Showing 201001 words to 204000 words out of 300844 words
son cin komai, bacci kawai nake so inyi"
Numfashin sa taji a fuskarta, tayi saurin jan fuskarta baya sai taji yayi dariya, sautinsa dai dai fuskarta amma ta kasa bude idonta sai da taji takunsa ya matsa sannan ta dan bude idon kadan sannan taga ashe babu komai a jikinsa sai dan karamim towel na kugu, tayi sauri ta mayar da idon ta rufe kirjinta yana lugude, bata taba ganin namiji a haka ba, ko a hoto ko a zahiri.
Wasu abs data gani a kafadun sa su suka saka yayan hanjinta suka kada, yana shiga toilet ta mike da sauri tana jin kifin duk ya fita daga kanta ta fice ta a hardewa kamar zata fadi. Dakinta ta shiga ta rufe kofa ta kashe fitila sannan ta zauna a kasa ta saka kanta a tsakanin cinyoyinta, nasihohin da akayi ta yi mata na hakkokin miji akan matarsa da kuma hakkokin mata akan mijinta.
Bata san tsahon lokacin da ta dauka a gurin ba, ga cikin ta yana kugin yinwa dan abincin rana bata samu ta ci ba tana asibiti gurin Ruqayyah. Kamar daga sama taji an bude kofar dakin sannan aka kunna fitila, ta sake rufe idonta, bata son ta kuma ganinsa babu kaya kamar dazu, sai taji kamshin turarensa sannan ta ji motsin sa ya zo gabanta sannan ta kuma jin hucin numfashin sa a fuskarta, ta sake rintse ido tana cije lebe, sai taji sautin murmushin sa.
"Shine kika gudu ko? Ba zaki ci abincin ba?" Ta gyada kai da sauri yace "to ki zo muyi sallah, ai dai ita sallah ba'a koshi da ita ko?" Bata ce komai ba sai ya hura mata iska a fiskarta, ta kara runtse idon, ya mike tsaye yace "ki bude idon ki, na saka kaya ai" ta bude a hankali sai taga ya saka jallabiya, ta danyi ajjiyar zuciya sannan ta tashi ta bishi suka koma dakinsa suka gabatar da sallar sunna ta ma'aurata, suka gabatar da adduoin samun dacewa a cikin zamantakewar su tare da neman zuri'a mai albarka sannan suka shafa.
Da kyar ya matsa mata ta ci abincin kadan ta sha lemo, duk da cewa shi kansa yasan bata koshi ba amma tsoro da fargaba sun hana ta ci, daga kwashe kayan abincin kuwa ta makale taki dawowa sai da ya bita ya kuma dawo da ita dakin yayi ta fama da ita akan ko hijab din jikinta ta cire amma taki, sai ta saka masa kuka. Ya sake ta ya hau kan gado ya kwanta tare da cewa "good night"
Da sauri ta fita daga dakin ta kuma shiga nata dakin tare da rufe kofa ta jingina da jikin kofar hawate suna bin idonta tana girgiza kanta. Wani bari na zuciyarta yana jaddada mata cewa ba zata iya ba wani barin kuma yana tuna mata da hukuncin laifin da take aikatawa. Tasan ba a son ransa ya kyale taba, kuma da yanayin da yayi maganar kamar wanda yayi fushi, sai ta tuna da abinda ta riga ta sani "duk matar da mijintaya kwana yana fushi da ita akan kin bashi hakkinsa da tayi to Mala'iku zasu kwana suna tsine mata" idan ta mutu a cikin daren nan kuma fa? Menene makomarta?
Sai ta juya ta fita, ta koma dakin nasa ta bude kofar ta tsaya a bakin kofa tana kallonsa hasken security light din daya shigo ta taga. Yana kwance ya lullube har kansa da abin rufa, amma tasan ba bacci yake yi ba kuma tasan yaji shigowar ta, sai ta tsaya a gurin bata ce komai ba, sai taga ya bude fuskar sa yana kallonta sai kuma ya bude abin rufar tasa sosai sannan ya miko mata hannu, ta tafi a hankali ta saka hannun ta a cikin nasa sai ya jawo ta kan gadon da hannu daya sannan ya cire hijab din jikinta da daya hannun, sai kuma ya saka hannayensa duk biyun ya rike fuskarta yana kallon cikin idonta a hankali yace "may I?" Ta rufe idonta tare da gyada kanta a hankali, and she felt his lips on hers together with some kind of feeling da bata taba jin irinsa ba a rayuwarta.
