Showing 171001 words to 174000 words out of 300844 words

Chapter 58 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2086

mana wani abu daga cikin dukiyar sa da muma mu kafa kanmu amma kaki bani hadin kai, saying wai kafi son sa akan kowa".

Hassan ya tuna da maganganun da Ruqayyah tayi ta gaya masa akan Hussain, akan Fatima, wato duk karya ce kenan, duk da ta hada su ne, wato duk dan taci dukiyar Hussain ne. Ya tuno maganar Baba, ya tuno maganar Hussain kamar yanzu yake gaya masa "me yasa bata je ta kira iyayenta sun taimaka maka ba sai ta zabi ta kama katanga ta haura?" Sai yau Hassan ya samu amsar sa.. yace "bayan wannan kuma sai me kika yi?" Tayi shiru tana kallonsa, yace "kina da hannu a gurin batan Adam?" Ta juya hannu "what does it matter? Sai me? Ni ba zan bari yaruwata ta auri wannan inyamurin drivern ba" yace "ke kika aikawa iyayensa suka zo suka tafi dashi" ta juya idonta, me za'a yi mata in an sani? Karkarinta Sumayya tayi fushi na wani lokaci da zarar kudi sun zauna kamar yadda take saka rai shikenan komai zai dawo normal tsakanin su tace "eh ni na aika musu, me za'a yi min?" Yace "you are not human being Ruqayyah ke shaidaniya ce. A devil in human form".

Sai kuma wani tunani yazo masa, tunanin da ya sa ya mike straight yana mantawa da ciwon da yake ji a zuciyarsa ya karasa gabanta tare da rike hannunta yace "what else did you do saboda kudin Hussain? Me kika yi? Did you cause the accident? Did you kill Fatima and her baby saboda kici gadon su?" Tayi kokarin kwace hannunta amma karfin rikon da yayi mata yasa ta kasa kwacewa, cikin wata irin budaddiyar murya yace "answer me!" Saboda karfin muryar da yayi mata magana da ita sai da taji dakin ya motsa, ta kalle shi taga yana yi mata wani irin kallo mai nuni da cewa zai iya yi mata komai, ta kalli cikin idonsa tace "wallahi, tallahi, billahillazi la ilaha illa huwa ban kashe Fatima ba ballantana abinda yake cikinta, kuma bani nayi sanadiyyar accident din mu ba" a idonta yaga cewa gaskiya take fada masa sai ya saketa, ta matsa baya tana murza hannunta inda ya rike din, ya juya hannunsa dafe da kirjinsa zai bar dakin sai tace "ina sake tuna maka, kar ka bayar dako kwandala a kudin nan" ya juyo yana kallonta da juyayyun idanuwa yace "are you threatening me?" Direct Tace "yes" ya juyo a kufule yace "me zaki yi? Idan na rabarda dukiyar mezaki iya yi akai? And after duk abinda kika gaya min kina tunanin zanyi abinda kike so?" Tace "ba zaka yi ba amma ni zan saka ka kayi. Ba dai Hussain ba? Ba dai dan kana son Hussain ne kace zaka rabar da dukiyar sa ba? To albishirinka, in dai kayi haka ni kuma sai na tabbatar nayi destroying duk wani kykykyawan fenti da Hussain ya shafa wa kansa sanda yana da rai, I will make sure mutanen da suke sonsa suke kuma yi masa addu'a sun dawo suna kinsa suna kuma tsine masa" yaji tamkar ta saka mashi ta chaki zuciyarsa, yace "and ta yaya zaki yi hakan?" Sai ta koma bakin gado ta dauki Hussain da yake kwance tace "zan je gidajen rediyo in fadi cewa wannan yaron dansa ne ba naka bane ba, in ce raping dina yayi har na haife shi. Nasan wasu ba zasu yarda ba amma da yawa zasu yarda saboda mutane sunfi yarda da labarin karya aka na gaskiya. Zan ce kudinsa na cult ne, ta yaya Mutun mai kananan shekaru kamar sa zai tara kudade irin wadannan? Zan fada cewa baban ku ya fara bayarwa, shine silar yin kudinsa, zan kuma ce sanadiyyar mutuwar sa shine matarsa aka ce ya bayar tare da abinda yake cikinta, shi kuma yaki bayarwa shine suka sanye jininsa a gabanka tare da drivern ku shi yasa drivern ya bata har yau ba'a ganshi ba, sannan kuma suka yi causing accident dinda matar da mutu da tsohon ciki dan su dauki fansar kin bin maganar su da yayi. Am sure wasu ba zasu yarda ba amma wasu zasu yarda. Kuma am sure su kansu wadanda basu yarda ba dinzan saka musu doubt a kan sa. Zan kuma ce wannan dalilin ne yasa ka rabar da dukiyarsa saboda kace ba zaka iya cin dukiyar haram ba........."

