Showing 264001 words to 267000 words out of 300844 words

Chapter 89 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2043

karkarwa. Babu Lukman a kusa da ita, dama ita kanta ba zata iya tuna rabon da su kwana tare ba. Ta zauna a saman gadon tana addu'a tare da goge gumin daya jika mata fuska, a ranta tana rarrashin kanta tana tunawa kanta cewa memory ne kawai. But ita bata gane last karar bindigar da taji ba, dan babu shi a memory din nata.

A lokacin taji an bude kofar dakinta an shigo kamar daga sama, bata fahimci ne yake faruwa ba taji an daga ta an dora akan wheel chair dinta sannan roughly aka tura ta zuwa palo, sai a lokacin ta fahimci me yake faruwa, sai a lokacin ta lura da maza kusan su goman da suke zagaye da ita fuskokin su rufe da bandana hannunsu dauke da mugayen bindigogi.


Tana gurin aka shigo da Sa'adatu wacce take a tsananin rude, tana zuwa ta tafi ta rungume Ruqayyah tana kuka, amma babu Sa'ad babu labarin sa a gurin, suka sakawa Lukman bindiga aka suka tafi dashi dakin sa suka tirsasa masa ya bude safe box din ya dauko musu jakar, daga nan kuma suka zagaya duk ɗakunan gidan da suke a bude suna dauko duk wani abu da suka san yana da tsada. Ruqayyah ta jima bata ga tashin hankali irin na lokacin ba, ta rasa da mamakin wannan uban kudin da aka fito dashi daga dakin Lukman zata ji ko kuma da bindigogin da ake ta waving a fuskarta, ko kuma da Sa'adatu data kankame ta tunda suka shigo tana cewa ta ceceta zasu kashe ta. Ko kuma da rashin ganin Sa'ad ko sanin halin da yake ciki?

Ta kara jawo Sa'adatu jikinta tana rarrashin ta "kiyi shiru ƴata I am here, babu abinda zai same ki kinji" for the first time tana jin zata iya bayar da komai da take dashi dan ta tseratar da ƴaƴan ta. Sai dai kuma wannan wani alkawari ne ta dauka wanda bata san cewa ba zata iya cika shi ba. Ba zata iya protecting yarta data girma ta shaku da ita ba daga hannun yan fashin, kamar yadda Fatima bata iya protecting danta daga nata hannun ba. Bata fahimci haka ba sai da taga shugaban yan fashin yayi signing cewa a dauki Sa'adatu a shigar masa da ita daki.

Wannan shi ya zamanto tonon asiri ga Sa'ad, wanda shine ya gayyato kuma yayi leading yan fashin har cikin gidan su, sai yanzu kuma yace ba yarda ayi raping sister dinsa ba. Ba Ruqayyah kadai ba, hatta Lukman da Sa'adatu sai da suka rude da ganin Sa'ad a cikin yan fashin "Ba haka muka yi daku ba, ni kudi kawai nace kuzo ku dauko mana mu raba 50/50 ni daku" sai Ruqayyah taji maganar tayi mata kama da yadda Hassan ya bata labarin abinda ya faru da kidnappers dinsa, mafarkin ta ya dawo mata a ranta.

Rokon Sa'ad bai samu karbuwa ba, duk suka fara yi masa dariya, ogan yace "and you think ana alkawari damu? Ka ka dauka in mun dauki kudin da gaske zamu baka? Da gaske kuma zamu barka da rai ka tona mana asiri?" Sai Ruqayyah ta tuna da abunda ya faru ranar da ta hadu da Hassan, ta tuna cewa harbi uku akayi a ranar and she silently pray cewa yau ba za'a yi ko daya ba, cewa ba zata rasa dan ta ba. Haka suma yayan a zuciyoyin su duk addu'ar suke yi

Amma addu'ar su bata karbu dan bata daga cikin adduoin da ubangiji yake karba tun da tun daga abincin da akaci aka samu maniyin da akayi cikin su dashi har zuwa sutturar da take jikinsu duk na haram ne, kowacce gaba ta jikin su an gina ta ne daga haram, to ta yaya za'a amsa musu addu'ar su?

