Showing 240001 words to 243000 words out of 300844 words
ka sani shima yana son ka sosai. An gode, Allah kai ma ya baka wanda zaiyi maka haka"
Ya gyada kai kawai sannan yace "ameen" muryarshi can kasan makogwaronsa. Bai juyo ba saboda baya son taga hawayen da yake fita daga idonsa.
Abubakar yana can yana soyewar sa, sai daya gama sannan ya fara tattaro kan su suzo su tafi, Fatima amma taki dawowa cikin gida ko abinci bata zo taci ba, sai da Aunty ta zagaya da kar sannan ta taho da ita shima kuma sai da ta nuna mata cewa lokacin sallah yana wucewa sannan ta taho, sai dai suna kiran Adam sai ya gay musu ya fasa komawa yau sai yayi kwana uku tukunna. Wannan yasa basu jira shi ba suka tafi. Fatima bata dauki kyautar da Hassan yayi mata ba, sai dai ya gaya mata duk lokacin da ta chanja shawara tazo ta dauka ya bata shi.
Bayan sun tafi ne Hassan ya hada kan boys din sa suka koma gida. Suna shiga suka hau sama da gudu suna rige rigen neman mommy, har da Abdullahi daya fara tattakawa kadan. Hassan ya bisu da kallo, amma shi jikin sa yana bashi cewa bata saman, sai ya tafi dining section dinsu, yana shiga kuwa yaganta tana ta aikin setting table, yatsaya tae da jingina bayansa da jikin bango yana studying din yadda take komai nata cikin nutsuwa kuma a tsare, kowanne plate dagurin ajiye shi kowanne spoon ma da gurin sa. Yana bin surarta da kallo yadda jikinta musamman hips dinta suke motsawa with every move da tayi making.
Tabbas Sumayya da Ruqayyah suna kama sosai ta fuska, amma jikin su sam ba iri daya bane ba, Sumayya a cike take ta ko'ina musamman hips din ta da bayan ta suna daukan hankalin sa sosai. Hatta fuskar Sumayya tafi ta Ruqayyah cika, musamman lips dinta, very beautiful. Ya danyi gyaran murya sai ta juyo da sauri, ta bata rai, "ka tsorata ni fa wallahi. Baka yi sallama ba" yace "sorry, but I enjoy watching you in kina abubuwan ku unaware of me" ta harare shi "so kake ka kare min kallo har ka hango munina ko?" Yayi dariya tare da jan kujera ya zauna, "muni kuma? A ina? Kin san kuwa yadda kike da kyau Sumayya?"
Ta zagayo ta zauna akan cinyarsa tana zagaya hannayenta a wuyansa, yace "ya babyna?" Tayi fari da idonta "lafiya lau. Me zaka siyo masa yau?" Ya dora hannunsa akan lips dinta yace "shshsh. Mata, macece ba namiji ba, I have got a lot of boys to last me a lifetime" tayi dariya "to shikenan baban baby, me zaka siyo mata" ya fara sansana jikinta yana lumshe ido, "me take so yau? goruba ko agwaluma" ta dago kansa daga jikinta tana kallonsa tace "you! Kai nake so" ya danyi gajeren murmushi yace "kamar dagaske, in baby taji sai ta dauka da gaske ana son babanta" ta mike ta zagaya daga vayansa ta saka kanta a wuyansa tace "waye ya gaya maka maman baby bata son baban baby" yace "to ta fada mana inji" tace "actions speaks louder than words" sai ya mike, tana kallon yadda yake kallon ta ta fara ja da baya, yace "show me. Ya kike guduwa kuma? Kar dai ki gaya min a bakine kawai abin"
Sai data kai karshen dakin ta hada bayanta da bango sannan shi kuma ya karaso ya bi jikin ta da nasa, ya saka fuskarsa a wuyanta kenan suka jiyo hayaniya an doso inda suke. Ya danja da baya yana bata rai, tayi dariya, ya nuna ta da hannu "tonight, I will get the words out tonight" yaran suna shigowa gurin ya hargitse, kowa yana kokarin bata labarin abinda ya faru a gidan aunty yau, sai da ta samu suka yi settling ta zuba musu abinci ta zubawa Hassan shima sannan suka nutsu suna ci dan sun san babu kyau surutu in ana cin abinci.
Sun fara ci kenan Hassan yace mata "Fatima tare suka zo da Adam" ya fada yana studying dinta, tayi murmushi "kai amma ya kyauta daya rako ta" yace "ba rako ta yayi ba, yazo ne dan ya gaishe da su Baba, yana can ma yanzu zai danyi musu kwanaki a can" ta bude ido "kai madallah, ya kyauta sosai, kullum Inna tana yi min maganar sa, suna so suji halin da yake ciki. I told them he is okay" yace "nima Baba yana tambayata shi. Ya kyauta sosai da yaje gurin su. Sun damu dashi sosai" sai kuma ya bata labarin tafiyar dasu adam din zasu yi, sannan ya gaya mata kyautar da yayi wa Fatima duk da cewa bata karba ba.