Wata shakada yayi mata tare da bugata da bango ce tasa sauran maganar ta tsaya a makogwaronta, idanuwan ta a waje, ta saka hannunta duk biyun tana kokarin raba hannunsa da wuyanta amma ta kasa, a take ta fara jin kamshin mutuwa, ta fara fitar da rai da rayuwa, lallai tayi playing too bad dan wannan rikon da yayi mata bata jin zai sake ta har sai numfashin ta ya bar jikinta. Ya fara magana da karfi kamar zai tsaga dakin "why??! Why?! A kan kudi? Akan kudin da baki san ta yadda yayi ya tara su ba? Akan sa zaki yi ikirarin yi masa wannan mugun sharrin? Saboda duniya? Saboda kina so ki samu duniya, Allah wadaran ki Ruqayyah. Allah wadaran haduwata dake Ruqayyah. Kaico na, ina ma dai na mutu a ranar dana hadu dake da ban kawo wa family na jaraba ba. Allah wadaran aure na dake Hassana"

Kafafunsa yaji an kama ana jan wandonsa, ya sunkuyar da idonsa da yake cike da hawaye zuwa kasa yana kallon yan biyun sa da suka rike kafafuwan sa suna kuka, bai ji shigowar su ba bai kuma ji kukan su ba kawai taba shin da suka yi ne ya dawo da hankalin sa kansu. "daddy don hut mommy" yusuf ya fada yana matso hawaye, Aminu yaje ya kama rigar Ruqayyah data kusan suma saboda azaba yace "mommy mommy".

Hassan ya cikata da sauri yana ja da baya yana girgiza kai, ta durkushe a gurin tana jan numfashi da kyar hawayen azaba yana zubowa daga idonta. Yaran suka tafi da gudu suka fada jikinta suna kuka ita kuma ta rungume su tana kallon Hassan. A hankali yace "Baba da Inna sunyi asarar haihuwa"

Sai ya juya ba tare da ya sake cewa komai ba yabar gidan, ya shiga mota ya dauki hanyar gidan su Ruqayyah a hanya yana iya kacin kokarin sa dan ganin bai concentrating akan maganganun ta ba har yaje kofa gidan yayi packing, yana fitowa Baba yana tsayawa a cikin Napep dinsa, amma ganin yanayin Hassan kadai ya saka hankalin sa ya tashi ya kira Sulaiman da sauri suka kama Hassan din da kyar yake iya taka kafarsa suka shigar dashi cikin gida suka ajiye shi a palo suna ta tambayar shi "lafiya Hassan? Wani abu ne ya faru? Wani ne ya kuma mutuwa? Ko Ruqayyah ce?" Hassan ya dago kai yana kallon Baba yace "Ruqayyah ce Baba, amma ba mutuwa tayi ba, mashi ta dauko ta soke zuciyata da shi" Baba ya dafe kansa, tabbas ranar da yake gudu kuma har ya fara tunanin ba zata zo ba tabbas tazo yau. Ruqayyah tayi aika aika, kuma daga yanayin Hassan yasan abinda tayi yafi abinda yake tunanin zata yi din. Ya wuce duk lissafin sa.

