Showing 282001 words to 285000 words out of 300844 words

Chapter 95 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2107

da sauri bayan tun da ta shigo gidan idonta a rufe yake. Tana kallon yadda kirjinta yake dagawa da sauri alamar numfashi take yi cikin tsoro. Amatullah ta bude kofar ta shigo, fuskarta dauke da tsoro, murna, excitement da kuma jerin tambayoyi. "Mommy shine, Amir ne, mommy kamar su daya da Daddy, har muryar, idonsu amma ba iri daya ba, Daddy ya fishi tsaho kuma, mommy fada yake yi amma bansan me yasa yake fada ba wai ke yake nema. Ke kika tura masa e-mail dinnan ai ko?"

Sai Sumayya ta zauna tare da kama hannun Ruqayyah ta rike a cikin nata, hawaye suka zubo a nata idanun kamar yadda suke zuba daga idanun Ruqayyah. Amatullah taji jikinta yayi sanyi, ta durkusa a gaban mommyn ta, "mommy lafiya? Me yasa yake fada? Me yasa kike kuka? Ji nake murna zai yi ya same mu kema kuma murna zakiyi cewa ya dawo gida" Sumayya ta juyo tana kallon ta tace "Amaty, na aika masa da sakon ne a matsayin nice Ruqayyah, ya dauka wacce ta yar da shi ce ta aika masa da sako shi yasa yake fada" Amatullah ta bude baki, ta kalli Sumayya sannan ta kalli Ruqayyah tana girgiza kai tace "mommy don't, kar ki dauki laifinta ki dora wa kanki, a zuciye yake, in yayi miki wani abun kuma fa? Ki bari in kira daddy yanzu su dawo, ki bari in jashi zuwa gida in kira su yaya A1 tunda yana gari kafin su Daddy su karaso, ko kuma in kaishi gidan Aunty"

Sumayya ta saje girgiza kai tace "Amatullah Ruqayyah is dying, laifin da tayi wa yaron nan yana da girma, ba wai ina so in dauki laifinta in dorawa kaina bane ba tunda ba zan iya haka ba, bansan ta inda zan fara ba amma ina fatan zai yafe mata ne kafin ta bar duniya" Amatullah ta fara girgiza kanta, hawaye yana zuba daga idonta, Sumayya tace "Amatullah hakkin Amir ba zsi bar Ruqayyah ta kwanta a kabarin ta lafiya ba. Ki taimaka min.. " ta mika mata littafin da yake kusa da ita, "ki ce masa gashi wannan in ji ta tace yaje ya karanta sai ya dawo suyi magana. Kar ki kira babanki, ki barshi ya karanta yazo kuma ya ganta kafin su dawo" Amatullah ta karbi littafin tana goge hawayenta, idonta akan Ruqayyah da taga lokaci daya ta koma kamar yarinya yar shekara goma saboda kankancewar da tayi. Ta tuno da Sa'adatu da kuma Sa'ad, ta tuno da Inna Ade da Baba. Sai ta juya ta fita da littafin a hannun ta idonta yana zubar da hawaye.

Sumayya tana jin duk abinda ya guda na a tsakanin su, kum ta tabbatar Ruqayyah ma taji, sannan kuma taji fitarsa daga gidan ta fahimci yana da zafin zuciya amma kasancewar ta zauna da masu zafin zuciya har biyu, Ruqayyah da Hassan, ta san suna da saurin saukowa, daga sun gama hayagagar fadansu shikenan zasu huce, amma kuwa anya Amir zai huce kuwa? Anya abinda akayi masa duk saurin saukowar mutum zai sauko da wuri kuwa?

Bayan tafiyar sa Amatullah ta dawo dakin, ta jingina da jikin bango tana kallon twin sisters din, one dying and the other one looking after her dying sister. Sai ta dauko wayarta tana ta jujjuya wa a hannun ta tana tunawa da cewa babanta yana can yana bulayi a Abuja yana neman mutumin da ita kuma yanzu ta rabu da shi. Anya kuwa in tayi haka tayi dai dai kenan? Amma kuma in ta kira shi bata kyautawa mahaifiyarta ba kuma kamar ta hada su rigima kenan.

