Showing 54001 words to 57000 words out of 300844 words
part of him tun sanda ya gaya masa zaiyi bincike a kansa but bai san zai zauna yayi ta jifansa da kananan maganganu ba, tunda har ya binciko Christian name dinsa kuma ya gaya masa Adam is his Islamic name ai ba kuma sai ya bashi labarin cewa he is a convert ba. Wannan tambarin shi yasa ya bar kano, ya bar iyaye sa da siblings dinsa da friends dinsa gabaki daya saboda ya kasa belonging, to the christians suna kallonsa a matsayin wanda yayi wa addininsa ya kuma yi musu butulci dan haka har farautar rayuwarsa suke yi, to the Muslims kuma suna kallonsa a matsayin wanda yake da wani bakin penti da komai yawan sallarsa da ibadar sa ba zai iya goge shi ba. Wannan yasa ya bar kano ya dawo Kaduna, to burry his past.
Asalin iyayen Adam mutanen jahar imo ne, neman kudi ne ya kawo babansa kano, anan aka haife shi a matsayin first born sannan aka haifi brother dinsa Samuel sai kuma sisters guda biyu Gloria da Martha. Lokacin da aka haifi Adam mahaifinsa bashi da kudi sosai, sai daga baya dukiyar sa tayi ta habaka kamar an sakawa flour yeast, dan haka Adam ya tashi ne tare da sauran yaran unguwa, wadanda yawancin su hausawa ne kuma musulmai. Duk gidan da Adam yake shiga wasa gidajen musulmai ne, makarantar da yake zuwa malaman da daliban yawancin su musulmai ne, a na kuma koya musu islamic studies har shi da ba musulmi ba. Kuma wasu lokutan idan abokansa zasu je islamiyya yana binsu ya zauna a aji tare dasu yaji karatun da ake yi musu, Tun daga nan yake son musulunci.
Alokacin takaicinsa shine sunday tayi mamansa da babansa su tafi dashi church suje ayi ta waka da kida da rawa, shi a zuciyarsa sai yake ganin a dira goshi a kasa kamar yadda musulmai suke yi a sallah yafi kama da ibada akan ayi rawa ayi waka. Shi kalaman da yake ji ana karantowa a cikin Alqur'ani sunfi yi masa kama da kalaman ubangiji akan abinda pastors dinsu suke fada musu a church. Behavoirs din da yake gani a gurin musulmai tafi yi masa kama data mutanen kirki akan wadda yake gani a gurin iyayensa da sauran Christians.
Tun daga nan ya saka musulunci a ransa, har ya girma ya shiga secondary school, a nan ne ya fara fitowa da abinda yake zuciyarsa yana nunawa a fili. Kullum ya samu musulmi sai yayi tayi masa tambayoyi akan addini, in ya shiga cikin abokan da basu san shi Christian bane ba sai yayi basaja ya bisu suje masjid suyi sallah. Anan ya iya sallah complete dinta, ya iya karatun wasu daga cikin surorin Alqur'ani kuma yake karantawa a cikin sallar kamar yadda yaga anayi. And he finds peace duk sanda yayi sallar. He finds peace in the masjid.
Tun daga nan ya sani har zuciyarsa cewa musulunci shine addinin gaskiya ba Christianity ba, yasan cewa kuma one day he is going to walk in cikin wani masallaci ya samu imam din yace a musuluntar dashi. Already yasan abinda ake reciting in za'a musulunta din ma kuma ya iya. Already har ya zabi sunan Adam a matsayin sunan da zai zaba. Ya daina zuwa church. Tun daga nan trouble dinsa ya fara, tun daga nan iyayensa suka gane halin da yake ciki.
Farkon abinda suka fara yi masa shine cire shi daga school sannan suka dauke shi gabaki daya suka mayar dashi gidan pastor, akayi ta masa wa'azi irin nasu ana yi masa adduoi irin nasu aka rarrataya masa cross iri iri a jikinsa but duk abinda suke yi shiga yake yi ta kunnen hagu yana fita ta dama. The more suka yi masa magana akan Jesus Christ da Bible da Christianity the more yake kara fahimtar cewa it is wrong. Yana kara jin cewa he never belong there, haifarsa kawai akayi a can.