Ya dago kai yana kallon Hassan, yana kara ganin rashin dacewar Hassan da Ruqayyah sai yace "Hassan zan roke ka wata alfarma duk kuwa da bansan abinda Ruqayyah tayi maka ba" Hassan ya fara girgiza kai tun kafin yaji alfarmar dan ba zai iya yafewa Ruqayyah na, amma sai yaji baba yace "Sulaiman dauko min takarda da biro" Sulaiman yaje ya kawo sai Baba ya mika wa Hassan yace "dan Allah Hassan, dan Annabi, ina rokon ka ka saki Ruqayyah" Hassan ya kalli Baba sai yaga cewa har cikin zuciyarsa hakan yake nufi, ya dauki biron ya dora akan takardar, lallai yasan Baba ya gaya masa haka ne dan ya cire masa nauyin sa kar yaga mutumcin su ya kasa sakin Ruqayyah shi yasa ya zamanto shine ma ya roke shi, sai yayi rubutu kamar haka...


*The Fifth Wave*

"Ni Hassan Aminu Abdullahi na saki matata Ruqayyah Yusuf saki uku"

Ya ajiye biron, amma sai ya kasa mikawa Baba takardar duk da yasan baban ba iya karatu yayi ba balle ya karanta abinda ya rubuta, sai dai a ransa da ace ana iya yin saki goma da kuwa tabbas shi zaiyi wa Ruqayyah. Dan babu abinda yake nadama a yanzu irin aurenta, babu abinda yake dana sanin yi irin hada zuri'a da ita, babu kuma abinda yake tausayi irin yayan da suke a tsakanin su.

Tunda ya fito daga gidan Hussain yake tambayar kansa dalilin da yasa haka ta faru dashi, ina carefulness dinsa ya tafi lokacin da ya zabi Ruqayyah a matsayin matar aure, ina smartness dinsa da dabarar sa da hangen nesan sa suka tafi, me yasa yayi failing akan abinda yafi komai muhimmanci a rayuwarsa? Ya ninke takardar a hankali ya ajiye a tsakiyar su shida Baba, ya kasa mikawa baban, sai Baba ya saka hannu ya dauka ya warware yana kallonta duk da cewa ba gane rubutun yake yi ba, dai kuma ya mikawa Sulaiman yace "karanta muji" sai Sulaiman ya karanta a fili, Hassan ya sunkuyar da kansa yana jin nauyin Baba amma ko kadan baya jin wani abu mai kama da regret na saki ukun da ya yiwa Ruqayyah.

Inna Ade ta fara kuka, Baba ya dago kai yace "ina rokon ka ka gaya min abinda tayi maka, saboda ina son insan muma iyayenta abinda ya kamata muyi mata" Hassan yana girgiza kansa yace "zuciyar ku ba zata iya dauka ba Baba, nima tawa zuciyar yanzu kuka take yi, Ruqayyah ta riga tayi mata mikin da ba zai taba goguwa ba" Baba yace "tunda har kana numfashi hakan yana nufin zuciyarka ta dauka, kai da ba dolen ta ba ballantana mu da muka haife ta, mu da ba zamu taba iya chanjata ba, ka gaya mana dan Allah dan musam ta yadda zamu taimaka mata".

Sai Hassan ya basu labari, labarin duk abinda Ruqayyah ta gaya msa da bakinta cewa tayi he told them everything har labarin abinda tayi wa Adam da kuma zargin da yake na cewa abinda tayi shine sanadiyyar batan Adam din. But duk wannan ba shine dalilin da ya saka ya sake ta ba, dalilin da ya saka ya sake ta shine abinda tace zata yi, sharrin da tayi ikirarin zata yi wa brother dinsa duk kuwa da cewa yana cikin kabarinsa a kwance, zata bata masa suna ta kuma bata nasabar dan ta data haifa da kanta duk dan saboda kudi. Yana tsoron cewa babu abinda ba zata iya yi ba saboda kudi.

