Showing 105001 words to 108000 words out of 300844 words

Chapter 36 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2097

haka ni banga tsibbu a cikin abinda yake yi ba, besides, burika na suna ta cika tunda yanzu gashi yayi min albishir cewa Alhaji Ahmed ya kusa aikoda kudin aurena, daga na shiga gidan na haifa masa yaya shikenan gidan ya dawo hannu na matar sa sai dai ta bini da kallo kawai" suka yi dariya tare, Ruqayyah tace "Allah ya bada saa, amma nikan ba dani ba" suka yi sallama Ruqayyah ta karasa gida.

A compound din ta hango Hassan da Hussain suna tsaye suna ta magana suna dariya, daga gani suna cikin murna ne. Tana zuwa Hussain yace "yauwa gata nan ta karaso, shawara nake bashi cewa ya ke turo ki kullum kina zuwa kina gaishe ni ko Allah zai taiamake ku ku haifi yaya masu kama da ni, kin dan ni din fa kyakykyawa ne" ta tabe baki tace "Allah ko? Ni dai ban gani ba" yace "ohh baki gani ba? Zo muje in nuna miki" ya wuce gaba zuwa part dinsa Hassan yana binsa a baya yana cewa "kar kasa matata a cikin maganar nan walllahi ranka zai baci. In ka sake kayi forcing dinta tace ka fini kyau ko? Ni kadai nasan me zanyi maka" suka shiga palon Hussain, Ruqayyah ta tsaya daga bakin kofa dan bata taba shiga gurin ba sai yau. Ya juyo yana kallonta yace "common in, ki fadi kuma tsakanin ki da Allah waye ya cinye hoton nan" ta shigo tana kallon hoton da yake nuna wa.

Su biyu ne a hoton, kamar kuma a wannan palon akayi saboda taga kujerar irin ta palon ce, Hussain yana zaune akan kujera ya harde kafafunsa fuskarsa da murmushin da yake bayyana dimple dinsa, Hassan a tsaye a bayan sa, ya dora guiwar hannunsa akan kafadar Hussain looking as serious as ever. Ta danyi murmushi tana rarraba ido tsakanin fuskokin su, ita sai yanzu take kara tabbatar da kamannin da suke yi sai dai banbancin fatarsu tana boye kamannin nasu. Ta jiya tana kallon Hassan ya bata rai yace "don't say it" tayi dariya tana kama hannunsa "me zance? Ai ko makaho ya shafa yasan mijina yafi na kowa kyau" Hussain yace "kin dai so kanki kawai" ta dauke idonta daga kan hoton tana kallonsa yace "ka manta da maganar hausawa da suka ce so duka so ne amma son kai yafi?" Hassan ya zagayo tabayanta ya tsaya suka jeru shima yana kallon hoton yace "gobe za'a kawo mana namu, this is just a sample. Hussain ne ya saka aka yi mana wai za'a kafe a duk kamfanonin sa dan kowaya shiga gurin yasan su waye masu gurin" ya karasa maganar yana dora habarsa a kafadarta. "Kin san halin kanin naki". Ta dan yi murmushi a ranta tace "kai zaka fada amma ni ban isa in fada ba sai aji haushi a gaya min magana".

Bayan sun koma part dinsu ne Aunty ta aiko musu da abincin dare da kuma sakon cewa cook dinsu zata fara zuwa gobe. Suka zauna suka ci abinci yana tambayar ta ya mutanen gidan su suke, tana yi masa bayani amma hankalin ta yana kan maganganun wannan mai duban, yace dama zata same ta wadda zata iya zabar abu daya cikin biyu, ko dai ta zabi yin kudi fiye da kudin da take saka rai ko kuma ta zabi xama a karkashin masu kudi, bata bukatar amsa tasan idan lokacin yazo wanne choice din zata dauka, tabbas tasan kudi zata dauka dan shine babban burinta a duniya amma kuma abinda bata sani ba shine yadda zabin zai zo mata, yace zata yi rayuwar kadaici, wanne irin kadaici yake nufi? Indai kuwa har zata yi kudi to kuwa ai babu zancen kadaici saboda tasan mutane kamar magnet suke da kudi, duk wanda yake da kudi shine yake da mutane, misali Hussain da Fatima kullum gidan su a cike yake da mutane saboda suna da kudi, ita ma in ta samu irin wannan haka nata gidan zai ke cika irin nasu. To kuwa in dai abinda ya fada gaskiya ne then bata bukatar bata lokacin ta gurin korar Fatima ko raba Hassan da Hussain ko duk wani abu da yake on agenda din ta. But ita kanta tasan ba komai da yan duba suka fada ne yake zama gaskiya ba, kuma tasan yadda da abinda suka fada shirka ne saboda babu wanda yasan abinda gobe take tafe da shi sai Allah.