Bayan ya dawo gida iyayensa suka fahimci babu chanji sai suka sake daukarsa suka mayar dashi imo gurin kakanninsa suna ganin cewa zama cikin musulmi ne ya jawo musa halin da yake ciki. A can imon kakanninsa suka dora daga inda iyayen suka tsaya, suka kara da binne binne da tsaface tsaface da preaching, pampering, promises amma a banza, a lokacin ne babansa yayi masa kyautar motar da yake ja yanzu saboda yaga yadda yake son mota da kuma alkawarin in dai ya cire musulunci daga ransa zai kai shi kasar waje yayi karatu acan saboda yasan yadda yake son karatun. Anan ne Adam ya nuna musu ya sauko, ya fara binsu zuwa church ana ayyukan ibada tare dashi, ganin haka yasa iyayensa suka dauko shi suka dawo dashi kano tare da su. A lokacin mahaifinsa yayi arziki sosai da sosai
Abinda Adam ya fara yi a ranar da suka dawo shine ya shiga cikin masallacin unguwarsu ya durkusa a gaban limamin masallacin yace "ina so a musuluntar dani" and that was it.
Babansa a ranar cewa yayi sai ya yanka shi. Limamin unguwar sune ya dauke shi ya boye shi sai ga uban da police wai an sace masa da. Inda ya samu sassauci kawai shine he was 19 years then dan haka he can stand up for himself legally, dan haka ya zamanto his words against his father's words. Ya fada cewa shi baya son komawa gidansu saboda babansa yace zai kashe shi tunda ya musulunta kuma yasan zai iya aikatawa. Wannan yasa dole aka barshi a gidan Imam din but still his father started to hunt him, har makaranta ya aika yan daba su kamo masa shi Allah ya taimaka masa ya gudu, sai liman din ya dauke shi daga unguwar ya mayar dashi hotoro gurin kaninsa. Ananne ya samu ya fara karatun addini ya kuma kammala secondary school dinsa, but anan ne ya fara fuskantar kyama daga gurin musulmai da kuma christians, hatta gidan da ake rikon nasa kyamatarsa suke yi basa barin yayansu su zama close to him. Akwai wata budurwa a gidan da mamanta ta taba zanewa saboda ta shiga dakin da yake ta kai masa abinci.
Kuma wani abinda yafi damunsa a lokacin shine in mutane suna kyamar sa sai ya tuno da family dinsa, ya tuno da irin soyayyar da suke yi masa musamman iyayensa shine favorite dinsu Saboda kwazonsa a makaranta da kuma kyawun halittar sa, haka siblings dinsa, ya shaku dasu sosai and he misses them everyday. Sai yayi taji a ransa cewa yana so ya gansu, yana so ya koma gidan su. Sai dai ya kasa chanza ra'ayin sa akan addini, fata kawai yake yi cewa suma su gane gaskiya suyi joining dinsa.
Shekarar sa daya a wannan gidan ya fahimci cewa zaman ba zai yi masa haka ba, and that's when his mother found him ashe nemansa take yi tsahon shekarar nan bata huta ba, tunda ta gane inda yake kuma bata huta ba ta cigaba da zarya tana rokonsa ya dawo gida, har siblings dinsa take kawo masa har cikin gidan da yake akan dan su ja ra'ayinsa ya dawo din amma bata saka ubansa a ciki ba saboda shi yayi fushi sosai.
