Showing 270001 words to 273000 words out of 300844 words

Chapter 91 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2027

yayi musu sukayi mishi kallo daya sukayi deciding basa sonsa? Suka yanke wa zuciyarsa hukuncin daurin talala na har abada?

Amma sai Allah almusawwiru ya juya lamarin sa ya aiko masa da yaron da har yau da suke magidanta bayan tsahon shekaru ya kasa yanke hukuncin menene matsayinsa a gurinsa. Abubakar Sadiq sunansa, Sultan ake ce masa, jika ne shi a gurin sarkin garin Abuja a wancan lokacin. Sun hadu ne a lokacin da kakansa wanda shine ya yi wa Amir huduba da sunan sa "Abdullah" sannan kuma yayi masa inkiya da Amir, yazo ziyara gidan marayu kuma ya taho dashi....

"Hi, can we play together? My name is Sultan. Will you like to be my friend?"

Da wannan friendship din ya fara, daga nan sai amintaka mai karfi sai kuma yanuwantaka wadda Amir baya jin ko da ace jini daya ne yake gudana a jikin su su biyun zaiyi masa irin son da yake yi masa tun daga lokacin har yanzu. Wannan soyayyar ce ta saka shi sarki Abdullahi wanda yake kakan Sultan yayi adopting Amir ya mayar da shi gidansa a matsayin dansa, ya hada su da jikan nasa ya rike su tare. Ta sanadiyyar Sultan Amir ya samu ilimi, na muhammadiyya dana boko, ya kuma sami family, duk kuwa da cewa kaf family din babu wanda bai san asalin shi ba kuma lokaci zuwa lokaci ana tuna masa a cikin bakar magana musamman idan aka ga yana kokarin shiga cikin abinda ake ganin bai shafe shi ba.

Wannan ya saka ko dai dai da rana daya bai taba manta asalinsa ko kuma muce rashin asalinsa ba. Kuma bai taba boyewa ba, sai ya mayar dashi tamkar identity dinsa yadda duk wanda ya san shi sai ya tabbatar cewa yasan ko shi waye saboda kar nan gaba kayi kokarin robbing abin a fuskarsa, bai taba boyewa ba kamar yadda bai taba goge murmushi daga fuskarsa ba duk kuwa da irin tarin wahalwalun rayuwa da suka gani tare shi da Sultan, har gidan kangararru sai da suka je suka zauna bytsahon shekara guda, sai da suka rasa kowa suka rasa komai amma basu rasa junan su ba har zuwa ranar da Allah ya gyara rayuwar Sultan ta hanyar hada shi da bafulatanar yarinya *Maimoon*, gyaran Sultan sai ya kawo gyara shima a tasa rayuwar, ya nutsu ya ajiye shaye shayen da da suke yi tare da Sultan sannan ya karbi aiki a sabon office din Sultan "Moon Construction Company" sannan kuma yayi aure, ya kuma samu karuwar yaya biyu, na farko mai sunan amininsa Abubakar, wanda suke kira da Sultan kamar yadda ake kiran wancan, sai kuma jaririyar da aka haifa yanzu, Auren da aka sha gwagwarmaya kafin samuwarsa saboda wannan tambarin nasa na rashin asali, sai da Sarkin lokacin, Sarki Sadiq, mahaifin Sultan, ya shiga maganar sannan kuma itama yarinyar "Aysha" ta dage tace "ni ina sonsa a haka, duk da bashi da asali ni ban damu ba" and so it came to be.

Wannan ne kuma abinda yake soya zuciyarsa a yanzu idan ya tuno kalamanta na jiya

"ka manta halaccin da nayi maka? Ka manta yadda na rufe ido na na aure ka duk da kasancewarka marar asali amma sakayyar da zaka yi min kenan? Ka rasa abinda zaka saka min dashi sai kishiya Amir"

Wannan maganar tata, a ganinsa ita ce dalilin mafarkin sa.....

