Showing 3001 words to 6000 words out of 300844 words
Ko da karambani zamu rike kan namu? Ana maganar reality ne fa anan, ana maganar future din mu ne data yaran nan kannen mu" Hussain yace "in ba zaka iya ba kawai kace ba zaka iya ba ba sai kayi min dogon sharhi ba" ya wuce shi ya dawo gaban Amina. "Aunty ki yarda dani dan Allah. Wallahi zan iya" tayi ajjiyar zuciya tace "zaka iya? Ta yaya?" Ya zauna a kan kafafuwansa yace "kasuwanci zan shiga, ba da akwai kudade a hannun mu ba? da akwai wasu a bank? Ga kuma motoci har guda uku a waje? Kuma ga filayen da Abba ya siya ya ajiye? Mu siyar dasu ku bani kudin in shiga business dasu.........."
Hassan ya dawo kusa da Aunty da sauri yace "hauka ma kenan. Yanzu in business din zamuyi Hussain sai mu dauki dukiya mu baka? Kai din? In ka lalata ta kuma shikenan sai mu dawo mu zuba tagumi? Gaba ake dubawa Hussain. Komai a hankali a kuma nutse ake binsa, kullum sai na gaya maka wannan amma kai baka ji"
Hussain yayi masa kallo daya ya dawo da dubansa kan Aunty yace "Please Aunty, ki bani wannan damar dan Allah. Wallahi zan iya, ki rabu da Hassan. Shi yana living ne in the future ni kuma ina living now, in dama tazo wa mutum kawai yayi amfani da ita ba sai ya jira wata damar tazo sanda yayi masa dai dai ba.
Yanzu ne damar mu Aunty, ki bani wannan damar dan Allah.
Aunty ta jima tana kallon sa, tasan halinsa sarai, tasan karambanin sa da daukan abinda yafi karfinsa ya dora wa kansa, tasan kuma kokarin sa dan duk sanda ya fadi baya zama a kasa yayi kuka mikewa yake yi ya cigaba da tafiya. Duk abinda yake bashi wahala kuma sai yayi ta maimaita wa har sai ya iya.
Ta tuna farkon sanda aka siyo musu kekuna, ana kawowa Hussain ya dauka ya hau ai kuwa ya fado ya kukkurje, amma bai hakura ba, yayi ta hawa keken nan yana faduwa har sai da ta dauke saboda tausayin sa sai babansu yace ta bar masa ai a haka ake girma. Hassan kuwa sai yayi ta studying keken nan yana gwada yadda komai nasa yake aiki har sai da ya fahimce shi sannan ya hau, shima kuma a hankali yadda ko ya fadi ba zaiji ciwo ba, kuma bai fadin ba, sai yake tukawa a hankali yadda in yaga zai fadi sai yayi sauri ya sauka, ko kuma yake bin jikin bango yana dafawa.
A karshe sai ya zamanto Hussain ya riga Hassan iya keke, amma kuma duk ya ci uban keken nasa ya babballashi. Sanda Hassan ya iya nasa keken, keken Hussain ya riga ya lalace.
Amma kuma akwai wani abu a dangane da Hussain tun yana yaro, yana balain, tsananin son sana'a. Duk wani abu indai ance abinda zai kawo kudi ne to Hussain ya sanshi kuma yana sonshi. Hussain har fruits din bishiyar umbrella din gidansu yake cira ya siyar wa da yaran unguwa. Hussain in yaje da abu makaranta wani yaron yace yana so yakan iya siyar masa ya kara riba sannan ya fito waje ya sai wani. Amma fa kudin in ya samu rabarwa mutane yake yi.
Ta tuna wata rana da ya dawo daga school da ulu da kwarashi, ta tambaye shi inda ya samu sai yace "Nanny din mu ta makaranta na gani tana saƙa, tace min ana samun kudi sosai in akayi saƙa, shine na bata kudi ta siyomin zan ringa yin saƙar hula ina bata tana siyar min" sai da baban su ya zane shi akan sakar nan sannan ya daina.
Babansu ya taba tambayar su abinda zasu zama in sun girma. Hassan yayi shiru yana tunani sannan yace "ban sani ba Abba, sai nan gaba in nayi tunani" ana tambayar Hussain sai ya washe baki yace "Dangote".