Ganinsa da ake yi da mahaifiyar sa sai aka kara kyamatarsa a unguwa ana ganin kamar komawa zaiyi zuwa Christianity, wadansu ma cewa suke yi ya koma, wannan ya saka mai rikon sa ya kirawo shi ya buga masa warning cewa in uwarsa ta kara zuwa gurinsa zai kore shi daga gidansa. And that's when he decided to leave Kano for good. Ya hada kayansa ya je har gidansu lokacin da yasan duk suna church ya sato motarsa ya saka kayan a ciki ya kama hanyar Kaduna. A hanya ne ya dauki waɗansu mutane zuwa Zaria suka biya shi kudin mota, sai kawai yayi deciding cewa he is going to be a taxi driver a haka har ya tara kudi ya kai kanshi makaranta.
But kudin sunki taruwa. Sannan yasan karatun ma kuma ba zai zo masa da sauki ba. That's why he needed aikin gurin Hassan saboda yaji possibility na komawa school, but yanzu yana jin cewa he doesn't need it anymore.
A ranar da Ruqayyah da Sumayya suka shirya zasu hada kai su tunkari Hassan da Maganar shirye shiryen biki, a ranar da rana sai ga kannensa mata sunzo gidan gabaki dayansu su biyar. A tare dasu akwai akwati guda biyu masu dan girma. Suka shigo da fara'ar su da kuma sallamar su, abinda Ruqayyah ta fara aiyanawa a ranta da taga akwatinan shine; "ba dai wannan ne lefen nawa ba". Daga nan sai ta tashi ta shige daki tun kafin su shigo palon.
Inna Ade da Sumayya suka tarye su sosai suma da fara'a, suka gaggaisa Inna tana tambayar su Aunty suka ce tana lafiya lau kuma tana gaisheta. Sai suka fara neman Ruqayyah "ina amaryar tamu take? Sumayya ta waiga tace "tana jin shogowar ku ta gudu daki" Nafisa tayi dariya "ba dai kunyar mu take ji ba? In kuwa har kunyar mu take ji to kuwa na tausaya mata dan kuwa ni ana gama bikin a cikin bedroom dinta zan tare" Hassana ta harare ta tace "kar ku ce zaku takurawa takwara ta dan kungan ta shiru shiru bata da magana, gashi kuma bana nan ballantana in tare mata" Sumayya tace "wacece shiru shirun? Lallai ba ki san Ruqayyah ba alkunya takw yi muku amma in ta saba daku sai kunyi mamaki, watarana sai kunji kamar ku dauki ta ku dawo mana da abarmu" suka yi dariya Safiyya tace "abarku ku abarmu? Ai daga an daura ta zama tamu ku da ita sai tarihi" Inna Ade da take jinsu tana ta murmushi tace da Hassana "ke ce daya amaryar ko?" Hassana ta sunkuyar da kanta kasa tana murmushi, Inna Ade tace Allah ya sanya alkhairi kinji? Allah ya baku zaman lafiya bakiɗaya".
Daga nan sai Inna Ade da Sumayya suka fara hidimar bakin su, suka kawo musu duk wani abin sha da abinci da yake available a gidan, su kuma bakin suka diba kadan suka ci banda Khadijah da tace ta koshi. Bayan sun gama ne Hassana tace "dama Aunty ce ta aiko mu, tace mu kawo muku wadannan kayan inji ta, akwati daga kayan amarya ne na fitar biki akwati daya kuma naku ne kuma ku saka da biki. Tata gudummawar kenan" Inna Ade ta rike baki tace "me yasa ta wahalar da kanta har haka? Da ta barshi ma Baban biyu duk zaiyi mana" Hassana tace "ita dai gashinan to ta riga shi samun ladan". Inna da Sumayya suka yi musu godiya sosai sannan kuma Hassana ta kara da cewa "kuma tace mu tambaye ku menene tsarin ku na hidimar biki? Kuma in akwai wata al'ada da kuke yi bayan lefe ku fada kar azo ba'a yi ba tunda bamu sani ba" Inna Ade tace "aa