**********. ************. **************
Washegari da Hussain yazo neman mommyn sa Hassan cewa yayi mommy tayi tafiya sai next week zata dawo, haka ya zauna yaci amarcin sa son ransa su rayan duk sun dauka da gaske tafiyar tayi, sai da sati yayi sannan yaje ya dauko su yace mommy ta dawo, har da tsaraba ya raba musu yace inji ta, su kuwa sai murna. A ranar aunty ta hado musu kayansu gabaki daya suka dawo gidan iyayensu. A ranar ne kuma aka sallamo Ruqayyah daga asibiti ta dawo gidanta bayan gwaje gwaje da akayi mata a karshe likita yayi concluding "mentally unstable".
Ya rubuta mata magunguna kuma ya bata shawarwari sannan ya hada ta da therapist din da zata ke gani duk sati. Abubuwan da suke damunta sune rashin bacci, halucination, rashin abokin magana, damuwa da kuma shan sleeping pills din da take yi. Yayi suggesting therapist din ne saboda yana tunanin at least zata samu wanda zata ke yiwa magana tana fitar da abinda yake ranta tana rage damuwarta. Ya bata shawarwarin ta koma gida cikin yanuwanta sai tace masa ita bata da yanuwa duk sun mutu.
Sai kuma ya bata shawarar ta nemi abinyi, something to keep her busy yadda kullum in ta tashi she will be looking forward to doing something kuma kafin dare zsta gaji yadda zata fi saurin yin bacci. And she already decided on abinda zata yi, she is going to make money. In mutane ba zasu so ta ba dan Allah to zata siye su da kudi. Tana zuwa gida abinda ta fara yi shine neman number din Umar, yayan Fatima wanda suke partny a H and H sai ta gaya masa tana son shiga business din sosai, tana son ta zama involved a duk al'amuran kamfanin kuma tana son ribar da take samu da share dinta a daina turo mata gabaki daya, ake bata rabi rabin kuma ana sake re investing.
Bayan sun gama wayar ta bude kofar valcony tashiga tana kallon duk saura gidajen unguwar a kasanta dan duk unguwar babu gidan da ya kai na Hussain tsaho. Ta danyi murmushi tana lumshe idonta, hayaniyar da taji a barin gidan Hassan ya saka ta juya tana kallon side din, Hassan ta gani hannunsa rike dana Sumayya suna dariya, sannan ga yayanta suna zagaye su da ball a hannun Aminu, bata jin abinda suke cewa amma duk a cikin farin ciki suke.
Sai taga Hassan ya cire rigarsa ya bawa Sumayya riko sannan sun fita a guje shida yaran suna ball, Sumayya kuma tana kallon su tana cheering dinsu, duk wanda ya buga yaci zai je Sumayya tayi masa kiss, yaran sai rige rigen ci suke yi amma uban yafi zakewa har sai da yaci ya tafi da gudu gaban Sumayya ya durkusa yana dariya ita kuma tayi kissing dinsa a both cheeks.
Ta juya tana barin gurin, ta koma palo sannan ta saka key ta rufe kofar valcony din ta tafi toilet ta jefa key din a cikin toilet tayi flushing.
*Home Coming*
*Amira ta gode da adduoin ku, ni kuma na gode da fahimtar ku. Allah ya bar kauna ya kuma bar zumunci. Nagode sosai*
Washegari Ruqayyah ta fara ganin therapist din da aka hada ta dashi. Dr Mahmud. Shi yazo har gidan ta suka zauna a kasa, he talked to her, trying to get her to talk amma babu abinda tace masa mai amfani har awa dayan da yayi scheduling for her ta kare sai yayi mata sallama ya tafi.
Daga lokacin kuma ya cigaba da zuwa duk sati suna zama suna hirata awa daya,a lokacin ya fahimci abubuwa da yawa a tare da ita, na farko akwai abinda da take boyewa a ranta, abinda ba zata bata iya fadawa kowa ba kuma yana tunanin wannan abin shine sanadiyyar shigar ta halin da take ciki, na biyu tana halucination, ma'ana tana gani tana kuma jin abubuwan da basa guri a lokacin, sai dai bai sam yaushe ne ta fara gani da kuma jin haka ba.
Ya kuma fahimci tana da high spirit, a never giving up spirit wanda baya jin zata yi giving up akan abinda ta saka a gaban ta kuma a yanzu abinda ta saka a gabanta shine business, sai ya bata shawarwaro tare da kara mata karfin guiwa akan hakan, dan yana ganin hakan sai kara mata mental health dinta wanda a gurinsa shine top priority dan aikinsa kenan.
Ita kuma sai ta kara kaimi, ta sake neman Umar akan maganar da suka yi kuma ya nemi su hadu a cikin kamfanin sak ta shirya taje, with crutches and all, for the first time taji bata damu da kallon da mutane zasu yi mata ba cos tana da missing, ta san abinda take so and she is going to get it. So take ta saka duk wadanda suka guje ta su fahimci irin mistake din da suka yi sannan su dawo gareta.