Ta dawo da tunaninta kansa da har yanzu yake durkushe a gabanta yana roko, ya kamata ta bashi dama, amma ya kamata tayi tunani, saboda kamar yadda Hassan ya fada wannan future dinsu ne basu kadai ba harda yan kananan yaranta mata. Dole zata yi tunani kafin tayi taking wannan risk din kuma dole zata yi shawara. Shawara da abokin shawarar ta sarkin tunani. Hassan.
Tace "shikenan Hussain ka bani lokaci inyi tunani, duk abinda na yanke kuma shine final babu jayayya"
Ba haka yaso ba, amma yadda take so dole hakan za'ayi.
Bayan ya fita sai ta juyo ta kalli Hassan, a take ya girgiza mata kai.
Ta sauke ajjiyar zuciya tace "bana son discouraging dinsa, ka bani shawara yaya zanyi?"
Ya gyara zama yana kallon carpet yace "dukiyar marayu ce aunty, ina ji masa tsoro, kinsan halin Hussain in ya kafa kasuwancin ma raba wa mutane zai tayi" Ta gyada kai cikin fahimta, ya cigaba da cewa "a shawarce ina ganin a raba, a fitar masa da kasonsa a bashi ya kafa kasuwancin dashi yadda ko sun rushe ba zai rusa mu gabaki daya ba, mu dashi zamu samu abinda zamu dogara dashi. Idan kuma ya zama successful sai a kara masa wata"
Aunty taji dadin wannan shawarar, amma kuma a ranta bata son rabon gadon nan saboda tana ganin kamar raba kan ƴaƴanta ne, taso a ce komai zasuyi tare zasuyi. Amma kuma shawarar abar dubawa ce.
Haka akayi, aka raba gado aka bawa Hussain nasa, sauran kuma suka ajiye suna amfani dashi gurin harkokin rayuwarsu. Hassan yayi amfani da wani kaso a cikin nasa gurin nema wa kansa makaranta.
A lokacin da shekara ta zagayo Hussain ya kira su yana nuna musu lissafin abubuwan da yayi da kudin da ya samu sai su ka ga cewa kudin da yake dashi a yanzu ya ninka wanda yake dasu a waccan shekarar sau huɗu har da doriya. Suka rike baki suna mamaki, shi kuma ya gyara zama yana murmushi yace "na gaya muku ai, Dangote zan zama"
Ga masu son siya zasu iya turo kudinsu ₦300 ta account
GT Bank
Account Name : Nafisa Usman Tafida
Account Number : 0139433741
Sai su turo shaidar transaction din ta hanyar WhatsApp zuwa wannan layin
08067081020
Wadanda basu da account zasu turo katin MTN na ₦300 zuwa wannan layin
08067081020.
Dan girman Allah banda kira, WhatsApp only
Sai na jiku....
Episode three : The Beginning 2
Free Episode
Labarin, ya samo tushensa na biyu ne daga gurin wasu ma'aurata. Yusufu da Sa'adatu. Sa'adatu wadda ake kira da Sa'ade, sai kuma yara suka sake rage sunan zuwa Ade, sunan Aden kuma sai ya bita har girmanta, asalinta mutuniyar zamfara ce a garin kauran namoda, kyakykyawa ce, irin kyawun da ake kwatance dashi a unguwarsu. Baka ce doguwa, kusan komai nata dogo ne sannan tana da sanyin hali da nutsuwa sosai. Kuma nutsuwar ta ta kara karfi ne saboda ta kasance mahaddaciyar Alqur'ani ce ita.
Babanta malami ne, mai tarin almajirai da suka zo saga garuriwa daban daban kuma suke daukan karatu a karkashin sa. Ita ma a gurin sa tayi karatun ta, ta sauke tayi tilawa sannan tayi hadda. Tsakanin son da take yiwa Alqur'ani ya saka takan zauna tayi ta rubuta ayoyi a jikin allo, hakan yasa ta kware sosai gurin rubutu yadda ko shi mahaifinta malam shehu ya sara mata a gurin iya rubutu, dan haka kusan duk rubutun da aka aiko masa dashi ita yake bawa tayi masa. Bata yi karatun boko ba, sai dai tana yin rubutu sosai da ajami.