A gaban idon Ruqayyah babban yan fashin ya daga bindigar sa ya auna Sa'ad da ita, ta kwalla kara da karfi, sai dai fitar karar tata tayi dai dai da yunkurawar da Sa'adatu tayi daga jikin ta ta shiga gaban Sa'ad, kuma hakan yazo dai dai da tashin bindigar. A tsakiyar goshin Sa'adatu. Wadda ta mutu ba tare da ko shurawa tayi ba, sai gangar jikinta ya zame ya fado jikin Ruqayyah da take zaune akan wheel chair dinta. Ta saka hannu ta riko kanta tana kallon fuskarta da jini ya wanke, tana kallon dan karamin ramin da bullet din yayi a tsakiyar goshinta, sannan tana kallon idanuwan ta da suke kallon ta itama, irin kallon da Minal tayi mata bayan ta mutu a accident.

"Sa'adatu" Sa'ad ya fada cikin kara, sannan ya kwace daga hannun wanda ya rike shi ya taho da gudu zai rike yaruwarsa sai dai kafin ya karaso Ruqayyah taji wani karar harbin, jininsa ya watsu a fuskar Ruqayyah, sannan gawarsa ta fado a kan cinyarta, a saman gawar yaruwarsa. Ta dago kai tana kallon yan fashin, kunnuwan ta suna amsa kuwwa da kalmar Allah ya isan da Fatima tayi mata, sannan bakinta yana motsi a hankali tana addu'ar Allah yasa bullet na uku ya kasance a cikin kanta. Amma sai taga sun dauki jakar kudin da sauran kayan da sauri suna fita ba tare da ko second look at her ba.

Sai da suka gama fita sannan ta mayar da dubanta ga gawawwakin ƴaƴanta, ta rintse idonta tana so hawaye ya zubo mata amma babu shi babu alamun sa. Ta rasa me yasa take tuno wa da kidnappers din Hassan, kuma take ji a jikinta kamar harbi uku za'a yi a yau? me yasa take jin sai an kara yin harbi daya sannan mugun daren zai kare?

Lukman ne ya dawo da ita hayyacin ta ta hanyar jijjiga yaran da suke kan cinyarta yana kiran sunayensu amma ko ba'a gaya mata ba tasan ba zasu kuma amsawa ba har abada. Lukman ya mike tashin hankali rubuce a fuskarsa ya hau sama da sauri. Shi a gurinsa ba yaya kadai ya rasa ba, ya rasa everything, dan duk wani abu mai daraja wanda zai dauku yan fashin sun dauke, kudin daya debo sun kwashe sai share din kamfani, sai kuma sauran kudin da ya rage a cikin account din Ruqayyah. Yadda yake ganinta din nan kuwa baya jin zata wuce ranar nan musamman saboda ciwon zuciya da hawan jini da take fama dashi, with his children dead, in ta mutu abinda zai samu bashi da yawa considering sauran yayanta.

Check book ya dauko da biro a dakinsa, a gefen gado yaga bindiga, daga dukkan alamu a wadanda suka shigo ne suka manta ta, ya dauka ya saka a aljihunsa ya fita, blindly ya kuma saukowa kasa inda har yanzu take zaune a kujerar guragu da gawawwakin ƴaƴanta a kan cinyarta ta cire hearing aid dinta ta jefar. Ya mika mata check book din sannan ya auna ta da bindigar hannunsa yana nuna gurin signing yace "sign here" ta bishi da kallo, her heart breaking into thousand pieces. Automatically tayi signing a inda ya nuna mata tana tunawa da threats din data yiwa Hassan dan ya bata kudi, tana tuna wa da maganar Hassan da yace "this money is going to be the death of you" ta mika masa tana cewa "this money is going to be the death of you". Ya karba da sauri ya saka a aljihunsa, niyyar sa sai ya fita zai duba sauran abinda ya rage a account din ya kwashe.