Da dare Adam ya fita taje boutique ya siyo kaya sakawa, sai ya nuna kamar a gidan aunty yaje ya karbo. Kwanan sa uku kamar yadda yayi alkawari sannan ya yiwa su Baba sallama dan next week suke saka ran tafiya, duk da dai yayi musu alkawarin in ya sauka a can zai nemi numbers din su su cigaba da gaisawa. Da zai tafi ya dauko sakon da mai martaba ya aiko wa Baba dashi ya bashi. Baba harda kwallar sa, ba wai kudin ne damuwar sa ba dan yanzu kam alhamdulillah kudi sai dai ya bawa wani, Hassan da Sumayya sun tsaya masa a komai. Sai dai the fact that sarki guda yasan da zamansa kuma har ya aiko masa da sako shine ya taba zuciyarsa.
******************************
Lukman yaci galaba akan Ruqayyah, da maganganu na tsoratar wa, duk da cewa ta nuna masa cewa ko tayi Confessing she won't be hanged, wannan ya nuna masa cewa indirectly tana nuna masa bata kashe yaron ba, sai kuma ya koma tsoratar da ita da irin horrors din da zata fuskanta a prison, musamman a matsayin ta na nakasashshiya. Sai kin gwammace ma kashe kin a kayi da rayuwar da zaki fuskanta a can. Ki bari a kaiki mental institution din, ni kuma I will do my best a waje inga cewa an fito dake da wuri, sai a nuna kin warke ayi faking result, sai ki cigaba da rayuwar ki normal ba wata matsala"
She fell for that, tana ganin zuwa mental institution din zai iya taimaka mata wajen samun waraka daga nightmares da kuma demons din da suke hunting dinta. In ta dawo kuma tana ganin kafin nan zuciyar wadanda ta bakanta wa tayi sanyi yadda zata ji dadin neman gafarar su.
A ranar da aka tafi da Ruqayyah asibitin mahaukata bayan ta danka komai a hannun Lukman tunda tayi tayi da Sumayya taki karba, a ranar ne kuma jirgi ya tashi da Fatima da Adam zuwa kasar da zasu bude sabon babi na rayuwar su.
*Five Years Later*
A shekara ta farko bayan an kai Ruqayyah mental institution, Sumayya ta haifi danta namiji, sanda ta haihu tayi tunanin Hassan ba zai ji dadi ba tunda ya gaya mata da bakinsa cewa yafi son mace yanzu, amma sai taga murnar sa har bata kwatantuwa, a take yayi wa yaro huduba ya saka masa suna Abdulrahman, sai kuma taga hidimar da yayi mata ita da baby da sauran boys dinsu har bata iya lissafawa. Tace "anya kuwa Habibi ba ka fi son yaran akan duk sauran yaran mu ba?" Yayi dariya, "kar kiyi min sharri Noorie, duk ina son su gabaki daya" tace "naga wannan hidima haka, kamar dan fari" yace "kowa ai rabonsa yake ci, kema kanki kinsan samu na na yanzu da na da ba daya bane ba, abinda zan iya yanzu da ba zan iya ba"
Ta gyada kai cikin fahimta, tabbas Hassan yanzu ba karamin kudi yayi ba kuma yake kanyi, sosai sana'ar sa take kawo masa kudi duk da dai har yanzu bai kuma gina wata estate din ba saboda kudi yake tara wa tukunna, yace mata "sai na hada kudin da zasu ishe ni complete sannan zan fara, within short time zaki ga anyi an gama kuma cost of labour din ma zai fi sauki, dan yin aiki kadan kadan yafi jan kudi da yawa, su kansu kayan aikin ma in aka siya in bulk sunfi sauki". Ya sayi dai fili ya ajiye, kuma in the mean time yana siyan gida yayi renovating zuwa tsari irin na zamani sai ya siyar. Mutane kuma duk sun san shi akan sana'ar sa dan haka duk mai son siyar da gida sai a hada shi da shi, mai siya ma sai a hada shi da shi.
A cikin shekarar ne kuma akayi bikin Zulaihat da Abubakar. Bikin da Sumayya tayi uwa tayi makarbiya a ciki, tana da role din babbar kawa kuma yayar amarya. Bikin shine lokaci na farko da Fatima ta dawo Nigeria, amma Adam bai samu zuwa ba dan yana tsakiyar exams a lokacin, a lokacin ne kuma Fatima tazo har gidan Hassan ta karbi kyautar daya bata ta little Hussain sannan ta kuma kai ziyara kabarin Hussain. Sumayya tayi mamakin yadda Fatima din ta shigo har cikin gidan ta kuma ta sakar mata fuska sannan tayi wasa da yaranta. Little Hussain yana ta murna musamman da yaji ance kasar za'a bari dashi.