Ta fada masa hakan ne kawai dan ya nuna mata yana tunanin maybe zai kara aure, bai tabbatar ba tunda har yanzu yarinyar da yake nema *Aisha Humairah* bata bashi wata cikakkiyar amsa ba amma a ganinsa gwara ya gaya wa iyalinsa su san da maganar kar suji a wani gurin kuma azo a samu sabani, he thought he was doing the right thing, amma yadda tayi reacting shine sanadin da ya saka shi a halin da yake ciki a yanzu.

Ya tashi ya koma toilet ya kunna wa kansa shower, yana so yasamu ya watstsake maybe ko mafarkin zai fita daga ransa, sannan sai ya dauro alwala ya zo ya saka rigarsa zai tafi masallaci, har ya wuce kofar dakinta sai kuma ya dawo da baya yayi knocking sannan yace "ki tashi kiyi sallah" sai kuma ya wuce. Bayan an ida da sallar bai bar masallacin ba sai yaja Alqur'ani ya fara karantawa a can edge inda masu shige da fice ba zasu dame shi ba. Sai daya dago kai yaga garo yayo haske sosai sannan ya yi adduoin sa ya tashi.

Baya son ganinta, gani yake inya ganta ranshi baci zaiyi, sai yaji ina ma zai iya tafiya office da kayan jikinsa da kawai mota zai kunna yayi tafiyar sa, amma ba zai iya ba, dole ya shiga gidan nasa, yana jin motsinta a kitchen daga dukkan alama breakfast take hada wa, on normal days, kitchen din zai bita su kammala hada abincin tare ko kuma yaje ya shirya little Sultan, first born dinsu, amma yau sai ya wuce war sa dakin sa ya fara shiryawa. Yana jin ta ta bude kofar dakin ta shigo ta tsaya daga bakin kofa amma bata karaso ba, ya juya yayi mata kallo daya ya dauke kansa. Ta zagayo ta gabansa ta zauna a bakin gado tana kallon yadda yake ta fama da links din hannun rigarsa. Tace "ina kwana?" Bai kalle ta ba yace "lafiya" sai ta tashi ta kama hannun tana saka masa "kayi hakuri dan Allah Abban Sultan. Nasan na fada maka maganar da bai kamata ace na gaya maka ba, ba nufi na in bata maka ba raina ne ya baci kawai, ban ma san me nake fada ba. Dan Allah kayi hakuri"

Ya bar inda take ya dauko turare yana sakawa kansa yace "abinda yake ranki kika fada, there is nothing more to it" tace "ba abinda yake raina ba kenan, wallahi ba abinda yake raina ba kenan, tunda muke tare da kai ka taba jin na fadi magana makamanciyar wannan? Dan Allah kayi min uzuri mana ina kishin kane shi yasa. Babu matar da take son mijinta kuma yace zai yi mata kishiya sannan ace ranta ba zai baci ba" ya juyo yana kallonta yace "in rai ya baci kuma sai hankali ya gushe? It is okay, at least na san irin kallon da kike yi min yanzu" sai ta zauna a bakin gado ta fara kuka, "haba Amir, ka yiwa zuciyata adalci mana, ni fa aka bata wa, ni fa kake kokarin yiwa kishiya kuma sannan kaine mai fishi ni ce mai bayar da hakuri? Ka bar ni inji da abu daya mana?"

Ya fahimci abinda take so tayi, tasan sanyin zuciyarsa musamman in yaga mutum yana kuka, mutum din ma ace matarsa uwar yayansa, so take ta karya masa zuciyarsa ya sauko daga fushin da yake yi. Ya dauke kai ya fita ba tare da ya lallashe ta ba ko kuma yayi mata wata magana. Yana fita yaga Sultan da cup a hannunsa yana shan tea, ganin ya fito ya saka yaron ya ajiye cup din hannunsa ya taho da gudu ya rungume shi "Abhi, yau ni na saka kayana da kaina" Amir yayi murmushi tare da sunkuya wa dai dai tsahon yaron yana gyara masa neck tie dinsa yace "kayi kyau kuma sosai, just like the handsome gentleman that you are. Kayi breakfast?" Yace "eh na sha tea" Amir yace "to ina baby?" Sultan yayi dariya "tana bacci a daki, Ammi tace in na tashe ta sai ta zane ni" Amir ya mike yana rike hannunsa yace "zo muje mu tashe ta muce mata good morning kafin mu fita"