Neman wanda zata gaya wa maganar tace yi, irin abun farin ciki ya same ka kana neman wanda zaku yi murna tare amma kuma tana gudun batawa mahaifiyar ta. Dan haka ta cigaba da zama wayar ta a hannun ta tana shige da fice a kafofin sadarwa amma bata da damar isar da sakon da zai faranta ran mahaifinta.

Sai dai, cikin lokacin da bai wuce awa daya da rabi ba Lami ta dawo ta kuma yin sallama tare da sanarwar cewa bakon daya fita dazu ya dawo. Akayi kallon kallo tsakanin Amatullah da Sumayya. Har ya gama karanta littafin kenan? Amatullah tace "mommy har ya dawo wai, kince yaje ya karanta ya dawo kuyi magana kuma gashinan har ya dawo" Sumayya tace "ah ah, bai karanta ba, isa ace har ya karanta ba, amma me ya dawo dashi?" Amatullah tace "mommy na gaya miki a fusace yake wallahi, ina jin tsoro fa, ki bari in kira wani in hada shi da shi yadda zasu fi fahimtar juna"

Lami ta sake knocking kofar tace "ace masa ya shigo?" Sumayya ta rintse idonta ta bude, gidan ubansa ne or rather gidan sa ne, babu yadda zata yi ta barshi a waje yana jira tace "ya shigo, a shigo da shi" sai Amatullah tayi sauri ta bude kofar ta fita, ita duk bata yarda da wannan dawowar ta Amir ba. Kafin ta fita Lami ta fita, sai ta jira ta tana dawowa tace "Lami taimaka min kije gidan Aunty, ki ce mata ina neman taimakon ta, ki ce mata ina nan gidan nan" Lami tace "akan bakon nan da yazo ne ko? Nima duk ban yarda da yanayin sa ba" Amatullah tace "bana son tsegumi Lami kije kawai kiyi abinda na saka ki"

Lami ta fita da sauri, a dai dai lokacin da Amir yake shigowa da mota cikin gidan, mai gadi ya tambaye ta "wannan bakon an san shine a cikin gidan kuwa? Ni ban yarda da yanayin sa ba. Ina aka aike ki kuma?" Lami tace "ina ruwanka? Ni bana son tsegumi" ta wuce zuwa gidan Aunty da sauri.

Sai da Amir yayi kokarin tsayar da karkarwar jikinsa sannan ya bude kofar motar ya fita tamkar an harba shi da kibiya yayi hanyar da yabi zuwa cikin gidan dazu. Bai rufe kofar motar ba kamar yadda bai rufe kofar palon ba bai kuma kula yarinyar dazu ba data fara yi masa magana tunda ya shigo palon dan bai ma san me take cewa ba. "Where is she?" Ya sake cika gidan da hargowa, sai kuma ya doshi dakin da yaga Amatullah ta shiga dazu ba tare daya jira komai ba ya murda komar ya kuma tura.

Sumayya ta saki hannun Ruqayyah ta mike tsaye tana facing dinsa, shima ita yake kallo dan bai ma dauka da akwai mutum akan gadon ba. Cikin mamaki yace "you?! Aka ce ba kya tafiya kuma ba kya magana? Karya dama akeyi min kenan?" Ya juya yana kallon Amatullah da ta ke tsaye a bayansa. Sannan ya sake kallon Sumayya wadda ta kasa dauke idonta daga kansa tana tasbihi ga ubangijin halitta, gashi dai kana kallon sa direct xaka ce yana kama da Hassan amma yanzu da yake tsaye a gabanta yake magana sai take ganin kmaar Hussain ne yake yi. Tayi murmushin da ita kanta tasan duk da cewa tana cikin rudani a yanzu amma har cikin zuciyarta yake, tace "welcome home son"