Sai kuma taga ya daga bindigar and while looking into her eyes ba tare da ko digon soyayyar ta ba a cikin zuciyarsa ya sakar mata third bullet din da take jira, a wuyanta. Sannan ya juya da gudu ya fita. Baya son yayi taking risk din cewa zata rayu ta tona masa asiri.

Komai daren dadewa, whatever goes up most come down......

Bar ganin lokaci yana tafiya, bar ganin kamar kowa ya manta, hakkin wani will eventually destroy you........

Your karma will eventually catch up with you........

Wannan littafin na siyarwa ne, idan kika ganshi a wani gurin na sata ne, in kina son ki karanta halaliyar ki kiyi min magana ta wannan number din through WhatsApp 08067081020

*Ina masu bukatar hadadu kuma ingantatun turarukan wuta da khumra masu dadin kamshi kuma a farashi me sauki to ga dama tazo muku Awwaba scent nada turarukan wuta humra burners kasko shisa coal dorot stool dilka body milk dadai sauransu masu bukatar na iya nemansu a whats app ko kuma kira ta wannan lambar 08034236800*
*bugu da kari duk wanda ya sayi humra ko turaren wuta a cikin wannan watan akwai kyautar dilka me kyau tafiyaya daga kasar chad wadda zata gyara jiki tay expoliating skin acikin minti 20 kawai ku garzayo dan kwasar garabasa*
*Adress kundila zoo road kano muna tura sako ko ina da iznin Allah*







*The Orphanage*

Forgive the typos please

*Have you seen my collection of abayas or are you yet to?........ Ki garzayo into my DM ki gani ki zaba ki biya a kai miki har garin da kike a Nigeria. Prices ranges from 10k _25k. Kar ki bari ayi babu ke!"*


Sumayya tana kwance tana tsakiyar baccin ta mai dadi, a kan gadon ta a kusa da mijinta a lullube da bargo. Karar bindigar da taji ne ya ratsa baccin nata ya kuma farkar da ita. Ta mike zaune a tsorace tana tunanin kamar tasan irin wannan karar, ta fara karanta addu'ar tsorata sai taji wata karar, a lokacin ta tabbatar da karar menene kuma kunnuwan ta suka tabbatar mata daga inda karar take fitowa. Tayi sauri ta kankame Hassan idanuwan ta a waje cikin tsoro. Ya bude ido cikin bacci yana kallonta, tsoron da ya gani a nata idanun ya saka ya watstsake.

"Lafiyar ki kuwa Sumayya? Menene yake damunki? Mafarki kika yi?" Cikin rawar murya tace "harbi akeyi, karar bindiga naji, yan fashi ne suka shigo" ya mike tsaye da sauri, automatically hankalin sa yana komawa kan ƴaƴan sa, musamman Amatullah da take budurwa. "Amaty" ya fada yana kokarin saka jallabiyyar sa, Sumayya ta sauko daga kan gadon tana kokarin daga labule ta leka sai ya rike hannunta, "don't" ya fada a hankali sannan ya jata zuwa bayansa shi kuma ya daga labulen kadan ya leka zuwa compound din gidan sa.

Bai ga kowa ba baiga komai ba duk da security light din data cika gurin da haske, gate a rufe amma kuma sai ya ga bai ga maigadi a gurin ba, sai da idonsa ya saba da yanayin gurin sannan ya ga mai gadin tare da securities dinsu guda biyu a lafe a jikin katanga hannayensu rike da makamai.