Inna ta kasa juye labarin sai ta tashi ta shiga daki tana kuka, Sumayya da take tsaye a kofar dakinta tun shigowar su tana jin abinda suke cewa ta juya ta koma daki ta turo kofa, sai ta zauna akan gado blindly tana kallon bango sannan sai ta dauko wayarta ta nemo number din Ruqayyah ta saka ta a blacklist sannan ta goge ta daga cikin wayar ta, sai kuma ta ajiye wayar ta kwanta tana tunanin hanyarda zata bi ta tafi imo...

A palo Baba da Sulaiman suna zaune har Hassan ya gama basu labarin duk abinda Ruqayyah tayi. Da kyar yake magana amma bai yi shiru ba sai da ya kai aya sannan yace "kayi hakuri Baba, zaman da nayi ma da Ruqayyah a baya da ace zan iya dawo da hannun agogo baya da banyi shi ba har na hada zuri'a da ita ba, da ace zan mayar da rayuwata baya da nabi zabi irin na Hussain, na zabi mace kamar Fatima ba kamar Hassana ba, na zabi wayayyiya mai zurfin ilimin boko yar gidan masu kudi mai budadden ido irin Fatima ba irin Ruqayyah ba, wata kila da nayi haka da yanzu ban samu kaina a halin da nake ciki yanzu ba" Baba ya girgiza kansa yace "tabbas kayi kuskure a gurin zaben matar aure, amma ba wannan ne kuskuren ka ba. Arzikin mutum, zurfin ilimin bokon sa, yanayin al'ummar daya taso a cikin ta, shekarunsa ko kuma wayewar sa basu suke nuna halayyar sa ba. Ita halayyar mutum da ita ake haifar sa, su duk wadannan abubuwan dana lissafa suna taimakawa ne gurin kara wa ko rage karfin halayyar mutum. Ana samun nagari a cikin kowanne kaso na al'umma kamar yadda ake samun bata gari a cikin kowanne kaso da al'umma. Ana samun shaidanin mutum a cikin malamai kamar yadda ake iya samun salihin mutum a cikin shaidanu. Dan mun kasance malamai hakan baya nufin cewa yayan da zamu haifa lallai zasu kasance na gari ba, mu dai iyakacin mu mu bada ilimi mu bada tarbiyya amma ita shiriya ta Allah ce, Allah ne kadai zai iya shiryar da bawansa a lokacin da yaso. Kamar kuma yadda na gaya maka cewa yana yin guri da yanayin al'ummar da mutum ya samu kansa a ciki yana karawa ko rage halayyar mutum, wannan shine abinda ya faru da Hassana. Tun farko Hassana halinta ba mai kyau bane ba, ni da mahaifiyar ta mun sani kuma kamar yadda mahaifiyar ta take yawan fada ita Hassana kamar harabawa ce ubangiji yayi mana dn yaga yadda zamu yi da ita, kuma munyi iyakacin kokarin mu, a inda muka yi kuskure shine da muka biye mata muka hada auren ku kai da ita, komawar ta cikin ku da shiga irin rayuwar ku da bude idon da t kara yi da duniya shi ya kara lalata mata halayyar ta, shi yasa har ta zama abinda ta zama. Wata kila da mun barta a gabanmu, ko kuma mun samu wani mijin wanda ba irin ka ba, mai rufin asiri dai dai gwargwado mun aura masa ita da ba zata ga dukiya irin taku ba har ta saka a ranta sai ta mallake ta. Wannan shine abinda naso in nunawa mahaifiyar ta a lokacin da kake neman aurenta, amm ita kuma sai tayi tunanin idan bamu bawa Ruqayyah abinda take so ba shine zata kara lalacewa. Wannan shine kuskuren mu, wannan shine inda muka fadi jarabawar mu. Amma hakan ba wai yana nufin shikenan mun hakura ba, zamu cigaba da kokarin ganin mun gyara kuskuren mu, abinda zamuyi kuma a yanzu shine zamu barta da duniya, zamu barta ota da kanta ta gane cewa abinda take yi ba dai dai bane ba muyi fatan kuma komai ba jima komai ba daɗe zata yi nadama za kuma ta nemi yafiyar wadanda ta zalunta. Ta haka ne kadai zata samu rahamar ubangiji. Ni ba zance kayi wa Hassana komai ko ince kar kayi mata komai ba, in ka ga dama zaka iya hada ta yan sanda kace ga ikirarin da tayi na cewa zata yiwa dan uwanka kazafi akan dukiyar sa, in kafa dama zaka iya duba ya'yan da suke tsakanin ku ka barta da duniya kamar yadda muma zamu barta din. Duk zabin ka ne."

