Showing 111001 words to 114000 words out of 300844 words
zo ya dauke ta su koma gida, sai kuma ta gaya wa Hassan tace Baba yace yazo ya dauke ta su tafi. Shi bai san me ta shirya ba yayi ta murna ya gaya wa Aunty, ita kuma ta saka aka gyarawa Ruqayyah part dinta duk dan ta faranta mata. Ita kuma Ruqayyah ta dawo da niyyar in Fatima ta taba mata ya'ya ta gurza mata amma sai ta tarar Fatiman ma bata kasar gaba ki daya. Wannan ya kona mata rai, ita gani take yi wannan tafiye tafiyen kamar dan a kona mata rai ake yin su. Farkon dawowarta tare da Sumayya suka dawo, Sumayyan ce kuma tayi mata register da online catering classes da yawa inda take koyon girke girke da sauran kitchen tips kuma suna gwadawa tare a kitchen dinta, sannan suka koyi yadda ake amfani da kitchen appliances din da suke kitchen din nata. Anan ne Sumayya ta gwada tambayar ta ko tana da niyyar komawa karatu? Tayi dariya Tace "karatu kuma? Ni dama tun farko ai kin san ina karatu ne saboda in yi kudi, yanzu already ina da kudin da ko aikin nake yi ba lallai in samu albashin da zai bani wannan rayuwar ba so why should I bother myself?" Sumayya tace "shi karatu fa ai ba dan ayi aiki ko dan ayi kudi ake yinsa ba ko? Nima da nake karatun ba lallai ne inyi aiki ba musamman in na samu mijin da baya son matarsa tayi aiki ai kinga dole in hakura ko ? Tunda dai ai auren yafi aikin" Ruqayyah tace "say what you may, ni dai ba wata school da zan koma".
A haka rayuwa ta cigaba da tafiya, bakar zuciyar Ruqayyah tana nan a kirjinta amma har yanzu dafinta bai bayyana ga Hassan ba. A haka akayi bikin Minal da alhajin ta lokacin su Yusuf suna da watanni uku a duniya. Ruqayyah tana tsananin son yayanta a zuciyarta amma being the Ruqayyah that she is, bata iya nuna soyayya ba dan haka sai ya zamanto yaran sunfi sabawa da Abban su, sai uncle dinsu wanda in dai yana gari to kullum suna tare har ya iya hada musu madara yayi feeding dinsu. Daga nan sai Aunty wadda dama daga sun dami Ruqayyah zata hada su da mai renon su su tafi gidan aunty, ita kuma ta dauki wayarta ta cigaba da daukan darasin mallakar miji.
A lokacin bikin Minal ne kuma Minal din da kawayenta suka zo gidan Ruqayyah da niyyar zasuyi bridal shower dinsu anan. Sai dai suk ayi rashin Sa'a suka tarar Hassan yana gida kuma Ruqayyah bata gaya masa za'a yi event din ba. Ya shigo yana kallon su, yana lura da yanayin shigarsu da kuma yadda babu wadda ta gaishe shi a cikin su. Sai ya sunkuya ya dauki yaransa y ahau sama da su, Ruqayyah ta bishi a baya.
Tana shiga dakin sa taga ya ajiye yaran akan gado yana musu wasa suna bangala masa dariya, ta tsaya a bakin kofa tana murmushi, bai kulata ba tace "dama bikin Minal dana gaya maka an fara, shine kawayen mu suka zo zasu dan yanka cake su kuma yi hotunan" ya juyo yana kallonta yace "kawayen ku? I thought you said kawayen Sumayya ne da na Minal? Ina ita Sumayyan take? Ko bata zo ba sai kawayenta?" Ruqayyah ta dauke kai gefe tana juya ido yadda ba zai ganta ba sannan ta karasa shiga dakin, ta dora kanta a bayansa tace "to yanzu menene dan nace musu kawayena? Ina laifin wanda ya kula ka? Ka manta su suka tsaya min da bikin mu?" Ya juyo yana kallonta yace "ina fa zan manta? Har duk rashin kunyar da suka yi min ina sane da kowacce kalma. I thought daga ranar ba zaki kara kula su ba saboda marar tarbiyya ne kadai zai riki wadannan a matsayin kawaye, baki san masu magana sunce 'nuna min abokin ka Ni kuma in gaya maka halayen ka ba?" Ta daga shi tana jin ranta yana fara baci tace "ni banga abin daga hankali a wannan maganar ba, ko ma menene sukayi ko suka ce ai ya wuce ko? Idan da kai wani ne yanzu da ba sai dai inji kace ka dauki nauyin duk abinda za'a yi a gidan ba, ko kuma inga ka fita ka siyo mana duk abubuwan da muke bukata ba? At least haka akeyi a gidajen arziki, at least da Hussain ne da hakan zai yi ba wai ya zauna yana mitar abinda akayi shekara guda data wuce ba"
Wannan littafin na siyarwa ne, idan kin ganshi a wani gurin na sata ne, in kuna son ki sayi halaliyar ki ki neme ni ta wannan number din through WhatsApp 07067081020
*Unveiled 2*
Farko daskarewa yayi a zaunen da yake, sai kuma yayi blinking idonsa dan ya tabbatar cewa ba wai mafarki yake yi ba, sai kuma ya saka hannu yana bubbuga kunnuwansa ko sune suke yi masa karya sannan ya juyo yana kallonta, bakinsa da idonsa a bude amma kalma daya ta kasa fita daga bakin nasa, so yake ya tabbatar ita ta fadi wadannan maganganun, har da waigawa yayi dan ya tabbatar su kadai ne a dakin ba wata ce ta shigo ta fada ba, sai dai yana yin daya gani a fuskarta kadai ya isa ya tabbatar masa da cewa ita ta fada din. Rashin gaskiya kiri kiri a rubuce a fuskarta. Ta tosa kanta da sauri tana nin gabaki daya jikinta ya dauki kaikayi, sai kuma ta juya da sauri zata bar dakin. Tana son ta kasance ita kadai tayi bitar abinda tace din ta kuma shirya abinda zata ce ta rufe maganar tata.