Ya rufe labulen da sauri, "ba gidan nan suka shigo ba, maybe makota ne* Sumayya ta rike hannunsa "eh ba a anan gidan dama naji ba ai, a makota naji, a gidan Ruqayyah naji" ya juyo yana kallon ta da budaddun ido sai kuma rike fuskarta yace "baki tabbatar ba, kina cikin bacci ne, you maybe be wrong, bara in je in bincika in gani" sai kuma ta sake riƙe hannunsa "kar ka fita fa, kar suyi maka wani abu fa, dan Allah kar ka fita" sai ya koma amma ba zama yayi ba wata drawer ya jawo ya dauko ajiyayyar bindigar sa daya dade da siya kuma ya sama mata license amma har yau bai taba amfani da ita ba, yayi checking ya tabbatar it is still loaded sai ya saka ta a aljihunsa sannan ya fita da sauri tare da rufe kofar dakin. Dakin Amatullah ya fara zuwa ba tare da bude kofar ba ya saka key yayi locking dinta ta waje sannan ya mayar da key din aljihunsa ya sauka kasa inda dakunan mazan yake, yana sauka yaji karar third harbin, a lokacin da Abdulrahman ya fito daga dakin sa da sauri shima, suka hada ido da uban sai yayi masa alama daya koma ciki amma yaki yana nuna masa shi ya koma sama. Yasan ba zai koma din ba sai yayi hanyar waje shima ya bishi a baya, Hassan yana godiya ga Allah da Hussain baya gidan da tuni ya wuce securities din ya bude gate din ya fita yana neman a inda ake harbin dan ya taimaki wanda aka harba.

A bakin gate yayi confirming abinda Sumayya ta fada, a gidan Ruqayyah ake harbin, amma kuma sai security din suka gaya masa sunji fitar motoci tun mintuna biyar da suka wuce. A take ya tambayi kansa "third harbin fa waye yayi shi?" Karar tashin motar daya ji daga gidan ne ya saka ya bude spy window din jikin gate din ya leka, idonsa ya sauka akan fuskar Lukman a lokacin da yake wuce gidan a cikin motarsa, fuskarsa cike da tashin hankali. "To ko police ya tafi kirawo wa?" Ya tambayi kansa lokacin da Abdulrahman ya karaso gurin yana janye shi daga jikin gate din. "Daddy ka koma ciki dan Allah, mu zamu fita mu gani".

Amma kafin ya bayar da amsa suka ga Sumayya a gaban su tana danna security pin din bude gate din. Kafin su rike ta har ta bude ta kuma tura ƙaramar kofar jikin gate din ta fita ba tare da tace musu komai ba, a second daya duk mazan uku suka fita suma ita kuma a second daya tayi hanyar gate din Ruqayyah, sai a lokacin ta lura ko hijab babu a jikinta, gate din a hangame yake babu kowa a gurin, daga inda take tana hango compound din gidan shima bata hango kowa a ciki ba, zata shiga kenan Hassan ya rike ta samarin kuma suka shiga gabanta, Hassan yana magana a hankali yace "menene hakan? Kika san ko suna ciki?" Ita kuma tace "basa nan sun fita, naga fitar su a mota, naga fitar Lukman a mota, my sister is injured dan Allah ka sake ni inje gurinta" yaki cikata sai ta fara kalla kira "Ruqayyah! Ruqayyah!" Hassan ya rufe mata baki yana tsorata da yanayin ta, yace "shshsh, zamu shiga yanzu amma kiyi shiru"

Ya damka ta a hannun Abdulrahman yace "rike ta, ku tsaya a waje gabaki dayan ku zan shiga in gani" amma ko rabin compound din bai kai ba yaga mazan sun biyo shi da sauri, ba zasu bar babansu ya shiga cikin danger ba, zasu tare masa kamar yadda shi kuma zai iya tare wa Sumayya yayinda ita kuma take jin zata iya tarewa kowa daga cikin su. That's what family means.