Washegari weekend, haka kawai Hassan ya tashi da aikin gyaran gida, sai yau ya gama kwashe kayansa daga tsohon dakinsa ya kuma shirya komai tsaf a dakinsa na yanzu. Ita dai tana ta binsa a baya tana yi masa hira har ya gama sannan suka yi wanka suka zauna breakfast. Bayan sum gama ne ya dauko littafi karami da biro ya zaunar da ita ya rubuta wasu adadin kudi a jiki yace mata "jiya anyi mana salary, wannan shine salary na" ta kalli numbers din mentally tana calculating abinda zata yi dasu ranar da tayi kudin da take saka rai, sannan ta kirkiro murmushi tace "masha Allah, Allah ya sa musu albarka" yayi murmushi yana jin dadi yace "ameen Precious. Yanzu kinga lissafi na shine, 50% zan ajiye, su zanke tara mana na ginin gidan mu" sai kuma ya shafa kai yana kallonta da murmushi a fuskarsa yace "though, ga babies kuma a hanya, but we can manage kudin su isa har hidimar babies din" ya cigaba da rubutu yace "20% zamu siya daily needs din mu, komai na bukatar gida da kuma personal needs din mu for a month, 10% zamu kaiwa Baba, 10% percent kuma ina so in bude miki account sai kike ajiye wa kema duk sanda kike bukatar wani abu sai dai kawai ki dauka ba sai kin tambaye ni ba. Ko zaki yiwa wani kyauta ko dai wani abu mai muhimmanci haka, kamar harkar makarantar su Zunnur zaki yi musu out of your pocket. Ragowar 10% din kuma sai mu ajiye a gida in case of emergency. Ya kika gani? Lissafin yayi?" Ta cire tagumin da tayi tun da ya fara lissafin sannan tayi murmushi tace "gaskiya baiyi ba, kusan komai a kaina zai kare? Kai kuma fa? Ni banji ka ware wasu kudade kace naka ba ne ba" ya dago kai yana kallon ta fuskarsa cike da yana yin da yake nuna yaji dadin maganar ta har cikin zuciyarsa yace "don't worry about me, kin manta all that 50% yana gurina? Sannan kuma already ina da kudade a account dina zan iya dauka inyi duk bukatu na. Ke dai kawai kiyi managing wanda zan baki. Kar kike siyan unnecessary things. Kin san yadda nake siyayya ta?" Ta girgiza kai yace "duk abinda na dauka zan siya sai in tambayi kaina "do I really need this? Can I live comfortably without this? Ko kuma da akwai wani abu da nake bukata more than this? Idan har na tabbatar bana buƙatar abin sai in ajiye shi inyi gaba. That is how I avoid unnecessary spendings" tayi dariya tace "nima na koya to, haka zan ke yi" ya shafa fuskarta yace "good girl" sai ya mike tsaye yana cewa "monday sai muje a bude miki account din ko? Bara in shirya in an jima zan kai su Hussain airport" tace "airport? Ina zasu je?" Ya juyo yana kallonta yace "Thailand zasu je, zai ji signing wani contract ne da wani kamfanin shinkafa a can" ya juya ya shiga ya barta da sakakken baki "kuturin kare! Wato mijin wata yana can yana daukan matarsa tana rakashi business kasar waje ni nawa yana lissafa min albashin sa a takarda?" Sai taji duk ranta ya baci, taji ta raina albashin nasa gaba ki daya ko da kuwa gabadayan sa zai bata.

Tana nan zaune har ya fito, yana daura agogo yana cewa "so nake in shiga gidan Aunty muyi rigima da ita, dama na gaya mata aure ba zai zaunar da Hussain a gida ba, in yayi auren ma daukan matar zai ke yi suna tafiya tare" sai kuma ya lura da chanjawar yanayin ta, yace "what's wrong?" Ta dago kai tana kallonsa, tace "babu komai, kawai dai zanyi missing din su ne" yayi mata murmushi sannan ya durkusa yayi kissing goshinta yace "kar ki damu, I will be here to keep you occupied" ya kashe mata ido, tadan dungure masa kai kadan ta juya baya tare da kwanciya akan kujera. Ya tashi yana dariya yace "sai na dawo. Please ki rubuta list din duk abinda muke bukata a gida kafin na dawo. Make sure you include everything. Ni kuma in na dawo zan biya in kaiwa Baba nashi kudin".