Charaf ya rike hannunta,bata juyo ba sai idonta data rufe, ya mike daga kan gadon ya zagayo gabanta sannan ya saka cika hannun nata ya rike fuskar ta da hannayensa biyu. "Hassana?" Ta kwace fuskarta ta na kokarin juya masa baya ya sake rike ta, jikinsa har rawa yake yi "Hassana me kika ce min? Me kike cewa? Wacce magana kike gayamin Hassana? Are You okay?" A ransa ya fara tunanin anya ba aljanu suka taba Precious wife dinsa ba?
Bata ce komai ba still, yace "gidan arziki Ruqayyah gaya min me kike nufi da gidan arziki? Hussain? Da ace ni Hussain ne? Me kike nufi da haka?" Tsabar zafin da maganar tayi masa ya hana ya nuna bacin ransa sai ma karyewa da zuciyarsa tayi. So yake tayi magana, so yake ta gaya masa bata fada masa wadannan maganganun ba kawai imagination dinsa ne.
Ta bude idonta ta sauke su a kansa "kayi hakuri mijina ban fada da niyyar in bata maka rai ba, kawai dai ji nayi nawa ran ya baci kuma ban san na fada maka haka ba" ya sake ta, ta fada din kenan, bawai kunnensa ne bai ji masa dai dai ba wai imagination dinsa bane ba Hassana ce tace gidansa ba gidan arziki bane ba, da Hussain ne zaiyi abinda shi ba zaiyi ba.
Tana jin ya sake ta ta juya da sauri ta fita tare da rufe kofar, da ace da key a hannunta ma da rufe shi zata yi ta waje dan ita kan ta tsorata da fuskarsa da kuma rikon da yayi mata. Amma wannan bai hana ta shiga dakin ta ta dauko kudi ta fito gurin kawayenta suka cigaba da hidimar su ba. Sai da suka gama sannan ta fito da kudin ta basu tace inji Hassan yace suyi kudin mota. Minal tace "shi wannan mijin naki wallahi da kayan haushi yake, maimakon ma yace ga driver nan a waje a kai kowa gidansu sai ya wani bamu kudi?" Daya a cikin kawayen ta karbe kudin tana lissafawa tace "mu dai muna so, ke dan kin samu zaki shiga daga ciki shine har zaki yi yanga in an baki kudi?" Suka raba kayansu kowa ta saka a jakarta. Ruqayyah tabi jakankunan su da kallo tana hadiye daci a ranta, ta jima tana tara kudin nan tana son siyan wata sarka.
Da zasu tafi Minal ta jata kefe "to sai kin shigo dinner gobe" Ruqayyah tayi ajjiyar zuciya "dinner nan Minal ba lallai bane in shigo ta" Minal ta bude ido "amma kuwa da kin cika babbar marar m...dinner din bikin nawa zaki ki zuwa" Ruqayyah tace "ba cewa nayi ba zan zo ba, cewa nayi ba lallai bane inzo din, kin san ai komai sai Allah yayi ko? Ku tafi kawai, zamu yi waya zan baki labarin abinda yasa nace haka" Minal ta bata rai "ko ma menene ni ba uzuri bane ba a gurina, kuma in baki zo dinner ba wallahi nasan matsayina a gurin ki kuma na san kema a gurin da zan a jiye ki a zuciyata" Ruqayyah dai ta lallabata ta raka ta waje suka shiga motar da alhajin ta ya aiko ta dauke su.