Jin sun biyo shi ya saka ya kara sauri ta yadda ya kasance shine na farko daya fara shiga cikin falon, hannunsa rike da bindigar sa, a lokacin ne idon sa ya sauka akan tashin hankalin da yake jin bai taba ganin irinsa ba idan ba'a media ba. Uwa, gurguwa kuma kurma, a zaune akan kujerar guragu kafarta daya mai lafiyan a kasa dayar kuma shanyayyiya a makale a gefen kujerar, yayanta twin teenager a kwance a jikinta daya akan daya, jini a zagaye dasu, babu alamar rai a jikin duk su ukun..

Farko sandarewa yayi a tsaye, yanajin shekarun sa suna sauka akan kafafunsa, sai kuma yaji karfi yazo masa, ya juya baya da sauri lokacin da Sumayya take kokarin ture yayanta ta shigo, sai ya saka hannunsa biyu ya tura su baya gabaki daya ya rufe kofar tare da murda key din daya gani a jiki. Sai kuma ya same ya zauna a jikin kofar yana jin yadda Sumayya take kuka tana buga kofar. In no way zai barta taga Ruqayyah a haka because he can't imagine seeing Hussain like that, yasan da yanzu yana lahira ko gidan mahaukata. Yana mayar da numfashi ya daga murya yace "take your mother home and lock her up. Call the police"

Yana jinsu suna rigima da Sumayya, daga baya sai yaji shiru da alama daukan ta sukayi suka fita da ita. Ya mayar da dubansa kan Ruqayyah, daga inda yake zaune yana hango yadda jini yake fita daga wuyanta yana jika gaban rigarta tare da sauka akan yayanta. Sai ya mike ya ciro labule dakin da sauri ya tafi da niyyar lullube su, a ransa yana tuno da ranar da ya fara ganinta da kuma rayuwar da suka yi tare musamman a farkon auren su. Sai dai yana zuwa inda take ya lura da yadda kirjinta yake dagawa alamar jan numfashi, numfashin ne kuma yaje kara bulbulo da jinin daga wuyanta. Da sauri ya yar da labulen hanunsa, a lokacin da yaji an bude wata kofa a cikin falon, ya kalli gurin ya ga ma'aikatan gidan ne suke lekowa daya bayan daya. "go back inside" yayi musu tsawa da budaddiyar muryar sa, sai kuma yaga wani saurayi a cikin su yace "you, come here, get me a towel" yaron ya tafi da sauri sauran kuma suka koma ciki, wasu daga cikin su suna kuka.

Ya kama gawar Sa'ad ya sauke shi kasa ya kwantar dashi akan carpet yana jin wani zazzaɓi yana rufe shi, a lokacin ya kalli gawar Saudatu, her eyes looking at her mother, sai yaji ya kasa taba ta ya zauna a kasa hawate yana zuba da gudu daga idanuwan sa.

Abdullahi ya gani a kusa dashi, bai ma san ta inda yaron ya shigo ba amma bai yi mamaki ba saboda kasancewar sa SS officer, sai ganin sa yayi yana dauke Sa'adatu ya kwantar da ita a kusa da dan'uwan ta sannan yaga ya cire t-shirt din jikinsa ya yaga ta biyu yana kokarin daure wuyan Ruqayyah da ita. Ya daga masa hanu "akwai bullet a ciki, kar ka danna da karfi" sai ya karbi karamin towel din da yaron daya aikaya kawo ya dora akan wuyan Ruqayyah sannan ya karbi rigar Abdullahi ya daure wuyan da ita. A ransa yana tunawa da ranar data daure masa wuyansa da dankwalin ta.

Bai san hannun sa ya sauka a cinyar ta ba sai ji yayi ta rike hannun da dukkan karfinta, tamkar rayuwar ta a hannun take, yayi sauri ya kalle ta yaga idonta a rufe yake but she is still concious, "innalillahi wa inna ilaihir rajiun" ya fada yana jin wani irin imani yana kara shigar sa, wato duk wannan abin Ruqayyah tana feeling komai. Lallai duk wandabai gide wa Allah ba tabbas zai godewa azabarsa.

Sai ya kai bakinsa dai dai kunnenta yadda yasan zata ji ko


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login