Umar ya amince mata a game da harkar H and H, ya bata office dimda zata ke zuwa kullum ko kuma duk sanda tasamu dama, sannan kuma za'a ke briefing dinta na duk abinda yake faruwa a kamfanin. She accepted that, sannan ta karbi copy din duk takardun da suka shafi harkokin H and H ta tafi dasu gida, daga nan ta mayar da hankali sosai wajen karantawa da fahimtar duk yadda al'amurran kamfanin suke tafiya, and then she got enrolled in online business classes, giving it her all, and within a year sai gata ta san komai da yake shiga kuma yae fita daga H and H.
A shekara ta biyu sai ya kasance Sau dayawa ma Umar yana bar mata ragamar kafanin tacigaba da juyawa saboda shi yafi mayar da hankali akan sarauta da ita yake so, business kawai yana yi ne dan ya cika aljihun sa but not because yana da interest akai. Ita kuma ta cigaba da investing, sai ga kudi suna ta multiplying kamar an saka musu yeast. A yanzu har bata damuwa da kudin da take biyan mai duba dashi dan bashi da wani yawa a cikin kudin da take samu.
Yes, wannan ua taimaka mata sosai gurin rage mata damuwa da yawan tunani, amma har yanzu yaki ya yalwata mata zuciyarta, ga kudi dai har kudi tana samu, ga yalwataccen gida ga kuma yalwataccen account amma zuciyarta kullum a kuntace take jinta. Sai tayi tunanin kadai ci ne, dan haka ta gayyato all her friends, duk wanda take buƙatar gurin zama ta taho ta zauna, wasu ma daga gidan iyayensu suka fandare suka dawo gidan Ruqayyah da zama ita ce cinsu ita ce shansu ita ce komai nasu wai dan kawai tana so su cike wani rami da take ji a zuciyarta amma sai taji ramin yaki cika.
Sai kuma ta yi tunanin ko dan nakasar da take da ita ne, sai ta dukufa gurin ganin ta nemo likitan da zai taho daga kasar waje yazo har gidaya duba ta amma ta rasa, ta samu guda biyu sunzo baya ta kashe musu uba kudi amma sai da suka zo suka ganta sannan suka gaya mata ba zasu iya duba ta ba sai da kayan aiki, kayan aiki kuma suna can kasar waje ba zasu iya dauko su su taho dasu ba. Sai dai kawai suyi mata prescribing magani wanda har yau babu abinda yake kara mata.
Ita kuma har yau ta kasa taking risk din sake shiga jirgi balle tabi su can. And she misses fita kasashen duniya musamman ida kadaici yayi mata yawa kuma ta gakudi account dinta sai taji babu abinda take so irin ta keta hazo zuwa wata kasar kamar yadda Hussain yake yi a duk lokacin da yayi niyya.
A duk tsahon wannan shekaru ukun da auren Hassan, shekaru biyar da mutuwar Hussain, babu moment guda daya da Ruqayyah ta daina jin kikan jariri a kunnen ta, babu kuma lokacin data rufe idonta ba tare da taga fuskar Minal ba, duk kuwa da magungunan da take sha wadanda likitan ta yake ganin zasu taimaka mata but it is getting worst everyday. Sai ya zamanto zuciyarta ta kara bushewa ma yanzu bata jin tsoron abubuwan da take gani da ji.
Kullum tana sak ran Fatima zata dawo, tunda akwai chances na cewa she is alive duk da dai rashin ji daga gareta na tsahon shekaru biyar ya saka ta fara kwantar da hankalin ta da tunanin maybe ta mutu da gaske. Ita bacewar Fatima is a mystery agurin ta, dan ita har ga Allah sanda Fatima ta bata baby bayan ta haihu data ta bata bata ji alamar rai a tare da ita ba, wannan shi ya kara mata karfin guiwar yar da jaririn. Amma duk da haka ta yanke wani hukunci a ranta.
Duk ranar da Fatima ta dawo, that's in zata dawo din, zata tubure tace ita Fatima bata bata jariri ba, it will be her word against hers tunda babu shaida, babu wanda akayi a gabansa dan haka da wahala alkali yayi convicting dinta. Zargi ne kawai, mutane zasu zarge ta yan uwa zasu kara nisanta kansu da ita amma sai dai suyi tayi, ba zata yi asara goma da ashirin ba, ba zata taba furta abinda tayi ba ballantana ta rasa dukiya da kuma freedom dinta. Yes, wannan shine abinda zata yi.