"Ina so ka sani, a yanzu ima tsananin jin kunyarka saboda abinda yata ta cikina tayi maka duk kuwa da irin kyautatawar ka a garemu. Sannan kuma ina so in tabbatar maka da cewa Ruqayyah ta aikata abinda ta aikata ne kawai saboda halin ta ne haka. Bawai saboda ta fito daga gidan talakawa ba. Ina rokon ka idan ka amince ina son ka auri SUMAYYA a madadin Ruqayyah. A lokacin ne zaka gane abinda na fada maka ranar nan, a lokacin ne kuma zaka gane abinda nake gaya maka yau"

Hassan ya bude ido yana kallon Baba da mamaki yace "Sumayya kuma Baba? Sumayya ai ƴar uwar Ruqayyah ce ciki daya ta yaya zan iya aurenta bayan ita Ruqayyan tana da rai?" Baba yayi murmushi yace "ni dai iya kacin sani na babu wata aya ko wani hadisi daya haramta aure a tsakanin ku a irin wannan yanayin. Abinda aka haramta shine hada yan uwa a aure su a lokaci daya, sai dai alkunya tana sakawa sau da yawa a ki yin irin wannan auren dan shi musulunci addinin zaman lafiya ne, amma mu a yanzu babu wata alkunya wadda zamuyi wa Hassana. Na baka auren husaina"

Hassan ya cigaba da girgiza kansa, abubuwan sunyi masa yawa, zuciyarsa ba zata iya dauka ba, kansa ya toshe a yanzu ba zai iya yin tunanin komai ba. Sai Baba yace "na sani, na san yanzu ba zaka iya bani amsa ba kuma nima bana son ka bani amsar a yanzun, kaje kayi tunani, ka nemi zabin Allah kayi addu'a, na baka daga nan har zuwa shekarar da Sumayya zata gama karatun ta na jami'a, idan har zuwa lokacin ba kaji zaka iya auren ta ba shikenan, idan kuma kaji zaka iya to alkawarin da nayi maka yana nan na baka ita ko bayan raina". Still Hassan bai ce komai ba.

Sai Baba ya aika Sulaiman ya kira Inna, ta zauna a kusa dashi idanuwan ta da alamar kuka sai yace "ki zama shaida, ko bayan raina in Hassan yazo neman auren husaina na bashi ita." Ta gyada kai tace "Allah yasa haka shi yafi musu alkhairi" sai kuma ya mika mata takardar sakin Ruqayyah yace "ga wannan ku tafi tare da Sulaiman gurin Hassana ki kai mata, sannan ki gaya mata in ji ni ni ubanta Malam Yusuf mai gadi nace ta baro gidan nan a yanzu ta taho gidana, kuma ban amince ta dauko koda tsinke na daga abinda yake gidan ba tunda sanda ta shiga bata shiga da ko tsinke ba. Wannan shine umarni na, idan kuma taki bi ki gaya mata nace babu ni babu ita har abada, ke ma babu ke babu ita har abada, babu ita babu duk kan abinda muka haifa a duniya, har sai ranar da tayi abinda nace sannan kuma ta nemi dukkan wanda ta batawa ta nemi gafarar su suka yafe mata to a lokacin nima zan yafe mata"

Inna ta fara kuka tana son ta rokar wa Ruqayyah gafara a gurin mahaifinta amma sai ya daga mata hannu yace "wannan umarni ne na baki a matsayi na na mijinki, sai ki zaba ko ki bi umarni na kiyi abinda nace ko kuma ki biye wason da kike yiwa yarki ki bita gidan da take son kwata daga


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login