Sai yace mata "ke ce Ruqayyah? Wacece Ruqayyah?" Sumayya ta kalli Ruqayyah da take kwance tana kallon sa, idanunta kamar zasu fado waje dan tsoron da suke bayyana wa tace "baka karanta littafin dana baka ba, daka karanta da ba zaka tambayi wacece Ruqayyah ba" ya takonzuwa tsakiyar dakin yana jin kamar ya faffalla mata mari yace "na karanta iya kacin inda na karanta" ya kalli inda take kallo sannan ya lura da mutum a wajen sai ya kuma kallon Sumayya lokaci daya yana lura da kamannin su duk kuwa da irin lalacewar da Ruqayyah tayi, yace "a cikin ku wacece Ruqayyah? Wacece Ruqayyah nace! Wacece ta dauke ni a ranar da aka haife ni ta raba ni da iyaye na har na tsahon shekaru talatin da biyar?!" Ya karasa cikin tsawa, Amatullah tazo ta sha gabansa tace "yaya Amir, daka karanta labarin da mommy ta baka da baka bukaci sanin ko wacece Ruqayyah ba, da ka fahimci cewa babu wani fushi daya rage maka wanda zaka huce akanta, babu wani abu da ya rage wanda zaka yi mata wanda Allah bai riga yayi mata ba. Da ka fahimci irin fushin da ubangiji yayi da ita saboda taba ka da tayi. Daka fahimci cewa duk wannan abin da kake yi is not necessary kamar kana nuna rashin godiyar ka ne ga ubangiji, kamar........"

Daga ta yayi chak daga gabansa ya ajiye ta a gefe sannan yace "shut your mouth" ya taka har gaban Sumayya yana kallon fuskarta, a cikin fuskar tata ya hango alamun gaskiya da kuma kamala, daga alama tana cikin rayuwa mai kyau, shi kuma yayi imani da cewa babu wanda zai yi masa abinda akayi masa sannan ya samu rayuwa mai kyau a duniya ko kuma a lahira sai ya mayar da idonsa kan Ruqayyah, a take ya hango abubuwa iri-iri a fuskarta, duk da cewa jikinta a rufe yake da bargo amma tsoron daya gani a fuskar ta kadai ta nuna masa cewa ita ce ta aikata masa duk wadannan laifuffuka, ita ce matar da tayi snatching 35years out of his life, ta hana shi samun duk wani abu da yaya suke samu a gurin iyayensu, ta shafa masa bakin fentin da duk wankan da yayi tayi ya kasa goge wa, ita ce ta dasa masa kiyayyar matar daya kamata ace ta zamanto mafi soyuwa a gare shi a zuciyar sa, ita ce Ruqayyah, his nemesis.

Ba tare da tunanin komai ba ya daga kafarsa wadda take sanye cikin wani kafcecen takalmi da niyyar talitse mata fuskar da take kallon sa da ita. Sumayya ta rufe bakin ta da hannu bibbiyu tana hana ihun da yake kokarin fitowa karasa fitowa, Amatullah tazo ta rike shi ta baya tana kokarin janyeshi duk da cewa ko irinta guda hudu aka hada ba lallai su iya ture shi ba.

Magana suka ji daga bayansu, maganar data dakatar dashi half way from doing abinda yayi niyyar yi, ya juyo da sauri yana jin kamar ya san sautin muryar duk da kuwa a zahiri bai sani din ba. Aunty ce a tsaye a bakin kofa, hannunta rike da sandan da take dogara wa saboda taji saukin tafiya. "Hassan" ta fada tana kallon sa, amma kuma wannan ai ba Hassan bane ba, ta kara sa shigowa dakin idon ta a kansa, yayinda shi kuma ya sauke kafarsa kasa tare da juyo wa yana facing dinta sosai, yana jin abinda yake jansa zuwa gare ta yafi wanda ya ja shi zuwa ga Ruqayyah karfi.