Yusufa almajirin malam shehu ne, mutumin garin Zaria ne. Tun zuwansa gidan zuciyarsa take son Ade dan haka ya ringa siyan ta da magana mai dadi da yabo da kyautatawa har ya samu nasarar kafa soyayyar sa a zuciyarta. Suka fara soyayyar su mai tsafta a boye dan gudun bacin ran Malam Shehu. A haka har ya kammala karatun sa ya koma Zaria, daga nan kuma sai yake aiko mata da wasika a boye itama tana bashi amsa, wani lokacin kuma sai ya shirya ya tafi kauran Namoda yace yazo gaishe da Malam amma a badini ganin Sa'adatu yazo.
Kwanci tashi har Sa'adatu ta isa aure, a lokacin ne Malam Shehu ya zabi wani babban malami anan garin faskarin jihar Katsina da niyyar ya hada su aure da Sa'adatu amma sai Sa'adatu ta nuna bata son shi, aka tambaye ta wanda take so sai tace Yusufa.
Malam shehu yasan Yusufa yasan halayensa,ya kuma san iyayensa da danginsa, kuma a iyakacin saninsa shine basu da wani aibu da zai hana a basu aure sai dai yana jiye wa yarsa zaman talauci, dan matalauta ne danginsu sai dai Malam yasan cewa shi arziki na Allah ne dan haka ya kira Yusufa ya bashi auren Ade
Yusufa ya dauke ta ya tafi da ita Zariya. Daga nan suka kara gaba zuwa Kaduna inda ya sama musu gida a unguwar hayin rigasa suka zauna shi kuma ya ke iyakacin kokarin sa gurin ciyar da ita da kyautata mata. Duk da cewa rayuwar tana yi musu wahala sosai, saboda Yusufa bashi da takamaiman aikin yi sai dai kullum in ya fita duk abinda ya samu na aikin karfi shi zaiyi yayo musu cefane ita kuma ta cancana ta sarrafa musu abinda zasu ci.
Ita kuma Sa'adatu sai ta bude makarantar allo anan tsakar gidan ta inda take dorawa yaran unguwa karatun Alqur'ani, har mata ma sukan shigo ta koya musu, tana dan samun abin sadaka daga iyayen yara da kuma dan sauran abubuwan buƙata, kuma tana yin kitso shima a biya ta. Da haka take samun abin da take taimakawa maigidan ta gurin kula da iyalin su.
Zama suke mai tsafta, basu da wadata amma cike suke da soyayyar juna a haka har Allah ya albarkaci Sa'adatu da samun ciki. Wata tara ta haifa musu tagwayen yammata masu tsananin kama da junansu, kyawawa kamar ita. Aka saka musu sunaye Ruqayya da Sumayya.
Tun daga jarirantaka Sa'adatu ta fahimci banbancin halayya a gurin tagwayen nata, Sumayya tana da hakuri sosai, Ruqayya kuma tana da zafin zuciya. Bayan sun fara girma sai banbancin ya sake bayyana sosai, in dai iyayen suka ji suna fada, ko kuma suka ji an kawo kara daga waje, to ba sai sun tambaya ba sun san Ruqayyah ce. Wata irin bakar zuciya ce da ita da wani irin taurin rai, bata da tsoro ko kadan kuma bata shayin yin komai ko fadar komai. Zata iya yiwa babba rashin kunya komai kuma girmansa, komai furfurarsa, hatta Inna Ade (Sa'adatu) Rukayya tana iya ta murguda mata baki tayi mata kunkuni. Babanta kawai take dan daga wa kafa shima kuma ko zai yi dukan duniyar nan ko fadan duniyar nan ba zata daga kai ta kalle shi ba ballantana ya saka ran zata bashi hakuri.