Amma Sumayya sai taji babu dadi da zai tafi, duk da ta fahimci dalilin da yasa Hassan ya bawa Fatima shi kuma gashi tana da yara da yawa a gabanta amma hausawa sunce sabo tirken wawa, sai dai bata yarda ta nuna ba dan kar Fatima taji babu dadi dan taga dokin daukan yaron take yi sosai shima kuma yaron haka, already akwai soyayya a tsakanin su. Bayan sun tafi ne Sumayya ta jinjina maganar, Ruqayyah ta salwantar da dan Fatima, and now dan Ruqayyah ya zama da Fatima.
A bangaren Ruqayyah, tun sanda za'a kaita mental institution din tayi signing takardar data ke nuna cewa ta barwa Lukman rikon dukiyar ta, sai kuma tayi masa bayanin fortune teller dinta da kudin da take bashi duk wata, "nayi niyyar zan daina bashi dama wannan watan, sai dai bansan how much ya sani ba, ba san kuma ko da gaske yake ko kuma empty threats yake yi ba" yayi murmushi tare da karbar number da kuma address din mutumin yace "don't worry, I will take care of him for you" sai kuma yayi mata alkawari "the most da zaki yi a can shine shekara daya, kawai ina so hankalin mutane ya dauke daga kanki ne for the mean time, daga na fahimci sun bar maganar sun koma harkokin su zan fito dake. And it will be as if nothing has happened".
Amma ita kanta Ruqayyah ta san ba haka bane ba, ta tabbatar she is never going to be normal or have a normal life again. Ga kudin dai tana da shi amma tasan she will never know peace but she is scared, she is scared of menene zai zamanto sakamakon ta idan har tayi admitting abinda tayi da bakin ta, will they really forgive her kamar yadda Fatima ta fada? Ta dauke mata da ta yar dashi tsirara anya zata yafe mata? And Hassan, bata jin ko zata yi kukan jini Hassan zai juyo ya kalleta ballantana yace ya yafe mata. Will they let her go to prison kamar yadda Lukman ya fada? And Lukman, ko kadan bata yarda dashi ba amma bata da choice dan tasan harkar kamfani komai a lussafe yake dan haka in dai yaci wani abu kafin ta fito to kuwa tabbas in ta fito zata sani. And he will definitely vomit it out, dan kare ba zai sha bugu ba sannan kuma gardi ya kwashe kaya ba.
Amma abinda bata sani ba shine sanda ta saka kafarta ta a cikin institution din, Lukman bashi da niyyar fito da ita har abada, a lokacin da ake cike ciken ciken yi mata registration, shi kuma a lokacin ya hada baki da wani staff a gurin da niyyar ake bata treatment din da yafi karfin ta, wanda zai rikita kwakwalwar ta ta yadda ba za'a taba barin ta ta koma gida ba, yadda zata zama mahaukaciya tuburan. Yes, kudin Ruqayyah yayi mata amfani gurin dauko mata lawyer din daya kare ta a court, without her knowing that wannan lawyer din shine daya daga cikin mugayen kaddarorin ta.
A cikin shekarar ta ta daya a gidan, maimakon ta fara warkewa daga mugayen mafarkai da kuma gane ganen da take yi sai ya kasance sai ma karuwa da suke yi, she stays up most of the nights saboda sun hana ta shan sleeping pills dinta. And that drove her crazy, rashin bacci, kadaici tinani da bakin ciki made her extremely depressed. Lukman yana zuwa ganin ta duk wata kamar yadda suka yi alkawari , yana zuwa yayi mata bayanin duk shige da ficen kudin data samu a watan, ya kuma kawo mata takardun d zata saka hannu akai, amma a zahiri abind yake kawo shi kenan dan yana bukatar saka hannunta kafin ya fitar ko kuma ya shigar da kudi. Tun a watan farko ya gaya mata cewa yayi mata settling problem dinta da malamin duba, bata san how ba amma she was grateful ta yarda kwallon mangwaro ta huta da kuda.
Sumayya, Baba da Inna da kannen su suna zuwa lokaci zuwa lokaci su ganta, amma basa jin dadin yadda suke zuwa su tarar da ita, sai suke ganin kamar kullum kara kamanni take yi da mahaukaciya. Ta rame ta koma kamar skeleton ta kuma yi baki fatar ta duk ta lalace. And sometimes in suna magana sai tayi ta repeating magana daya, irin dai yadda zararru suke yi, kamar in akayi mata addu'a sai tayi ta repeating "Ameen ameen ameen" har sai ka gaji da ji, ko kuma in ta tambayeka abu in ka bata amsa sai anjima kuma sai ta kuma repeating the same tambaya.