"Hussain!" Ta kuma fada cikin mamaki tana kare masa kallo, sai ta yarda sandan hannunta, hannun yana karkarwa ta dora a fuskarsa ta sake cewa "Hussain dina" sai kuma kuka ya kwace mata. Ta jawo shi jikinta tana kuka, "Hussain" ta sake fada. Sumayya tazo ta kamata, "Aunty Amir sunansa, yaron Hussain da Fatima ne Allah ya dawo mana dashi gida" ya juyo yana kallon Sumayya da sauri, sai yanzu ne ya tabbatar da sunayen mahaifan sa Hussain da Fatima. Shi farko da tsohuwar ta shigo ya dauka ita ce Fatima din , ya dauka ita ce ta haife shi.

Sai Aunty ta sake shi sannan ta kama fuskarsa a hannun ta tana kallon sa kamar yadda shima yake kallon ta amma a ransa yana lissafin wacece wannan, ko kakarsa ce? To babar Hussain din ce ko kuma babar Fatimah? Ko ma dai wacece shi yaji har cikin ransa yana kaunarta kamar yadda ya gani a idonta cewa tana tsananin kaunarsa. Sai yaga ta cika shi sannan ta koma gefe daya ta kalli gabas sannan durkusa duk da tsufanta ta dora goshinta a kasa tana sujjada, sujjadar godiya take yi ga ubangiji daya ja da ranta har zuwa yanzu sannan kuma ya cika mata burinta na ganin tilon dan Hussain. Kuma ganin nasa ma irin wannan ganin, a nutse a kammale ba wai a wulakance a kuma tarwatse ba.

Sai yaji abin ya taba zuciyarsa sosai, dama ana sonshi har haka? Har za'ayi sujjadar godiya saboda ganin shi, wacece wannan. Amatullah ta matso kusa dashi ta tsaya tana kallon Aunty itama tace "Aunty kenan. Ita ce kakarmu" ya juya yana kallon ta yace "wacece ke?" Shi dai yaga suna kama amma kuma a iyakacin labarin daya karanta ya fahimci an yar dashi ne a ranar da mahaifinsa ya rasu. Kenan bashi da kanwa da suke same father same mother.
Sai tayi murmushi tana share hawayen ta tace "ni kanwarka ce yaya Amir" shi bai taba jin an ce masa yaya Amir ba, sai yaji wani iri. "Mahaifina da mahaifin ka twins ne" ta kalli Aunty tace "Aunty kanwar mamansu ce, amman ita ce kamar mahaifiya a gare su dan mu da muke yayansu ne kadai muka san ba ita ta haife su ba." Ya kalli aunty sannan ya dawo da kallon sa ga Amatullah dan ya fahimci tana da amsoshi a bakin ta yace "ina Fatima? Ina mahaifiya ta?" Ta lura da tension din cikin tambayar, amsar ta ita zata nuna masa ko mahaifiyarsa tanada rai ko kuma a'a, and she was so happy to answer him.

Wannan littafin na siyarwa ne, idan kika ganshi a wani gurin na sata ne, in kina son ki karanta halaliyar ki kiyi min magana ta wannan number din through WhatsApp 08067081020


*Beloved Son*

Tun daga yadda yaga murmushi a fuskarta da haske a idonta yaji abinda ya hana shi jin cikakken farin ciki har yanzu yana narkewa yana bawa farin ciki wajen zama a zuciyarsa, "tana nan da ranta yaya Amir, tana Dubai a yanzu tare da family dinta. Ba zan iya kwatanta irin farin cikin da zata yi ba idan wannan labarin ya same ta dan har yau bana jin akwai abinda take so sama da kai. Duk da ta haifi wasu yayan amma kai din na daban ne a gurin ta" ya lumshe ido sa ya bude, yana so ya kwatan to kamannin ta a zuciyarsa amma kuma ya kasa, bakin cikin sa kawai daya kasance ba yau zai ganta ba. Yana so ya cigaba da yiwa Amatullah tambayoyi amma ganin Aunty ta dago daga doguwar sujjadar ta sai ya tafi gurinta, yaga matar nan ita ma mai lafiyan ta taho gurin auntyn tana kamata ta mikar da ita tsaye.

