a matsayin gift dina na kammala ssce" tace "kammala ssce? Ssce din dana tabbatar da cewa babu abinda zaka ci a ciki shine har zanyi maka wannan gift din? Da ace kayi abin kirki ne ma da sai in baka something amma ba wannan kudin ba".
Ya harzuka "wallahi baki isa ba, chafdi, bayan na riga na gama gayawa abokai na duk cewa za'a siya min wannan motar? Har fa hoton ta na nuna musu, wallahi sai an bani kudin nan ko sama da kasa zasu hadu" tayi shiru tana kallon sa, tsananin kamar da yake yi da ita yasa take ganin fuskarta sanda ta gama secondary dinta a cikin tasa, maybe da iyayenta sun tsaya strong a kanta sun hana ta auren Hassan, maybe da bata samu kanta a inda take a yanzu ba, she is going to be strong for her children, tace "to nace ba zan bayar ba, in kuma zaka kwata ta karfi ne to bismillah"
Sai yayi murmushi "baki san irin abinda zan iya yi saboda kudin nan ba wallahi da baki ce haka ba"
Sunfi sati a haka, yayi mata iya rashin kunya ta ki bashi tana ganin hakan a matsayin hanyar taimaka masa, uban ma yayi magana ya nuna ta bashi kudin still taki, the first time da tayi masa musu, wannan yasa ya sha jikinsa cewa malam mai tsubbu ya tafi lahira da asirinsa, dole ne kuma ya dauki wani matakin. Wannan dalilin ne yasa yaga lokaci yayi daya kamata ya debi rabonsa a cikin dukiyar, ya debi kudin pension dinsa sannan ya nemi inda dare zaiyi masa. Ya shirya komai ya rubuta check kamar yadda ya saba bata tana signing a matsayin na house maintenance, ya bata ta duba amount taga dai dai sai tayi signing ta bashi, sai daya fita ya shiga mota sannan ya dauko biro ya kara zeros guda shida a amount din ya fita.
Jaka guda ya ciko da kudi, amma basu ishe shi ba dan haka ya taho dasu gida da niyyar zai hada da duk golds da duk abubuwa masu amfani na gidan ya tafi dasu. Yana shigowa Sa'ad yana kokarin fita, sai ya kama masa jakar suka shiga da ita ciki suka hau sama da ita, shi duk Lukman bai yi tunanin Sa'ad ya san menene a cikin jakar ba, shi ya kai sama ne dan yasan Ruqayyah bata iya hawa. Dakin sa ya shiga ya kuma bude safe box din cikin dakin ya saka jakar sannan ya saka pin ya rufe safe box din.
A take zuciyar Sa'ad ta yanke masa abinda zai yi .........
A daren ranar yan fashi suka shigo musu gida, abinda ba'a taba yi musu ba, kuma abin mamaki shine yadda alamu suka nuna ta cikin gidan aka bude musu gate din.
Ruqayyah tana dakinta tana bacci, a cikin baccin ta fara mafarkin da yafi mata kama da memory, mafarkin ranar da ta fara haduwa da Hassan, ranar da ta zamo farko kuma karshen rayuwarta.
Ta gansu suna karatu tare da Sumayya a daki, sai kuma ta ji harbin bindiga, sannan ta kuma jin wani harbin. Sai ta dauki buta ta tafi toilet, Sumayya tana ta gaya mata kar taje. A toilet din taga Hassan, wuyansa da kafarsa suna zubar jini. Ya rike ta.
"Help me please, ki taimaka min dan Allah"
Kuma sai taga toilet din ya rikide ya koma dajin da suka yi accident a ciki, Fatima tana tsaye a gaban ta hannunta rike da cikin ta, jini yana zuba daga sholder dinta, tace
"Help me please, ki taimaka min dan Allah"
Sai taji karar harbin bindiga na uku. Wanda shine ya tashe ta a tsorace tana salati jikinta yana