Ta gefen idonta ta hango Adam yana fitowa daga part din Hussain yana tafiya hanyar shiga part din Aunty, a can yaje tare da sauran yaran Hussain a tsofaffin dakunan su Hassan. Ya saka hannunsa a aljihu yana taku dai dai jikinsa sanye da kaya masu kyau, in ka ganshi zaka iya tunanin kanin mai gidan ne dan yarintar sa ce kawai zata sa ba zaka ce shine mai gidan ba. Tayi tsaki, ta tsane shi har cikin zuciyarta, ya tsani guts dinsa, yadda yake tafiya da yadda yake magana da komai nasa. More importantly ta tsani alakar sa da only sister dinta. God knows tana son Sumayya har cikin ranta kuma zata yi iyakacin kokarin ta ta ga cewa alakar Sumayya da wannan tubabben bata cigaba ba, bata je inda su suke son taje dinba. She can't imagine having nephews and nieces masu Christian blood a jikin su, masu kama da kedarai. Ta kara tsaki tana juyawa cikin gidan ta, dole zata nemi hanyar raba wannan alakar duk da tasan ba zata samu goyon baya daga Sumayyan ba ko Baba ko Inna but duk da haka she will find a way, zata yi shawara da zuciyarta kuma tadan zata samu mafita kamar yadda kullum zuciyar tata take bata mafita a duk problems dinta. Yanzu ma already ta bata mafita akan problem dinta da Hassan.
A palo ta fara tsayawa tana bawa yaran ta directives na yadda zasu gyara gidan, sannan tayi musu sallama ta hau sama. Dakin ta ta shiga ta fara yin wanka ta shirya cikin kayan bacci masu daukan hankali ta dauko ajjiyoyin kayan matan ta ta sha na sha ta shafa na shafawa. Tunda suka yi aure bai taba resisting dinta ba kuma bata jin zai fara daga yau.
Tunda Ruqayyah ta juya ta fita Hassan ya zame ya zauna a bakin gado ya dafe kansa da hannayensa biyu. "What just happened? What happened to his perfect precious wife? Did she just said what she said ko kuma zuciyarsa ce take playing tricks on him? Ta tabbas there must be an explanation to her behavior ko dai yayi mata wani laifi ne mai girma da out of anger ta fada masa haka? Amma shi duk a tunaninsa bai tuno wani abu da yayi mata marar dadi ba.
Ya tuna a yanayin da ta gaya masa maganar, babu wani emotions irin kamar normal mutum yana magana ne directly from her heart, daga dukkan alamu itama bata san ta fada ba sai bayan data fada din. Zuciyarsa tana ta kokarin kawo masa wani excuse da zai kare ta amma kwakwalwar sa taki karbar excuse din, sai ma wadansu maganganu da suke fado masa a rai.
Farko maganar Baba "zan so ka janye auren Hassana ka auri Hussaina a madadin ta"
Hussain "in har zata iya yaudarar top criminals ta haka mudu rami su fada ciki why not you?"
Sumayya "kayi ta hakuri, kana addu'a kuma kana saka ido".
Ya mike yana jiyo karar kidan da suka kunna a kasa, Yusuf ya fara kuka, ya dauke shi yana rarrashinsa, Aminu ya saka kuka shima yana miko masa hannu, ya durkusa shima ya dauke shi yana zagaya wa dasu a hannunsa yana raba idonsa a tsakanin fuskokin su. Sai ya samu kansa da tambayar kansa
"Did he make the worse choice for the most important thing?"
"Did he chose a bad wife for himself and a bad mother for his children?"
Where was his carefulness?
Ya shiga da yaran toilet dinsa ya saka su a wash hand basin ya wanke musu jikin su da ruwan dimi, suna ta wasa suma jika shi, ya fito da su ya kashe acn dakin ya goge musu jiki sannan yaje dakinta ya samo musu kaya yazo ya saka musu, ya koma ya dauki madara ya hada musu ya basu, a take suka yi bacci ya kwantar dasu yana kallon su sannan shima ya kwanta a tsakiyar su tare da rufe idonsa, amma bacci shine abu na karshe a zuciyarsa.