Sai ta sake kama shi ta rike kamar mai tsoron kar ya gudu tace wa Sumayya "ina Hassan? Tun safe ya shiga ya gaishe ni yace wai zai je Abuja" Sumayya tayi murmushi tace "gurin sa ya tafi ai abujan, nemansa ya tafi da kan shi" Aunty tace "au dama an samu labari shine ni ba'a sanar da ni ba?" Sumayya tayi dariya "baya so ya tayar miki da hankali ne aunty, bamu tabbatar shi din ne ba yafi so sai ya tabbatar sai ya kai miki shi har gida" Aunty tace "to alhaki nane to ya saka yayi gajen hakuri ya tafi, gashi nan ni na riga shi ganinsa" Amatullah tayi dariya, Amir shima yayi murmushi, murmushin sa na farko a ranar, sai dai shi gabaki daya a rude yake, su waye wadancan twins din? Amatullah tace masa mahaifiyarta ce ta tura masa sako, meaning daya daga cikin su ita ce matar auncle dinsa Hassan kuma ita ce babar su Amatullah amma kuma mai lafiyan yaji Amatullah ta kira da mommy bayan kuma jikinsa ya bashi marar lafiyan ce ta jefar dashi. How is that so?

Ya juya yana kallon Ruqayyah da duk abinda suke yi tana jin su kuma tana ganin su, sai Aunty ta kamo shi, "kar ka kula ta, kar ma ka kalli inda take dan ita waccan guba ce, macijiya ce duk wanda ya rabe ta sai ta zuba masa dafinta, sai ta gurbata masa rayuwarsa, ita din albasa ce wacce bata yi halin ruwa ba. Kar ka kulata, ka barta a yadda Allah ya nannade ta ya ajiye ta a gurin ta cigaba da rayuwa a haka har sai ranar da wanda ya bata rai ya karbe kayansa" sai ta ja hannunsa suka fita daga dakin Amatullah tana binsu a baya, Sumayya ma haka, Ruqayyah ta mayar da idanunta ta rufe tana rokon Allah akan kar yabata ikon sake bude su.

A nan palon suka zauna, Aunty ba zata iya tuna rabon ta da cikin gidan Hussain ba, dan tun da Hassan ya barwa Ruqayyah shi bata kuma taka kafarta zuwa cikinsa ba. Ta zauna akan kujera tare da aika Lami gidan ta ta dauko mata wayarta, hanyanza hawaye ne yake fita daga idonta, kuma har yanzu hannun ta yana rike rike dana Amir ta kasa sakinsa, Sumayya ta zauna a gefenta tana dauko tata wayar, a ranta tana lissafin wanda zata fara kira ta sanarwa da zuwan Amir. Duk da dai plans dinta bai tafi accordingly ba amma tayi achieving something, at least Amir yaga Ruqayyah da idonsa kuma tasan image dinta zai tsaya masa a rai, kuma yadda tayi masa kallon mai imani tana saka ran akwai tausayi a ransa, maybe wata rana ko ba yau ba zai iya yafe mata.

Wayar Hussain ta kira tana tunanin ko a ina suke yanzu? Ko suna jirgi a hanyarsu ta dawowa gida in sun samu Amir din baya nan. Sai taji ya dauka da sauri yana cewa "mommy yana ina? Ya karaso?" Tayi murmushi tace "gashi nan a hannun matarsa ta rike shi kam kam, ina jin ma sai yayi ciwon hannu yau" Hussain yayi dariya yace "Hajiya Aunty ko?" Tana jin sa yana magana da daddyn sa sai kuma yace "gamu nan, yanzu muka sauka a Kaduna, munje har gidansa aka ce mana ya taho kaduna, mun san nan ya taho shine muka juyo" ya fada muryar sa cike da excitement, tace "gashi nan fa, idan baku yi sauri ba Aunty sai ta lashe shi tas ta bar muku saura"

Ta ajiye wayar tana kallon Amir tana dariya, ta kasa karantar emotions dinsa dan shi kansa bai san menene emotion dinsa a lokacin ba, he was so furious sanda ya shigo gidan amma wannan dattijuwar, irin soyayyar da ya gani a idonta melted that anger and that hatred da ta cika zuciyarsa, matar kuma da aka gaya masa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login