Kullum Sa'adatu addu'ar ta akan Ruqayyah ne, ta dauke ta a matsayin wata jarabawa da ubangiji yake musu ita da Yusufu dan yaga yadda zasuyi tarbiyyar ta kuma ta dage sosai wajen kokarin ganin sunci wannan jarabawar. Wannan yasa duk sanda Yusufu yake dukan ta sai tayi kokarin hana shi tace "Duka baya gyara Baban biyu, addu'a zamu yi ta mata da nasiha, mu kuma saka idanuwa sosai a kanta. Allah zai gyara mana ita insha Allahu" ya kan bata amsa da cewa "tsoro nake ji Maman biyu, tsoro nake ji kar mu kasa yi mata tarbiyya a karshe duniya tayi mata"
Bayan tagwayen, Sa'adatu ta haifi Suleiman, sannan kuma ta haifi Usman mai sunan Malam Shehu, wanda suke kira da Zunnoor.
Sai dai fa duk wannan halayyar ta Ruqayyah to kuwa tana son iyayenta, tana kuma son yanuwanta musamman Sumayya. Ita ce babbar kawarta ita ce kuma abokiyar shawarar ta sannan ita ce abokiyar sirrinta. Wannan ya saka Sumayya ce kawai tasan sirrin Ruqayyah, ita kadai tasan dogon burin Ruqayyah na zama mai kudi a nan gaba. Ita kadai tasan frustration din Ruqayyah. She hates kasancewarta ƴar talakawa.
Bayan Shekaru Goma
Low-cost, Unguwar Rimi
Kaduna.
A wani gida, wanda yake daya daga cikin manya manyan gidajen da suke layin, za kuma a iya kiran sa da daya daga cikin kayatattun gidajen da suke jahar ta kaduna, anan gidan ne labarin ya cigaba.
A compound din gidan na hango wasu tagwayen samari, masu tsananin kamanni a fuska amma masu tsananin bambanci halayya. Alhassan da Alhussain. Marayu, wadanda suka rasa mahaifiyar su a gurin haihuwar su sannan suka rasa mahaifinsu a lokacin da suke da karancin shekaru.
A harabar gidan na hango samarin su biyu sun fito daga cikin gidan, sun jera suna tafiya suna hira suna dariya. Kallo daya zaka yi musu ka fahimci cewa kaunar da suke yiwa junan su mai yawa ce, shakuwar su mai karfi ce, bond din da yake tsakanin su special ne wanda babu wanda zai fahimta sai wanda aka haife shi irin haihuwar su. Tagwaye.
Daya baki ne, daya fari.
Bakin ne ya kalli farin yana dakatawa daga dariyar joke din da farin yayi "Hussain yanzu wai da gaske kake? Kana nufin komawar zakayi gobe? Wai yaushe ka dawo Nigeria ne ma gabaki daya? Ayyuka fa sunyi min yawa anan Hussain nasan Aunty ma in taji zaka koma ba zata barka ba" farin, wanda aka kira da Hussain yayi dariya yana bayyanar da dimple din sa guda daya tare da kyawawan jerarrun hakoransa. His eyes twinkling. Daga gani zaka fahimci shi mutum ne mai yawan fara'a, mai yawan murmushi, irin mutanen nan da murmushi baya barin fuskarsu no matter how much they try.
"Ta yaya Aunty zata san zan koma? Ni dai bazan gaya mata ba sai dai in naje can mayi waya, kai ma kuma ai nasan ba zaka gaya mata ba ko Hassan?" Ya karasa maganar cikin shigar lallashi, wanda aka kira da Hassan ya dauke kansa tare da ture hannun Hussain daga kafadarsa daya dafa yace "aikin ka kenan ai, in anyi maka Magana ka kalallame mutum da dadin baki" sai kuma ya juyo yana kallonsa tare da jingina bayansa da jikin motar da suka zo gabanta yace "ka dai bi a hankali Hussain ina gaya maka, you are too open, ga ka da seeking attention, kudin da kake samu suna da yawa and you are showing it to the world. Ni ina jiye maka halin mutane" Hussain ya jingina shima a kusa da Hassan yace "mutane rahama ne Hassan" "eh mutane rahama ne idan da ace nagari ne zasu biyo ka, yanzu mutane nagari wahala suke yi. Mutum ake kiwo yanzu a duniya ba wai dabba ba"
Hussain ya daga kafada tare da juyawa yana kallon motar da suke jiki cikin kokarin chanja topic ya yamutsa fuska yace "phew! What a mess! Wannan motar wai dama haka ta tsufa? Ji duk tail lights dinta sunyi scratches? Amma a hakan kake cewa in tafi da ita Kano?"