"At least haka akeyi a gidan arziki, da Hussain ne da haka zaiyi va wai ya zauna yana complain akan abinda akayi shekara guda data wuce ba"
Ya girgiza kansa yana son ya cire maganar ta daga cikin kansa amma ya kasa. A haka yaji ta bude kofar dakin ta shigo ta tsaya tana kallon su
Ta dan jima a tsaye tana assessing din sa shi da yayansa, yaran bacci suke yi amma shi tana kallonsa ta san idonsa biyu rufe idon kawai yayi. Ta karasa tare da dauke Yusuf ta mayar dashi kusa da dan uwansa sannan ta zauna a inda ta dauke shin tana dora hannunta akan goshin Hassan. Ya bude ido yana kallon ta, tayi masa murmushi "dama nasan ba kayi bacci ba shine ka wani rufe ido ko?" Bai ce mata komai ba amma ta hango wani bakon al'amari a cikin idon nasa, tace "wai fushi kake yi dani mijina? Kayi hakuri mana dan Allah ai kasan dai babu wani wanda yake baya kuskure a rayuwa ko? Nayi kuskure, raina ne naji ya baci a lokacin ka yafe min kaji mijina?" Sai taga yayi dan murmushi, a take taji hankalin ta ya kwanta, dama ta san babu inda fushin nasa zai je in dai har ta bayar da hakuri musamman kuma ace da wannan shigar a jikinta tana kuma wannan kamshin ai magana ta riga ta wuce. Sai taji yace "ranki ne ya baci ko? Kinsan wani abu. A lokacin da ran mutum ya baci a lokacin ne yake fadar duk abinda yake cikin zuciyarsa, so chances are very high cewa abinda yake zuciyarki shi kika fada min" ya fada idanuwan sa cikin nata.
Ta fara jujjuya hannunta tana kokarin controlling anger dinta tace "don't be like that mana, haba mijina, ya kamata kayi min uzuri mana. Nima fa ina da zuciya a kirjina, kuma zuciyata tana son irin rayuwar su Hussain da matarsa yadda suke wadaka da dukiya suna zuwa duk ƙasar da suka ga dama a lokacin da suka yi niyya. What do you expect your wife to do? How do you expect me to feel bayan ka kawo ni ina zaune da kanin ka da yake da everything while you have nothing?"
Ya mike zaune yana kankance idonsa a kanta, "do you just said "nothing"? Do you mean I have nothing?" Ta juya idonta, yau me yake faruwa ne da ita? Me yasa bata da sa'ar magana ne? Daga dukkan alamu yau da hannun hagu ta tashi daga bacci.
Tace "ah ah. Me kake so ne ince mijina? Ina nufin kamfani nasa ne, gidan nan da muke ciki nasa ne, motar da kake hawa tasa ce, motar da nakr hawa shi ya siya. Komai da muke takama dashi a rayuwa nasa ne" ya ture hannunta daga jikin da ya mike tsaye, idanunsa sunyi ja jijiyoyin kansa sun fito, ya bude bakinsa zaiyi magana amma voice din ya kasa fitowa saboda ciwon da zuciyarsa take masa, da kyar yace "I understand. I now understand everything. Ni da ke Hassana yanayin yadda muke kallon rayuwa ba iri daya bane ba. Rayuwa ni a gurina ba wai tana revolving around yawan kudin da kake dashi bane ba, tana revolving ne around things that are much more important than money, like love, honor, friendship. But you have no idea me wadannan suke nufi do you? Yes, Hussain yana da kudi, but that doesn't mean ni bani da komai. Yes, gidan sa ne wannan shi ya gina da kudin sa but that doesn't mean ni bazan iya gina nawa ba. Na karba na zauna a ciki ne dan in faranta masa tunda burinsa shine mu zauna tare mu da iyalin mu, saboda yana so na, nima kuma na karba saboda ina son sa. Na fasa gina mana namu gidan ne saboda in siya wa Baba gida, saboda naga yafi mu bukata, saboda ina ganin sa kamar family na ne shima"
"Ruqayyah bayan rai da lafiya da imani da Allah ya bani sai ya bani family, Aunty da siblings dina, masu sona sosai yadda na tabbatar ko da bani da komai zasu kula dani, ko d abana duniya zasu kula da bayana. Sannan ina da aikin yi ba zaman banza nake yi ba, wahalar da nake yi a aikin nan shi kansa Hussain yasan cewa ko shi baya yiwa kamfanin nan wahalar da nake yi masa. Ke kinfi kowa sanin cewa albashi na can more than sustain me, you and ko yaya nawa zamu haifa. And I have these...." Ya fada yana nuna babies din da suke bacci abin su "I have abinda babu wanda ya isa ya samar wa kansa sai Allah ya bashi. Do you know that last week Fatima ta matsawa Hussain sun fara zuwa ganin fertility doctor? Suna nema but mu Allah ya bamu gida biyu" ya tsaya yana kallon ta da jajayen idanuwan sa yace "I tot I also have a pious wife. Ashe I was wrong" ya bude toilet ya shige ya rufo kofa. He just can't stand the sight of her.
Ta mike tsaye tana kallon kofar toilet din, tunda taaure shi tasan baya son nonsense shi yasa kullum in suna magana take jinta kamar mai tafiya akan tight rope kamar slight mistake in tayi zata fada ramin da ba zata