Showing 228001 words to 231000 words out of 300844 words

Chapter 77 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2037

gyara zaman hularsa, tana dan murmushi tace "Allah yasa dai bamu makara ba, naga har karfe tara tayi" yana kallonta yace "ban dake zamu je ai. Kiyi zaman ki a gida" ta bude ido cikin mamaki "ban da ni kuma? What if aka neme ni ko bukatar inyi wata maganar ta taso? Yace "babu wanda zai neme ki, an gama bayar da shaida ai, hukunci kawai za'a yanke"

Taji ranta ya baci, wato hukuntata yake so yayi ko? Ko tunanin sa zata je taga Adam ne ko wani abu? Ta bishi da kallo yana sauka daga stairs ta dan daga murya tace "this is not fair, you are doing exactly what she wants" sai ya juyo da sauri ya dawo yayo kanta gadan gadan, bata motsa ba har yazo daf da ita ya tsaya sannan yace "at least ni ba a gabanta nayi abinda take so din ba, ke kuwa a gabanta, a gaban kowa da kowa kika nunawa duniya cewa kin damu dashi"

Tace "of course na damu dashi a matsayin sa na musulmi dan uwana, yes, na damu dashi a matsayin sa na mai gaskiya da ake neman a makala wa laifin da bai aikata ba kuma...." Yace "duk kanin mu mun damu dashi, duk munsan cewa makirci ne kawai Ruqayyah ta shirya akan sa amma babu wani acikin mu da yayi feeling the need to raise his voice sai ke, a matsayin ki na matar aure" tayi shiru tana kallon sa sannan tace "are you jelouse? Yace "of course I am, what where you thinking?" Ta sauke idonta kasa tace "kayi hakuri".

Yayi ajjiyar zuciya, da wannan take cinsa da yaki, ko tayi masa laifi, wanda hardly ne ma tayi masa laifin, to da ya hau zata bashi hakuri wani lokacin ma sai daga baya sai ya fahimci ashe shine bashi da gaskiya ba ita ba, amma ita already har ta bashi hakuri. Ya dan rage tsaho kadan yayi kissing dinta yace "sai na dawo" still baya jin zai barta taga Adam yau.

Yana sauka kasa akayi masa waya, ya daga suka yi magana da wanda ya kira shi sai kawai ya juyo ya dawo palo ya zauna akan kujera ya cire hularsa ya dora ta akan fuskar sa, Sumayya ta ajiye Abdullahi ta zauna kusa dashi tare da dafa kafadarsa "lafiya naga ka dawo? Wani abun ne kuma ya faru" bai bude fuskar sa ba yace "Fatima ta janye karar gabaki daya"

Suka yi shiru gaba dayansu, tama rasa me zata ce masa dan bai bari taga fuskarsa ba ballantana ta karanci halin da yake ciki. Babu motsin kowa a gurin sai na Abdullahi da yake ta bin kujeru yana waƙoƙin sa. Sunfi minti goma a haka sannan ya mike da sauri zai fita, ta mike itama tace "ina zaka je?" Ya juyo yana kallonta, sai taga fuskarsa tayi so calm ba kamar yadda ta saka ran gani ba, yace "zanje gurin Ruqayyah. Ina son magana da ita".

*************************

Ruqayyah kamar kowa itama yau ta tashi da niyyar zuwa court, sai dai zuciyarta jin ta take yi kamar bakar tukunya, kuma haka take jin ta tun last zama da akayi a court dan bata jin cewa ranta ya taba baci irin na ranar nan, wai ita Ruqayya ita ce a zaune tana sauraron duk wani wanda take jinsa a zuciyarta yana keta mutuncin ta a cikin jama'a, ciki kuwa harda babanta mahaifi, twin sister dinta, da kuma mutumin da a yanzu rake jinsa a ranta sama da kowanne namiji.

Kawayen ta ma ba'a barsu a baya ba, munafukan kawayen da a yanxu ita take yi musu komai na rayuwar duniya, tana nan tana jiran ta ga ranar da zadu dawo neman wani abu a hannunta. Duk da dai bata san ya hukuncin zai kasance ba amma ita kawai tana ganin it won't be on her favor, duk da cewa Lukman yayi ta gaya mata cewa wannan result din na likita ya shafe duk wata shaida da aka gabatar a court din amma hankalin ta bai kwanta ba, musamman da taji yace "highest da za'a yi miki shine a kaiki gidan mahaukata" wannan shi ya kara daga mata hankali, yama za'a yi a kaita gidan mahaukata? Ita ina zata iya zama a gidan mahaukata?