Sai Sumayya ta fahimci wani abu...... That smart and sharp brain of Ruqayyah is deteriorating. She is gradually loosing her sanity. Kuma bata yi kasa a guiwa ba tayi complain ga hospital management din amma sai suka nuna mata cewa suna yin iyakacin kokarin su akan ta. Babu yadda Sumayya zata yi a dole ta hakura, amma halin da take ganin Ruqayyah sai ya kara mata tunanin cewa Ruqayyah may be innocent akan abinda ake zargin ta da shi. Watakila ma duk bata san me take yi ba. Amma wani side ba zuciyarta yana tuna mata who Ruqayyah truly is.
A bangaren Lukman kuwa tun a satin da aka kai Ruqayyah mental institution ya shirya kamar yadda yayi wa Ruqayyah alkawari yaje gidan malamin dubanta, direct ya dauko masa ID card dinsa na aiki a matsayin cikakken lawyer mai zaman kansa ya nuna masa kuma ya gaya masa yasan abinda yake tsakanin su da Ruqayyah "kasan hukuncin blackmail kuwa a court? Kasan hukuncin da za'a yanke maka? Yarinyar nan bincike ya tabbatar da tana da tabin hankali dan haka in ma kaje ka tona mata asiri kamar yadda ka fada to kaine a ruwa ba ita ba, ita yanzu an gama ta tata, saura ta ka kai kuma a matsayinka na mai yaudarar kananan yara marasa wayo irin ta kuma tura su ga halaka sannan kuma kuna amfani dasu gurin samun kuɗi".
Nan take hankalin sa ya tashi musamman saboda ganin ID card din Lukman, dama kuma duk yana following yana jin abinda yake faruwa da ita, a ransa kuma ya riga ya saka ran cewa cin batin sa ya kare kenan. Amma bai saka ran za'a biyo shi har gida ayi maganar rufe shi ba. Sai ya rikice ya fara bada hakuri, sai da Lukman ya tabbatar ya gama tsorata sannan ya nemi ya gama masa gabaki daya abinda ya sani a game da Ruqayyah, shi kuma ya gaya masa iyakacin abinda ya sani " tabbas naga sunyi hatsari, kuma naga mutuwa na kuma ga haihuwa a wajen da akayi hatsarin, amma ban tabbatar waye ya mutu waye kuma ya haihu ba, batan Amina da kuma kasancewar Ruqayyah ita ce mutum na karshe da ya ganta shi yasa na tabbatar da abinda na gani farkon zuwanta shine ya tabbata. Ta zabi kasancewa mai kudi maimakon zama a karkashin masu kudi, abinda ni kaina tun sanda na gani din ban san me hakan yake nufi ba."
Lukman yace "amma kuma ka bata tsoro da cewa zaka tona mata asiri? Kace zaka fadi inda ta ajiye yaron?" Mai duba yace "tsoro ne kawai na bata amma nima ban sani ba, ba komai nake gani ba sai abinda Allah ya nufe ni da gani" Lukman yace "yanzu dai baka san inda yaro yake ba" mai duba yace "ban sani ba, nasan dai yana raye tunda a mutuwar da na gani banga tasa ba" Lukman yayi shiru yana tunani sannan yace "shikenan, ba zan rufe ka ba kamar yadda na fada a baya, kuma zan cigaba da baka rabin wanda Ruqayyah take ba ka, amma ina son wani abu daga gare ka" malamin duba yaji dadi, yace "menene? Me kake so?" Yace "ina so kayi min aiki akan ta, wannan taurin kan nata ka sauko min dashi. Kasa take amincewa da duk abinda na gaya mata ba tare da musu ko jayayya ba ko bin kwakwkwafi ba".
Wannan, hadi da magungunan da ake bunkawa Ruqayyah a asibiti kullum shi yasa ko wacce takarda Lukman ya kai mata take saka hannu akai ba tare da lissafi ko tunanin komai ba duk kuwa da cewa ita a zuciyarta bata yarda dashi ba. Shi kuma sai yayi rashe rashe akan dukiyar da take hannun Ruqayyah, dukiyar da ita kanta ba tata bace ballantana shi. Yayi ta bunkawa cikin sa haram yana tunanin yaci bati, ya manta cewa wasu Allah ya kan basu dama ne su tuba tun a duniya wasu kuma ya kan dauke ransu lokaci daya sanda kuma suke tsaka da cin duniyar su da tsinke.
A lokacin da Ruqayyah tayi shekara biyu a rufe ne Adam da Fatima suka kammala karatun su na masters, a lokacin ne kuma mai martaba sarki ya bukaci Adam daya dawo gida a nema masa aiki kuma yayi settling down amma jin Fatimah bata da niyya dawowa Nigeria sai yace shima bai gama karatun da zai dora da PhD ne. Itama sai ta biye masa dan itama deep cikin