Hassan ya juyo yana kallon motar shima yace "wannan motar ce ta tsufa? Da yaushe ka siye ta?" Hussain ya dan sosa kanshi kadan yana kankance ido alamar tunani sannan yace "it doesn't matter. Ni ba zanje da wannan motar gurin gimbiya ta ba" ya fadi kalmar gimbiyar dramatically, har yana bowing kansa kamar mai gaisuwa, wannan ya saka Hassan dariya, yana girgiza kai yace "kar Allah yasa kaje da ita din, mai gimbiya, in kayi wasa sai inyi maka addu'a Allah yasa mai martaba ya fasa ba ka auren ta inga ta tsiya"
Hussain ya zaro ido waje "what! Amma da kafi kowa ƙina a duniya" Hassan ya zagaya side din driver yayin da Hussain ya jefa masa key ya cafe yace "common, get in, muje in nuna maka warehouse din dan in ka tafi bansan ranar dawowar ka ba".
Sai da Hussain ya gyara zaman hularsa sannan ya bude motar ya shiga kusa da danuwansa, mai gadi ya bude musu gate suka fita, Hussain ya juya yana kallon gate din bayan an rufe shi sannan yayi tsaki yace "gate din nan so nake a zo a cire shi a saka wani" Hassan ya bude baki yana kallonsa shi kuma ya dauke kai gefe yana murmushi, Hassan yace "saboda me? If I may ask your highness?" Yace" saboda baiyi kama da gate din gidan dangoten Kaduna ba"
Gabadaya suka yi dariya. Hassan yace "oh sunan da ka rada wa kanka kenan? To Allah ya taimaka" Hussain ya daga kafada yace "to me yayi saura? Menene maraba ta da shi? Wannan fa companyn da zan bude wata mai kamawa will be my third. Kuma, it is just the beginning of *H & H group of companies* " Hassan ya saka hannu daya ya ture masa hular kansa yace "Allahu ka shirya min wannan kanin nawa".
Ga masu son siya zasu iya turo kudinsu ₦300 ta account
GT Bank
Account Name : Nafisa Usman Tafida
Account Number : 0139433741
Sai su turo shaidar transaction din ta hanyar WhatsApp zuwa wannan layin
08067081020
Wadanda basu da account zasu turo katin MTN na ₦300 zuwa wannan layin
08067081020.
Dan girman Allah banda kira, WhatsApp only
Cigiya!
Ina cigiyar wasu bayin Allah su biyu da suka turo kudinsu tun jiya har yanzu basu yi magana ba.
Episode Four: Gimbiya Fatima
Hayin Rigasa,
Kaduna state
Yammata biyu na gani suna shigowa cikin gidan su wanda katangar sa ta kasa ta zube dan haka aka zagaye shi da tsohon langa langa, sai dakuna guda biyu a tsakiyar gidan suma dakunan na kasa ne amma anyi musu plaster da siminti, a gefe akwai bandaki shima rabinsa na langa langa ne kuma babu rufi, tsakar gidan gabaki dayansa kasa ne da bishiya a gefe a kasanta akwai murhu da tukwane da sauran kayayyakin da suke nuna anan ake girki, sai kofar dakunan da akayi yar karamar baranda, wadda simintin ta duk ya mutu yayi ramuka.
A gefen barandar akwai jerin alluna da gwangwanin tauwada.
Jikin yammatan sanye yake da uniform. Kansu daya, kamannin su daya, yanayin su daya dan sai ka kalla sosai, ko kuma wanda ya riga ya sansu sannan ake iya gane banbancinsu.
Dariya suke yi suma, karar dariyar su ta hade da karar kofar gidan da suka bude, wanda ko soro babu, hannayensu sarkafe dana juna suna tafiya ƙafafuwan su suna hardewa cikin na juna.
"Ruqayyah baki da kirki wallahi, hahhaha, kinga yadda kika ruda shi kuwa ya kasa gane ina ne kofar fita daga ajin?" Wadda aka kira da Ruqayyah ta rike ciki tana dariya, sannan tace "kinga ai gobe ma ya kuma dan kaniyar sa....., Ko waye ya gaya masa ni sa'ar sa ce? Harda