Dakin Aysha ya tafi gurin jaririyar yarsu da a wannan satin ne suka dawo daga wankan jegon haihuwarta da Aysha ta je. Ya tsaya yana kallon babyn tana ta baccin ta a cikin crib dinta, ya saka hannu ya shafa gashin kanta yana kara mamakin hasken fatarta kasancewar daga shi har Aysha ba farare bane ba, ko a ina babyn ta samo fari har haka? Shin hakan yana nufin wani daga cikin iyayen sa fari ne? Ya tuno matar da ya gani a cikin baccin sa jiya, wadda ya saka a ransa cewa itace mahaifiyar sa, fatarta bata kai ta baby Afnan haske ba.

Ya dauki yarinyar ya daga ta tayi mika sannan ta bude idon ta tana kallon sa, yace "good morning angel, how is the most beautiful girl in Abuja" ta dan tabe baki irin na jarirai, sai kuma kamar an saka mata battery ta fara tsandara kuka. Sultan ya ja baya yana rufe baki. "Babu ruwana Abhi, Ammi zata zaneka babu ruwana" ya juyo ya ganta a tsaye a bakin kofa, in normal days ta tuni ta shigo ta fara korafin ya tashi baby Afnan amma yau sai yaga tayi shiru, ya lura da yadda idon ta yayi alamar kuka, sai ya ajiye jaririyar ya kama hannun Sultan yace "let's go" kafin su fita tace "abinci fa?" Bai juyo ba yace "na koshi"

Sai da ya ajiye Sultan a makaranta sannan ya wuce office, cikinsa yana ta karar yunwa, Aysha yake punishing amma nasa jikin ne yake gaya masa. Shi baiga dalilin da zai sa ta wani rikice har tana gaya masa maganganu ba. Shin dan shi bai kasance mai asali ba sai ya zama ba cikakken namiji ba kenan? Sai ya zamanto shi bashi da wannan damar da Allah ya bawa maza na auren mata daya zuwa hudu? Ya tuna da Aisha, yarinyar kirki, shi kansa bai tabbatar idan soyayya ce yake yi mata ko kuma tausayi ne, tun ranar da ta bashi labarin ta, tun lokacin da tasa matar ta tafi gida wankan jego, sai yaji kamar akwai wani link a tsakanin su duk da bai san wanne irin link bane ba, maybe ya na da nasaba da yadda mutane suke treating dinsu saboda abinda ba su suka dora wa kansu ba.

Ya tarar da aiki a office kamar kullum, dan kusan babu ranar da ba'a kawo musu sabuwar kwangila ta gina gida ko masana'anta ko kuma wani abu daban, hakan kuma yana da dangantaka da irin aikin da suke yi mai kyau da inganci. Wannan aikin daya riƙe shi shi ya fara mantar dashi da damuwarsa, a haka har Aisha ta kira shi ta sanar dashi cewa ta gama da school, ya riga ya sabar mata da cewa duk sanda ta tashi daga school shi zai mayar da ita gida kuma baya son ya saba wannan alkawarin dan haka ya dakatar da sauran abubuwan da suke gabansa ya dauki mota ya fita daukan ta, daga nan kuma yana son yaje ya bawa Dr Maimoon labarin mafarkinsa yaji nata view din akai, shin tana ganin mafarki ne ko kuma memory ne? Sai dai a cikin saurin da yake yi ya manta wayarsa a office din nasa, wayar da dama babu isasshen charge a cikin ta.