Tan gam shiryawa Lukman yazo, ita haushi yake bata, asarar kudi kawai, ashe ma reputation din nasa na banza ne. Yazo yana yake mata baki "kar ki wani damu. Tunda medical report din ya sake nunawa kamar wancan, muna zuwa alkali zai yanke hukuncin kuma na tabbata bamu da matsala" tace "bamu da matsala? Tafiya gidan mahaukatan shine ba matsala? " Yace "ba lallai bane ba wannan, tunda na rusa shaidar Adam basu da wata hujjar da zata saka ace....." Tace "ka rusa shaidar Adam ko kuma na rusa shaidar Adam? Wai kai me kayi ma a cikin maganar nan? You just sat there like a zombie a lokacin da ake keta mutunci na a cikin mutane, a gaban media, you sat there and did nothing"

Yaji zafin maganar ta amma yayi shiru, shi dai so yake ya lallaba ya karbi sauran kudin sa ya kara mai. A haka ya lallaba ta suka fita, a ranta tana jin maybe ta fita kenan daga gidan nan, tayi sallama da guards dinta tace zata kira su inta dawo dan bata so ta tafi dasu court saboda yan social media, tafi son take zuwa court a matsayin abar tausayi. Sai dai basu yi nisa da tafiyar su ba sai ga waya cewa Fatima taje ta janye kara.

Maganar ta basu mamaki gaba ki dayansu, dan basu taba tsammanin haka ba, sai Ruqayyah taji a ranta kamar there is something behind wannan janye karar. Bata jin Fatima zata yi giving up this easily, ta san zata so ko da gidan mahaukatan ne a kaita. Dan haka sai taji bata ji wani dadi sosai a labarin ba. Suka juya suka koma gida, amma Lukman yana ajiye ta shi kuma ya huya zai tafi Abuja dan akwai takardun da zaije yayi signing kuma ya karbo. In ya dawo kuma sai yazo Ruqayyah ta sallame shi.

Bayan tafiyar sa bai fi da minti uku ba sai ga Hassan ya shigo, kamar daga sama ta ganshi a gabanta, sai a lokacin ta tuna cewa ta sallami guards dinta. Gabanta ya fadi, wato plan din da suka shirya kenan? Ita Fatima ta janye kara shi kuma yazo yayi ta jibgar ta harsai ta fadi gaskiya sannan sai su sake shigar da fresh kara. Lallai kuwa zasu sha mamaki dan babu a binda zata fada.

Ta fara ja da baya a kan wheel chair dinta, tana saka ran zai biyo ta amma sai taga ya jingina da bango ya rungume hannunsa yana kallonta, sai data kai jikin bango sannan ta tsaya tare da dauke numfashin ta tana kallonsa tana jiran taga abinda zaiyi sai taji yace "ki dana guduwa, I won't lay a single finger on you Ruqayyah, kin san saboda me?" Ta girgiza kai da sauri, yace "saboda idan na kama ki ba zan barki ba har sai na tabbatar kinyi numfashi na karshe a duniya. Ni kuma ba zanso haka ba, saboda in nayi haka tamkar na taimaka miki ne na kwashe miki tarin alhakin da yake kanki. Kuma na san ko mai zan yi miki ba zaki fadi gaskiya ba dan haka ba zan bata lokaci na ba. Na barki da Allah."

"Ni nasan kin aikata laifin da ake tuhumar ki dashi Ruqayyah, you killed a baby, Hussain's baby, Hussain's only child, a ranar da Hussain ya bar duniya. Kuma nasan kinyi haka ne saboda ki ci dukiyar Hussain, shi yasa na baki ita, gata nan, na baki ita ne a lokacin da bansan cewa an haifi dan Hussain ba, amma yanzu na sani, dan haka ina tuna miki cewa bani da gadon Hussain indai har namiji Fatima ta haifa. A yanzu kuma babu wanda ya san me ta haifa sai ke, ke kuma ba zaki fada ba, dan haka babu mai karɓar dukiya a hannun ki kije ki rike dukiyar gado, ki ci ki sha kiyi suttura ki more rayuwar ki da dukiyar maraya, marayan kuma da kika halaka da hannun ki. Wannan shine punishment dina a gare ki. Wannan shine hukuncin da ni Hassan na yanke miki because you know what? Wannan dukiyar" ya fada yana nuna gidan "is going to be the end of you"

"Ga dukiyar maraya nan a hannun ki, kiyi ta bauta mata, irin bautar da ko Ubangijin daya halicce ki baki yiwa ba, kiyi ta ninkata tana karuwa amma kuma duk ba taki bace ba, ita kuma zata yi ta cinki, slowly, piece by piece har sai ya zamanto kina addu'ar ki mutu ki huta saboda babu abinda zaiyi saura naki sai your pathetic soul, wannan kuma sai ya koma gurin ubangiji sannan ne zaki fahimci cewa ashe mutuwa ba hutun bace ba a gare ki, ashe mutuwa mukulli ce ta bude lodi lodin azabar da ubangiji ya tanadar miki a can, azaba ta musamman saboda kasancewar ki mai ilimi"

"Ni Hassan, a madadin Hussain, da dukkan ya uwanmu da kuma yayan da Allah ya bamu a tsakanin ni da ke, Allah ya isa. Da ina yi miki fatan shiriya kuma shine dalilin da yasa nake ta fafutuka a kan ki, ko dan yayan mu, amma a yanzu, a kan maganar jaririn Hussain ba zamu taba yafe miki ba".