babu wata al'ada wallahi, mu lefen ma da dan tamu ne ai zamu iya cewa Hassan ya barshi" Nafisa tace "ai kuwa lefe kan an riga an gama hada shi, jira kawai ake yi lokaci yayi azo a kawo" Inna Ade tace "maganar biki kuma ki gaya mata mu nan kamu kawai zamuyi sai yini, shikenan sai ku zo ku dauki amaryar ku" Hassana tace "ita amaryar ba zata yi komai ba?" Sumayya tace "jiya muka yi Magana da ita, ita wai kunyar angon ta ke ji ta kasa tambayarsa ko akwai abinda yake shirya musu" Hassana tayi dariya tace "lallai an gaishe ta, to ki gaya mata wallahi sai ta shafawa idonta toka ta cire kunyar nan, dan in dai yaya H1 ne na tabbatar babu abinda yake shiryawa. Gwara ita ta shirya sai ta gaya masa" Sumayya tace "to insha Allahu zan gaya mata" Hassana ta kuma cewa "Inna, kuma Aunty tace in rokar mata ku, dan Allah tana son za'a dauki amarya ranar juma'a da daddare, saboda assabar ne yinin da za'ayi a kano na amaryar yaya Hussain, to Aunty tana so a tafi harda ita Ruqayyah din mu kwana acan lahadi sai a dauko waccen amaryar a dawo" Inna tayi saurin cewa "babu komai ai insha Allah, in babansu ya dawo zan gaya masa kuma shima nasan ba zai ki ba. Sai a daura auren juma'a da safe in yaso da daddare sai a dauke ta".
Daga nan suka cigaba da tsare tsaren bikin, maganar kawo lefe da sauran su. Nafisa ta mike, "ni ina ne dakin da yayar tawa take ne inje in ganta, dan ita nazo kuma ba zan tafi ba sai na ganta" Sumayya ta nuna mata kofar dakin da Ruqayyah take ciki sannan ta juya suka cigaba da maganganun su. Sai da suka gama sannan Sumayya ta mike ta shiga zata kirawo Nafisa. Tana shiga dakin ta gansu dare dare akan gado suna hura har da dariya, da alama tasu ta zo daya. Nafisa tana cewa "wallahi ina baki labari, shi yasa wannan karon da Aunty zata tafi dubai karaso siyayyar kayan lefen ki naki binta sai ta tafi da Zulaihat. Kinsan ita Aunty bata son tafiya ita kadai tafi son ta dauki wata a cikin mu ta yafi da ita, shi yasa muke shifting in ya tafi da wannan yanzu wata tafiyar kuma sai ta dauki wata. Kinga in akayi bikin ku kema sai ki shiga layi ake yin shifting din da ke" Ruqayyah baki har kunne, already har ta fara hango kanta a Dubai tace "eh wallahi, sai mu shiga layi dani da wannan yarinyar da Hussain zai aura, Fatima sunan ta ko wa?" Nafisa ta bata rai tace "yarinya? Gimbiya Fatima ba yarinya bace ba dan tare suka gama service da yaya Hassana. A England tayi karatun ta ma ita." Murmushin fuskar Ruqayyah ya dauke, tace "Gimbiya Fatima? Ke ma bakin Hussain kike bi kike ce mata gimbiya?" Nafisa tace "to ai gimbiyar ce, ya ce fa a gurin maimartaba sarkin kano kuma naji ance ita ce favorite dinsa. Kinsan kuma yadda suke da kudi, shi yasa yaya H2 ya zage dantse sosai gurin hada kayan lefenta dan kar azo aji kunya. Jiya ma naga sunzo sun bude gidan sun shiga, wata kila a cikin satin nan zasu fara kaso kayan dakinta. I can't wait to see irin kayan da zasu yi mata" idanuwan Ruqayyah suka chanja kala "you mean she is a real princess?" Nafisa tace "ta gasken gaske ma kuwa"
Nineteen: Shattered Dreams