A daidai lokacin ne kuma mota dauke da Yusuf, Hussain, da Abdulrahman ta sauka daga kan titi zuwa karamar hanyar da ta tafi zuwa gidan marayu na kasa. Fuskokin su cike da tsoro tare da fargabar abinda zasu tarar. Sanda zasu taho sai da sukayi drama da Hassan, yace lallai sai sun gaya masa inda zasu je su kuma basa son su gaya masa matsayar maganar su dan kar su tarar da abinda ba zai faranta masa rai ba, gwara daga baya in sun samu good news sai su gaya masa. Jin ba zasu gaya masa abinda suke shiryawa ba ya saka ya ce ba zasu taho gabaki daya ba, dole wasu daga cikin su suka hakura.

Zuciyoyin su cike da zulumin abinda zasu tarar suka yi packing suka fito suna karewa gida marayun kallo, tare da lodin yaran da suke zazzaune guri guri, ƙanana da manya, mata da maza, suna mamaki cewa akwai possiblity na cewa da ɗaya tilo na Hussain Aminu Abdullahi anan gidan cikin wadannan yaran ya tashi, hakan yana nufin da yawa daga cikin yaran nan suma kowa da akwai nasa story din. Sai suka ji a ransu suna fatan ba'a nan din bane ya tashi, suna fatan they are wrong, amma kuma wata zuciyar tana tuna musu da cewa kasancewar yayi rayuwa anan shine zai taimaka musu wajen gano inda yake anan a yanzu.

Tambaya suka yi aka nuna musu office din shugabar gurin, an elderly lady, wadda ta tarye su cikin murmushi da karramawa tana fatan zuwa suka yi suyi adopting one of the kids, ko kuma zuwa suka yi su kawo musu donations dan taga alamar da maikomaiko a jikin su. Ta basu kujeru suka zauna sannan itama ta zauna tana kara yi musu sannu da zuwa, a ranta tana lura da wani yanayi a tare da su wanda ta kasa placing a zuciyarta. Suka sake gaisheta, sannan Yusuf yace "tambaya muke dan Allah. Shekaru talatin da biyar da suka wuce, ranar goma ga watan January, ko kun tsinci jariri ko kuma an kawo muku jariri gidan nan?"

Matar ta saki baki tana kallon sa, sannan ta bi sauran samarin da kallo tace "shekarun da yawa ai" Hussain yace "shekarun da yawa Hajiya. Adadin shekaru na kenan a duniya" Abdulrahman yace "ba kwa keeping records? Na dauka duk yaron da aka kawo muku zaku bude masa file inda zaku ke saka bayanan sa na tsahon zaman da yayi a tare da ku da kuma inda ya tafi bayan ya barku" ta gyada kai tana kallon wasu tsofaffin drawers din da suke ajiye a gefe, takardu suna lekowa daga ciki saboda tsabar cika da drawers din suka yi. Sai tace "za'a iya samu a cikin takardun can, amma aikin da yawa" Hussain ya mike yana nannade hannun rigarsa yace "ta ina zamu fara? Idan bamu gama yau ba sai mu dawo gobe, ba zamu bar garin nan ba sai mun sami tabbacin in ya zauna anan ko kuma bai zauna ba. Daga nan zasu san daga inda zamu dora"

Haka akayi, mazan uku plus ma'aikatan gurin suka yi dai dai da takardun gurin, amma har suka zo karshe basu tarar da na shekarar da suke nema ba, "shekarun da yawa" matar ta maimaita. Yusuf ya mike yana goge gumin fuskar sa da hanky dinsa yace "babu wasu takardun?" Ta girgiza kai. "Shekarun da kuke magana akai tun kafin in fara aiki anan ne, nima wadannan takardun su kadai na tarar, ina tunanin lokacin da akayi sababbin gine gine ne aka rasa takardun" Hussain ya zauna yana buga hannun sa a hankali a kan table, sannan yace "a cikin ma'aikatan ku, babu wanda kike ganin zai kai shekarun nan yana aiki a gurin nan?" Ta dan dafe goshinta tana tunani sannan ta dago kanta da murmushi tace "akwai Baba asabe, tafi kowa dadewa a gurin nan ta kuma fi kowa sanin yaran da aka raine su a gurin nan"