Daga nan ya juya, and without another word, ya fice ya bar gidan. Sai taji kamar maganganun sa suna amsa kuwwa a cikin kunnuwan ta, sai taji kamar gidan gabaki daya yana nanata kalmar Allah ya isan da yayi mata. Tasa hannayenta biyu ta toshe kunnuwan ta amma sai taji Allah ya isan a cikin kanta take ba wai daga kunne take shiga kan ba. Ta rufe idonta tana kokarin digesting maganganun sa, cursing dinta yayi fa, lallai ma Hassan din nan. Amma kuma tasan maganganun sa zasu zauna a cikin zuciyarta har ranar da zata koma ga mahaliccin ta.

A jikin ta taji kamar ana kallon ta, sai ta bude idonta da sauri tana tunanin ko shine ya dawo ko ya chanja shawara akan dukan ta. Amma abinda tagani ne yasa taji kamar zata kifo daga kan kujerar guragun ta. Fatima ce a tsaye tana kallon ta, as smartly dressed as ever, ita sai taga kamar ma kyau fatiman ta kara a cikin shekarun nan. Ta tako a hankali tazo kujerar da take facing Ruqayyah ta zauna, sannan ta daga kai tana kallon gidan a ranta tana kokarin cire memories din rayuwar ta a gidan daga ranta dan kar ya hana ta yin maganar da tazo zatayi.

Ruqayyah tace cikin rawar murya "me kike yi anan?" Fatima tace "zuwa nayi in tambaye ki, ina dana?" Ruqayyah ta dauke kanta gefe kirjinta yana dukan tara tara, ko da wasa datasan abinda zai faru da rayuwarta kenan da bazata taba yaron nan ba. Amma shi hannun agogo idan ya wuce ba'a iya dawo dashi baya. Fatima ta sake tambaya "what have you done with my child?" Ruqayyah tace "ni bansan me kike magana akai ba" Fatima tace "kudi kike so? Nawa kike so? Gidan nan, kudin da already yake hannun ki, babu abinda zan karba daga gareki in dai zaki dawo min da dana, ni dana kawai nake bukata in kari kike so ma na kudi zan kara miki"

Ruqayyah ta sake cewa "ni bansan me kike magana a kai ba, ni bansan wanne dan kike magana akan sa ba" a ranta tana tunanin tarko ne Fatima take dana mata dan tayi confessing, wannan shine kadai abinda suke bukata dan su rufe ta kuma su kwace komai.

Faima ta mike tsaye tana goge hawayen daya taru a idonta tace "shikenan, dama last chance nabaki a matsayin ki na mutum kuma musulma, amma tunda kinyi watsi da damar ki shikenan. Ki sani, na janye karar daga court ne ba dan komai ba sai dan naji ance sentence din da zaki samu ba zai wuce yan shekaru a gidan mahaukata ba, and my son is worth much more than that, shi yasa ni nazo zanyi miki nawa hukuncin. Idan da naso zan iya daukaka kara zuwa court din da za'a yi ta jan shari'ar har ki rasa kudin daukan lawyer, ko kuma in biya doctors suyi faking wannan result din kwakwalwar ki kuma in je in ce na tuna abinda ya faru, in kirkiri labarin da zai nuna cewa ke kika dauki dana, yadda Shari'a zata kamaki ta matsanta miki kiyi confessing abinda kika yi wa dana a karshe a yanke miki hukuncin rataya. Amma duk ba wannan nake so ba. Yin wannan tamkar taimako ne a gare ki"

"Dani da ke dukka munsan cewa ke kika salwantar min da rayuwar dana. Dani da ke dukka munsan cewa in ma kina da mental problem to kin same shine bayan kin aikata abinda kika aika ta, maybe ma sanadiyar abinda kika aikata ne yasa conscious dinki yake playing tricks with you. Maybe mental problem din yana daya daga cikin azabobin ubangiji da suka fara sauka akanki sanadiyyar abinda kika yi" ta fada tana kallon Ruqayyah. Sai tayi murmushi tace "shi yasa na fasa Shari'a dake na barki dashi, domin abinda zaiyi miki ko rabi rabinsa ni bazan iya yi miki ba. A matsayi na na wadda na haifi yaron nan sannan kika raba ni dashi ba tare da kin barni ko fuskarsa na gani ba, ba tare da ko kukan sa naji ba, ba tare da ko dumin jikin sa naji ba, Allah ya isa. Daga yau na dauki alkawarin a duk sallar da nayi zanyi miki Allah ya isa har zuwa ranar da zan daina numfashi"