Kanenta maza ne kawai suke kai mata ziyara sometimes, duk da cewa ta fahimci Inna Ade ne take turo su su duba lafiyar ta ba da sanin Baba ba. Tana jin dadin zuwansu sosai duk da bata nunawa amma tana jin dadin yadda taje jin labarin gida a gurinsu, ta fahimci kowa yana lafiya, sannan a gurin su ta ji labarin haihuwar Sumayya, amma duk da yadda suka so su jata ta shiga gidan taga baby sai taki zuwa. Bata jin akwai tsautsayin da zai kaita gidan Sumayya ballantana har taga abinda zai saka zuciyarta ta buga. Wanda ta riga ta gani ma is enough.
***************. ***************. ****************
Shekaru uku sun wuce bayan auren Hassan da Sumayya, rayuwa mai kyau suke shimfidawa abinsu tamkar basu da sauran wani problem a duniya. Sumayya ta gama karantar Hassan kuma ta taya yar uwarta bakin cikin rasa miji irin Hassan ta kuma yiwa kanta murnar samun miji irin Hassan. Hassan irin namijin nanne da in suka samu abinda suke so a gurin mace su kan iya zama tamkar bayi a gun matansu. Ta fahimci abinda yake so din kuma, na farko yana son respect, baya son raini ko kadan duk kuwa da cewa yana da wasa da dariya amma yana so a girmama shi, yana son other room sosai da sosai dan baya taba bari ya wuce shi indai ba da wani kwakwkwaran dalili ba, ita ma kuma sai ta fahimci ashe tana so din, dan haka sai suka kara makalewa da manne wa juna ta wannan bangaren.
Sai kuma ta fahimci baya son rainuwa kuma ya tsani mita, and she wondered yadda har suka iya rayuwar aure ta tsahon shekara biyu shida Ruqayyah dan ita a rayuwarta bata taba ganin mutum mai mita mai kuma rashin godiya ba irin Ruqayyah. Lallai Hassan ba karamin hakuri ne dashi ba, kuma tabbas ba karamin so yayi wa Ruqayyah ba.
Basu jima da aure ba aka yi posting din ta a service, aka tura ta bayelsa, amma haka Hassan ya shige mata gaba har sai da aka dawo da ita nan Kaduna musamman saboda a lokacin tana fama da laulayin ciki. Sai ta fahimci cewa shi din tsayayyen mutum ne irin wanda zaka iya gayawa problem dinka ya tsaya maka har sai kun samu solution. And she wondered yadda akayi Ruqayyah take kiran sa da matsolo. A gurin Sumayya sam Hassan bashi da maƙon kudi kawai dai baya son almubazzaranci, baya son unnecessary spendings, irin mutum ya sayi abu ba tare da yana bukatar saba, ko ka sayi abu kawai dan kaga wani ya siya kai ma sai ka siya dan ace kana da shi, amma kuma duk abinda yake da amfani Hassan zai siya in abundance, dan kayan abinci drinks fruits kala kalan nama har sai tace sunyi yawa kar su lalace. Musamman duk abinda ya fahimci cewa tana so ko kuma yaran suna so to ya ringa siyowa kenan. Kuma ta lura haka yake yiwa su Aunty ma, kafin su nemi abu ya kai musu shi indai yasan suna bukatar sa. Baya sai ya Aunty gwala-gwalai, baya chanja wa kannensa waya duk wata irin yadda Hussain yayi musu but yana kula da dukkanin bukatun su yana tsayawa a duk kanin al'amuran su kamar yadda ya tsaya a auren Nafisa bayan ya tabbatar yayi mata securing aikin da zata mori ilimin ta dashi, babu wanda zai ce marainiya ce dan Hassan ya cike gurbin uba a gurin ta kuma a yanzu yana kan cike wa a wajen Zulaihat dan ya matsa mata number akan ta fito da miji haka nan tunda har sun gama service dinsu.
A bangaren Hassan kuma bayan abinda ya faru tsakanin sa da Ruqayyah bai taba tsammanin zai samu farin ciki a rayuwar aure ba amma sai gashi ya samu more than abinda yayi tunani ma. Sumayya ta kawo haske sosai cikin rayuwarsa shi yasa ya makala mata suna "Noorie". A yanzu ne kuma ya gaskata maganar Baba, a yanxu ne kuma ya fahimci mistake dinsa na danganta wani category na mutane da munanan halayya.
Tabbas auren sa da Ruqayyah tamkar lesson ne ubangiji ya koya masa kuma ya dauki darasi sosai, sannan kuma aurensa da Sumayya shi kuma sakayya ce Allah yayi masa saboda yadda ya bude hannayensa duk biyun ya karbi kaddarorin rayuwarsa tare da gode Allah a bisa niimomin sa.
Gasu dai Sumayya da Ruqayyah tagwaye ne, uwa daya uba daya, ciki daya mahaifa daya, sun kuma sha nono daya a lokaci daya, sun rayu a guri daya, an yi musu tarbiyya iri daya sun kuma