Sai ta aika aka kirawo dattijuwar da aka kira da Baba Asabe, ta shigo tana gyara gilashin idonta tare da kikkifta ido tana kallon bakin, sannan tace "Sarki, kaima shafe shafen nan na zamani ka fara ne? Dan dai ince na dawo da auren to bana yi nima" duk sai suka tsaya suna kallon ta, Madam marry tace "Baba Asabe ba Amir bane ba fa? Ko dai idon ya karasa mutuwa ne?" Baba Asabe ta murza idonta tace "ke ashe ba shi din bane ba, har zance ina tarin gashin ya tafi? Na dauka yaji fada na yaje ya aske" Yusuf yace "Sarki? Baba waye sarki? Jikan ki ne?" Sai Madam marry ta mike tsaye, sai yanzu ta fahimci abinda ta gani a tare dasu wanda ta kasa fahimta, gabadayan su suna kama da juna kuma suna kama da Amir, daya daga cikin wadanda ta hannun su ne orphanage din yake cigaba da running har zuwa yanzu.

"Amir" ta fada, "Amir kuke nema" ta maimaita. Duk duka mike suma suna kallonta. "Waye Amir din kuma yaushe aka kawo shi gidan nan? Yana ina yanzu? Ya akayi kika san shi muke nema" suka jero mata tambayoyin a tare, ta kalle su daya bayan daya tana jin hawaye yana sauka daga idon ta, tace "ban san ranar da aka kawo shi ba dan ban ma same shi a gidan nan ba. Na dai san cewa duk daga inda kuke ku yanuwansa ne, na kuma san cewa yana daga cikin yaran da aka yaye daga gidan nan wadanda har yau basu fitar da ran samun iyayen su ba".

Abdulrahman ya zauna yana dafe kansa, yana jin kamar hawaye zai zubo masa. Yusuf a hankali yace "where is he?" Madam Merry tace "he was here last week, akan wannan kujerar da kake zaune a zauna, he was asking me ko anzo neman sa kamar yadda yake yi duk sanda yazo gidan nan" Hussain yace "ranar goma ga watan January aka kawo shi?" Baba asabe da take tsaye tana bin su da kallo kuma tana jin abinda suke cewa tace "ban san kwanan matan ranar da aka kawo shi ba, na dai san cewa ranar juma'a ne" Hussain yace "yes! Juma'a ne. A ina aka same shi?" Tace "da magariba, muna kokarin raba wa raya abincin dare muka ji kukan sa a waje, muna lekawa muka ganshi a kasa, cikin kasa da duwatsu, babu ko riga a cikin sa" ta goge guntun hawayen daya fito mata tace "ko cibiya ba'a yanke masa ba, ko zani ba'a saka an rufe shi ba duk kuwa da sanyin da akeyi a lokacin".

Hussain ya zauna shima, how can their mother be this cruel? Anya ma kuwa akwai zuciya a cikin kirjinta? "Where is he?" Ya sake maimaita wa, yana tuna wa kansa cewa tunda tace he was here last week, hakan yana nufin he is alive kenan. Baba Asabe ta zauna akan daya daga cikin kujerun robar da suke gurin, tana kallon sa tace "yayanka ne?" Ya girgiza kai yace "kani na ne" tace "babarku bata da imani, ko kadan bata da imani" Hussain ya gyada kai cikin gamsuwa yace "haka ne Baba, bata da shi" ta cigaba "kuma tayi babbar asara na jefar da yaron nan da tayi. Yaron kirki ne, jarumi ne, bana jin gabaki dayanku wadanda bata yar din ba bana jin a cikin ku akwai wanda ya kai shi, bana jin akwai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login