Yana fita taja tsaki. "Ni bansan wanne iyayin ne ma yasa Hussain ba zai dauki driver ya kaisu airport din ba sai yasa Hassan ya kai su sai kace wani yaron su" ta sake tsaki tana jin bacin ranta yana karuwa, sai kuma ta mike ta shiga daki ta dauko hijab ta saka ta fita. A part din Aunty ta same su suna ta magana suna dariya har da Fatima, ta gaishe da Aunty da take rike da hannun Fatima sannan ta gaishe da Hussain tare da yi masa fatan alkhairi. Tace da Fatima "yanzu kuma shine zaku tafi ko sallama babu?" Fatima tayi murmushi tace "ban san baki san da tafiyar ba ai, tun jiya nake ta zuba idon ganin kin shiga munyi sallama" Ruqayyah ta juya ido, wato ita ba zata shiga tayi mata sallama ba saboda ita yar sarki ce.....

Lokaci ya cigaba da tafiya, Ruqayyah ta lullube kanta da barguna na mutum mai kirki ta yadda a gurin Hassan ta zama the best wife he could have ever asked for, sometimes tana dan kwace mata ta dan saki baki haka ko tadan nuna halin ta kadan amma sai tayi saurin basarwa, shi kuma in hakan ta faru yana dangana hakan ne da maganar da Baba ya gaya masa na cewa Ruqayyah tana da zuciya tana kuma da saurin fada. Dai ya dage wajen ganin duk abinda tayi ba dai dai ba sai ya nuna mata ya kuma gyara mata ya gaya mata wanda zata yi dai dai din. Tsakanin ta da mutanen gidan kuma dai mutunta juna, duk da ita ta sani suma kuma sun san cewa ta sani sunfi son Fatima akanta saboda Fatima ta fita sakin jiki da su kuma ta fita kyauta. A tsakanin lokacin ne kuma Sumayya da Adam suka samu admission a tare suka fara zuwa makaranta, Hussain ne ya dauki nauyin komai na Adam, Baba kuma yabiya na Sumayya duk da cewa Adam ya so ya biya mata amma pride din Baba ya hana ya barshi ya biya din. Shigar su makaranta tare ta kara shakuwa a tsakanin su ta yadda har sai da Inna tayi wa Sumayya magana kan cewa ya kamata ta rage alakar ta da Adam saboda shaidan ya kan iya shiga even the most purest of hearts, wannan ya dan taka musu birki kadan, amma kuma bai rage musu kaunar junan su ba ko da da kwayar zarra. Sai dai har yanzu bai fito officially neman aurenta ba saboda bai san ta inda zai fara ba, bai kuma san ko za'a bashi ita da considering ko shi waye, duk da dai bai taba ganin kyama ko kiyayya a idon Baba ba.

Bangaren Hussain da Fatima soyayya sai abinda ta karu, amma kuma even after months da bikin su babu ciki, abin yana ransu duk da cewa a tsakanin su babu wanda ya taba furtawa dan uwansa damuwarsa akan hakan, sai dai kullum suka zauna sai sunyi zancen haihuwa, har list ne dasu na sunayen da zasu saka wa ƴaƴan su, in an samu wani sunan kuma sai a kara sannan a rage wani. Da wahala su zauna tsahon wata daya a Nigeria, kullum Hussain yana tafe harkar neman kudin sa kuma duk inda zai je Fatima tana gefensa.

Ruqayyah ciki ya girma. Tun kafin ya tsufa kusan duk wanda ya santa ya san tagwaye ne a cikin ta kuma babu wanda yayi mamakin hakan saboda daga ita har mijinta duk hakan ne, sai dai duk yadda Hassan yaso ta yarda a duba musu gender din babies din kin yarda tayi tace babu kyau, amma a cikin zuciyarta tana tsoron abinda zata gani ne, idan maza ne to maganar wannan mutumin mai duban nan zata tabbata kenan idan kuma mata ne to sauran maganar sa ma zata kasance karya ce kenan kuma hakan yana nufin dole ta sake sabon shiri dan ba zata iya cigaba da wannan zaman ba kullum cikin bakin cikin yadda Hussain da Fatima suke bushasha da kudi ita kuwa tana faman lissafi.

Hassan yana ta fama da tarin kudin siyan kayan babies yana lissafin nawa ne zasu isa nawa ne ba zasu isa ba sai gashi rana daya Hussain da Fatima sunyi wata tafiya suka dawo musu da komai da ake bukata na haihuwa. Komai da komai, tun daga kan crib har kan diaper kuma komai na twins. And knowing the Hussain we know, komai na zamani ya siya kuma komai mai tsada. Rashin sanin gender ya saka suka siyo gender neutral, suna dawowa aka shiryawa babies din nursery dinsu a kasa using grey color da theme na forest. Duk rashin godiyar Ruqayyah sai da tasan cewa sun kyautata musu dan dakin babies dinta ko a films ita dai bata ga irin sa ba, hatta nata kaya bukatun na haihuwa an siyo mata, sannan Hussain yace Fatima ta tambayeta in akwai wani abu kuma daban da take bukata ta fada ayi mata. Sai kuma yayi suggesting in watan haihuwarta yayi a fita da ita waje ta gaihu a can dan tafi samun medical care mai kyau.