Yadda Ruqayyah ta bude bakinta a haka ta barshi, magana ta kasa fitowa. Sumayya tayi saurin cewa "Nafisa ki zo suna jiranki zaku tafi" Nafisa ta sauko daga kan gadon tana gyara skirt dinta sannan ta dauki mayafin ta. "To yayata. Na ganki naji dadin hira dake kuma. Zamu koma sai mun dawo daukan ki" ta fada da yanayin tsokana, but Ruqayyah is in no mood for wasa, Sumayya tayi dariya tana distracting Nafisa tace "haba dai, yanzu kina nufin ba zaku zo komai ba sai daukan amarya? Nafisa tace "ai kinsan can din ma wasu events din ne, kin san biki uku ne zamuyi amma dai nasan ko bamu zo duk ka ba zamu zo wasu abubuwan" Khadijah ta budo kofa tana cewa "to suda me bakin magana, ki taho mu tafi" sai ta kalli Ruqayyah tayi mata murmushin da yafi kama da yake itama Ruqayyah ta mayar mata da irin sa, tana jin murmushin yana kokarin bude fanfon emotions din da take ta kokarin rufewa. Nafisa da Khadijah suka fita a tare, Sumayya tayi wa Ruqayyah alamar ta taso suje su raka su amma sai ta makale kafada ta kwanta ta ja bargo, Sumayya ta fita da sauri tana yi musu Allah ya kiyaye hanya tare da kara yi musu godiya.
Ruqayyah ranta kuna yake yi, kalmar Princess ce take ta yawo a cikin kanta, wai yar sarkin kano, sarkin kano fa? Sarkin kanon da take ganin pictures dinsa yanzu a social media, sarkin kanon da tasan kudin takalmin sa daya zai iya siyan duk sutturar da Baba yake da ita har da ciko, yarinyar da akace tayi karatu a kasar waje bayan ita a Nigeria tayi nigerian ma a makarantar gwamnati kuma iyakacin secondary school sannan secondary din ma ko waec bata yi ba saboda talaucin ubanta? Gaskiya akwai aiki a gabanta. Ta tuno maganar Nafisa na she can't wait to see kayan dakin Fatima, ita kuwa babu wanda yake zancen nata tunda kyauta ma za'a yi mata kayan dakin, kuma ta tabbatar watarana sai an goranta mata. Dadin abinma kudin na mijinta ne, shi kansa Hussain din da ake zancen ya hada kayan kefe na gani na fada saboda zai kai gidan sarki ai da dukiyar mijinta yayi, dan zai auri yar sarki hakan bai chanja komai ba, dole ne ta shafawa idanunta toka kafin ta shiga gidan nan kuma dole ta kwatarwa kanta yanci a gurin Hassan dan in babu hadin kansa ba inda zata je za'a mayar da ita ne kamar takalmi kowa ma yake takata da wanda ya isa da wanda bai isa ba.
A haka Sumayya ta dawo ta same ta a kwance idanunta a rufe, ta zauna akan bedside tana kallon ta a ranta tasan tunanin da take yi sai tace "it doesn't mean anything. Dan tana yar sarki ke kina yar malam Yusuf mai gadi ba komai bane ba, dan tana gimbiya Fatima ke kina plain Ruqayyah doesn't mean anything, rayuwarki daban rayuwarta daban, Allah ya halicce mu different for a reason, we are all unique for a reason, Allah yana amfani da uniqueness din mu dan yayi testing din mu, dashi yake jarabtar mu dan yaga yadda zamuyi. Idan mukayi kokarin copying others, ko muka yi kokarin comparing kan mu da others to kuwa zamu fadi jarabawar mu saboda mu da su ba daya bane ba. You are Ruqayyah, yar malam Yusuf da yake aiki kullum ba weekend babu annual leave yake ciyar da ke da duk sauran bukatun ki, ita kuma Fatima yar sarkin kanon da shima a sarautar aka haife shi ba wahala yasha ya samu ba, let her be gimbiyar ta matar Hussain while you be Ruqayyah matar Hassan cos that's your role, that's what............" Ruqayyah ta yaye rufar ta ta mike ta shiga toilet tana