"Ina ji a jikina cewa dana is in a good place, ko yana duniya ko baya duniya nasan he is safe, but you are not. Azabobin ubangiji suna da yawa Ruqayyah, ki fara lissafi daga kan kunnuwan ki, kafafuwan ki, kwakwalwar ki da sauran abubuwan dani kaina ban sani ba. This is just the beginning. Ina miki fatan tsahon rai, tsahon rayuwar da har duk wadanda kika zalinta zasu mutu su barki a yayinda ke kuma zaki yi nadama amma wadanda kika zalunta sun mutu ballantana ki neme su gafara. A lokacin ne zaki fahimci abinda yasa mutane suke addu'ar samun kyakkyawan karshe. Ke kuma bazaki samu ba. These are my wishes for you"

Sai ta juya ta bar gurin, har ta kai bakin kofa sai ta juyo tana kallon Ruqayyah, hawaye yana zuba daga idonta tace "you are not going to tell me where my son is, are you?" Still Ruqayyah tayi shiru, amma daga inda Fatima take tsaye tana iya hango hawayen da yake bin fuskarta. Sai ta dauko sun glasses ta saka a idonta dan ta boye hawayen ta sannan ta juya ta fice.

*Jungle Justice*

Adam da tun da ta shiga ciki yake tsaye yana kallon kofar shiga gidan, ji yake yi kamar ya bita ciki ya tsaya a gefenta har ta gama maganar da tace zata yi da Ruqayyah ta fito, shi bai yarda da Ruqayyah ba, duk da gurguwa ce amma ai maciji ma gurgu ne kuma a haka yake cutarda mutane nasu kafafuwa. Yana nan a tsaye, zuciyarsa tana ta tsinkewa har ya fara tunanin ya shiga sai gata ta fito, tana gyara glasses din idonta wanda sanda ta shiga babu shi a fuskarta. Kallo daya yayi mata ya san ranta a matuƙar bace yake sai ya bude mata kofar mota ta shiga shi kuma ya zagaya side din driver ya shiga suka dauki hanya.

Bata nemi Hassan ko Aunty ba kuma Adam ma bai yi mata maganar su ba har suka bar gidan, sai ta kwantar da kujerar ta kwanta tana kuka. Bai tambayeta inda zai kaita ba dan bai san daga ina ta taho ba amma kawai sai ya dauki hanyar kano dan yasan tana bukatar iyayenta, sai ban maganar da suka yi da Ruqayyah ba, bai san zafin da take ji a zuciyarta ba amma ko ma menene yasan soyayyar iyayenta zata yi mata magani.

Ya kunna radio ya saka mata karatun Alkur'ani sannan ya dauke kan mota da niyar barin gari. Suka wuce hanyar gidan Baba, ya kalli layin yana ji a ransa cewa yana so yaje ya gaishe shi amma yasan ba zai iya kai Fatima gidan su Ruqayyah ba, ko da kuwa bata cikin halin da take ciki a yanzu. Dole zuwa gidan Baba ya jira zuwa nan gaba, amma very soon zai dawo Kaduna musamman saboda wannan niyyar.

Har suka iso Kano bata ce masa komai ba kuma shima bai tambaye ta komai ba, suna zuwa kofar fada aka bude musu gate suka shige direct ya kai ta har bakin kofar da zata shiga cikin gida. Ta dago kai tana kallonsa, tace "Nagode sosai, ka tafi da motar gida ka dawo da ita later" yace "nine da godiya Madam. Duk da dai baki fada min dalilin ki na janye kara ba, but am very great full that you did, you have no idea how much it means to me. Sannan kuma duk da daki gaya min maganar da kuka yi da Ruqayyah ba, shima ia fatan a samu maslaha a cikin lamarin" ta girgiza kanta tana jin hawayen daya tsaya yana dawowa tace "babu maslaha a cikin lamarin Adam. Nayi kokarin im hada ta da Allah ko kuma in tsorata ta wai ko zata gaya min gaskiya amma taki magana. Bayan duk abubuwan dana gaya mata bana jin zata taba fadar gaskiyar maganar nan, bana jin zansan abinda ya faru da baby na Adam" yaji kukan ta yana taba shi yace "listen Fatimah, baki da bukatar Ruqayyah dan sanin abinda ya faru da baby, wata rana, you are going to remember, kinji? You will remember" ta share hawayen ta tace "ni tsoro nake ji, bana son in tuna ma Adam, what if abinda zan tuna din yafi karfin ƙwaƙwalwa ta? What if i remembered my baby's death? What if akan ido na ta kashe min dana" ya dafe kansa "stop thinking like that, kinsan dai baki da lafiya ko? Let me tell you something, ninina da hope, gani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login