Tashin farko Hassan yace a'a "idan masu kudi suna fitar da matan su waje in zasu haihu ka gaya min ta yadda za'a gyara asibitocin kasar nan" Hussain yace "ohhh. Takan matarka za'a fara misali kenan? Sai ka bari idan matar president ta haihu a Nigeria sai kaima taka ta haihu a nan, at least sai in san footsteps din shugabanni kake bi" Hassan yace "ni ban damu da shugabanni ba fa, ni kaina na sani and I know that I can make a difference. Idan da kowa a Nigeria zai saka a ransa cewa zaiyi making a difference, zaiyi setting good example, dana tabbatar abubuwa zasu yi mana sauki a kasar nan" Hussain yace "to Allah ya bada saa good samaritan, ni dai duk ranar da matata zata haihu to sai na samu asibitin da yake one of the best a duniya sannan zan kaita ta haihu" Hassan yace "a dawo lafiya, mu muna nan kuma in dai an haihu lafiya din ai shine abinda ake nema"

Duk da cewa a tare take da Aunty, ga kuma yaran da suke gidan ta amma da watan haihuwar yazo sai da Hassan ya roki Baba akan cewa Sumayya ta dawo gidan su da zama saboda ba'a san sanda haihuwar zata zo ba. Allah yasa su Sumayya suna hutun semester dan haka ta taho din dan itama tana son ayi komai a gabanta da inda hali ita mai iya karbar wa yar uwarta wani part na ciwon haihuwar ne. Tare suke wuni da rana, da dare kuma Ruqayyah ta tafi gurin mijinta su kwana tare, wanda duk juyi sai ya tambaye ta ko akwai abinda take buƙata. Da ranar ma kuma haka Sumayya take lallabata tana koya mata irin abubuwan da take koyo a makaranta da kuma abubuwan da suke haduwa suyi browsing tare da al'amuran da suka shafi ciki, haihuwa da kuma prenatal. Suka yi installing wani application mai suna Baby Center wanda yake taimakawa masu juna biyu sosai gurin tracking cikin su sunan kowanne stage da kuma abinda ya kamata suyi expecting a stage din, akwai tips na abubuwan da zasu kara wa mai ciki lafiya da kuma abinda ya kamata ta guda wadanda zasu iya harming dinta ko abinda yake cikin ta. Sannan kuma akwai signs and symptoms na labour, yadda mace zata banbance true labor da false labor, yadda zata ke timing contractions dinta dan tasan how far along in labor take da kuma yadda zata ke counting baby kicks dan ta tabbatar da lafiyar abinda yake cikinta. (Try using it in kina da ciki, am sure zaki ji dadin app din)

Sanda Sumayya take yi mata wannan bayanin sai Ruqayyah ta tabe baki tace "they are always kicking, bana jin ina bukatar wannan". Wannan ilimin data samu ya saka laborn yana zuwa ta fahimci shine, anan ne kuma hankalin ta ya fara tashi tana jin tsoron wahalar haihuwar amma kuma bata jin tsoron mutuwa "in na mutu a haihuwa nayi mutuwar shahada kenan"

Tun safe ta fara, ita da Sumayya suna ta timing contractions din suna son sai ciwon ya fara zuwa kurkusa sannan zasu fada wa Aunty, dan haka wajen azahar Sumayya ta kira Aunty ta gaya mata, ai kuwa sai gata da kanta tazo, tana ganin yadda Hassana already ta fara shan wahala sai ta kamata da kanta ta saka ta a mota, Sumayya ta debo kayan da suka hada a jaka na zuwa asibiti suka tafi, dama Hussain da Fatima basa kasar a lokacin. Duk sun dauka ba zasu dade a can din ba Ruqayyah zata haihu amma sai gasu har magrib, dole suka kira Hassan suka gaya masa dan kar yaje gida ya tarar basa nan, amma duk da haka aunty tace kar a gaya wa Inna saboda kar hankalin ta ya tashi gwara a bari sai ta haihu tukunna a kira ayi musu albishir.

Karfe goma sha biyu na dare Ruqayyah ta haifi santalelen jaririnta namiji, bayan ta leka lahira ta dawo, karfe daya na dare kuma ta haifi na biyu, shima namiji, dukkanin su masu kama da baban su da yake tsaye a bakin kofa cikin dimuwa yana jira.


Sorry for the typos


Wannan littafin na siyarwa ne, idan kin ganshi a wani gurin na sata ne, in kina son ki karanta halaliyar ki ki neme ni through WhatsApp ta wannan number din 08067081020

*Unveiled*

Bakin Aunty har kunnen ta saboda murna, aka miko mata na biyun ma ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login